Katsina24 Hausa

Katsina24 Hausa Wannan gidan Jarida mun buɗe shi ne domin kawo maku labaran gida dana waje.

Gwamna Aminu Bello Masari ya halarci (shaida) daurin Auren diyar Gwamna Muhammad Badaru Abubakar a garin Kano. An daura ...
24/11/2019

Gwamna Aminu Bello Masari ya halarci (shaida) daurin Auren diyar Gwamna Muhammad Badaru Abubakar a garin Kano.

An daura wannan aure a Masallacin Al-Furqan dake a cikin Nasarawa GRA, kuma Alhaji Dahiru Bara'u Mangal shi ya amshi auren UmmaHani Badaru Abubakar a madadin Ango Alhaji Mukhtar Abdullahi Dantunkura.

Limamin Masallacin Dr Bashir Aliyu Umar ya daura auren akan sadaki Naira Dubu Dari.

Daga cikin manyan bakin da s**a halarcin daurin auren sun hada da Gwamna Atiku Bagudu da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihohin Kebbi da Sokoto, akwai kuma tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido, tsohon Gwamnan Jihar Sokoto Alhaji Attahiru Dalhatu Ba farawa, tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Abdulaziz Yari da Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Dr Nasiru Yusuf Gawuna.

Gwamna Masari ya sami rakiyar Mai bashi Shawara kuma Shugaban Ma'aikatan Gidan Gwamnati Alhaji Muntari Lawal Katsina, Alhaji Salisu Iro Isansi, Alhaji Sani Aliyu Danlami da wasu mukarraban Gwamnatin Jiha.

A karshe kuma anyi addu'o'i na musamman ga ma'auratan da kuma kasa baki daya domin zaman lafiya da karuwar arziki.

24/11/2019
22/11/2019

CEO, ILM Tingilin Oil And Gas Nigeria Ltd

18 November 2019Gwamnan Jahar katsina. Rt. Hon. Aminu Bello Masari, Ya rantsar da kwamishinonin Jahar katsina, Guda Sha ...
18/11/2019

18 November 2019

Gwamnan Jahar katsina. Rt. Hon. Aminu Bello Masari, Ya rantsar da kwamishinonin Jahar katsina, Guda Sha Bakwai da Majalisar jaha ta Amince tare da tantance su, Ga sunayen su Nan da ma'aikatun su a kasa.

(1) Hon. Dr. Rabe Nasir ( Kimiya da fasaha) MINISTRY OF SCIENCE AND TECHNOLOGY.

(2) Hon. Faruk Lawal Jobe (Ma'aikatar kasafin kudi da cigaban tattalin arziki) MINISTRY FOR BUDGET AND ECONOMIC PLANNING.

(3) Hon. Muntari Kado Dutsinma (Ma'aikatar ciniki da masana'antu) MINISTRY OF COMMERCE, INDUSTRY AND TOURISM.

(4) Hon. Hamza Suleman Faskari (Ma'aikatar kulada Muhalli) MINISTRY OF ENVIROMENT.

(5) Hon. Abdullahi Imam (MINISTRY OF RESOURCES DEVELOPPEMENT

(6) Hon. Abdulkadir Zakkah (Ma'aikatar Ayyuka na musamman) MINISTRY OF SPECIAL DUTIES

(7) Hon. Tasiu Dahiru Dandagoro (Ma'aikatar Ayyuka da Gidaje) MINISTRY OF WORKS AND TRANSPORT.

(8) Hon. Prof. Badamasi Lawal Charanci (Ma'aikatar Ilmi) MINISTRY OF EDUCATION

(9) Hon. Mustapha Kanti Bello (Ma'aikatar kulada ma'adanai) MINISTRY OF MINE AND MINERAL RESOURSES.

(10) Hon. Musa Adamu Funtua (Ma'aikatar Ruwa) MINISTRY FOR WATER RESOURCES.

(11) Hon. Yau Umar Gwajo, Gwajo (Ma'aikatar kulada kananan hukumomi da masarautu) MINISTRY FOR LOCAL AND CHIEFTAINCY AFFIARS

(12) Hon. Usman Nadada (Ma'aikatar kasa da safiyo) MINISTRY OF LAND AND SURVEY.

(13) Hon. Kasim Mutallab (Ma'aikatar Kudi) MINISTRY OF FINANCE.

(14) Hon. Yakubu Nuhu Danja (Ma'aikatar lafiya) MINISTRY OF HEALTH

(15) Hon. Abdulkareem Yahaya (Ma'aikatar watsa labarai) MINISTRY OF INFORMATION.

(16) Hon. Sani Aliyu Danlami (Ma'aikatar Raya karkara, walwala da jin dadi) MINISTRY OF RURAL AND SOCIAL DEVELOPPEMENT.

(17) Haj. Rabiya M. Daura. (Ma'aikatar harkokin Mata) MINISTRY FOR WOMEN AFFIARS.

A daren jiya shugaba Buhari ya dawo gida Najeriya bayan kammala ziyarar daya kai a kasar Birtaniya.
16/11/2019

A daren jiya shugaba Buhari ya dawo gida Najeriya bayan kammala ziyarar daya kai a kasar Birtaniya.

Gwamnan jahar Katsina ya bada takardar shedar gina Federal Polytechnic Daura ga Shugaban Hukumar (NBTE)Da maracen jiya A...
15/11/2019

Gwamnan jahar Katsina ya bada takardar shedar gina Federal Polytechnic Daura ga Shugaban Hukumar (NBTE)

Da maracen jiya Alhamis 14 ga watan Nuwamba 2019, Gwamna Rt Hon, Aminu Bello Masari ya mika takardun shaidar mallakar filin gini na sabuwar makarantar Babbar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta kasa a garin Daura watau (Federal Polytechnic Daura), ga Shugaban Hukumar kula da Ilimin Kimiyya ta kasa Dokta Mas'ud A. Kazaure. National Board For Teachnical Education (NBTE).

Da yake gabatar da jawabinsa mai girma gwamna, yaja hankalin shugaban hukumar dasu samarma makarantar shuwagabanin da zasu iya tafiyar da wannan makaranta tsakaninsu da Allah. sannan ya kara da cewa gwamnatin jahar katsina zata bayar da gagarumar gudun muwa wajen tafiyar da cigaban wannan makaranta.

Shima a nasa jawabin shugaban hukumar, ya yaba da kuma jinjina ga mai girma gwamnan, inada ya bashi tabbacin, cewa zasuyi iyakar kokarinsu wajen samawa makarantar wanda zasu tafiyar da ita abisa adalci domin cigaban ilimi. yace ya zuwa yanzu sun samu sama da mutane 160 masu shaawar shiga makarantar. kuma suna saran daga nan zuwa farkon shekara mai kamawa za'a fara karatu a makarantar.

Daga cikin wanda s**a sheda bayar da takardun akwai mai girma sakataran gwamnatin jahar katsina Alhaji Dr, Mustapha Muhd Inuwa sai shugaban maaikata na gidan gwamnatin jaha Alhaji Muntari Lawal. Tsohon kakakin majalisar dokokin jahar katsina Alhaji yau umar gwajo gwajo, Sai wasu daga cikin hakimai daga masarautar daura , yan siyasa yan kasuwa dadai sauransu. Daga Gidan Gwamnatin jahar katsina.

Gwamnati Gwamnatin Masari ta sayi na’urar sa-ido domin sa ido kan ayyukan 'yan fashi a cikin garin Katsina. Gwamnati Gwa...
06/11/2019

Gwamnati Gwamnatin Masari ta sayi na’urar sa-ido domin sa ido kan ayyukan 'yan fashi a cikin garin Katsina.


Gwamnati Gwamna Masari ta sayi na’urar sa-ido domin sa ido kan ayyukan 'yan fashi a ci

Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da tura sabbin injunan sa ido na zamani wanda Darakta na Ma'aikatar Tsaro ta jihar, DSS, ke jagoranta don bin diddigin masu yin garkuwa da mutane tare da sa ido kan sayen makamai da amon makamai a wasu don dakile hare-hare a jihar.

Sakataren gwamnatin jihar kuma shugaban kwamitin tsaro, Dakta Mustapha Mohammed Inuwa wanda ya yi wannan bayanin ayauranar Talata a karamar hukumar Dan Musa da ke jihar yayin da yake sa ido kan rarraba kayan agaji ga 'yan gudun hijirar da wadanda ke fama da fashi da makami zuwa sansanoni 11. a karamar hukumar, ya ce Gwamnatin jihar ta shirye tsaf da sa kafa saya da 'yan fashi da ba su tuba ba don tabbatar da an dawo da zaman lafiya da tsaro baki daya.

Ya ce “Babban aikin da gwamnati ke yi shi ne zaman lafiya da tsaron mutane da dukiyoyinsu. Sauran abubuwan da Gwamnati ta sanya a gaba sun hada da, kiwon lafiya, ilimi, ababen more rayuwa, samar da ruwa da sauransu.

“Kafin lokacin da muka taru anan munyi hanzarin watsawa kafin dare yayi amma yanzu akwai 'yanci na mutane, nagartattu da aiyuka, godiya ga tattaunawar da akayi tsakanin Gwamnati da kungiyoyin' yan fashin an dawo dasu, an kuma dawo da rayukan jama'a cikin sauki. Manoma s**an tafi gonakinsu kyauta.


"Gwamnati ta tura kayan aikin dabarun kwata-kwata don ganowa da magance masu aikata laifi da 'yan fashi da ba su tuba ba, yanzu haka muna da bayanai kan ayyukansu da duk abin da ke faruwa kuma muna fatattakar duk wani abu da ka iya haifar da koma bayan' yan fashi."

SGS ta kara tunowa wani lamari inda aka kutsa kai wani sarkipin ta hanyar sa ido yayin da suke kokarin samar da makamai ta hanyar Jos, Babban birnin jihar Filato.

Tun da farko a cikin jawabin maraba da aka yi a wajen bikin, Shugaban mai barin gado na karamar Hukumar Dan Musa, Alhaji Abbas Sanusi Dangi ya ce, kayan agajin sun samo asali ne daga ragowar rabon da Hukumar bayar da Agajin gaggawa ta jihar, SEMA. , haɗe da waɗanda karamar hukumar s**a siya.

Abubuwan da aka raba kayan abinci sun hada da Rice, masara ta Guinea da masara mai tarin jaka 333 tare da kowace gunduma tana tattara jaka 33.

Al’umma ta tuno da cewa zaman lafiya da tsaro sun dawo jihar Katsina sakamakon yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin jihar ta yi da wasu ‘yan fashin da a baya s**a tayar da hankalin jihar.

ANYI KIRA GA MASU HANNU DA SHUNI DA SU DINGA TALLAFAMA MASU KARAMIN KARFI MABUKATAUwar Gidan Mataimakin Gwamnan Jihar Ka...
05/11/2019

ANYI KIRA GA MASU HANNU DA SHUNI DA SU DINGA TALLAFAMA MASU KARAMIN KARFI MABUKATA

Uwar Gidan Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Hajiya Mariya Mannir Yakubu tayi wannan kiran lokacin da takai ziyara a babbar Asibitin Funtua, Gidan Yari da Gidan Marayu na Shiyyar Funtua.

Hajiya Mariya Mannir Yakubu ta ziyarci dakunan jinya na mata da maza, dakin haihuwa da dakin yara da wasu wuraren a asibitin funtua.

Hajiya mariya ta bayyana qudirin ziyarar da niyyar gaisuwa ga yan'uwa mabukata da tallafamasu da kayan masarufi da kudi cikin aljihun ta.

Kayan tallafin da ta rarraba ga mabukata asibitin sun hada da kayan abinci, sabullai, omo, da kudi ga dukkan mutanen da ta ziyarta a asibitin funtua da gidan yari da gidan marayun shiyyar funtua.

Bayan tattaunawa da wadanda ta kaima ziyarar Uwar gidan mataimakin gwamnan ta tausaya ma wadanda ta ziyarta matuka tun daga asibiti zuwa gidan yari zuwa gidan marayu.

Ta kara jaddada kira ga masu iko da su dinga tausayama mabukata musamman wadanda suke a asibitoci da wadanda ke gidajen marayu da wadanda suke kulle agidajen yari.

Aziyarar gidan yarin funtua Hajiya mariya mannir yakubu ta samu tarba daga shugaban ma'aikatan gidan yarin na shiyyar funtua Alh Jafaru Ahmad da sauran ma'aikatan shi.

A ziyarar gian marayu hajiya mariya ta samu tarba daga shugaban ma'aikatar jin dadi da walwalar al'umma da ma'aikatan shi

Bayan bada tallafin kayan masarufi da kudi a gidan marayu ta bada gudummuwar kudi na musamman don karawa cikin hidimar biki ga yara biyu da za'a auras.

Hajiya mariya mannir yalubu ta dauki nauyin karatun yara goma marayu biyar har su kammala primary school da biyar har su kammala secondary school.

A gidan yari sunyi roko ta gyara masu masallacin su sunyi rokon ta saya masu injin din bada hasken lantarki (generator) ta bada umurnin akai masu injin din bada hasken lantarki gobe masallacin kuma ta bada damar aduba bikatun masallacin.

Hajiya mariya mannir yakubu ta bada damar a nemo gidan haya mai kyau zata dinga biya ga wata ma'aikaciyar gidan mai renon marayu a gidan wadda ta reni marayu kimanin 70 daga sadda ta fara aiki kawo yanzun.

Uwar gidan mataimakin gwamnan tayi addu'o'in neman sauki ga marassa lafiyar da ta ziyarta a asibiti da wadanda ke gidan marayu da wadanke ke gidan yari da sairan al'ummar jihar katsina da najeriya baki daya.

Jihohi Goma Da S**a Fi Talauci A Nijeriya A Shekarar 2019 Daga Comr Abba Sani PantamiHukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta ...
05/11/2019

Jihohi Goma Da S**a Fi Talauci A Nijeriya A Shekarar 2019

Daga Comr Abba Sani Pantami

Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta yi amfani da wasu abubuwa a matsayin mizanin auna yawan talauci a jihohin Najeriya, inda ta fitar da jerin jihohi da kuma matakin da suke kai a yawan talauci.

Yawancin jihohin Najeriya na fama da talauci ne saboda rashin shugabanci nagari, almundahana da almuubazzaranci da dukiyar gwamnati da sauransu.

Jerin jihohi guda 10 da talauci ya fi yawa a sune kamar haka;

1. Sokoto

An bayyana jihar Sokoto a matsayin jihar da tafi kowacce talauci a Najeriya, inda take da kaso 81.2% a sikelin auna talauci. Ana ganin cewa yanayin marar dadi yana hana bakin haure da masu saka hannun jari zuwa jihar Sokoto.

2. Kastina

Katsina jiha ce da ke kuryar yankin arewa maso yamma na Najeriya, kuma ta fada cikin jerin malautan jihohi saboda rashin wasu masana'antu ko bangarori da zasu samar wa da jihar kudin shiga.

3. Adamawa

Tattalin arzikin jihar Adamawa, kamar na wasu jihohin yankin arewa maso gabas, ya samu nakasu sakamakon yawaitar hare-haren mayakan kungiyar Boko Haram, lamarin da yasa jama'a da dama ke nesanta kansu daga jihar saboda dalilan tsaro.

Hakan yasa jihar ta samu kaso 74.2% a sikelin auna talauci.

4. Gombe

Kusan matsalar jihar Gombe iri daya ce data jihar Adamawa da sauran wasu jihohin yankin arewa maso gabas.

Jihar Gombe ta samu kaso 73.2% a mizanin auna talauci.

5. Jigawa

Jihar Jigawa tana da kaso 72.1% a sikelin auna talauci a jihohin Najeriya.

Ana alakanta talaucin da jihar Jigawa ke fama da shi da rashin ilimi na mafi yawan jama'ar jihar da kuma rashin bunkasar tattalin arziki.

6. Plateau

Duk da kasancewarta jiha mai wuraren ban sha'awa da ke jan hankalin masu yawon bude ido, yawan rikicin kabilanci ya durkusar da tattalin arzikinta, lamarin da yasa ta samu kaso 71% a sikelin auna talauci.

7. Ebonyi

Ebonyi ce kadai jihar yankin kudu maso gabas da ta fada sahun matalautan jihohi a Najeriya. Tana da kaso 70.6% a sikelin auna talauci.

An alakanta talaucin jihar da karancin masu ilimi da kuma gwamnati marar kyau.

8. Bauchi

Hukumar NBS ta saka Bauchi a cikin jerin jihohin Najeriya matalauta.

Kididdiga ta nuna cewa mafi yawan jama'ar jihar basu da abubuwan more rayuwa sannan yakin Boko Haram ya shafi jihar.

9. Kebbi

Jihar Kebbi na da kaso 72% a sikelin auna talauci a tsakanin jihohin Najeriya.

10. Zamfara

Hukumar NBS ta saka jihar Zamfara cikin jerin jihohi matalauta na shekarar 2019, saboda tana da kaso 70.8 a sikelin auna talauci.

Buhari ya tsayar da ranar bude iyakokin Najeriya Daga Comr Abba Sani PantamiShugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince d...
04/11/2019

Buhari ya tsayar da ranar bude iyakokin Najeriya

Daga Comr Abba Sani Pantami

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da kara tsayin wa'adin atisayen da aka yi wa lakabi da 'Exercise Swift Response' wanda ya jawo aka rufe iyakokin Najeriya na kasa da makwabatan kasashe.

An rufe iyakokin Najeriya ne tun ranar 20 ga watan Agusta, kuma ana saka ran bude iyakokin a ranar 31 ga watan Janairu, sabanin tsammanin da wasu ke yi na cewa za a bude iyakokin kafin lokacin bikin Kirsimeti domin 'yan kasuwa a yankin kasashen Afrika ta yamma su samu su sarara.

A cikin wata sanar wa mai lamba kamar haka: NCS/ENF/ABJ/221/S.45 mai dauke da sa hannun Victor David Dimka, shugaban sashen tilasta biyayya ga dokokoki a hukumar Kwastam, ya ce sun samu takardar neman su yi biyayya ga umarnin dakatar da atisayen daga ranar 31 ga watan Janairu.

An fitar da takardar sanarwar ne ranar 1 ga watan Nuwamba, 2019.

Matemakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo Ya Halarci nadin Sarautan Danmadamin Daura Fassara Hon Buhari Sallau Hadimin Shuga...
03/11/2019

Matemakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo Ya Halarci nadin Sarautan Danmadamin Daura

Fassara Hon Buhari Sallau Hadimin Shugaban kasa a bangaren gidajen Rediyo da Talabijin

Matemakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, "Yau Asabar ya Halarci nadin Sarautan Danmadamin Daura, wanda aka gudanar a garin Daura dake jihar Katsina Yau asabar biyu ga watan sha dayan shekarar 2019...
2nd Nov 2019.
Photos; Tolani Alli

Gwamnan jihar Katsina tare da wasu sauran jiga-jigan Gwamnatin jihar sun halarci bikin bude wani katafaren wurin cigaba ...
02/11/2019

Gwamnan jihar Katsina tare da wasu sauran jiga-jigan Gwamnatin jihar sun halarci bikin bude wani katafaren wurin cigaba na Hayatt Regency Suites

Amadadin Hon Danlami Kurfi Na miqa sakon Godia ga Gwamnatin Jahar Katsina Karkashin jagorancin Rt. Hon Aminu Bello Masari (Dallatun Katsina, matawallen Hausa) da Sauran Daukacin Al'ummar da s**a halarci bikin bude katafaren Wajen Daya bude ranar Juma'a.

Wannan Waje anbude shine Domin Ayyukan yau da kullum wanda s**a hada da Wajen cin abinci, wajen kwana, Dakin taro da wajejen shakatawa Da sauransu, kuma an tabbatar duka ma'aikatan wajen yan asalin jahar katsina ne masu bukatar a daukesu aiki.

Governor Masari yaji jawabin Godia kan yadda wannan Bawan Allah yake kokarin yaga har gobe ya Gina Al'umma da kawoma katsina cigaba a koda yaushe wanda Daman Halayyarsa ce haka.

Hon. Danlami Kurfi ya nuna jin dadinsa matukar Gaske kuma yayi Godia ga mutanan da s**a halarci wannan Biki dama wanda basu samu Damar zuwa ba, Allah SWT cikin Amincinsa ya mayar da kowa Gidan sa Lapia Ameen.

Majiya Katsina Post.

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!Jaridar Katsina24 mai yada labaranta a shafin sada zumunta na Internet, na farin cikin sana...
02/11/2019

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!

Jaridar Katsina24 mai yada labaranta a shafin sada zumunta na Internet, na farin cikin sanar daku cewa, ta bude shafin Hausa, mai suna Katsina24 Hausa.

Da fatan za kuyi like wannan sabon shafi wanda muka kaddamar a yau ranar 2 ga watan Nuwamba, Alub 2019 dai dai da 4 ga watan 3 Hijira ta 1441 da misalin karfe 7:02:50 da minti biyu da dakika 50 Agogon Najeriya, Nijer, Kamaru, da Chadi, wato karfe 6:02:50 da minti biyu da dakika 50 kenan Agogon GMT da Ghana.

Address

No: 57, Shema Central Market Malumfashi
Malumfashi
832103

Telephone

+2349076968454

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Katsina24 Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share


Other Media/News Companies in Malumfashi

Show All

You may also like