Labarai daga tushe

Labarai daga tushe shafin labarai daga tushe shafi ne Wanda ya kuduri aniyar lada labarai na gaskiya bisa dogaro da hujja mai karfi

Barkan ku da Asuba Ga takaitantun labarai wanda Jaridun najeriya s**a buga a wannan safiyar ta lahadi.An kashe mutane da...
27/08/2023

Barkan ku da Asuba
Ga takaitantun labarai wanda Jaridun najeriya s**a buga a wannan safiyar ta lahadi.

An kashe mutane da dama a hare-haren da aka kai a kauyen Chito da ke karamar hukumar Ukum a jihar Benue. Shaidu sun ce sabon kashe-kashen ya faru ne a yankin da aka kashe akalla mutane biyar a kwanakin baya

Ga cikankun labaran a kasa

Tasa wirar Nijeriya 1.Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Asabar din da ta gabata ya bayyana cewa babu wata kas...

Kwamitin aiki na kasa (NWC) na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a karkashin jagorancin Abdullahi Ganduje, shuga...
26/08/2023

Kwamitin aiki na kasa (NWC) na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a karkashin jagorancin Abdullahi Ganduje, shugaban jam’iyyar na kasa, ya rantsar da nasa bangaren wanda zasu maye kujerun jihar a matakin kasa jihar Kogi.

Adaidai lakacin da Gwamnan jihar Kogi ya nuna rashin Amincewar sa ga wanda aka nada daga jihar kogin.

Ga cikanken rahoton a kasa

Anyi zanga-zangar, a karshe APC ta rantsar da sabbin mambobin NWC, ta yi alkawarin bayar da tukuicin ga wasu. Kwamitin ayyuka ...

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta karyata ikirarin cewa wasu kasashen waje ne ke rike da...
26/08/2023

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta karyata ikirarin cewa wasu kasashen waje ne ke rike da kungiyar yankin domin kai wa Jamhuriyar Nijar hari. Omar Alieu Touray, Shugaban Hukumar ECOWAS ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin da yake magana da manema labarai a Abuja.

Kadan kenan daga cikin manyan labaran da manyan jaridun Najeriya s**a buga a safiyar yau Asabar.

Ga cikanken labaran a kasa

1.Rundunar sojan Nijar ta kori jakadan Faransa Sylvain Itte daga kasar. A cikin wata sanarwa a ranar Juma'a, ma'aikatar harko...

Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Afirka ta Yamma (Ecowas) ta yi  da zarge-zargen cewa wasu ne daga ƙasashen waje ke ingiza...
25/08/2023

Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Afirka ta Yamma (Ecowas) ta yi da zarge-zargen cewa wasu ne daga ƙasashen waje ke ingiza ta a kan lallai sai tilasta wa sojojin Nijar, mayar da ƙasar kan tafarkin tsarin mulki.

Ga cikanken rahoton a kasa

Ba mu da niyyar ruguza Nijar - Ecowas Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Afirka ta Yamma (Ecowas) ta yi da zarge-zargen cewa wasu n...

An kashe alkaliya jar lahira Lamarin dai na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke hasashen hukuncin kotun zaben s...
25/08/2023

An kashe alkaliya jar lahira Lamarin dai na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke hasashen hukuncin kotun zaben shugaban kasa.

Ga cikanken rahoton a kasa.

Rahotanni sun bayyana cewa an kashe tsohuwar shugabar kotun daukaka kara ta gargajiya ta jihar Benue, Misis Margaret Igbeta a g...

01/08/2023

Da dumi-dumi: Mu yi watsi da labaran karya, ba mu da dalilin dakatar da zanga-zangar – NLC

ZANGA-ZANGA BA MAFITA BACEBANA GOYON BAYAN TA. Daga Sani salisu Darma Bana goyon bayan zanga zangar da yajin aikin da ku...
01/08/2023

ZANGA-ZANGA

BA MAFITA BACE

BANA GOYON BAYAN TA.

Daga Sani salisu Darma

Bana goyon bayan zanga zangar da yajin aikin da kungiyoyin kwadago zasuyi Gobe a Nigeria, babu abinda zai canza saima kara jifa alumma cikin wani mugun hali.

Akwai hanyoyi guda biyu Wanda ya k**ata muyi amfani dasu domin ganin mun fita daga wanna halin da muka samu kan mu a ciki.

1. Wajibi ne kowa ya zauna ya yiwa kan sa hisabi shin daidai yake aikatawa a rayuwar sa ta kowace fuska,

Shin kana tausayawa dan uwan ka a saye da sayarwar ka ?

Yaya tsakanin ka yake da Allah ?

Shin kana bin dokokin sa ko shalhuliyarka kake kuma kake mafarkin ka samu kyankyawar rayuwa?

Wanna shine matakin farko kuma wajibi ne kowa ya gyara kuskuren sa kafin ya kalli na shugabanin sa.

2.mataki na biyu shine adua ko musulmi ko kirista Sun yadda da adua wajibi ne adaidai wannan lokacin mu rumgumi adua, mafita mu tana wajen Allah duk wanda zamu k**a muce shine zai fitar damu mun k**a kafar wala mun tafi bulayi.

Mu sani Allah bazai kalle mu ba koda munyi adua mutakar bamu gyara halayen mu ba k**ar yadda na fada a matakin farko.

Zanga zanga ba mafita bace mafitar mu tana hannun mu tana hannun Allah.

Rubutawa:
Sani Salisu Darma
1/8/2023

Wata sabuwa:Gwamnatin jihar Kano ta sanya hoton tsohon sarkin Kano sunusi lamido sunusi a cikin babban Dakin taron gida....
30/07/2023

Wata sabuwa:

Gwamnatin jihar Kano ta sanya hoton tsohon sarkin Kano sunusi lamido sunusi a cikin babban Dakin taron gida.

Ko menene ke shirin faruwa?

Abubuwan da ya k**ata ku sani akan sabon shugaban Jam'iyar APC
30/07/2023

Abubuwan da ya k**ata ku sani akan sabon shugaban Jam'iyar APC

Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR. NCE: Takardun Ilimin Najeriya 1972 – Advanced Teachers College, Kano. BSc.Ed: Bachelor a Kimiyyar Kimiyya : 1975 – Jami’ar Ahmadu Bello Zaria, Nige…

22/07/2023
Gwamnan Kano: INEC ta rufe shari’ar ba tare da kiran wani shaida ba Minti 54 da s**a wuce Labaran Zamani A ranar Alhamis...
20/07/2023

Gwamnan Kano: INEC ta rufe shari’ar ba tare da kiran wani shaida ba
Minti 54 da s**a wuce
Labaran Zamani

A ranar Alhamis din da ta gabata ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta rufe karar da ta shigar kan jam’iyyar APC ba tare da gabatar da wani shaida a kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar Kano ba.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa jam'iyyar APC mai shigar da kara na kalubalantar INEC kan ayyana Abba Yusuf na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.

Mai shigar da karar ya kuma bukaci kotun da ta bayyana cewa jam’iyyar NNPP ba ta da dan takara domin Kabir-Yusuf baya cikin rajistar masu zabe da s**a mika wa INEC a lokacin zabe.

Wadanda s**a amsa sun hada da INEC, Yusuf da kuma New Nigeria Peoples Party (NNPP).

A lokacin da ake ci gaba da sauraren karar, Lauyan Hukumar INEC, Emmanuel Oshayomi, ya shaida wa kotun cewa bayan ta yi nazari sosai kan karar da aka shigar, INEC ta yanke shawarar kada ta kira wani shaida.

“Bayan tuntubar shugaban tawagarmu kan rashin samun shaidarmu. Mun yi nazari kan karar da masu shigar da kara s**a kasa nuna cewa INEC ba ta gudanar da zaben ba bisa ka’idar zaben 2022.

"Muna cikin tawali'u muna neman a rufe karar," in ji Oshayomi
Lauyan Yusuf, R A Lawal SAN da Lauyan NNPP, John Olusola SAN, ba su ki yarda ba.

Tun da farko dai, Lauyan wanda ya shigar da kara, Offiong Offiong SAN, a ranar 15 ga watan Yuli, ya rufe karar su da shaidu 32 a gaban kotun.

"Shaidu sun hada da wakilan jam'iyyar, tauraruwar shaida da kuma shaida"
Kwamitin mutane uku karkashin jagorancin mai shari’a Oluyemi Akintan-Osadebay ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 21 ga watan Yuli, domin wanda ake kara na biyu ya bude nasu kare.(NAN)

Umbrella Of Kano Concerned Civic Society Groups.A Binciki Barr Muhuyi Magaji Rimingado. Sun Turawa Kwamitti Karbe Mulki ...
05/07/2023

Umbrella Of Kano Concerned Civic Society Groups.

A Binciki Barr Muhuyi Magaji Rimingado.

Sun Turawa Kwamitti Karbe Mulki Sakon Tuhuma Tare da Bincike Akan Barr Muhuyi Magaji Rimingado Bisa wasu Zarge Zarge na Almundahana da Kudaden Al'umma.

1. Kungiyar ta Zargi Muhuyi da Karbar Zunzurtun Kudi daga hannanun Gwamnati a Shekarar 2019 Naira Million 7 da dari bakwai da hamshin da shida Akan siyan akwatuna da ake sawa a Ma'aikatu Domin bada Shawara, (Public Suggestion Box). An bada kudi Sannan Ba'a Siyo waddanan Akwatina ba.

2. 36.960.0000 aka sakarwa Hukumar korafe korafe ta jahar Kano domin Gabatar da Saminer ga zababun Chairmomi na jahar Kano. Kudin an fitar dashi ta Ministry for local Government. Kuma a Karshe Baayi wannan saminer ba.

3. Barr Ya Naimi Gwamnati Ta bashi Naira Million 37.800.000.00 domin ya Gudanar da Training wa Ma'aikatan sa bayan da aka bashi kudi daga office din Accountant General Amma baiyi wannan Training ga Ma'aikatan sa ba.

4. Muhuyi dai ya karbi 60.500.00 (USD) wanda Isa pilot ya kawowa Muhuyi akan Case din Gandun Sarki dake Dorayi amma Muhuyi bai sa wannan kudade a Account na hukumar ba. Kuma bai ajiye a matsayin Hujja akan wanda ake kara ba.

Ana Zargi Muhuyi da Karbo Kudi Naira Million 185 akan Case din Ado Bayero Royal Estate Sannan ya turawa Kano Emirates Council Naira Million 50 kawai. Ina Sauran 135 Million???.

Wannan Kungiyar ta roki Gwamnati Kano data Binciki Muhuyi akan waddanan Zarge Zarge da akeyi masa.

Congratulations Dr. Abdullahi Umar Ganduje 💪
02/07/2023

Congratulations Dr. Abdullahi Umar Ganduje 💪

Ana zaton wuta a makera :Shugaban hukumar karbar korafe korafe na jihar kano muhiyi Magaji rimin Gado,Shima ya karbi kya...
24/06/2023

Ana zaton wuta a makera :

Shugaban hukumar karbar korafe korafe na jihar kano muhiyi Magaji rimin Gado,
Shima ya karbi kyautar fili daga Hannun Tsohon Gwamnan kano Abdullahi umar Ganduje.

22/06/2023

24/6/2023

Save the day

A kano ba siyasa i hasssada  kawai ake Allah ya kyauta.Mutum ya saka kudin  ya biya kudin  aikin  haji Duk wata ka'ida K...
21/06/2023

A kano ba siyasa i hasssada kawai ake Allah ya kyauta.

Mutum ya saka kudin ya biya kudin aikin haji Duk wata ka'ida Kwamanda Ya cika ta

Saboda kwai yana hamayya da gwamnatin Abba Ku hanashi viza

Wannan zalumci ne

AA ZAURA /HANGA...A jiya  20/6/2023 a  kotu.....A jiya 20/6/2023,kotun Shari'ar zaben kujerar Sanatan Kano ta tsakiya  t...
21/06/2023

AA ZAURA /HANGA...

A jiya 20/6/2023 a kotu.....

A jiya 20/6/2023,kotun Shari'ar zaben kujerar Sanatan Kano ta tsakiya ta zauna an cigaba da sharia tsakanin Sanata Rufai sani hanga na Jam'iyar NNPP da kuma AA ZAURA na Jam'iyar APC ga abinda ya faru.

Alkali :ya tambayi lawyer Rufa,i sani hanga Ina takaddun da akayi dashi zai kawo yau..

Lawyer Rufa,i sani hanga cikin dimuwa yakasa gabatar da takaddun da yayi alkawari zai kawa a wacan zaman,

Shine dalilin dayasa aka bashi kwana 10 domin gabatar da shedar takardun fidda gwani wacce jamiyya NNPP tayi zaban fidda gwani ranar 8 September 2022 ...

Rashin hujja yasashi fucewa daga kotu baki daya ....

ALKALI...duba da tsawan lokacin da aka dauka kotu ta Kara saka ranar 24 July 2023 domin yin hukunci na kusan karshe .......

AA ZAURA IS coming..........

A KULA:

Shi hukunci kotu duk abinda ake chajinka dashi sai anyi hukunci akansa daya bayan daya dole sai alkali ya tsife Aya da tsakuwa yake hukunci dalili idan mutum yaga baayi Masa adalci ba saiya daukaka Kara ..

Sunayen guraren da gwamnatin Abba zata kuma rusawa a kano.
20/06/2023

Sunayen guraren da gwamnatin Abba zata kuma rusawa a kano.

19/06/2023

Kujerar Dan majalisa mai wakiltar kumbotso
Jam'iyar APC zata karbe a KOTU
Ku rubuta Ku ajiye

16/06/2023

Allah shi kadai yasan mutanen da rusau din nan ya jefa a masifa.
Adua itace maganin maganin masifa

Kotun ta tsayar da Ranar 20 ga watan yuni ranar karshen Amincewa da Jawabin  Akan karar Hanga/Zaura Kotun sauraren karar...
09/06/2023

Kotun ta tsayar da Ranar 20 ga watan yuni ranar karshen Amincewa da Jawabin Akan karar Hanga/Zaura

Kotun sauraren kararrakin zabe ta jihar kano da ke zamanta a Kano ta tsayar da ranar 20 ga watan Yuni, 2023 don amincewa da rubutaccen jawabi na karshe a cikin karar da Abdussalam Abdulkarim Zaura na APC ya shigar, yana kalubalantar nasarar da kuma ayyana Rufa'i Sani Hanga a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar Sanatan Kano.

Mai shigar da kara, A.A Zaura yana rokon kotun da ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben tare da dawo Sanata Rufa’i Sani Hanga a matsayin wanda ya lashe kujerar Sanatan Kano ta tsakiya.

An bai wa wadanda ake kara wa’adin kwanaki bakwai kowannensu su fara gabatar da bayanai yayin da aka baiwa wanda ake kara kwanaki 3 ya gabatar da amsarsa da kuma karin kwanaki 3 ga wadanda aka kara da su gabatar da amsa a cikin doka.

Kotun ta umurci Lauyan Rufa’i Sani Hanga, Barista Ikpe da ya gabatar da Takaddun Shaidar Gaskiya na dukkan takardun da ya jera a cikin martanin da ya bayar.

Wasu daga cikin takardun da aka jera sun hada da rajistar masu kada kuri’a, rahoton zaben fidda gwani na jam’iyyar NNPP da aka gudanar a ranar 8 ga Satumba, 2022 da dai sauransu.

Sai dai Sanata Hanga ya bayar da shaida a gaban kotun domin kare nasarar da ya samu.

Karkashin tsattsauran ra’ayi, wanda ake kara na 2 ya shaida cewa babu sunansa a cikin rajistar ‘yan takarar da INEC ta wallafa.

Sanata Hanga ya kuma shaida cewar ba zai iya tuna adadin da ke cikin katin zama dan jam’iyyar NNPP ba.

A karkashin tsattsauran ra’ayi, Hanga ya ci gaba da cewa shi ba jam’iyya ba ne a cikin takardar karar da NNPP daga babbar kotun tarayya ta Kano zuwa kotun koli.

Yayin da kotun ta koma jiya domin ci gaba da kare shari’a, Sanata Hanga da NNPP sun rufe karar ta hannun wakilinsu na lauya Barista Meshak Ikpe.

Haka kuma Justice Watch News ta lura cewa masu amsa na 1 da na 4, INEC da Mallam Ibrahim Shekarau sun rufe kariyarsu ba tare da gabatar da wani shaida ba.

Tribunal Sets Date For Adoption Of Final Addresses On Hanga/Zaura’s PetitionThe National/State House of Assembly Electio...
09/06/2023

Tribunal Sets Date For Adoption Of Final Addresses On Hanga/Zaura’s Petition

The National/State House of Assembly Election Petition Tribunal Sitting in Kano has slated 20th June, 2023 for the adoption of final written addresses in the petition filed by Abdussalam Abdulkarim Zaura of APC, challenging the victory and declaration of Rufa’i Sani Hanga as the winner of the Kano Senatorial District Election.

The Petitioner, A.A Zaura is praying the Tribunal to declare him winner and set aside the declaration and returning of Senator Rufa’i Sani Hanga as winner of the Kano Central Senatorial seat.

The respondents were given seven days each to start filing their addresses while the Petitioner was given 3 days to file his response and another 3 days each for the respondents within which to file reply in the point of law.

The Tribunal ordered Counsel to Rufa’i Sani Hanga, Barrister Ikpe to submit the Certified True Copies of all the documents he listed in his response

Some of the documents listed include register of voters, report of the NNPP primary election conducted on the 8th September, 2022 among many other documents

However, Senator Hanga testified before the Tribunal in defence of his victory.

Under cross extermination, the 2nd Respondnt testified that his name was not in the register of All candidates published by INEC.

Senator Hanga also testified that he could not remember the number contained in his NNPP membership card.

Under cross extermination, Hanga further said he is not a party in a suit file NNPP from Federal High Court, Kano to Supreme Court.

When the Tribunal resumed yesterday for continuation of defense, Senator Hanga and NNPP closed their case through their legal representative, Barrister Meshak Ikpe.

Similarly Justice Watch News observed that 1st and 4th Respondents, INEC and Mallam Ibrahim Shekarau closed their defense without calling any witness.

SAKON JAJEGA AL'UMMAR KANOMai faruwa ta faruwa ta faru abinda muka fada aka zage mu akaci mutumcin mu akan Abba kabir yu...
08/06/2023

SAKON JAJE

GA AL'UMMAR KANO

Mai faruwa ta faruwa ta faru abinda muka fada aka zage mu akaci mutumcin mu akan Abba kabir yusif tun ba'aje ko ina ba gaskiya tayi halinta.

Nidai a kananan shekaruna ban taba ganin rashin imani da tausayi irin na gwamnan kano Abba kabir yusif ba, Allah ne kadai yasan irin hasarar da Al'ummar kano s**ayi a sak**akon wannan rushe rushen.

Ga duk mai hankali da hangen nesa zai yadda dani abinda zai biyo bayan wannan rushe rushe yafi rusau din hadari ga jihar kano.

Matasa nawa ne s**a rasa aiki a dalilin wannan rusau din ?

Shin kuna zaton nan gaba akwai wani kamfani ko mai dukiyar da zai yadda ya kuma zuba dukiyar sa a kano ?

Gwamnati itace take rabawa gurare kwankwaso da shekarau duk sun bada gurare an gina shin Ganduje bashi da wannan damar ?

A Karshe zan mika jaje ga yan uwa da abokan arziki wanda rusau din Abba ya shafa Allah ya mayar muku da alheri kuma ku sani Allah baya zalumci ku cigaba da kai karar Allah kotun Allah tabbas zai saka muku.

Daga Sumayya AlsanMu bamu da karfin ja da gwamnatiAmma mun kai karar Abba kotun AllahAbba kabir yusif Allah ya Isa.
08/06/2023

Daga Sumayya Alsan

Mu bamu da karfin ja da gwamnati

Amma mun kai karar Abba kotun Allah

Abba kabir yusif

Allah ya Isa.

ABIN NEMA YA SAMUTuni zababurawa masu jira a rusa su kwashi ganima sun dira a filin sukuwa inda Abba  yayi rusau a daren...
03/06/2023

ABIN NEMA YA SAMU

Tuni zababurawa masu jira a rusa su kwashi ganima sun dira a filin sukuwa inda Abba yayi rusau a daren jiya.

Ikon Allah harda mata masu jajayen hijabi

KAMAR Abba Kabir Yusuf  BAI FAHINCI MATSALAR KANO BA.Na bibiyi abubuwan da sabon gwamnan kano Abba kabir yusif yace zai ...
30/05/2023

KAMAR Abba Kabir Yusuf BAI FAHINCI MATSALAR KANO BA.

Na bibiyi abubuwan da sabon gwamnan kano Abba kabir yusif yace zai mayar da hankali a gwamnatin sa abubuwa ne wanda suke k**a da ramuwar gayya karara ya nuna cewa Abba ya shigo gwamnati da gilli, idan muka kwatata abubuwan da takwarorin sa gwamnonin Jiha kaduna da zamfara s**a fada zasu mayar da hankali abubuwa ne gwanin sha'awa duk sun bayyana cewa zasu ba harkokin tsaro matukar muhimmanci sun nunawa duniya sun san matsalar jahohin su.

A yau a jihar kano babbar matsalar da take da mun mu itace rashin aikiyi ga matasa wanda ya haifar da matsalar tsaron a cikin birnin kano, mutum nawa yan fashin waya s**a kashe ?

Mutum nawa aka haura har gida aka kashe basu jiba basu gani ba ?

Idan akwai abinda yake damun mutanen kano bai wuce wannan ba a halin yanzu, k**ata yayi muji sabon Gwamnan kano ya bayyana shi a matsayin babban abinda zai mayar da hankali sama da komai.

Abinda Abba kabir yusif ya k**ata ya sani shine Allah bazai k**a shi da laifin abinda gwamnatin Ganduje tayi ba saboda haka bai k**ata ka bata lokaci wajen duba abubuwan da tayi ba matukar ba ramuwar gayya kazo yi gwamnati ba.

SHAWARACE BA ADAWA

JAM'IYYAR NNPP TA SHIRYA RUDU DA HANIYA.A bisa abinda ya bayyana a gare mu a halin yanzu da Kuma wasu bayyanai da muka s...
08/03/2023

JAM'IYYAR NNPP TA SHIRYA RUDU DA HANIYA.

A bisa abinda ya bayyana a gare mu a halin yanzu da Kuma wasu bayyanai da muka samu ta karkashin kasa Jam'iyar NNPP a jihar Kano ta shirya yada rudu da haniya a zaben Gwamnan kano wanda za'a gabatar ranar 11/3/2023.

Tun ba'a shiga zaben ba jam'iyar sai fito da wasu korafe_korafe take Akan hukumomin daban daban.

A jiya Sunyi zanga-zangar a hukumar Yan sanda ta jihar Kano akan wai sun samu labarin Za'a kawo abokin Gwamnan Kano Albdullahi Ganduje a matsayin Kwamishinan Yan sanda a jihar Kano, hukumar Yan sandan Kano ta karya wannan labarin nasu inda tace " Babu wani official Document Wanda yake nuna wannan zargin nasu".

A yau sun Kuma Bayyana a hukumar zabe ta Jihar kano suna neman dole sai Admin Secretary ya sauka daga mukamin da kafin zaben Gwamnan Kano.

Magana ta gaskiya wadannan zarge zargen da Jam'iyar NNPP take yi zargi ne Wanda bashi da tushe b***e mak**a, haka Kuma zargin zai haifar da rudani da haniya a wannan zaben Mai zuwa.

Muna Kira ga Jami'an Tsaro da su kalli wannan matsalar kafin tazo domin cigaba da dorewar zaman lafiya a kano a yanzu da Kuma bayan zabe.

Muna sanar da Jami'an Tsaro cewa Jam'iyar NNPP tana da tsarin yada propaganda a daidai lokacin da aka Fara kirga kuria a jihar Kano domin hargitsa zaman lafiyar Kano.

A karshe muna Aduar Allah yasa ayi zabe lafiya a Gama lafiya ya bawa Kano zaman lafiya Ameen

19/02/2023

ABINDA YAKE NEMAN FARUWA
ABIN KUNYA NE GA DAN AREWA

Wannan cigaban rubutun nane Mai taken MENENE MAKOMAR DAN AREWA DA SIYASAR SA BAYAN ZABEN 2023.

Tabbas abinda yake shirin faru da Tinubu a siyasa, zai iya kawo rashin jituwa ta har abada tsakanin kabilar Yarabawa da Hausa/Fulani.

Kuma zai iya shafar kowa da kowa,ako wace Jam’iyya matukar Kai Dan Arewa ne, Kuma zai iya shafar ya’ya da jikoki.

Sannan zai iya kawo rashin yarda da amincin a cikin kasa da Kabilun Kasa baki daya.

Zaku fahinci hakan idan muka kalli wanene Alh Ahmad Bola Tunubu ? wance irin gudummawa ya taka wajen magance sabanin dake tsakanin mutanen kudu maso yamma da Hausa/fulani.

Ya Dan uwa na Dan Arewa Sanin kowane cewa Asiwaju Bola Tinubu ya bada babbar gudunmawa wajen ganin an samu kyankyawar fahintar juna tsakanin kabilar sa da Hausa/Fulani tun daga zaben 2007 har zuwa 2019.

A zaben 2007 Tunubu ya bawa Alh Atiku Abubakar damar zama Dan Takarar shugaban kasa a Jam’iyar sa ta AC, haka Kuma a zaben 2011 ya Kuma dauko Dan Arewa Nuhu Rubado daga ya bashi Takara a jam'iyar ACN, Sanin kowa ne Alh Ahmad Bola Tunubu ya bada Gagarumar gudummawa wajen kafa jam'iyar APC, haka Kuma ya taimakawa Shugaban kasa Buhari ya samu nasarar zama Dan Takarar jam’iyyar APC a zaben 2015, haka a zaben 2019 ya Kuma marawa Buhari baya ya Kuma zama shugaban kasa a karo na biyu.

Menene ke Shirin faruwa da Alh Ahmad Bola Tunubu Kuma menene abin kunyar ga Dan Arewa ?

Dan Allah kuyi hakuri ku biyo ni bashi.

ABINDA KE SHIRIN FARUWA DA TUNUBU ABUN KUNYA NE GA AREWA DA KUMA DAN AREWA.Daga Aliyu Sani madakin GiniTarihin siyasa a ...
16/02/2023

ABINDA KE SHIRIN FARUWA DA TUNUBU ABUN KUNYA NE GA AREWA DA KUMA DAN AREWA.

Daga Aliyu Sani madakin Gini

Tarihin siyasa a NIgeria ya nuna cewa,akwai rashin jituwa a siyasan ce,tsakanin Hausa/Fulani da Mutanan Kudu Maso Yamma (South West) wannan rashin jitiwa ya faru tun lokacin Jamhuriya ta Farko(First Republic)a wannan lokaci akewa su Akintola(Premier na South West)ganin k**ar sunci amanar yan’uwan su Yarabawa don suna goyan bayan jam’iyyar NPC,jam’iyyar da akewa ganin ta Hausa/Fulani ce.

A tarishin siyasar NIgeria duk jam’iyyar da Hausa/Fulani sukeyi,to wannan jam’iyyar ba’a yinta akasar Yarabawa.Wannan yasa mulkin siyasa a NIgeria ya zama k**ar hamayya ce,tsakanin Hausa/Fulani da mutanan South West(Wato Yarabawa).

Wannan magana haka ce ta faru a jahuriya ta biyu,sanda mutanan Hausa/Fulani suke jam’iyyar NPN su kuma Yarabawa suke UPN,kuma duk wanda yake Bayarrabe inya shiga NPN ganin sa ake k**ar yaci amanar yan’uwansa Yarabawa.Wanna ne,yasa ko sanda akayi jam’iyyar PDP ta kuma tsayarda Obasanjo dan takara,amma a 1999 ba’a zabe shi a Jahohin Yarabawa ba don,yan’uwansa sunai masa ganin a jam’iyyar Hausa/Fulani ya fito Takara.

Amma a Magana ta gaskiya,shi Bola Ahmed Tinubu yayi ta kokarin ganin an sami fahinta irin ta siyasa tsakanin Kabilarsa ta Yarabawa da Hausa/Fulani.A shekarar 2007,yayi kokari wajen atsaida Atiku Abubakar Takarar shugaban kasa a jam’iyyar AC wadda yake jagoran ta,sannan a shekarar 2011,ya sake tsayar da Ribadau Takarar shugaban takarar shugaban kasa a jam’iyyar ACN da yake jagoran ta.

Sanin kowane cewa Asiwaju Bola Tinubu ya bada babbar gudunmawa wajen kafa jam’iyyar APC,sannan yayi iya kokarin sa wajen ganin Buhari ya zama dan takarar jam’iyyar APC a jihar Lagos inda akai primary election.Maiyuwuwa in banda kokarin Tinubu da amfani da damar yin primarily a Lagos,da Jagora na Sen Rabiu Musa Kwankwanso shine zaici zaben.

Jama’a musanman kabilar Hausa/Fulani su sani,sanda Tinubu yake ta wannan kokarin ganin anyi hadaka tsakanin Kabilarsa ta Yarabawa,Yan’uwansa Yarabawa sunata gayamasa cewa ya guji hadaka da Hausa/Fulani,wai acewar su,mu maciya amana ne,a siyasance.Wannan batu na karanta sau da yawa.

Inna son mai karanta wannan rubutu ya sani,ni Aliyu Sani Madaki dan Jam’iyyar PDP ne,kuma dan Kwankwasiyya mai addu’ar Allah Ya bawa jam’iyyar PDP nasara a zaben 2023 kuma ya bawa Kwankwaso shugaban kasa.Mai karatu zai iya cewa,meya hada ni da matsalar Tinubu da APC.Dalilin wannan rubutu shine,mu guji yin duk abunda zai kawo rashin yarda da aminci acikin Kabilun Kasar mu NIgeria.Mu Hausa/Fulani da ansanmu da amana da gaskiya,da kuma ciki alkawari.

Abunda yake neman ya faru da Tinubu,ko kuma ya faru zai iya kawo rashin jituwa ta har abada tsakanin kabilar Yarabawa da Hausa/Fulani.Kuma zai iya shafar kowa da kowa,ako wace Jam’iyya.Kuma zai iya shafar ya’ya da jikoki.Sannan zai iya kawo rashin yarda da amincin acikin kasa da Kabilun Kasa baki daya.

Ni a matsayina,na dan Jihar Kano,kuma dan Kwankwasiyya Inna zargin Asiwaju Tinubu da bada gudunmawa wajen karbe mana zaben Governor da mukaci,amma wannan ba zaisa nayi shiru ba,innaga yan’uwana suna neman jawomun gabar har abada banya babu ruwana.Manya Jam’iyyar APC musanman kabilar Hausa/Fulani susan ramin da suke gina wa,yana da zurfi,kuma zai haifar da barna ta har abada.Wannan shiri na awulakanta Tinubu zaizo da matsala da tsada ta gaske.Wallahi da abun zai tsaya kan Tinibu ne,bazan magana ba,amma zai iya shafar dukkan Kabilun(Wato Hausa/Fulani da Yarabawa).

Daga karshen inna addu’ar Allah Ya tsare mu da mugun ji da Mugun Gani.Allah Ya kare mana lafiyar mu da mutuncin da imanin mu,amin.

Allah Ya bada ikon fahinta.

Rep Aliyu Sani Madaki

Yayi wannan rubutun Ranar 25/Jun 2020

AREWA ZAMU RAMA HALLACIAlh Ahmad Bola TunubuYa yiwa Yan Arewa hallaci  tun 2007 ,2011, da 2015 sannan 2019 duk Yan Arewa...
10/02/2023

AREWA ZAMU RAMA HALLACI

Alh Ahmad Bola Tunubu

Ya yiwa Yan Arewa hallaci tun 2007 ,2011, da 2015 sannan 2019 duk Yan Arewa Alh Ahmad Bola Tunubu Dan Arewa ya dauko ya Masa baya don ya zama shugaban kasa.

A zaben 2007 ya marawa Atiku Abubakar bayan ya zama shugaban kasa a jam'iyar ACD.

A zaben 2011 Tunubu ya Kuma Danko Dan Arewa ya Marawa Nuhu Rubado Don ya zama shugaban kasa a jam'iyar ACN.

A zaben 2015 Babu Wanda Bai San gudummawar da Alh Ahmad Bola Tunubu ya bawa muhammadu Buhari ba Dan Arewa domin ya zama shugaban kasa.

A zaben 2019 jagaba ya Kuma marawa Dan Arewa baya shugaban kasa muhammad Buhari ya zama shugaban kasa.

Yanzu saboda Allah yanzu 2023 muce Wannan mutumin shi zamu kwarewa baya ?

Mu Yan Arewa Yan hallakar ne,mun San hallaci Kuma zamu Rama hallaci da karanci.

A wannan zaben na 2023 zamuy JAGABA zamu nunawa Arewa mu Yan Arewa mu Yan hallakan ne.

31/10/2022

KAR KA BARI A BAKA LABARI

ALLAHAMMDULLAH.MUN MIKAWA DATTIJO MUHAMMAD BELLO SAKON KU.Kamar yadda mukayi alkawarin cewa yau Lahadi 30/10/2022 zamu m...
31/10/2022

ALLAHAMMDULLAH.

MUN MIKAWA DATTIJO MUHAMMAD BELLO SAKON KU.

Kamar yadda mukayi alkawarin cewa yau Lahadi 30/10/2022 zamu mikawa Dattijo Muhammad Bello taimakon da kuka bashi cikin hukunci Allah mun bashi.

Mun samu taimakon naira 27500 daga hannun ku ga lissafin su Kamar haka
1. ARUNA AISHAT HASSAN YA TURO 500
26/10/2022

2. Sulaiman Abdullahi ya turomin 1000
3. 27/10/2022.

4. Naziru sani Jega ya Turomin
1000
28/10/2022.

5.bawan Allah ya nemi mu boye sunan sa ya turomin
2000
29/10/2023.

6.Aboye suna na ya turomin
5000
29/10/2022.

7.Aboye suna na ya turomin
2000
29/10/2022.

8.Charity foundation ta hannu Halima sun turo 15000.

Kudin sun k**a 27500.

Mun saiwa Dattijo Muhammad Bello kayan Abinci domin sune yafi tsananin bukatar su ga lissafin kayan da muka saya Masa.

1. Sabulun wanki
2. Omo
3. Sabulun wanka

2. Magi

3.mai na girki

4. Gero
5. Shinkafa
6. Wake
7. Masara

Dattijo Muhammad Bello yace mu Mika Masa godiya a gare ku Allah ya saka muku da Alheri.
Har yanzu kofa a bude take wajen taimakawa Dattijon muhammad Bello domin Yana neman muhalin zama shida iyalan sa haka Kuma Yar da da aka sako Masa da Tsohon ciki haihuwar yau ko gobe tana bukatar taimako.

Ga Mai son ganin muhammad Bello ya Kira wannan numbar 08168345151.

Account numba
0260182507
GT bank
Ishaq sani Darma

Daga

Shugaban kungiyar Gidauniyar Alheri via Facebook
Comrade Sani salisu Darma

JAMA'A DATTIJON MUHAMMAD BELLO YANA MATUKAR BUKATAR TAIMAKO.Akwai abin tausayi ga rayuwa wannan dattijo,a lokacin da yak...
29/10/2022

JAMA'A DATTIJON MUHAMMAD BELLO YANA MATUKAR BUKATAR TAIMAKO.

Akwai abin tausayi ga rayuwa wannan dattijo,a lokacin da yake jihar sa ta zamfara Mai arziki ne ga garken shanu ga garken tukakai Amma dare daya Yan Ta’adda s**a Kore su daga karshe s**a Fara barazana ga rayuwar sa, hakan ya sa dole ya baro jihar zamfara ya dawo Kano.

A Nan jihar Kano Dattijon ya samu kan sa cikin mawuyaciyar rayuwa sak**akon damuwa da kunci yasa ya rasa idanuwan sa gaba daya ya makance.

Allah sarki gashi ya tara iyalai mutum 18 ne ya'yan sa mafiyawan su Mata ne da maza kanana, kullum sai ya fito yayi bara yake ciyar dasu.

A ziyarar da muka Kai Masa mun fahinci Dattijon muhammad Bello Yana matukar bukatar taimakon na musanman.

Yana matukar bukatar Abinci, sannan muhalli domin a filin Allah yayi bunka yake zaune shida iyalan sa a haka Damuna ta Kare akan su yanzu Kuma ga sanyi Yana tafe.

A cikin wannan halin aka sako Masa yar sa da Tsohon ciki daga zamfara yanzu haka itama ta dawo Nan Kano wajen sa haihuwar yau ko Gobe.

Munyi kokarin nema Masa taimako a wannan kafar ta sada zumunta ( social media) a karkashin kungiyar Gidauniyar Alheri,Amma har zuwa yanzu mutum uku ne s**a turo da taimakon su ta Hanyar Account din da muka saka ga sunayen Kamar haka.

1.Aruna Aishat Haruna Hassan ya turo 500 ranar 26/10/2022.

2. Sulaiman Abdullahi ya turomin 2000 ranar 27/10/2022.

3. Naziru sani Jega ya turo 1000 ranar 28/10/2022.

Wadannan sune kudaden da muka samu Wanda kuka taimakawa Dattijon muhammad Bello, jama'a Muna Kara nemawa muhammad Bello taimakon musanman mu samu kudin da zamu sai Masa kayan abinci.

Saboda halin da yake ciki na matsanancin neman taimako Gobe Lahadi 30/10/2022 da misalin karfe Biyu na Rana 2:00 zamu kaiwa Dattijon abinda muka samu, idan kana bukatar kaima kaje ka ganewa idon ka sai ka Kira wannan numbar 08168345151.

Account Numbar 0260182507

Name Ishaq sani Darma

Bank GT bank

ALLAH YA BADA IKON TAIMAKAWA

Daga Comrade Sani salisu Darma shugaban kungiyar Gidauniyar Alheri via Facebook
29/10/2022.

28/10/2022

ANYI ZABE AN GAMA.

Dr Nasiru Yusif Gawuna ya lashe zaben da gagarumin rinjaye.

Gawuna sabon Gwamnan Kano

LABARIN WANNAN MUTUM AKWAI ABIN TAUSAYI!Wannan Mutum da ke jikin hoton nan wani dattijo ne dan asalin Jihar Zamfara, ya ...
27/10/2022

LABARIN WANNAN MUTUM AKWAI ABIN TAUSAYI!

Wannan Mutum da ke jikin hoton nan wani dattijo ne dan asalin Jihar Zamfara, ya kasance mutum mai arziki da wadata, ya mallaki garken shanu, karshe dai yan ta'adda s**a zo s**a kore garken shanun nan baki daya, sama da shanu guda Hamsin (50)

Ba a fi wata daya ba Allah Ya jarrabce shi da rashin gani (Makanta) Baki daya idanuwansa sun rufe, ba ya iya ganin komai. Ya dawo nan Kano da zama sak**akon ta'addanci yan ta'adda ya ta'azzara a kauyensu. Yanzu haka yana kusa da BUK NEWSITE a wani gida da ba a kammala gininsa ba.

Kullum zai fito da sassafe shi da wannan Yaro nasa da ke kwance mai suna Malami. Za su yi ta zagaye, tun daga BUK NEWSITE har Kabuga, suna barar abin da za su ci. Yana da matan aure biyu, da Yara Maza da Mata su Tara (9)

Akwai Yarsa da ke aure a Zamfara, yanzu haka Mijinta ya gudu neman kudi kudancin Nigeria, ya turo ta nan Kano wajen wannan Mahaifi na ta Makaho Talaka ga tsohon ciki, haihuwa yau ko gobe.

Na san shi sama da wata guda baya, na dan ba shi kudi kadan.

Yau na sake haduwa da shi a inda na ke dan zama a Kofar masallacinmu a nan Kano.

Sama da wata guda tufafin da ke jikinsa kenan, yau na ba shi tufafi kala biyu masu kyau sosai. Na kuma ba shi naira dari uku (300)

Na rage abubuwan tausayi masu yawa a labarinsa. Bisa haka, na dan kwatanta abin da zan iya, bari na yi amfani da kafar sadar da zumunta don nema masa tallafin abinci, ko tufafi.

Shi kansa Yaron da ke yi masa jagorar zagaya wa cikin gari yin bara, daga ka kalli idanuwansa ka san ba shi da lafiya.

Wannan bawan Allah kuwa ba shi da aiki sai addu'a, sai Tawakkali.

Na yi nufin na sanar da inda za a same shi, amma duba da sharrin zamani, gaskiya na janye, saboda yana da Yara Maza da Mata, duk mai son taimaka masa zai iya tuntubata ta inbox. In sha Allah zan yi masa jagora inda zai same shi ido da ido, ku kuma isar masa da sakon da ake son taimaka masa hannu da hannu.

Zaku iya taimaka Masa ta hanyoyi Biyu

1. Ku Kira wannan numbar 08168345151 zamu Kai ku Gidan sa ku taimaka Masa .

2.Zaku iya tura taimakon ku ta wannan Account din 0260182507 GT bank ishaq sani Darma Inshaallahu sakon zai Isa gare shi inshaallahu.

ALLAH YA BADA IKON TAIMAKAWA

JAMA'A GA AIKIN ALLAHMAL MUHAMMAD BELLOYANA BUKATAR TAIMAKODaga Comrade Sani Salisu DarmaA jiya laraba 26/10/2023 na sam...
27/10/2022

JAMA'A GA AIKIN ALLAH

MAL MUHAMMAD BELLO

YANA BUKATAR TAIMAKO

Daga Comrade Sani Salisu Darma

A jiya laraba 26/10/2023 na samu damar dattijo muhammad Bello zamfara, mutumin da Musa muhammad Dan kwano ya wallafa labarin halin da yake Mara Dadi a sak**akon danyen aikin Yan Ta'addan jihar zamfara.

Kafin ya hadu da mugun aikin Yan Ta'addan jihar Zamfara ya kasance mutum mai arziki da wadata, ya mallaki garken shanu, karshe dai yan ta'adda s**a zo s**a kore garken shanun nan baki daya, sama da shanu guda Hamsin (50),k**ar yadda ya sheda Mana a zantawar mu dashi.

Yanzu haka ya dawo jihar Kano ya zama makaho baya gani Yana yawon bara tare da Dan sa Mai suna malami, sai yayi yawon bara sannan yake samun abinda zaici shida iyalan sa maza da Mata da Kuma shi da matar mutum Ashirin (20).

Tunda daga sabuwar jami'ar Bayero University( y/New site) unguwar Danbare yake fitowa yawon bara har kofar ka buga tare da wannan yaron.

Jama'a wallahi wannan mutumin Yana matukar bukatar taimakon naje har Gidan naji wasu Karin matsalolin daga wajen iyalin sa na ban tausayi, yanzu haka akwai wata Yar sa Wanda aka sako Masa daga zamfara da Tsohon ciki haihuwa yau ko Gobe.

Muhammad Bello Yana bukatar taimakon Abinci da tufafin sawa da muhali k**ar yadda zakuji daga bakin sa a cikin wannan video.

https://www.facebook.com/100063798075650/posts/534765955326669/?app=fbl

Hanyar da za'a iya taimaka Masa

1.ka Kira wannan numbar zamu Kai ka idon ka ya gane maka halin da Malam muhammad yake ciki ka taimaka masa. 08168345151.

2.zaka iya tura taimakon da kayi niyyar bashi ta wannan Account 0260182507 GT bank Inshaallahu sakon ka zai iske shi.

ALLAH YA BADA IKON TAIMAKAWA

Address

Kaduna Hayin Banki
Lere
234

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Labarai daga tushe posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share

Category


Other Lere media companies

Show All

You may also like