ARZ Tv

ARZ Tv Labarai cikin harshen Hausa.

24/05/2024
23/05/2024

Gwamnatin Zamfara za ta fara biyan mafi ƙarancin albashi dubu 30.

21/05/2024

YANZU YANZU: Tsofaffin Yansanda wayanda s**a ajiye aikinsu suna gudanar da zanga-zanga a gaban zauran majalissar tarayya akan rashin biyan su kuɗin Fanso ɗinsu.

21/05/2024

LABARI DA ƊUMI ƊUMIN SA: Yan bindiga sun kashe mutane 40 a garin Zuruk Komoani da ke jahar Plateu.

Garin Zuruk Kompani dai gari ne da ake haƙo ma’adanan ƙasa.

21/05/2024

Tsohon kyaftin din Super Eagles, Kanu Nwankwo, ya kai wa tsohon dan wasan Najeriya Tijjani Babangida ziyarar jaje bayan hatsarin mota da ya yi da iyalinsa, wanda ya yi sanadin mutuwar kaninsa da dansa.

~VOA Hausa

📷 X/Kanu Nwankwo

20/05/2024

Karim Khan ya tsokano sama da kara.

Daga Shafin Abubakar Umar Abubakar

Karim Khan shine babban alkalin kotun laifukan yaki ta ICC da take birnin Hague, Netherland, a yau za'a iya cewa ya kafa tarihi ta hanyar bayyana kudurinsa na mikawa alkalan kotun mujallar sammaci zuwa ga Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da Ministan tsaron Isra'ila Yoav Gallant da Shugaban Kungiya Hamas Isma'il Haniyye da Yahya Sinwar da kwamanda Muhammad Deif!

Tare da kasancewar kudurin kotun ta ICC cike yake da siyasa da kokarin daidaita azzalumai (Isra'ila) da wadanda ake zalunta tsawon zamani (Falastinawa) acikin laifi iri daya, da kawar da kai daga wasu manya-manyan tuhumce-tuhumce da suke kan Gwamnatin Netanyahu na kisan kare dangi (Genocide), da kuma kawar da kai game da abinda yake faruwa a West Bank tare da kasancewar akwai kararraki da aka jima da shigarwa a kotun tasa akan wannan al'amari, sai dai hakan bai fishsheshi ba daga gargadi da barazanar Gwamnatin Amurka, dama Sanatoci kusan 12 sun lashi takobin sai sun kai shi kasa tare da iyalansa idan har ya kuskura ya bayarda sammacin k**a Netanyahu, to yau ya kekasa kasa ya daki kirji ya bayyana aiwatar da hakan a zahiri.

Amurka wacce ta taimaka wajen ganin an sanya Putin acikin wadanda kotun ta bada sammacin cafkewa idan ya taka daya daga cikin kasashen da suke da yarjejeniya da kotun, itace kuma yau ta yiwa kotun tofin alatsine akan kokarin k**a Netanyahu.

Ga wanda yake bibiyar yakin Isra'ila akan Mutanen Gazza, zai shaida cewa tabbas wannan kudurin na kotu yayi matukar yin rangwame game da adadin Mutanen da ya k**ata ace an k**a, ina Ministan cikin gida Itamar Ben-Gvir, ina Ministan kudi Smotrich? Kusan su sunfi kowa ma miyagun kalamai da kira zuwa ga yiwa Falastinawa kisan kare dangi.

20/05/2024

YANZU YANZU: Kotun Hukunta Masu Aikata Mugayen Laifuka (International Criminal Court) ta Duniya ta ba da izinin K**a Prime Finistan Israil Netanyahu. Kotun ta bada izinin k**a shine abisa ta’addancin da ya hauka a Gaza.

20/05/2024

Kashi 80 cikin ɗari na matsalar Najeriya Gwamnoni ne.

~ Prof Usman Yusuf.

Shin ya ku ke ganin wannan maganar?

20/05/2024

SHUGABAN ƘASAR IRAN YA RASU.

A jiya ne jirgin shugaban ƙasar Iran Ra’is ya yi hatsari tare da ministan harkokin waje Hussein Amir da wasu kuma mutune 9. Rohoto ya tabbtar da cewa duka fasinjojin jirgin babu wanda ya yi rai.

19/05/2024

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ta buɗe gidan Radiyo.

19/05/2024

Da zuwan mu a cikin gwamnati mun magance matsalar tsaron jahar Katsina da kaso 70 cikin ɗari - Gwamna Dikko Radda

18/05/2024

Shugaba Tinubu ya ruguza Najeriya, in ji Babacir Lawal

Tsohon Sakataren gwamnatin Najeriya, Babacir David Lawal ya bayyana cewar kasar ta ruguje a karkashin gwamnatin Bola Tinubu saboda halin da ta samu kan ta a yau.

Lawal yace matsalolin da s**a kai ga kasar shiga irin wannan mummunar yanayi sun fara ne tun ranar da shugaban kasa Tinubu ya sanar da janye tallafin man fetur, ba tare da tattaunawa da majalisar ministocin sa ba a kan illar dake iya biyo baya ba.

Tsohon Sakataren yace wannan mataki ya sanya harkokin sufuri sun yi tashin goran zabbi da kuma shafar kusan kowanne fanni na rayuwa ga talakawa da ma masu hanu da shuni.

Lawal yace a lokacin yana sayen mota guda na abincin dabbobi a kan kudi naira dubu 270, amma da cire tallafin sai farashin ya yi tashin da ba zai iya saye ba, saboda yadda kudin sufurin da yake biya kawai ya kai kusan naira miliyan guda.

Tsohon jami'in ya shaidawa Jaridar Daily Trust cewar a makon jiya ya sayi motocin aikin noma guda 3 a Kano, amma kudin daukar su kawai ya kai naira miliyan 3, saboda irin wannan yanayi da jama'a s**a samu kan su a Najeriya.

Babacir wanda ke cikin 'yayan jam'iyyar APC da s**a bijire mata saboda tsayar da Bola Tinubu da Kashim Shettima da s**a fito daga addini guda, yace 'yan Najeriya na cikin mawuyacin hali a karkashin wannan gwamnatin dake cika shekara guda a karagar mulki.

Majiya ~ RFI Hausa

18/05/2024

Kwamitin malaman musulunci a Najeriya ya goyi bayan auren marayu a Neja

Batun auren marayun ya ja hankali sosai a wannan makonImage caption: Batun auren marayun ya ja hankali sosai a wannan makon

Kwamitin malaman addinin musulunci na Najeriya ya goyi bayan auren marayu 100 da kakakin majalisar dokokin jihar Neja ya ƙuduri aniyar ɗaukar nauyi.

Cikin wata takarda da kwamitin ya fitar, mai ɗauke da sa hannun shugaban kwamitin, Malam Aminu Inuwa Muhammad da sakatarensa, Engr Basheer Adamu Aliyu, sun ce abin da kakakin majalisar ke shirin yi abin a yaba ne, ba na kushewa ba.

Kwamitin ya ce duba da matsalar tsaro da matsin tattalin arziki da wasu yankunan arewacin Najeriya ke fuskanta, ɗaukar nauyin aure wani nau'i ne na tallafa wa marasa ƙarfi

''A shekarun baya-bayan nan jihar Neja da wasu jihohin arewa maso yammacin Najeriya na fama da matsalar tsaro da 'yan bindiga masu satar mutane domin neman kuɗin fansa, lamarin da ya shafi rayuwar mutanen yankin, iyalai da dama sun rasa iyayensu, kan haka ne shugabannin al'ummar yankin ke ƙoƙarin magance musu wahalhalun da suke fuskanta ta ɓangarori daban-daban, k**ar yadda kakakin majalisar dokokin Neja ya yi yunƙurin yi'', in ji sanarwar.

''A matsayinmu na musulmi muna ƙoƙarin yin abubuwa k**ar yadda shari'a ta tanadar, su kansu 'yan matan sun zaɓi su yi aure, a maimakon su faɗa karuwanci ko a yi safararsu zuwa Turai k**ar yadda wasu da ba su da hali ke yi don rage wa kansu matsin rayuwa'', k**ar yadda sanarwar ta yi bayani.

Kwamitin malaman addinin musuluncin ya ce abin da ministar ta yi bai dace ba.

''Abin da minista ta yi nuna wariya ne da wargaza abu mai kyau da rashin ƙwarewar aiki da kuma ƙabilanci, domin kundin tsarin mulkin Najeriya ya amince da 'yancin addinin tare da amincewa ta shari'ar musulunci da ta amince da aure'', in ji sanarwar.

A makon da ya gabata ne dai ministar mata ta Najeriya ta kai ƙarar kakakin majalisar dokokin jihar Nejan zuwa ga babban sifeton 'yan sandan ƙasar bisa zarginsa da tilasta aurar da 'yan matan da ta ce masu ƙananan shekaru ne.

Ministar ta ce idan taimakon 'yan matan kakakin majalisar ke son yi, me zai hana ya ɗauki nauyin karatunsu, ko ya basu jari domin su tsaya da ƙafafunsu, a maimakon yi musu aure.

To sai dai ɗan majalisar ya kare matakin da cewa taimakon yaran ya yi, yana mai cewa galibinsu marayu ne waɗansa s**a rasa iyayensu sak**akon matsalar tsaro da wasu sassan jihar ke fuskanta.

Majiya~ BBC Hausa

Address

Justice Dahiru, Farm Centre
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when ARZ Tv posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share

Category

Nearby media companies


Other TV Channels in Kano

Show All