Rijiyar Labarai.

Rijiyar Labarai. Labarai,Ilimantarwa,Fadakarwa,Nishadantarwa

Hajiya Fatima Aliko Dangote ta tallafawa Fitacciyar kungiyar yan jaridu ta (Arewa Online journalist Forum) da tallafin S...
03/04/2024

Hajiya Fatima Aliko Dangote ta tallafawa Fitacciyar kungiyar yan jaridu ta (Arewa Online journalist Forum) da tallafin Shinkafa don rage raɗaɗi a watan Ramadan mai alfarma.

Hajiya Fatima tayi shura wajen ganin ta saka farin ciki a fuskokin Alummar Najeriya musamman arewacin Najeriya.

Hajiya Fatima ta kasance daya daga cikin jigo a kamfanin mahaifinta Dangote, ta biyo kalar kyawawan hali na mahaifinta Alhaji Aliko Dangote wajen ganin ta kyautatawa na kasa da ita

Shugaban Kungiyar yan jaridu ta (Arewa Online journalist Forum) Malam Barrah Almadany ya mika sakon godiya ga Uwar marayu Hajiya Fatima Aliko Dangote wajen yadda ta tsaya tsayin daka wajen tallafawa mabukata da kayan abinci a wannan wata na Ramadan.

Kazalika Almadany ya bukaci masu hannu da shinu suyi koyi da kalar halaye na Hajiya Fatima Aliko Dangote wajen taimakawa mabukata idan halin haka ya samu don rage raɗaɗi ga Yan kasa..

GAMAYYAR KUNGIYAR MATASAN FULANI (FUYAN) TA YI KIRA DA A SAKI BELLO BODEJO -Muna kira ga shugaban ƙasar Najeriya Bola Ah...
05/02/2024

GAMAYYAR KUNGIYAR MATASAN FULANI (FUYAN) TA YI KIRA DA A SAKI BELLO BODEJO

-Muna kira ga shugaban ƙasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya gaggauta ba da umarni a saki Dr Abdullahi Bello bodejo.

Ta nuna ɓacin ranta matuƙa akan ci gaba da tsare Alhaji Dr Abdullahi Bello Bodejo, ta ce, tsarewan an yi shi ne ba bisa Ƙa'ida ba.

Kungiyar matasan ta Najeriya mai suna Fulani Youth Association of Nigeria (FUYAN) ta koka akan ci gaba da tsare Alhaji Dr Abdullahi Bello Bodejo, shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal H**e, Wanda ta ke raya al'adun Fulani a kasa.

A cikin Sanarwar da ta aikewa manema labarai a ranar juma'a da safe ta hannun mai Magana da yawun ta kuma jami'in hulda da jama'a na kungiyar Miyetti Allah na kasa Ambasada Muhammad Tasi'u Sulaiman (FUYAN) ta ce cigaba da tsare Alhaji Dr Abdullahi Bello bodejo da sojojin Najeriya ke yi ba bisa ka'ida ba ne.

A faɗin ( FUYAN) sojoji ba su da iko a bisa dokar ƙasa su tsare ko wanne mutum Fiye da awa ashirin da huɗu (24h) kuma kungiyar tana kira da babban murya ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga Lamarin a bada umarnin sakin shi da gaggawa.

Sun ce shugaban Miyyetti Allah Kautal H**e an ɗauke shi ne a ofishin sa da ke tudun Wada a karamar hukumar Karu da ke jihar Nassarawa, kuma an tsare shi a hannun Sojojin Najeriya a Asokoro da ke birnin tarayya Abuja.

Sojojin a Najeriya ba a ba su iko, a dokan kasa su tsare ko wanne ɗan ƙasa ba . Jami'an ƴan sanda da DSS su ne kaɗai aka ba iko su tsare mutum.Tsare Alhaji Dr Abdullahi Bello bodejo na tsawon lokacin nan ba bisa Ƙa'ida ba ne.

Ya kamata Sojojin su miƙa shugaban zuwa ga ƴan sandan Najeriya ko kuma su ba DSS, takardan ko wanne irin bincike da su ke masa akan wannan abin da ba bisa ka'ida ba, sojojin sun tsare shi ba tare da ikon kundin tsarin aiki ba.

Muna kira ga shugaban ƙasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya gaggauta ba da umarni a saki Dr Abdullahi Bello bodejo.

Sojojin Najeriya ba su da ikon tsare ko wanne mutum fi ye da awa ashirin da huɗu (24h) ba tare da an Kai shi kotu ba. Saboda haka tsare shugaban Mu Alhaji Dr Abdullahi Bello bodejo ya saɓawa doka ko kuma ya zama sabo a kan dokar ƙasar Najeriya, a faɗin (FUYAN.)

Malam Sulaiman ya roƙi mambobin wannan ƙungiyar da shuwagabannin ta da su cigaba da natsuwa da bin doka kamar yadda su ke jiran sakin shugaban su.

Cigaba da tsare Alhaji Dr Abdullahi Bello bodejo da sojojin Najeriya ke yi ba tare da an kai shi kotu ba. Shugaban matasan Fulani ya ce: wannan ƙarfin ikon su ne, wanda sojojin su ke ganin ba wanda ya isa ya hukunta su kuma lauyoyun su na nan suna shiri akan wannan al'amarin.

Idan sojojin Najeriya na da wani hujja a kan Dr Abdullahi Bello bodejo, akan laifin da ya yi wanda doka ta sani a kaishi kotu ya fi tsare shi da aka yi ba bisa Ƙa'ida ba domin wannan ya saɓawa yancin ɗan adam da ke zayyane a dokokin ƙasa.

Hukumomin jami'an tsaron Najeriya Wanda aka san su da korewa akan girmama dokokin ƙasa da nuna ɗabi'o'i da aka san su da shi, a yi amfani da su ta wajen sakin Bello bodejo kamar yadda dokar ƙasa ta bashi iko a matsayin ɗan ƙasa mai bin doka da odar Najeriya, kuma a barshi ya taho gida, yadda ake cigaba da tsare shi ba bisa ka'ida ba ne kuma ba bisa dokar ƙasa ba ne.

Alhaji Dr Abdullahi Bello bodejo an tsare shi ne kwananan a maƙasudin ƙaddamar da yan sa kai mai suna Nomad vigilantee Group a Lafia hedkwatar jihar Nassarawa a ranar 17 ga watan Janairu 2024 wanda ya biyo bayan ce-ce-kucen jama'a a kasa.

Alhaji Dr Abdullahi Bello bodejo ya ce,. Maƙasudin manufofin kafa Wannan yan sa kai don a taimaka wajen tsare rayukan manoma da makiyaya kuma da taimakawa wajen tattaro bayanan sirri ga hukumomin tsaron Najeriya daga munafukai da yan ta'adda daga ƙauyuka kuma da bunƙasa zaman lafiya a ƙauyukan mu.

YANZU YANZU: Alhaji Uba Zaki Ya Raba Kyautar Motoci Da KuɗaɗeA yayin da yake ganawa da masu zaben fidda gwani EXCO na ja...
28/12/2023

YANZU YANZU: Alhaji Uba Zaki Ya Raba Kyautar Motoci Da Kuɗaɗe

A yayin da yake ganawa da masu zaben fidda gwani EXCO na jam'iyyar APC a karamar hukumar Karu dake jihar Nasarawa Alhaji Uba Zaki Magajin Garin Shamaki, ya amsa kiran magoya baya don tsayawa takarar kujerar shugabancin karamar hukumar Karu.

Tashin farko yaba Ma'aji na APC jiha Alhaji Lirwanu kyautar mota tare da sakataren yada labarai Mr. Otaru na APC jihar Nasarawa kyautar mota, haka nan suma mahalarta taron ya ba su kyautar Naira Miliyan Ɗaya don su sha Ruwa.

Jim kadan da kammala jawabin sa a wajen taron shugaban jam'iyyar APC na Karu Uba Zaki ya bashi kyautar Naira dubu Ɗari, sai kuma shugabar Mata da ta samu Dubu Hamsin, daga karshe an ba ƴan Soshiyal Midiya Dubu ɗari biyar.

Kotun Koli Ta Bayyana Dan takarar PDP Davic Ombugadu na PDP ya lashe zaben Gwamnan Jahar NasarawaKotun sauraren kararrak...
02/10/2023

Kotun Koli Ta Bayyana Dan takarar PDP Davic Ombugadu na PDP ya lashe zaben Gwamnan Jahar Nasarawa

Kotun sauraren kararrakin zabe ta gwamna (GEPT) da ke zamanta a garin Lafia a jihar Nasarawa ta sauya sakamakon zaben ranar 18 ga watan Maris tare da bayyana David Ombugadu na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben.

Da take zartar da hukuncin kusan a ranar Litinin din da ta gabata, Kotun da ke karkashin Mai Shari’a Ezekiel Ajayi ta soke sakamakon da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana wanda ya ba Gwamna mai ci, Audu Alhaji Sule na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) nasara.


Karin bayani Daga baya....

Jama'a Mu Ceci Ran Kanwarmu Amirah.Yanzu Rayuwar Amirah Abdullahi ta Rataya A Wuyar mu Sakamakon Wani Mummunar hatsarin ...
16/09/2023

Jama'a Mu Ceci Ran Kanwarmu Amirah.

Yanzu Rayuwar Amirah Abdullahi ta Rataya A Wuyar mu Sakamakon Wani Mummunar hatsarin Babur da Ya Afku da Ita A Kafa.
Zamu Iya Ceto Rayuwar ta da Samar Mata da Wata Dama ta Samun Kyakkyawar Makoma, Muna Buƙatar taimakon ku cikin Gaggawa.

Amira Wadda ‘Yar Asalin Garin Keffi ne A Angwan Mada, da ke Karamar Hukumar Keffi Cikin Jahar Nasarawa,

Yanzu haka tana Nan Hasibitin Gwaunatin tarayya FMC Keffi, Kuma Likitoci sun ba da Dhawarar cewa ya Zama Dole A Yanke Jiki nan take don Gudun kada A sake samun matsala.

Zamu iya Baiwa Amirah damar samun Waraka, kar mu bari Burin Yarinyar nan ya ruguje saboda rashin kudi.

Kuna iya ba da Gudummawa ga;
Lambar Asusu: 1016702902
Account Name: We Care Bridge Builders Foundation.
Zenith Bank Plc.

Don ƙarin tambaya, tuntuɓi 08161444700
(Yar uwarta)

Zaku Iya (Share) tura Wannan Sako ga Wasu Domin Adace da taimakon da Ake Nima.

© .

Bana da Burin Auren Mai Kudi,Burina In samu Wanda zai Bani Kulawa Shine Abinda Nake Nima,Inji:: Halima Haruna.
04/08/2023

Bana da Burin Auren Mai Kudi,
Burina In samu Wanda zai Bani Kulawa Shine Abinda Nake Nima,

Inji:: Halima Haruna.

Takaitaccen tarihin Adamu Ɗan Maraya Jos.Dan Maraya Jos (an haife shi Adamu Wayya, 20 Disamba 1946 – 20 Yuni 2015) fitac...
15/07/2023

Takaitaccen tarihin Adamu Ɗan Maraya Jos.

Dan Maraya Jos (an haife shi Adamu Wayya, 20 Disamba 1946 – 20 Yuni 2015) fitaccen mawakin Hausa ne daga Jos, Najeriya. Ya shahara da salon wakokinsa na musamman wanda ya hada wakokin Hausa da jigogi da kayan kida na zamani.

An haifi Dan Maraya Jos a Sabon Gari, al’ummar Hausawa da s**a fi yawa a garin Jos na Jihar Filato a Najeriya. Ya girma a cikin iyali na kiɗa kuma ya fara yin wasa tun yana ƙarami. Kakansa ne ya zaburar da shi, wanda ya kasance mawakin gargajiya na Hausa, ya kuma koyi yin kida daban-daban da s**a hada da kora, lute, da ganguna.

A shekarun 1960, Dan Maraya Jos ya shahara da salon wakokinsa na musamman wanda ya hada jigogi da kayan kida na zamani cikin wakokin gargajiya na Hausa. Ya kasance daya daga cikin mawakan Hausa na farko da s**a fara amfani da gitar wajen wakarsa kuma wakokinsa s**an yi magana kan batutuwan da s**a shafi zamani kamar siyasa, zamantakewa, ilimi, kasuwanci da kuma tarbiyya.

Dan Maraya Jos ya shahara a duk fadin Najeriya da Afrika ta Yamma, kuma an rika kade wakokinsa a gidajen rediyo da wuraren taron jama’a. Ya fitar da wakoki da dama a tsawon rayuwarsa, wadanda s**a hada da "Malam Uban karatu," "Mai akwai da babu," "Dan adam mai wuyan gane hali" da "lebura" da dai sauransu.

Shi ma Dan Maraya Jos ya shahara da salon sawa na musamman, inda galibi yana sanye da kayan gargajiyar Hausa masu haske da jar hula. Ya kasance alama ce ta al’ada da al’adar Hausawa kuma mutane da yawa suna girmama shi saboda irin gudunmawar da ya bayar wajen kiyaye wakokin Hausa.

Dan Maraya Jos ya rasu ne a ranar 20 ga watan Yunin 2015 a birnin Jos na Najeriya yana da shekaru 68 a duniya. Wakokinsa da kade-kadensa na ci gaba da zaburar da mawakan da dama a Najeriya da ma wajenta, kuma ana tunawa da shi a matsayin daya daga cikin manyan mawakan Hausa na gargajiya.
Allah Yajikansa Allah Yayi Masa Rahma.

© .

SANARWA SANARWADon Allah idan kun san duk wanda ya yi ritaya a matsayin malami Makaranta A Shekarar 2009 da 2010 Ku Gaya...
15/07/2023

SANARWA SANARWA

Don Allah idan kun san duk wanda ya yi ritaya a matsayin malami Makaranta A Shekarar 2009 da 2010 Ku Gaya Masa Ya je Ofishin Fansho na Jihar Nassarawa, Don Karban Gratuity kafin 25th of August 2023.

Don Allah ku tura wannan sakon ga Yan Uwa, Kamar Yadda aka Gani.

© .

14/07/2023

Breaking News.
Bincike Ya Nuna Cewa za'a samu Cikin Shege Guda Dubu 700 a Wannan Shekarar ta 2023 a Najeriya😊

16/06/2023

EFCC Sun Gayyaci Ministocin Buhari Guda 8 Bisa Zargin Almundahana.
.

Kubi Rayuwa A Hankalitsohon Shugaban Majalisa Kenan A Zaune Hon Ahmad Lawal
14/06/2023

Kubi Rayuwa A Hankali

tsohon Shugaban Majalisa Kenan A Zaune Hon Ahmad Lawal

Innalillahi Wahinna Ilaihin Rajiun.Allah Yayiwa Hafiz Ibrahim Ahmad Rasuwa Yau Bayan Yayi Fama da Yar Gajeriyar Jinya,Da...
13/06/2023

Innalillahi Wahinna Ilaihin Rajiun.

Allah Yayiwa Hafiz Ibrahim Ahmad Rasuwa Yau Bayan Yayi Fama da Yar Gajeriyar Jinya,
Daga Bisani Allah Ya Dauki Abinsa Yau,

Ibrahim Ya Kasance Hafizin Alqur'ani ne Mai Girma, Kuma Mutum ne Mai Kula da Bin Allah da Riko da Sunnah Ako da Yaushe.

Za'a Gudanar da Jana'izar sa Yau A Garin Keffi Dake Jahar Nasarawa.

Muna Rokon Allah Yayi Masa Rahma.

.

EDUCATION BANK OR STUDENTS LOAN A TAKAICE...Dalibi ya samu admission a university har an fara registration shi kuma bash...
12/06/2023

EDUCATION BANK OR STUDENTS LOAN A TAKAICE...

Dalibi ya samu admission a university har an fara registration shi kuma bashi da kudi iyayensa basu dashi, maimakon ya hakura ko yaje gidan rediyo neman temako, Gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta samar da sabon tsarin da dalibi zai ranci kudaden da zai biya registration wadanda zai dinga biya a hankali har zuwa lokacin da zai fara aiki ko ya samu kudin biya..

Sannan bashin da zaa bawa dalibin ba mai ruwa bane, idan yaci bashin dubu dari to dubu dari zai biya koda kuwa a shekara goma ne...

Sabuwar dokar da shugaba Tinubu ya sanyawa hannu kenan...

.

Na Rantse Bazan Bar Son Zuciya Yayi Tasiri Kan Aiki Da Matakin Da Zan Dauka Ba ~Inji Asiwaju.
12/06/2023

Na Rantse Bazan Bar Son Zuciya Yayi Tasiri Kan Aiki Da Matakin Da Zan Dauka Ba ~Inji Asiwaju.

Shugaban Kasa Bola Tinubu Ya Dakatar  Godwin Emefiele, Gwaunan Babban Bankin Najeriya Central Bank of Nigeria (CBN).Ya K...
09/06/2023

Shugaban Kasa Bola Tinubu Ya Dakatar Godwin Emefiele, Gwaunan Babban Bankin Najeriya Central Bank of Nigeria (CBN).

Ya Kuke Kallon Wannan Mataki.

.

Dr. Mohammed Wakil El Kabir, ya tsallake rijiya da baya daga hannun wasu ‘yan bindiga A Keffi.Daga: David Dari.Dan takar...
23/05/2023

Dr. Mohammed Wakil El Kabir, ya tsallake rijiya da baya daga hannun wasu ‘yan bindiga A Keffi.

Daga: David Dari.

Dan takarar jam’iyyar New Nigerian People’s Party na jihar Nasarawa ta Yamma, NNPP, a zaben da aka kammala, Dr. Mohammed Wakil El Kabir, ya tsallake rijiya da baya daga hannun wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba, wadanda s**a kai farmaki gidansa da ke GRA Keffi a jihar Nasarawa ranar Juma’a. .

Dan siyasar wanda ya bayyana haka ga wakilinmu jim kadan bayan ya kai rahoton lamarin ga rundunar ‘yan sanda da ke karamar hukumar Keffi a jihar, ya bayyana lamarin a matsayin siyasa.

“Tabbas, na tsere wa mutuwa da kyar a jiya saboda ‘yan bindigar da ba a san ko su waye ba sun shigo da karfi kamar yadda ‘yan uwana da s**a hadu da su a lokacin da suke gudanar da ayyukansu s**a fada, kuma s**a yi barazanar kashe su, idan s**a kasa bayyana inda na ke.

An kuma shaida min cewa hudu daga cikin barayin da s**a kutsa cikin masaukina suna dauke da bindigogi kirar AK 47 guda uku da bindiga guda daya.

“Niyyarsu ta kasance gare ni ne saboda suna ta tambayar inda nake, amma matata ta gaya musu cewa na tafi wani taro, kuma ba su iya yin wani abu da ya wuce su sanya dukkan iyalina bindiga. Ina so in bayyana abin da ya faru dangane da wannan da cewa yana da wasu muhimman batutuwa guda biyu; daya na siyasa ne yayin da dayan kuma ba za a fada ba a yanzu, wanda na fi sani da shi,” El Kabir ya jaddada.

Da aka tambaye shi ko za a iya alakanta batun da ya ke yi gabanin zaben da ake yi a kotun, sai ya ce, “Ina fata haka, kuma a bayyane yake haka. Mu mutane ne masu ilimi kuma lokacin da irin wannan lamari ya faru, abu na farko da za a yi shi ne na kai rahoto ga 'yan sanda, wanda na yi ne don su fara bincike. Tabbas muna zargin wasu daga cikin 'yan kasuwanmu da 'yan siyasa.

“Kwana biyu da s**a wuce, an kai wa wani dan takarar majalisar jiha mai wakiltar mazabar Uke-Karshi hari mai suna Abdulrashed Haruna hari a gidansa kuma ana cikin haka aka harbe wani mutum daya har lahira yayin da wani kuma aka harbe a kafa.

"Hakika, ba shakka yawancin wadannan matsalolin da ke haifar da jingin siyasa kuma za mu binciki wannan batu da cikakken iko.

Sai dai jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa, PPRO, DSP Ramham Nansel, ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho cewa har zuwa lokacin da ake gabatar da wannan rahoto, har yanzu batun bai kai ga teburinsa ba.

NationPride ta kuma tattaro cewa dan takarar Sanatan ya shigar da kara a gaban kotun zabe yana kalubalantar ayyana Hon. Ahmed Aliyu Wadada a matsayin wanda ya lashe zaben da aka ce.

El Kabir dai yana kalubalantar sakamakon zaben ne a bisa watsi da tambarinsa da wasu gajarce a kan katin zabe na INEC.

.

An Kori Sanata Ishaku Abbo Daga Jami'yar APC,Kwanaki 46 kafin zaben 2023, wata babbar kotun Yola a jihar Adamawa a Ranar...
10/01/2023

An Kori Sanata Ishaku Abbo Daga Jami'yar APC,

Kwanaki 46 kafin zaben 2023, wata babbar kotun Yola a jihar Adamawa a Ranar Talata ta kori Sanata Ishaku Abbo A Matsayin Dan takarar Sanatan Adamawa ta Arewa a karkashin Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben 2023.

SIYASAR NIGERIA ta Rawaito cewa kotun da ke karkashin Mai shari’a Mohammed Danladi ta kori Sanata Abbo ne bisa hujjar korar sa daga jam’iyyar a karamar hukumar Mubi ta Arewa (LGA) ta Adamawa.

Mai shari’a Danladi ya bayyana cewa Sanatan da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na da nasaba da kudurin da majalisar zartarwa ta karamar hukumar Mubi ta Arewa ta yanke na korar shi daga jam’iyyar a ranar 7 ga watan Oktoba 2022.

Kotun ta kuma yi watsi da cewa Sanata Abbo ba shi da hurumin samun wani hakki ko wata gata da aka bai wa ‘yan jam’iyyar APC.

Ku tuna cewa a ranar 7 ga watan Oktoban 2022 ne shugaban karamar hukumar Mubi ta Arewa ya amince da korar Sanatan kamar yadda kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar ya bayar.

Kotun ta kuma hana jam’iyyar APC da Sanatan ke neman tazarce a karkashinta kar ta amince da shi a matsayin dan takararta, inda ta ce ba zai iya zama dan takarar jam’iyyar ba a zabe mai zuwa.

©By Ashimawy Salisu Keffi

.

A Abuja Nigeria Akesaida Wannan Biredin Duk ɗaya 8,000.Me za kuce.?
23/12/2022

A Abuja Nigeria Akesaida Wannan Biredin Duk ɗaya 8,000.

Me za kuce.?

Ancire Musa Isah Mustapha Agwai Daga Sarautar Uban Garin Lafia.Daga: Hauwa Muhammad.Majalisar Masarautar Lafia Barebari ...
21/11/2022

Ancire Musa Isah Mustapha Agwai Daga Sarautar Uban Garin Lafia.

Daga: Hauwa Muhammad.

Majalisar Masarautar Lafia Barebari Dake Nan Jihar Nasarawa ta kori Ubangari Lafia (Dan Marigayi Isa Mustapha Agwai)

Masarautar Lafia ta sauke Musa Isa Mustapha Agwai daga sarautar Ubangarin Lafiya.

Har yanzu dai babu wasu kwararan dalilai A Bayyane da ya Nuna Dalilin Sauke shi.

Yanda Aka Maye Gurbinsa Nan take Usman Isa Baba ya zama sabon Ubangarin Lafiya.

Har ya zuwa korar tasa Musa Isa Mustapha Agwai shi ne na uku a matsayi na sarauta a Masarautar.

Sanarwar da Mawallafin Masarautar Rayyanu Isa ya fitar ta ce Masarautar a zamanta na ranar 19 ga watan Nuwamba 2022 ta amince da tsige Musa Isa Mustapha Agwai daga mukamin Ubangarin Lafiya cikin gaggawa.

Idan Baku Mance ba A Shekara 2020 . ta Rawaito Maku Labarin da Katar dashi Uban Gari tun Farko Nadin shi Sabon Sarki,
Yanda Wasu ke Asashen Rashin yin Mubai'a Gashi Sabon Sarki Lafia Justice Sidi Bage, ne Ya Aifar da Dakatarwarsa a Wanchan Lokacin,

Amma A Yanzu Babu Wani Bayani Dake Nuna Dalilin Ciresa, Wakiliyarmu ta Garin Lafia Hauwa Muhammad ta Nimi tajin Bakin tsohon Uban Garin Lafia din Amma Akan Yaci tura.

FILIN RA'AYI
Masu Sauraran mu Ya Kuke Kallon Wannan Mataki da Masarautar Lafia Barebari da Dauka Akan Shi Musa Isah Mustapha Agwai din Hakan Yayi Dai-dai ko Yaya ?

© KESMONEWS24.

08/11/2022

indai Atiku musulmi ne to nima musulmi ne

~inji Obasanjo.

ZAN ƊAUKI NAUYI KARATUN ƳAN SOCIAL MEDIA NA GIDANA ZUWA UNIVERSITY HAR SAI SUN GAMA DA IKON ALLAH Ina kira da duk masu y...
08/11/2022

ZAN ƊAUKI NAUYI KARATUN ƳAN SOCIAL MEDIA NA GIDANA ZUWA UNIVERSITY HAR SAI SUN GAMA DA IKON ALLAH

Ina kira da duk masu yaɗa manufofina a kafar social media da kowa yaje ya nemi admission a University kafin nan da January ko After January domin samun ingantaccen rayuwa insha Allahu zan ɗauki nauyin ku har ku gama University yadda kuke son kuga rayuwata ta inganta insha Allahu kuma zaku zamo masu ingantacciyar rayuwa, kusani bazan karɓi kowane excuse ba, idan baka da paper mai kyau ga November/December ka tabbatar kayi sitting

Wanda baiyi secondary ba ya sanar dani don nema masa makarantar NCE kangare dake Bauchi

Kuma Insha Allahu kafin mu shiga zaɓe zan tabbatar na sama muku kasuwa tare da jari daidai ƙarfina domin dogaro da kanku duk wanda yake da Admission acikinku ya tura min domin yaje yabiya kudin makaranta tare sayan kayan shopping mai inganci batare da yunwa ta hanaka karatu ba

Kuyi hakuri bazan sake siya muku wayar hannu ba kokuma na taraku na baku na data da hulana, zanfi jin daɗi idan kuna University kuna yaɗa manufofina

Wannan saƙon ya shafi iya ƴan social media masu yaɗa manufofina

Duk wanda ya shirya ya turamin saƙo ta WhatsApp ko Facebook dm nawa

Ina godiya da tarayya daku na tsawon lokaci tare da hakuri da juna.

Mainene Ra'ayinku Kan Wannan Kyakyawar Manufa ta Malam Abbas Galadima.

.

17/09/2022

Jihar Nasarawa Sabuwa

28/07/2022

Bazamu Lamunci Ganin An Baiwa Wasu Yan Jam'iyar SDP Matsayi ba, A Karaman Hukumar Keffi.
Inji Matasan Jam'iyar APC na Keffi.

Injiniya Sule Ya Gargadi Masu Rike da Mukamin Siyasa Bisa Gwaunatinsa ko su Cigaba da Biyayya ga APC ko kuma Su Fice Gab...
25/07/2022

Injiniya Sule Ya Gargadi Masu Rike da Mukamin Siyasa Bisa Gwaunatinsa ko su Cigaba da Biyayya ga APC ko kuma Su Fice Gabanin Zaben 2023,

Daga:© Ashimawy Salisu Keffi

Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya Gargadi Masu Rike da Mukaman Siyasa Sama da 200 da su Kasance Masu Biyayya Ga Gwamnatinsa, da Kuma Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ko Kuma Suyi Murabus.

Injiniya Sule Ya yi Wannan Gargadin ne a Wata Ganawa da ya yi da Daukacin Masu Rike da Mukaman Siyasa, A Gidan Gwamnati A Ranar Litinin. A Cewar Gwamnan, duk da cewa ba shi da Ninyar Korar Kowa, Amma ya yi Kira ga Wadanda Abin Ya Shafa da su Sauya Salon tafiyarsu, su Kasance Masu Biyayya ga Gwamnatinsa ko Kuma su yi Murabus.
” Injiniya Sule, Ya Bayyana wasu daga Cikin Masu Rike da Mukaman Siyasa. Ba su Dauki Kansu A Matsayin Wani Bangare na Gwamnati ba, Suna ba da Amincinsu ga wasu a Wajen Gwamnati.” Abin da Mai Hankali da Mutunci Bazaiyi ba.

Gwauna Yace, Idan ba ni Biyayya ga Wani ba, Ba ni da Hakki Yiwa Wannan Mutumin Aiki ko Biyayya A Siyasa. Idan Baza Kayi Biyayyar Ga Gwamnati ba, Don Allah Ka Zama Mutum Ka yi Murabus,” in ji shi.
"
Gwamnan ya yi amfani da damar taron wajen tabo wasu muhimman batutuwan da s**a shafi jam’iyyar,

Hakazalika Injiniya Sule ya Bukaci Masu Rike da Mukaman Siyasa da su tabbatar sun Zaburar da Masu Kada kuri’a, A Yankunansu Daban-Daban Domin Cin Gajiyar Cigaba da Gudanar da rijistar Masu Kada kuri’a da Hukumar zabe mai Zaman Kanta ta kasa (INEC) ke yi da kuma yin rijistar Gagarumi.

Mafi Rinjayen ku ba maki zuwa ga al'ummarku Don Ganin an Gudanar da Wannan Aikin, Kun bar shi A Hannun 'Yan tsirarun Mutane da ke Aiki tukuru Don yin ta. Ina za ku samu masu kada kuri'a idan ba ku yi CVR ba." Ya tambaya.

Dangane da Kamfen din Siyasa da ke Gabatowa Gabanin Babban Zaben Gwamnan Ya Bayyana Cewa Kwamitin zai Zagaya Domin Samar da Dabaru da za a ba wa Wadanda aka Nada Aiki da su tabbatar da Nasarar Jam’iyyar A Matakin Kasa da Jaha da Yanki Baki Daya.
••
25/07/22

KALUBALEN TSARO: WAJIBI NE MU DAUKI YAKI DA MIYAGU In ji Engr A A Sule.®Daga: Daheeru Galadima Gwamna Jihar Nasarawa Eng...
01/07/2022

KALUBALEN TSARO: WAJIBI NE MU DAUKI YAKI DA MIYAGU In ji Engr A A Sule.

®Daga: Daheeru Galadima

Gwamna Jihar Nasarawa Engr A A Sule. Ya koka kan tabarbarewar tsaro a karamar hukumar Kokona da kewaye.
Gwamna Sule wanda ya ce Laifuffuka da aikata laifuka ba su da wani matsayi a jihar ya bukaci a kara Hadin Gwiwa tsakanin Hukumomin tsaro da Hukumomin farar hula da su kai farmaki ga masu aikata miyagun laifuka domin a tantance munanan ayyukansu.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wata ganawa da ya yi da shugabannin tsaro a fadar Abaga Toni da ke Garaku. Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da zage damtse da bayar da tallafi ga jami’an tsaro a jihar.

Gwamna Sule ya yi alkawarin gina titin Gurku - Dari da kuma hanyar Angwan Takwa - Moroa - Ninkoro a yankin domin samun sauki. Ya kuma yi alkawarin bayar da tallafin ababen hawa da kayan aiki ga jami’an tsaro nan take domin kara musu kwarin gwiwa da kwazo.

A nasa martanin, Maimartaba Abaga Toni, Lawrence Ayih, Ya Godewa Gwamna Sule Bisa irin soyayyar da yake yi wa al’ummar Kokona da kuma yadda a kullum yake daukar matakan tsaro don kare rayuka da dukiyoyin Al'umma.

Wadanda s**a halarci taron sun hada da Wakilan Runduna ta 177 Guards Brigade, NSCDC, DSS, ‘yan sanda da shugaban karamar hukumar Kokona Hon Awwalu Adamu da dai sauransu.

Write ✍️Keffi Social Media Organization.

Photo 📷 Engr A A Sule Mandate.

NASARAWA STATE ZATA KARBI GASAR KARATUN ALQUR'ANI NA KASA.®Daga: Hauwa'u Marafa Lafia.A Ci Gaba da Shirye-shiryen Gasar ...
01/07/2022

NASARAWA STATE ZATA KARBI GASAR KARATUN ALQUR'ANI NA KASA.

®Daga: Hauwa'u Marafa Lafia.

A Ci Gaba da Shirye-shiryen Gasar Karatun Alqur'ani ta kasa karo na Daya na Nana Asma'u na Dalibai Mata na Sakandare, Ko'odinetan jihar Nasarawa Wanda Kuma Shine na Kasa.

(Ustaz Aliyu Tahir) Yayi Karin Haske kan Matakin Shirye-shiryen. Ustaz Aliyu Tahir ya ce Wannan Gasar Mai Albarka da Za a yi a Rana Kun 5 Zuwa 11 ga Watan Satumba A Garin Keffi da ke Jihar Nasarawa, tana samun kulawa sosai da kuma irin taimakon da ake samu a Ciki da Wajen Jihar.

Ustaz Aliyu ya Kara da Cewa an tsara Duk Wani Shiri da ya Shafi Masauki, Wurin Karatu, Ciyarwa, Kiwon lafiya.

Haka Kuma; An yi tanadin Matakan tsaro don Mahalartar taron Jama'a da Yawa da za a Gudanar a Wannan Gasa Kuma Za a yi ta ne a Wani Yanki da ke da Sauƙin Shiga da Zirga-zirgar Jama'a.

Ya kuma jaddada shirye-shiryen ‘ya’ya Maza da Mata na jihar Nasarawa na Karbar Baki tare da ba su tabbacin Cewa Gasar za ta Kasance Daya daga Cikin Mafi kyawu kuma mafi Girman Kyautuka a Matakin Gasar Kasa da Kasa.

Iliyasu Alhaji Akilu Media and publicity, Nana Asma'u Foundation 1st Yuli 2022.

Karda Ku Kuskura Ku Zabi ATIKU Sakon Obasanjo Ga Yan Najeriya.Atiku Shine Ya Fara Haifar da Cin Hanci da Rashawa A Majal...
29/06/2022

Karda Ku Kuskura Ku Zabi ATIKU Sakon Obasanjo Ga Yan Najeriya.

Atiku Shine Ya Fara Haifar da Cin Hanci da Rashawa A Majalisar Sanatoci, A Shekarar 1999, A Lokacin ne Ya Baiwa Sanatoci Dala
$5,000 Domin A Sauke Shugaban Majalisa na Farko A tarihin Najeriya Mr Evan Enwerem,

Cewar Obasanjo A Cikin littafinsa Mai Suna (MY WATCH).

Shin Mainene Ra'ayin Ku ??

.

Keffi Social Media Organization.

Ministan Walwala da Jindadin na Kasar Ethiopia. Mr Genza Oduka Molu.Wani Fata Zakuyi Masa ?
27/06/2022

Ministan Walwala da Jindadin na Kasar Ethiopia. Mr Genza Oduka Molu.
Wani Fata Zakuyi Masa ?

Wani Fata Zakuyiwa Shugaban Jam'iyar APC na Kasa Sen Abdullahi Adamu.
25/06/2022

Wani Fata Zakuyiwa Shugaban Jam'iyar APC na Kasa Sen Abdullahi Adamu.

19/02/2022

Bikin Naɗin Gimbiya Rabi'atu Sa'idu Umar (Fulani) Garkuwar Matan Pindaga Jihar Gombe

Address

Abdu-Zanga Way
Keffi
4441

Opening Hours

Monday 08:00 - 17:00
Tuesday 00:02 - 17:00
Wednesday 10:00 - 17:00
Thursday 03:00 - 17:00

Telephone

2348148482056

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Rijiyar Labarai. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Rijiyar Labarai.:

Videos

Share


Other Media/News Companies in Keffi

Show All