08/10/2023
FG ta dakatar da N-Power, ta fara bincike.
Gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin N-Power.
"Ministar al'amuran jin kai da yaki da talauci, Betta Edu, ta sanar da dakatarwar yayin da take magana a wata hira da ta yi da gidan talabijin na TVC a ranar Asabar."
Edu ta ce akwai kura-kurai da dama a cikin shirin kuma zasu kaddamar da bincike kan yadda aka yi amfani da kudaden tun lokacin da aka fara shirin.
Ministan ta yi nuni da cewa, akwai wasu da s**a ci gajiyar tallafin da ake ba su alawus duk wata amma ba sa wurin aikinsu. Edu ta kuma ce ya k**ata wasu daga cikin wadanda s**a ci gajiyar shirin su fice daga shirin tun 2022 amma har yanzu suna kan biyan albashi.
Tace "Dole ne mu koma mu duba N-Power mu fahimci mene ne matsalolin don haka za mu dakatar da shirin a yanzu har sai an kammala binciken da ya dace kan yadda ake amfani da kudi a cikin shirin N-Power"
Ministan ta ce ya k**ata wasu daga cikin wadanda s**a ci gajiyar shirin su fice daga shirin tun 2022 amma har yanzu suna kan biyan albashi. Ta bayyana cewa ba a samun wasu daga cikin wadanda suke cin gajiyar tallafin a wuraren aikinsu amma suna sa ran samun alawus na wata-wata.
Ta kara da cewa Muna son sanin adadin mutanen dake asalin cin gajiyar acikin shirin a yanzu, mutum nawa suke bin bashi.
Kuma zamu sake fasalin N-Power gaba daya tare da fadada shi
Source: VANGUARD NEWS
https://www.vanguardngr.com/2023/10/fg-suspends-n-power-begins-investigation/amp/?fbclid=IwAR3V3gvV2AFYslpf4Ivl71jpWnGb-ubSgukZS1QffbQohXcVuFTh-tErqaw
The Federal Government has suspended N-Power program indefinitely.