Alkarrar Media

Alkarrar Media Domin yaɗa karantarwa Ahlin Gidan Annabta (as)

16/12/2023
12/08/2023
IMAM ALIYU ZAINUN ABIDIN.WASIKAR IMAM ZUWA GA ZUHURI Sak**akon munanar tarihin zuhuri a fada Imam Sajjad (a.s) ya rubuta...
29/05/2023

IMAM ALIYU ZAINUN ABIDIN.

WASIKAR IMAM ZUWA GA ZUHURI
Sak**akon munanar tarihin zuhuri a fada Imam Sajjad (a.s) ya rubuta zazzafar wasika mai nauyi kuma daidai wannan lokaci tana kunshe da fatan alheri da nasiha gareshi, ya zo cikin wasikar: "Allah ya karemu tareda da kai da ga fitina, ya kuma nesanta mu da ga shiga wuta baki daya. Haqiqa kana cikin wani hali da matsala duk wanda ya san halin da kake ciki ya k**ata ya tausaya maka kada kayi tsammanin cewa Allah zai karbi uzurinka, kuma kada kadauka zai yafe maka zunubabbanka sam-sam.
Allah ya yi alqawari a cikin littafin sa tsakaninsa da malamai , cewa su yi ma mutane bayanin gaskiya Ina matukar jin tsoron a samakon zunibbanka ranar gobe qiyama matsayinka ya zama daya tare da maha'inta, kuma sabida sak**akon hadin gwiwarka tare da azzalumai na yin yaki ya dawo gareka.

ka sauka da ga matsayinka da zalunce zaluncenka ka kasance tare da Tsarkaka mutane kirki. Ubangiji ya zabeka ya sanya ka da ga cikin mutanen da suke dauke da ilimin kur'ani ya kuma ajiye amanar ilimin addini gurinka sai dai cewa ka tozarta wannan ilimi, ubangiji…….

YADA HUKUNCE HUKUNCE DA TARBIYYA DA KYAWAWAN HALAYE
Wani bangare daban da ga sansannin gwagwarmayarsa da zalunci da kuma kawar da barna a zamaninsa, shi ne yada hukunce hukunce muslunci da bayyanar da bahasosin tarbiyya da kyawawan halaye, a wannan fage Imam ya taka babbar rawa da gudummawa da manya malamai sun yi mamakin wannan gudummawa tasa, alal misali babban Malami a duniyar shi'a Shaik Mufid ya rubuta cewa: Takai ga cewa ba'a san adadin malamai (Fakihai) na Ahlus sunna da su ka nakalci ilimi da ga gareshi ba, ya shahara an nakalci wa'azozi da addu'a da falaloli da Kur'ani da ga gareshi, wanda idan mu ka ce za mu yi sharhi dalla dalla zai kallafa ma na doguwar magana.

Samfuri da ga ta'alim da tarbiya da Aklak da aka nakalto da ga gareshi suna nan a sun wanzu a cikin littafin (Risalatul hukuk) saqon Haqqoqi wanda ya kunshi wazifofi daban-daban da suke wuyan mutum da ga wazifarsa cikin hallarar ubangijinsa da wazifarsa kankin kansa da alaqarsa da sauaran mutane, duka anyi bayaninsu a ciki, wadannan wazifofi adadinsu ya kai 50 Imam ya kawo su a dunkule da ga baya kuma ya bisu filla filla. Risalatul hukuk da malaman hadisi su ka nakaltota aka rubutata cikin litattafan hadisi an tsamota ita kadai dabba'ata an kuma tarjamata.

_Abdullahi Shuaibu Allamah.

IMAM SAJJAD A.S4) GWAGWARMAYARSA DA MALAMAN FADAR SARKI  Da ga  yanki mafi daukar hankali da shahara a ranyuwar Imamai s...
28/05/2023

IMAM SAJJAD A.S

4) GWAGWARMAYARSA DA MALAMAN FADAR SARKI

Da ga yanki mafi daukar hankali da shahara a ranyuwar Imamai shi ne gwagwarmayarsu da dauki ba dadi da malaman fada ina ma'ana muatne da suke mamaye wurin da basu cancanta da shi ba, waxanda ake kira, Fakihai malaman hadisi da tafsiri Kari'ai da Alkalai, shi ne mutanen da suke sarrafa kwakwalen muatne su sanya qarqashin ikon Azzaluman shugabanni da ga Abbasiya da Umayyawa domin karfafa mulkinsu, shi ne yadda suke bayar da gudummawa wajane taimakawa don mika (talakawa) su yi musu biyayya da sallama musu.

Babban samfuri a wannan gwagwarmaya shi ne rayuwar siyasa ta Imami na hudu (a.s) haqiqa ya yi xauki ba dadi da fitacce Malamin hadisin nan na fada wato [muhamnmad Ibn Muslim Zuhuri] da aka haifa 58 hijiri ya mutu 124 hijiri.

WANENE ZUHURI?

Zuhuri daya ne da ga cikin tabi'ai Faqihai a wancan zamanin, acikin rayuwar samar takarsa haqiqa ya yi almajiranta a hannun Imami na hudu ya kuma nakalci hadisai da riwayoyi masu tarin yawa da ga hallararsa sannan yana da ga cikin manyan malaman hahdisi a birnin Madina, ya kasance cikin jerin Fakihai bakwai a makarantar Ahlus sunna a wancan zamani, sannan ya riski mutane goma da ga sahabbai, haqiqa ya kasance da ga shahararrun magabata a wurinsu sunansa ya shahara a zauruka da matsugunan ilimi da fikhu a wancan zamani,20

Ya samu wani matsayi a zamanin Mulkin Banu Umayya wanda su ka bashi xaukaka ta musamman, ta yadda yakan kira mutane zuwaga Ita Hukumar ta Umayyawa, sai ya zamana wannan jin dadin na haduwa da Hukumar Banu Ummayya ya sanya shi zama makusancinsu, ya kasance yana yawan zuwa wajen khalifa Hisham bin Abdul Malik bin Marwan ko da yaushe, bayan shi sai ya cigaba da samun kusanci tare da 'ya'yan Walid, Sulaima da Yazid Hisham, duk wadannan (kalifofin Banu Umayya) ya samu kusanci dasu.

Zuhuri ya kasance an bashi matsayi na musamma wato babban malami na 'ya'yan Hihsam bin Abdul, ya zamana yana tare da Banu Umayyah ta yadda ya yi ta amfani da Hadisai wajen qarfafa mulkin Banu Umayyah, ko ya riqa kawo hadisai masu kishiyantar karantar war gidan Annabta (Banu Hashim) da canza matsayi ko falalar Imam Ali zuwaga wasu Khalifofi daban.

_Abdullahi Shuaibu Allamah

Me ya sa ƴan Shi’a suke haɗa zuriyar Muhammadu (S.a.w) a lokacin da suke yi masa salati, suna cewa: “Ya Ubangiji ka yi s...
25/02/2023

Me ya sa ƴan Shi’a suke haɗa zuriyar Muhammadu (S.a.w) a lokacin da suke yi masa salati, suna cewa: “Ya Ubangiji ka yi salati ga Muhammadu da alayensa”?

A fili yake cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya koyar da musulmi yin salati a gare shi. Yayin da ayar nan ta sauka: "Lallai Allah da Mala'ikunSa suna yin salati ga Annabi, Ya ku wadanda s**a yi imani ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama a gare shi." (33:50), Musulmi s**a tambayi Annabi, "Ta yaya za mu gaishe ka?"

"Kada ku yi min sallama ba cikakke yaba," Annabi ya amsa.

"To, ta yaya za mu gaishe ka?" s**a maimaita.

Ya ce: “Ka ce: Ya Ubangiji ka yi salati ga manzonka Muhammadu da alayensa.

Yin sallama ga zuriyar Muhammadu yana da matukar muhimmanci, har Shafi'i, a cikin shahararriyar wakarsa yana cewa:

"Ya ku zuriyar Manzonmu mai tsira da amincin Allah, son ku umarni ne da Allah ya yi umarni da shi a cikin Al'ƙur'ani, daga muhimmanci da ɗaukakar matsayinku ya isa ku ce duk wanda bai yi muku sallama ba, to bai yi salla ba".

1• Ibn Hajar, Al-Sawa'iq al-Muhriqah, littafi na 11, babi. 1, ku. 146; al-Durr al-Manthur, vol. 5; tafsirin aya ta 56 a cikin surar Ahzab, da malaman hadisai da mawallafin Sihah da Masanid (tassoshin hadisai) k**ar su AbdulRazzaq, Ibn Abi-Shaybah, Ahmad, al-Bukhari, Muslim, Abu-dawud. , al-Tirmidhi, al-Nasa'i, Ibn Majah, Ibn Mardawayh-duk sun kawo irin wadannan maganganu daga Ibn Ajrah, wanda shi kansa ya nakalto daga Annabi mai tsira da amincin Allah. [1] Ibn Hajar, Al-Sawa'iq al-Muhriqah, littafi na 11, shafi. 148; al-Shabrawi, al-Ithaf, p. 29; al-Hamzawi al-Maliki, Mashariq al-Anwar, p. 88; al-Zarqani, al-Mawahib, p. 119; Sabban, al-Is’af, shafi na 119.

H. Ɗan Sister Katsina.
25/February/2023 M.

SOYAYYAR MANZON ALLAH TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARESHI, NUNA SOYAYYA CE, GA ALLAH (SWT). Cewar Sheikh Yaƙub Y...
20/02/2023

SOYAYYAR MANZON ALLAH TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARESHI, NUNA SOYAYYA CE, GA ALLAH (SWT). Cewar Sheikh Yaƙub Yahaya Katsina.

____Hassan Abubakar Ahmad Ɗan Sister Katsina.

Manzon Allah (S.a.w) yana cewa; "kuso Allah (Swt) da ni'imomin da yake ciyar daku" ya baibayeku da ni'imomi kala-kala. Sannan ku soni saboda son da Allah yakeyi mani. Sannan Manzon Allah (S.a.w) ya umarcemu da mu Tarbiyyartar da 'ya'yanmu, Son Al'kur'ani, karatun Al'kur'ani, son 'ya'yansa, dashi kansa Annabin. Wannan umarce-umarce ne daban-daban, a wurare daban-daban a mu halli daban-daban.

A irin wannan Rana ta Mauludin Manzon Allah (S.a.w) wani nau'ine na nuna wilaya, da soyayya ga Manzon Allah (S.a.w), da irin wannan salo na bukukuwa. Biki ko shagali, ko wani abu mai k**a da haka. ɗabi'a ne a cikin ɗan Adam saboda ɗan Adam, tun a salin haliltar sa, Allah (Swt) ya halilceshi da nuna farin ciki a lokacin farin ciki, da nuna damuwa a lokacin damuwa.

Kuma ko wacce Al'umma a kwai hanyar ta da take bi tana nuna farin cikin ta, da murnar ta, a kwai kuma bukukuwa daban-daban. Ko da Musulunci yazo Manzon Allah (S.a.w) ya iske Mutane suna bukukuwa daban-daban, suna nuna murna daban-daban, ta fuskancin da ya shafi haihuwa ne, ko abun da ya shafi aure ne, ko abun da ya shafi zagayowar Shekera a kan wani abu, sai Musulunci ya yi ma abun ƙwasƙwarima a ka ɗorashi a kan dai-dai.

Bukukuwa ko a nan inda muka samu kan mu, zamu ga cewa, a kwai bukukuwa daban-daban da Mutanen daban-daban suke ta tayi. Ina faɗin wannan maganar ne, saboda a gurin waɗan su, Mutane waɗannan bukukuwan a gurin su, k**ar wani bakon abu ne, ko nace suna kallon shi a matsayin (Haramun) bidi'a ko wani abu mai k**a da haka. A halin sunna sunaji suna gani ba bikin da ba ayi. A yau muna Asabar 08/October/2022 M. To Ranar ɗaya ga watan anyi bikin kirkiro Nijeriya. Wanda kuma manya duka, sun yi tarayya a cikin wannan biki, har da ma masu Addini. Har da Malamai, har dawasu ma sun taka fareti, da sunan ƙungiyar su, ta Addini.

Amma Bai taɓa zama matsala ba, tare da cewa, ita Kasar an ƙirƙireta ba tare da Addini ba, ba an kirkireta ba saboda Musulmi ba, bama a ƙirƙireta ba saboda da ƴan ƙasa ɗin ba. Waɗanda S**a ƙirkƙieta sun ƙirƙiri ƙasar ne saboda buƙatar kansu kawai. Amma a haka zakaga cewa; "anyi irin waɗannan bukukuwa anyi tarayya, sunyi Murna, amma bai taɓa zama matsala ba". Abun da ke matsala nuna murna, da farin ciki da haihuwar Manzon Allah (S.a.w) shi ne Kawai matsala.

To, da yake al'amrin na Allah (Swt) ne, a kwai hannun Allah (Swt) a ciki abun, ba baya yakeyi ba, gaba yake ƙarawa. Kuma in sha Allahu Ta'ala wani nau'ine na salo, in sha Allahu ga Maulud Manzon Allah (S.a.w) ne za a samu (Sauyi a kasar nan insha Allah) ina tsammanin babu wanda bai gaji da halin da ake cikin ba. Ina tsammanin babu wanda bayason a samu sauyi, tunda a gwada tsarinrika daban-daban to, a gwada na Annabi Muhammad (S.a.w) mana.

Na'am nasan su ba zasu ce, a zo a gwada na Annabi ba. To, amma mu mun k**a hanya... Kuma in sha Allahu Ta'ala ga Maulud Manzon Allah (S.a.w) ne a wannan kasar za a samu Sauyi. In sha Allahu...

_____Malam Yaƙub Yahaya Katsina ya gabatar da wannan jawabin ne a ya yin rufe muzaharar Mauludin fiyyayan haliltar Muhammad (S.a.w) da ta guda a cikin jahar katsina.

H. Ɗan Sister Katsina
Update
20/February/2023 M.

HARAMUN NE A DAI-DAITA IMAM ALI DA WANI. Cewar Sheikh Yaƙub Yahaya Katsina.___Daga Hassan Abubakar Ahmad Magini Ɗan Sist...
05/02/2023

HARAMUN NE A DAI-DAITA IMAM ALI DA WANI. Cewar Sheikh Yaƙub Yahaya Katsina.

___Daga Hassan Abubakar Ahmad Magini Ɗan Sister Katsina.

Haramun ne A dai-daita Imamu Ali da wani Imamu Ali ba dai-dai yake da kowa ba. Haramun ne ya haramta sai dai in zakace waɗannan Mutanen da kake cewa; "baiɗaya suke da Imam Ali (A.s) sannan kuma sai ka dawo kace Annabi dasu baiɗaya suke". Tana yuyuwa da Annabi da Almajiranshi iri ɗayane?. To hakanan ma Imamu Aliyu da Almajiran Annabi k**ar sama da ƙasa ne, fiye ma da haka. Wannan ba cika baki bane, sannan kuma ba kaishi matsayin da Allah (Swt) bai kaishi bane dama matsayin sa ne.

Allah (Swt) yana cewa; "kace, masu suzo da 'ya'yansu kazo da 'ya'yanka sai a kaga Manzon Allah (S.a.w) yafito da Imamu Hassan Da Hussain (A.s) sai yafito da Sayyida Faɗimatu Azzahra (S.a)". Tare da cewa, akwai 'ya'yan Sahabbai akwai kuma Mata kuma shima yana da Matansa amma bai fito da ko ɗaya daga cikinsu ba. Kuma bai fito da 'ya'yan Sahabbansa ba, bai fito da danginsa na kurkusa ba, sai ya fito da Sayyida Fatima ita kaɗai. Wannan yasa Malamai s**a fahimci Ni'ana Sayyida Fatima Kenan. "Abna'ana" Hassan Da Hussaini. Wa'anfusna muzo da kanmu Wa'anfusakum kuzo da kanku.

Sai Annabi (S.a.w) Yazo da Ali (A.s), Manzon Allah (S.a.w) yana cewa; "Ali k**ar nine k**ar tsagin karane ko an ɓara Goro". To haka suke yanzu idan wani tace, akwai wani wanda yafi Ali bai ƙaryata wannan Ayar ba? Idan wani yace wani da Ali kunnen Doki suke to abunda yake cewa; "da Annabi da wancan kunne Doki suke". Kuga kenan ya ƙaryata Aya! Soboda maganar dai-daita Ali da wani batama taso ba. Manzon Allah (S.a.w) na cewa: "ya Ali ba wanda yasan Allah (Swt) yadda ya k**ata a sanshi dagani sai kai". Kuma ba wanda ya sanni daga Allah (Swt) sai kai, ba wanda ya sanka dagani sai Allah (Swt).

Ku kawo mana wani Mutum mai irin wannan a duk Duniya daga farkonta har ƙarshen ta, ku kawo wani Mutum mai irin wannan. Babu shi sannan kuma zakuce dai-dai yake da kowa.

____Sheikh Yaƙub Yahaya Katsina ya yi wannan jawabin ne a Shekarar 13/Rajab/1443 H. Wanda ya yi dai-dai da 15/February/203/22 M.

H. Ɗan Sister Katsina.
Update
14/Rajab/1444 H.
05/February/2023 M.

BAN CIKA SON IN KARE KAINA BA, KO INCE NI KAZA, KAZA BA. DA SAURAN SU. Cewar Sheikh Yaƙoub Yahaya Katsina.____Daga Hassa...
03/02/2023

BAN CIKA SON IN KARE KAINA BA, KO INCE NI KAZA, KAZA BA. DA SAURAN SU. Cewar Sheikh Yaƙoub Yahaya Katsina.

____Daga Hassan Abubakar Ahmad Ɗan Sister Katsina.

Mutane da yawa musamman in nayi magana, yanzu in nayi magana yau to itace kasuwar Social Media. To, amma muyi ma kanmu adalci, mu zama masu adalci. Kusan Shekera Arba'in (40) Muna wannan harka. Malam ko ƙidi da rawa aka koya mana mun iya wani abu ciki.

Ko ƙidi da rayawa ake koya mana a ciki ai mun iya wani abu. Bamuce mun iya komi da komi ba don bamu ne Malam (H) ɗin ba. Amma mun iya wani abu, kuma k**ar yadda Malam Mukhutar Sahabi, Allah (Swt) ya gaggauta bayyanarshi, yake cewa, "Ko kamun kura Malam (H) ya koya mana to, mun isa mu kamo Ɗan Kure." Kilama harda kurema mu kamoshi.

Amma sai kayi magana wani yaro bisa tafin hannunka yake, wani ma kai ka ɗaura auren mahaifiyarsa, da mahaifinshi. Ko kaci goron Mahaifiyarshi, ko kaje walimar Auren Mahaifiyarsa da Mahaifinsa. Yanzu Yana ganin baka iya ba. Bak**a san inda aka sa gaba ba.

Akwai adalci cikin wannan? Ba adalci. to, amma mu mun harbo "JIRGIN" nasu. Bawani Mujaddadi bawan Allah Musilihi, face yana da 'Hawarihiin' Manzon Allah (S.a.w) yana cewa, "duk wani Annabi yana da Hawariyawa". Duk wani Annabi yana da Hawariyawa. Ma'anar Hawariyawa, 'Zaɓaɓɓaɓu na kurkusa, masu fahimta, waɗanda sune idanun sauran Jamai'a. Ba wani Annabi face yana dasu, bawani Mujaddadi face yana dasu. To, amma abun da akeso ace anan Malam (H) baya dasu waɗanda s**a san inda aka dosa. Shi ka Ɗai Ne, in baya nan shikenan, ba kowa kuma. Kaga harka tazo karshe kenan? To shi ne, hadafin nasu kenan.

Can s**a nufa abun da ake son a samar kenan, a koya wa Mutane raina kowa! Kowa ba, bakin komi yake ba. "Duk abun da ake ba dai-dai yake ba, ko da ko dai-dai ne to, ba dai-dai bane". Saboda Target ɗin nasu Malam (H), sai ya zamana babu hannun dake dafa masa. Baida wanda yasa abun da ake, baida wanda yasan dai-dai, shiknan tunda dukanmu ba dauwama zamuyi ba, Ranar da ta Allah (Swt) ta kasance to, shiknan yanzu harka ta k**a gabanta.

Kowama ya k**a gabansa, tunda ba wanda ake saurare, ba wanda ake kimantawa, ba wanda ake ganin ya iya, ko yasani. To, shi ne 'Target' ɗin Jahiliya. Wallahi Tallahi, shi ne Target ɗin nasu, wannan kuma aikin Maƙiyane. Su ake mawa don suke da hadafin ba wani ɗan Harka nan dayake da wannan hadafin. Amma sun ɗauki ma'aikata cikinmu dayawa, wasu nayi sunsani, wasu nayi Basu sani ba.

To, shiknan nasha ta dubu na faɗa duk abun da za a faɗa a faɗa. Itace Gaskiyar anso ko anƙi,

______A Ranar Asabar 13/02/1444 H. 10/09/2022 M. A wajen Mu'utamar ɗin Tattaki. Na Shekerar.

H. Ɗan Sister Katsina.
Update 03/02/2023 M.

Abunda su Malam kullum suke cewa, ko suke ƙarfafawa shi ne wannan hadafin dai na tabbatar da Addini da tsamar da Mutane ...
30/01/2023

Abunda su Malam kullum suke cewa, ko suke ƙarfafawa shi ne wannan hadafin dai na tabbatar da Addini da tsamar da Mutane halin da s**a samu kansu aciiki.

Wannan hadafin yana nan tabbatacce kuma a kansa ake aiki. Saboda haka fatanmu Allah (Swt) ya cika wa Malam gurinsa. Kuma Allah (Swt) ya yi amfani damu wajen dafa wa Malam (H), ya barmu da su Malam Duniya da Lahira.

H. Ɗan Sister Katsina.
Monday 30/01/2023 M.

A HARKANCE  ƘARƘASHIN JAGORANCI SAYYID ZAKZAKY (H) YADDA AKE TAFIYA SHI NE, KU TASHI GARI YA WAYE. Cewar, Sheikh Yaƙub Y...
27/01/2023

A HARKANCE ƘARƘASHIN JAGORANCI SAYYID ZAKZAKY (H) YADDA AKE TAFIYA SHI NE, KU TASHI GARI YA WAYE. Cewar, Sheikh Yaƙub Yahaya Katsina.

___Daga Hassan Abubakar Ahmad Magini Ɗan Sister Katsina.

Aikin harkar Musulunci ƙarƙashin jagorancin Sayyid Ibrahim Yaƙub Al'zakzaky (H), da takeyi shi ne, ku tashi gari ya waye ma'ana; mu falka musan mi mukazo yi. Dayawa Mutane basu samu wannan gata ɗin ba, dayawan Mutane basusan mi ya kawosu wannan filin Duniya ɗin ba, ballantana mi zasuyi, ballantana Ina zasu tafi... Na'am susan cewa; "Mutane suna zuwa suna komawa ta hanyar haihuwa da hanyar Mutuwa". Amma mike faru? Ta k**aimai wannan sai wanda Allah (Swt) yema taufiƙi sai ya rikaji a jiki. Ko Kuma in ya samu mai faɗakar dashi...

Alhamdullihi mu munyi sa'a ta namu ɓangaren mai tayar damu bayan dogon baccin da mukeyi harma aka nuna mana cewa; "Akwai hadafi na ɗaiɗaiku akwai hadafi na Al'umma". Hadafi na ɗaiɗaiku shi ne, ya za ayi ka haɗu da Allah (Swt) salin alin, shi ne hadafi na ɗaiɗaiku. Da yunkurin Mutum na ƙoƙarinsa na halartar program ko kuma a yi dashi ya danganta da dai-dai gwargwadon fahimartsa da abunda yakeso wajen Allah (Swt). Dai-dai gwargwadon abunda yakeso a wajen Allah (Swt) da dai-dai da kumajinsa da jajircewarsa. Mutum mai so dayawa ko da yaushe za a iskeshi yana nan. Mai son Matasakaici zaizo jefi-jefi. Mai son ɗankaɗan za a kwana dayawa ba a ganshi ba.

Kaga abun ba wata ka'ida bane cewa; kowa sai yazo bane, mi kakeso wajen Allah (Swt) shi ne zakayi, shi zaisa kazo... Saboda abunda mukeyi ibada mukeyi, bautar Allah (Swt) mukeyi... Cikin Hadisin Manzon Allah (S.a.w) yana cewa; "Mutum bazai ɗaga kafarsa ba Ranar alƙiyama in aka mike sai an tambayeshi abubuwa guda huɗu (4) sai an tambayeshi: An'umurihi fima'abina, wa anshababihi fima'abina. Sannan wa'anmalihi min'aina'kasasdahu min'aina'ankasa. Sune abubuwa guda huɗu da za a tambayi Mutum, ya k**ata ace Mutum hakoran karɓa wannan tambayar yake kafin aje ga tambaya ta gaba...

akwai tambaya ta farko in an sanya Mutum ƙabari, ana sanya Mutum ƙabari Mutane zasu tashi su tafi subar wajen za ace mashi "Marrabuka"? Wamadinika, Wamannabiyuka, wamakitabatu, gasunan dai tambayoyi daban-daban. Galibi Mutane basuna hankoron karɓa waɗannan tambayoyi bane a cikin hidimominau na yau da kullum. Galibi suna ganin su Rayu ne... In dai an Samu rufin asiri, anyi Riga, anyi kaya, anci abinci, anyi gida, an auri kyawawan Mata, anse Motar Hawa, shiknan magana ta ƙare asiri ya gama rufuwa.

Na duniya kenan, to na Lahira kuma fa? To wannan shi ne Mutane basa tambayar kansu. to ɗan'uwa wanda ya Fahimci wannan harkar kiran da Malma ya yi shi ne wannan. Shi ne cewa; "kazo ka samu mafita a kashin kanka ba a rayuwar Duniya ba". Ita wannan harkar harkace tace ta ibada kuma ba Ranar da za a gamata sai Ranar da aka haɗu da Allah (Swt).

Hankoron harkar nan shi ne Mutane su farka su San ciwon kansu, susan su suwanene... Ina suke fuskanta, sannan su sadaukar wa Allah (Swt) komai dai-dai gwargwadon abunda zasu iya su saurari alƙawalin Allah (Swt) domin zai cikar alƙawalinsa ko damu ko da 'ya'yanmu.... Alhamdullihi ko bamunan muna da ladar farawa 'ya'ynmu na da ladar kammalawa.

_____Sheikh Yaƙub Yahaya Katsina ya yi wannan jawabin ne a yayin ganawa da ƴan uwa na Mani Local Government ta jahar Katsina. A Ranar Laraba 25/January/ 2023 M.

H. Ɗan Sister Katsina
25/January/2023 M.

MI YA SA ALI (A.S) ƊAN ABU-TALIB YA ZAMA MAGAJIN ANNABI (S.A.W)?___Daga Hassan Abubakar Ahmad Magini Ɗan Sister Katsina....
19/01/2023

MI YA SA ALI (A.S) ƊAN ABU-TALIB YA ZAMA MAGAJIN ANNABI (S.A.W)?

___Daga Hassan Abubakar Ahmad Magini Ɗan Sister Katsina.

Dangane da wafatin Manzon (S.a.w) kuwa, ƴan Shi’a sun ƙudurce cewa wannan matsayi ne na ƙwarai. Suna raya cewa matsayin imamanci, ta wani fanni, k**ar na Annabta ne. Magajin Annabi, k**ar yadda Annabi da kansa, ya k**ata Allah ya gabatar da shi. Haka nan tarihin Manzon Allah Muhammad (S.a) y shaida wannan ka’ida: Annabi da kansa ya nada Ali (a.s) a matsayin magajinsa a lokuta da dama, daga cikinsu akwai:

1. A farkon aikin Annabci, lokacin da Allah (Swt) ya wajabta wa Annabi mai tsira da amincin Allah ta hanyar ayar “kuma ka yi gargaɗi ga danginka makusanta” (26:214), sai ya yi musu jawabi yana cewa: “Wane ne zai taimake ku daga cikinku. ni da wannan al'amari in zama ɗan'uwana, mashawarcina, maƙiyina kuma magajina?" Ali (a.s) ne kawai ya amsa wannan kira na sama. Sai Annabi ya yi magana da danginsa ya yi bushara da cewa: “Wannan mutum (Ali) zai kasance ɗan’uwana ne kuma magajina ne a cikinku, sai ku saurare shi, ku bi shi.

2. A yakin Tabuka Annabi mai tsira da amincin Allah ya tambayi Ali cewa: “Shin ba ka so ka zama a gare ni k**ar yadda Haruna ya kasance ga Musa face ba wani Annabi a bayana?” Haruna shi ne magajin Annabi Musa, haka nan Ali zai zama magajin Annabi.

3. A shekara ta 10 bayan hijira, a lokacin da ya dawo daga hajjin ƙarshe zuwa Makka a wani kwari da ake kira Ghadir Khumm, a gaban dimbin jama'a, Annabi ya gabatar da Ali (a.s) a matsayin Jagoran Musulmi da Muminai. A farkon jawabinsa, Annabi ya tambayi mutane cewa, “Shin, ba ni da iko a kanku fiye da yadda kuke da ku a kan kanku?” Yayin da dukan mutanen da s**a taru a wurin s**a tabbatar da hakan, sai Annabi ya yi bushara da cewa: man kuntu mawlahu fa hadha ‘Aliyyun mawlahu”. Duk wanda na kasance shugaba, Ali zai zama ubangidansa daga yau. A fili yake cewa abin da Annabi ya faɗa da kalmar mawla (shugaba) shi ne iko da cikakken fifikon da yake da shi a kan muminai wanda ya tabbata ga Ali shi ma.

A wannan rana Hassan Ibn Thabit ya sanya waki'ar Ghadir na tarihi cikin waka da ke cewa: Annabinsu yana kiransu a ranar Ghadir Sai wani mai bushara ya sanya wawasi a cikin kunnen manzo. "Wanene ubangijinka kuma annabi?" Ya tambaya. S**a amsa, kuma babu jahilci s**a yi riya: “Allahnka ne ubangijinmu, kai kuma annabinmu ne har abada Kuma babu wani daga cikinmu da za ka samu mai adawa da shi har abada."

Sai ya ce: “Tashi kai Ali”. "Shugaba da Imam bayana na yarda da kai." "To Ali ne shugaban wadanda na kasance shugangijinsu". Kuma ina son ku mabiyansa gaskiya ku kasance bayansa. Ya Allah! Ka zama abokinsa. Sannan ya yi addu’a: “Kuma duk wanda ya bijire mashi kasance maƙiyansa.

Hadisin Ghadir na ɗaya daga cikin hadisai da s**a biyo baya waɗanda ba wai dukkan malaman Shi'a ba ne, har ma da na Ahlus-Sunnah kusan dari uku da sittin, waɗanda s**a kawo dari da goma daga cikin sahabban manzon Allah (S.a.w) a cikin jerin maruwaitan wannan hadisi. Haka nan kuma, manyan malaman musulmi ashirin da shida sun rubuta littafai daban-daban kan naɗe-naɗe da kuma yadda aka saukar da wannan hadisin. Misali, shahararren malamin tarihi na musulmi, Abu-Ja'afar Tabari ya rubuta littafai guda biyu akan wannan lamari. Littafin encyclopedic na Allamah Amini, al-Ghadir, ya ba da ƙarin bayani game da wannan.

(1) Tarikh al-Tabari, vol. 2 shafi na 62-63; al-Kamil fi al-Tarik, vol. 2, shafi na 40-41; Musnad Ahmad, vol. 1, ku. 111; Sharhin Nahj al-Balaghah na Ibn Abil-Hadid, juzu'i. 13, shafi na 210-212.

(2) Sirat Ibn Husham, juzu'i. 3, ku 520; Al-Sawa'iq al-Muhriqah, littafi na 9, babi na 2, shafi. 121.

(3) Kharazmi, Maliki, al-Manaqib, shafi na 80; Sibt Ibn al-Jawzi, the Hanafi, Tadhkirat al-Khawass, p. 20; al-Kanji, the Shafi’i, Kifayat al-Talib, p. 17.

(4) Misali duba littafin Al-Sawa'iq al-Muhriqah na Ibn Hajar. (Misira) littafi na 9, babi. 2.

H. Ɗan Sister Katsina.
26/Jimada Sani/1444 H.
19/January/2023 M.

MU A SALAL BA YAN NAN DUNIYA BANE MU YAN ALJANNA NE. Cewar  Sheikh Yaƙub Yahaya Katsina.___Daga Hassan Abubakar Ahmad Ɗa...
14/01/2023

MU A SALAL BA YAN NAN DUNIYA BANE MU YAN ALJANNA NE. Cewar Sheikh Yaƙub Yahaya Katsina.

___Daga Hassan Abubakar Ahmad Ɗan Sister Katsina.

"Mu a salal ba ƴan nan Duniya bane mu ƴan Aljanna ne, mu daga Aljanna ne muka taho muyi wata jarabawa mu koma" Saboda haka karda matsaloli sú da maiku, karda kace akwai wani abu ko a Mutu ko ayi Rai! Sai ka samu.

Abunda ke muhimmi shi ne kaga taya zaka koma cikin waɗancan bayin Allah da aka fiddosu daga Aljanna taya za ayi ka koma. Haka Imam Khumaini (Q.z) yake faɗa, yana cewa; "mu asalinmu ƴan Aljanna ne, daga Aljanna aka fito damu mu rubuta jarabawa mu koma". To hanƙoronka, ka maƙale ma wanda za ya yi maka Jagora ya mai daka inda kafito.

Shi ne matsalar ka, baka da wata matsala illa wannan kuma daga cikin abunda Allah (Swt) ya tanadamana daga cikin waɗannan hanyoyin, harda Azumi. Wanda yake sanya taƙawa, taƙawa shi ne lizimtar abunda Allah (Swt) yace, ayi da kuma barin abunda ya hana ayi, dai-dai gwargwado iyakar ikon Mutum. Wanda kuma Mutum bai iya yiba sai Allah (Swt) ya yi mashi uziri. In dai ya ga niyarsa da gaske abunda yakeyin ƙoƙarin hamɓakashi. Wato umarnin Allah (Swt).

A Ranar 30/Apr/2022M. Wanda ya yi dai-dai da 29/Ramadan/1443H. Sheikh Yaƙub Yahaya ya yi wannan jawabin a wajen buɗa bakin kwamitin ƴan kasu na Harka Musulunci ƙarƙashin jagorancin Sayyid Ibrahim Yaƙub Al'zakzaky (H) da s**a shirya.

H. Ɗan Sister Katsina.
Update 14/Jan/2023 M.

02/12/2022
01/12/2022

"Ba a tabbatar da gaskiya, sai da gaskiya. Ba a yin ƙarya don a tabbatar da gaskiya."

📸 Congratulations to Ahlulbayt (A) & Followers of Ahlulbayt (A) on the auspicious birth anniversary of   , Baqiyatullah ...
19/03/2022

📸 Congratulations to Ahlulbayt (A) & Followers of Ahlulbayt (A) on the auspicious birth anniversary of , Baqiyatullah Imam Mohammad Al-Mahdi (ajtfs)

O Master ! May Allah Hasten Your Reappearance.

"The Birth Anniversary Of The Promised Mahdi (May Allah Hasten His Reappearance) Is Indeed A Celebration For All Pure And Free Humans Of The World." -

19/03/2022

YAUMUL QA'IM ALMUNTAZAR💞
NISFU SHA'ABAN

17/03/2022

١١٨٨ سنة مِن الحُبّ و الانتظار ♥
المخلّص المهدِي عُمره الشرّيف ١١٨٨ سنة من الحُب والأمَل الموعوُد* 💙

Hadith🌙▫️▫️◻️◽🕋◽◻️▫️▫️Daga Nahjul Fasaha Qarfin Addu'ar Wanda Aka Zalunta:من نهج الفصاحة:اِتَّقُوا دَعْوَةَ الْمَظْلُومِ...
07/03/2022

Hadith🌙
▫️▫️◻️◽🕋◽◻️▫️▫️
Daga Nahjul Fasaha
Qarfin Addu'ar Wanda Aka Zalunta:

من نهج الفصاحة:
اِتَّقُوا دَعْوَةَ الْمَظْلُومِ؛ فَاِنَّها تَصْعَدُ اِلَى السَّمَاءِ كَاَنَّها شَرَارَةٌ.
```Avoid the prayer of the oppressed, for it ascends as a flame high to the sky.```
*KU GUJI ADDU'AR WANDA AKA ZALUNTA; LALLAI (ADDU'AR TASA) TANA HAWA SAMA KAMAR TARTSATSIN WUTA*

📖 نهج الفصاحة: الحديث ٦٠٧
Sayyed Kabiru Kano
+2348035172181
Facebook.com/pg/Sharifkbr

📚...✍️⭕⭕🌍6️⃣0️⃣7️⃣🤲🏻

Religion & Social lifestyle

Address

Katsina Ala

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Alkarrar Media posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share

Nearby media companies


Other Digital creator in Katsina Ala

Show All

You may also like