KHM TV

KHM TV KHM TV HAUSA - Kamfanin Jarida Ce Mai Zaman Kanta, Da Take Watsa Ingantattun Labaran Duniya.

Kocin Manchester United ya bayyana matsalar da yake fama da ita inda ya ce ƙungiyar na buƙatar ƴan wasa da s**a iya jago...
05/01/2025

Kocin Manchester United ya bayyana matsalar da yake fama da ita inda ya ce ƙungiyar na buƙatar ƴan wasa da s**a iya jagoranci cikin fili don su taimaka wa sauran da ke fargaba.

Amorim ya kuma ce rayuwarsa ta sauya saboda yanayin da ƙungiyar ke ciki.

YANZU-YANZU: Mawaƙi Alhaji Dauda Kahutu Rarara ya shirya addu'o'i na musamman domin yi wa Nijeriya addu'ar kariya daga ƙ...
05/01/2025

YANZU-YANZU: Mawaƙi Alhaji Dauda Kahutu Rarara ya shirya addu'o'i na musamman domin yi wa Nijeriya addu'ar kariya daga ƙasashen waje

Me zaku ce?

Ina Hausawa? Menene sunan Data da Hausa?
05/01/2025

Ina Hausawa? Menene sunan Data da Hausa?

05/01/2025

KAI TSAYE: Cigaba da taron Mauludin Shehu Ibrahim Inyass (RA) wanda yake gudana yanzu haka a garin Saminaka.

Taron Mauludin wanda Majma'u Ahbab Shehu Ibrahim Inyass reshen karamar hukumar Lere dake jahar Kaduna ta shirya kaman Yanda ta saba.

KHM TV HAUSA

"Babu wanda ya isa ya hanani buɗe gashin kaina, domim ni yin magana ne ma kesa nayi abu. Koda abun da nai ba mai kyau ba...
05/01/2025

"Babu wanda ya isa ya hanani buɗe gashin kaina, domim ni yin magana ne ma kesa nayi abu. Koda abun da nai ba mai kyau bane, muddin za'a ce na daina ni kuma a wannan lokacin nema zan fara. Bana son katsalandan a rayuwa ta."

~ Cewar Nafisat Abdullahi

05/01/2025

KAI TSAYE: Rufe taron Mauludin Shehu Ibrahim Inyass (RA) wanda yake gudana yanzu haka a garin Saminaka.

Taron Mauludin wanda Majma'u Ahbab Shehu Ibrahim Inyass reshen karamar hukumar Lere dake jahar Kaduna ta shirya kaman Yanda ta saba.

KHM TV HAUSA

SAQON GAYYATA : Hukumar makarantar Jundullahi dake sabon layi Saminaka suna farin cikin gayyatar ku zuwa wurin taron Wal...
05/01/2025

SAQON GAYYATA :

Hukumar makarantar Jundullahi dake sabon layi Saminaka suna farin cikin gayyatar ku zuwa wurin taron Walimar Sauka da Haddar Alqur'ani Mai girma na wasu daga cikin Ɗaliban ta.

Taron zai kasance kamar haka :
Rana : 12 ga watan Janairun shekarar 2025
Wuri: Ƙofar gidan Malam Nuhu Aliyu Liman Saminaka.
Lokaci: Da Misalin ƙarfe 10:00 na safe.

Allah ya bada ikon halarta.

©KHM TV

05/01/2025

Ku ziyarci shagon Xauress photography domin a yi muku hotuna masu kyau kuma ingantatattu. Sannan kuma zaku iya gayyatarsu zuwa wajen taro kowane iri domin su cire muku zafafan hotuna na zamani.

KHM TV mun jaraba su kuma mun ga aiki Mai kyau.

Fasto (Dr.) Yohanna Buru, babban limamin cocin bishara da rayuwa ta Kirista, ya bayar da gudummuwa ga sabon masallacin d...
05/01/2025

Fasto (Dr.) Yohanna Buru, babban limamin cocin bishara da rayuwa ta Kirista, ya bayar da gudummuwa ga sabon masallacin da aka gina a Tudun Biri, jihar Kaduna. Wannan gagarumin aiki na gudummuwa ya hada da sabbin butocin alwala, tabarmu, da itatuwan da za a dasa a wajen taron buɗewa.

An gudanar da taron buɗe sabon masallacin ne tare da addu’o’i na musamman ga waɗanda harin bom ya rutsa da su a Tudun Biri a cikin shekara guda da ta gabata. Faston ya bayyana cewa wannan gudummuwa na nufin ƙara dankon zumunci da zaman lafiya tsakanin Kiristoci da Musulmi a yankin.

Malam Ibrahim Sheikh Dahiru Usman, wanda ya karbi gudummuwar, ya gode wa Fasto Buru, yana mai cewa al’ummar yankin sun taru domin gudanar da addu’o’i ga wadanda s**a rasa rayukansu, tare da bude sabon masallacin a hukumance.

Wannan lamari na gudummuwa daga Fasto Yohanna Buru ya jawo hankalin mutane da dama, yana nuni da kyakkyawar alaka tsakanin mabiya addinai mabanbanta a Najeriya.

HOTUNA: Yanda aka daura auren kanin Manager Director na KHM TV wato Najib Haruna a yau Asabar 4-1-2024 a garin Saminaka ...
04/01/2025

HOTUNA: Yanda aka daura auren kanin Manager Director na KHM TV wato Najib Haruna a yau Asabar 4-1-2024 a garin Saminaka dake karamar hukumar Lere jahar Kaduna

Angon mai suna Abdullahi Haruna an daura aurensa ne tare da Amaryarsa mai suna Jamila bayan soyayya da s**a yi na wani lokaci. A madadin dukkan al'umman KHM TV muna yiwa amarya da ango fatan alkairi.

KHM TV HAUSA

04/01/2025

KAI TSAYE: Yanda taron Mauludin Shehu Ibrahim Inyass Na Majma'u AHBAB Shehu Ibrahim Inyass ta shirya

RANA TA FARKO: Yanda aka gudanar da taron Mauludin Shehu Ibrahim Inyass (RA) rana ta farko wanda Majma'u Ahbab Shehu Ibr...
04/01/2025

RANA TA FARKO: Yanda aka gudanar da taron Mauludin Shehu Ibrahim Inyass (RA) rana ta farko wanda Majma'u Ahbab Shehu Ibrahim Inyass reshen karamar hukumar Lere dake jahar Kaduna s**a gudanar a shekaran jiya Alhamis 2/1/2025 a garin Saminaka.

Taron ya samu daman halartar al'umma da manyan malamai daga sassa daban-daban na karamar hukumar Lere. Taron dai an shirya gudanar dashi ne na tsawon kwanaki 4.

KHM TV HAUSA

Jarumar Kannywood Radeeya Jibril, ta sanar da daina yin fim sakamakon Aure da tayi.Tsohuwar jarumar, ta godewa wasu daga...
04/01/2025

Jarumar Kannywood Radeeya Jibril, ta sanar da daina yin fim sakamakon Aure da tayi.

Tsohuwar jarumar, ta godewa wasu daga cikin 'yan masana'antar da s**a ba ta gudunmawa.

Radeeya ta ce "zan yi anfani da wannan damar tawa ta yau domin sanar da ku cewa (NAYI AURE), nagode wa Allah da ya nunamin wannan rana da zan bar Kannywood lafiya kamar yanda na shigo lafiya, Alhamdulillah."

Jaruma Radeeya na cikin jerin jarumai mata masu tasowa da tauraruwarsu ke haskawa.

Daga ƙarshe ta yiwa duk kanin al’ummar dake cikin Kannywood godiya tare da fatan alkhairi.

Wane fata zaku yi mata?

CIGIYA!  CIGIYA!!  CIGIYA!!!MUNA CIKIYAR WANNAN YARO MAI SUNA MUSTAPHA IBRAHIM U/BAWA MUKULLAH. YARON YA FITA MASALLACIN...
04/01/2025

CIGIYA! CIGIYA!! CIGIYA!!!

MUNA CIKIYAR WANNAN YARO MAI SUNA MUSTAPHA IBRAHIM U/BAWA MUKULLAH. YARON YA FITA MASALLACIN JUMA'A TUN JIYA HARYANZU BAI DAWOBA, DUK WANDA ALLAH YASA YA GANSHI KO YAJI LABARIN WANDA YA GANSHI A KIRA WANNAN NUMBER WAYAR: 07030448413 ALLAH YASA ADACE AMEEN.

KHM TV

MASU BIBIYAR MU BARKAN MU DA WANNAN LOKACI.Karo na biyar wasu daga cikin mutanen da muke Saran zasu halarci taron mu ran...
04/01/2025

MASU BIBIYAR MU BARKAN MU DA WANNAN LOKACI.

Karo na biyar wasu daga cikin mutanen da muke Saran zasu halarci taron mu ranar 10/01/2025.

Idan har kanason zuwa kaima zaka iya aje mana hoton ka da cikakken suna a inbox ko comment section.

KHM TV HAUSA.

DA ƊUMI-ƊUMI: Hukumar tace finafinai da ɗab'i ta jihar Kano ta dakatar da jaruma Sahma M. Inuwa daga shiga harkar fim na...
04/01/2025

DA ƊUMI-ƊUMI: Hukumar tace finafinai da ɗab'i ta jihar Kano ta dakatar da jaruma Sahma M. Inuwa daga shiga harkar fim na tsawon shekara ɗaya, tare da ƙwace shaidarta ta zama halastacciyar 'yar fim.Hakan kamar yadda sanarwa daga jami'in yaɗa labaran hukumar Abdullahi Sani Sulaiman ta ce ya biyo bayan zargin jarumar da shigar banza da kuma furta wasu kalamai da ake ganin sun saɓa addini da al'adar Hausawa.

Me zaku ce?

Sabbin jami'an hukumar Hisbah na jihar Katsina na cigaba da amsar horo kamar yanda Ya kamata.Menene fatan ku a gare su?
04/01/2025

Sabbin jami'an hukumar Hisbah na jihar Katsina na cigaba da amsar horo kamar yanda Ya kamata.

Menene fatan ku a gare su?

Address

Lere Local Government
Lere

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when KHM TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share