30/08/2023
Babu wanda ya isa ya kori Kwankwaso daga NNPP - Buba
Galadima Wani tsagin na jam'iyyar NNPP mai mubaya'a ga Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya sanar da korar ƴan kwamitin amintattun da s**a dakatar da jagoran jam'iyyar.
Ɗaya daga cikin jigo a jam'iyyar da ke biyayya ga Kwankwaso, Injiniya Buba Galadima ya shaida wa BBC cewa sun ɗauki matakin ne a wani taro da s**a gudanar a Abuja a wani yunkurin na fasalta al'amuran jam'iyyar.
Wannan mataki na zuwa ne bayan a ranar Talata an samu labarin da ke cewa NNPP ta dakatar da Kwankwaso kan zargin yi wa jam'iyyar zangon-kasa.
Sai dai Injiniya Galadima ya ce sun yi mamakin jin labarin dakatar da Kwankwaso saboda su ne kwamitin amintattun, kuma ba su san da zaman ressan jam'iyyar da ke cewa sun dakatar da Kwankwaso ba.
Ya ce akwai lokacin da s**a kaddamar da kwamitin bincike kan waɗanda s**a aikata laifuka a jam'iyyar kuma shi a iyakar saninsa babu Kwankwaso a ciki.
Duk da, a cewar Buba Galadima, Kwankwaso bai fi karfin bincike ba idan akwai zargi a kansa.
Sannan Buba Galadima ya ce su wadanda s**a yi sanarwar dakatar da Kwankwaso sun yi hakan ne bayan samun labarin za a kore su daga jam'iyyar.
Kuma ya shaida cewa babu wani lokaci da Kwankwaso ya gana da ɓangaren APC ko shugaban kasa ba tare da ya tattaunawa da uwar jami'iyyar ta NNPP ba.
Wasu jam'iyyu ne ke son ganin bayanmu'
Da yake musanta zargin da ake yi wa Rabi'u Kwankwaso, Buba Galadima ya ce jagoran na NNPP ya tuntuɓi jam'iyyar kafin ya yi ganawa da Shugaba Tinubu.
Ya yi iƙirarin cewa Shugaba Tinubu ne ya yi ta ƙoƙarin ganawa da Kwankwaso a karo da dama, amma abin bai yi nasara sai a karon farko da s**a yi ganawa a birnin Paris.
Ya ce ko da yake Mista Boniface Aniebonam na cikin mutanen da s**a kafa NNPP amma kusan gaba ɗaya a durƙushe take kafin shigarsu cikinta gabanin zaɓen 2023.
Ya zargi wasu jam'iyyun siyasa na Najeriya cewa su ne suke kitsa wutar rikici a NNPP saboda a cewarsa sun ga ba za su yi nasara ba sai murƙushe jam'iyyar wadda ta tsokane musu idanu.
Buba Galadima ya yi iƙirarin cewa suna sane da ɗumbin ƙulle-ƙullen da ake yi wa ɗan takarar nasu da kuma jam'iyyar a ƙarƙashin ƙasa.
Me ɓangaren Lagos ya ce?
"Kwamitin amintattun (na Boniface Aniebonam) ya tabbatar da naɗin sabbin shugabannin NNPP na ƙasa, inda Dr. Agbo Major zai kasance shugaban jam'iyyar na riƙo, sai Kwamared Ogini Olaposi, matsayin sakataren NNPP na ƙasa da kuma sauran jami'ai kimanin 18."
Kafofin yaɗa labarai sun ambato Boniface Aniebonam wanda shi ne shugaban kwamitin amintattun NNPP a cikin sanarwar bayan taron da s**a fitar a Lagos yana ayyana kwamitin zartarwar jam'iyyar na ƙasa da "maras ƙwarewa.
Kuma saboda turka-turka da gazawar mambobin kwamitin na tabbatar da aiki da tsarin mulki da bin ƙa'ida wajen cike guraben da ke akwai, sun tabbatar ba zai iya ci gaba da aikin da aka ɗora masa alhaki ba, kuma ba shi da wani amfani a idon doka".
Ƙungiyar ta kuma gargaɗi Buba Galadima ya daina gabatar da kansa a matsayin sakataren kwamitin amintattu na NNPP.
A cewarta yin hakan ya saɓa wa tsarin da ya fayyace ƙunshin mambobin kwamitin bisa tanadin tsarin mulkin jam'iyyar.
Sanarwar bayan taron na Lagos ta kuma ambato Boniface Aniebonam na bayyana sauka daga matsayin shugaban kwamitin amintattu, kuma nan take taron ya zaɓi Tope Aluko matsayin wanda zai maye gurbin sa, sai kuma Babayo Abdullahi a matsayin sabon sakataren kwamitin amintattun.
Ɓangaren Abuja ya tabbatar da korar Aniebonam
Sai dai, ɓangaren Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya gudanar da taron kwamitin zartarwa a Abuja ranar Talata inda ya tabbatar da korar Aniebonam da Agbo Major daga NNPP.
Ɓangaren na Abuja ya kuma ayyana matakin da ɓangaren Lagos da cewa "haramtaccen abu ne da ba ya kan doka don haka ba shi da wani tasiri".
Taron na Abuja ya kuma gabatar da wasu ƙudurori da yawa masu alaƙa da tambarin jam'iyyar da gyaran tsarin mulki da tabbatar da kwamitocin riƙon ƙwarya na jihohi da dakatar da shaɗarori guda biyu na tsarin mulkin NNPP na shekara ta 2022.
Mallam Buba Galadima dai ya ce taron ɓangarensu na Abuja dai ya samu halartar shugabannin riƙo na jihohi daga faɗin Najeriya
•
✍️ Young Ameeyr
Hausa