ZTG Hausa Tv

ZTG Hausa Tv Tashar Z.T.G Hausa t.v Tashace wacce ke gudanar da Shirye shiryenta, A kafafen Sadarwa da Harshen Hausa.

Yau Shekara 123 Da Haihuwar Maulana Sheikh Ibrahim INyass (R.A)An Haifi Sheikh Ibrahim INyass A Wata Alqarya Da Ake Kira...
28/02/2023

Yau Shekara 123 Da Haihuwar Maulana Sheikh Ibrahim INyass (R.A)

An Haifi Sheikh Ibrahim INyass A Wata Alqarya Da Ake Kira Daiba Dake Cikin Kasar Senegal 🇸🇳 Bayan Sallar La’asar Ranar Alkhamis 8/Nov/1900 Wanda Yayi Dai-dai da 15/Rajab 1318Ah, Ya Tashi Karkashin kulawar Mahaifinsa Inda Ya Haddace Alqur'Ani da wasu fannona na Ilimi, shehu yazama cikakken malami a kowanne Fanni Koh Da Yakai Shekara Ishirin Da Daya A Duniya,

Shehu ya fara rubuta Littafin Ruhul -Adab yana dan shekaru ashirin da daya, ya rubuta Littafi 75 Duka a rayuwar sa, shehu ya kare a cikin soyayyar ma’aiki Tare da Tsamo Halitta daga 'bata zuwa shiriya, shehu ya watsa Addini a fad'in duniya sannan ya shigar da mutane da dama a Darikar Tijjaniyya, shehu yayi Tarbiyyar malamai da yawa har s**ayi Usuli s**a sadu da Allah.

Shehu yakarar da rayuwar sa cikin hidima ga Allah da manzon Allah, Shehu yayi Qafatii 26/July 1975 A Asibitin Thomas London Dake UK 🇬🇧

Allah yakara masa karamar barzahu, Allah ya jaddada Rahma gareshi, Allah yabamu Albarkarsu Alfarmar manzon allah S A W

Aisha Abubakar Hussain daga Dorayi Quarters a Kano ta samu matsayi na 2 a haddar Alkur’ani ta duniya da aka gudanar a bi...
20/10/2022

Aisha Abubakar Hussain daga Dorayi Quarters a Kano ta samu matsayi na 2
a haddar Alkur’ani ta duniya da aka gudanar a birnin Dubai na kasar UAE.

Kano tana kan gaba wajan son Ma’aiki (SAW) son Sahabbansa da son Ahlin gidansa. Da Kuma karatun Alqur’ani Haddarsa da koyar dashi a cikin zauruku da tsangayu, makarantun Islamiyya da makarantun zamani.

Allah ya karawa malamanmu ‘yayanmu albarka. Amin.

Kaptain Ibrahim Traoré Kenan, ɗan kimanin shekaru 26 a duniya wanda ya jagoranci kifar da gwamnatin Soja a Burkina faso....
02/10/2022

Kaptain Ibrahim Traoré Kenan, ɗan kimanin shekaru 26 a duniya wanda ya jagoranci kifar da gwamnatin Soja a Burkina faso.

To saidai ya zuwa yanzu abinda ba'a sani ba shine, shin yana wane bangare ne ? Yana tare da 🇫🇷 ko kuwa yana tare da Russia 🇷🇺 wacce ke yiwa ƙasashen Afrika ɗauki daya dai ?

Duk Musulmin daya je aikin hajji to yayi Maulidi- "Inji Sheikh Dahiru Bauchi.Mauludi Umarnin Allah ( S.W.T.) ne- Sheikh ...
01/10/2022

Duk Musulmin daya je aikin hajji to yayi Maulidi- "Inji Sheikh Dahiru Bauchi.

Mauludi Umarnin Allah ( S.W.T.) ne- Sheikh Dahiru Bauchi...

Sheikh Dahiru Usman Bauchi yace, "Idan ka ji Mutum Yana Sukar Maulidi To Ka Ce Masa; ai Maulidi Iri Biyu Ne.

A cikin zantukan Babban Malamin, ya Cigaba da cewa; akwai Mulidi Na Zamani Wato Watan Rabi'ul Auwal, a Watan Bature Kuma a afrilu Wannan Shi Ne Maulidin zamani, bisani Akwai Kuma Malidi na Makan i(Wuri) Wato Makkah da Madina.

Shehin Ya Ci Gaba Da Cewa; Idan Mutum Ya Samu Kudin Zuwa Hajji Zai Tafi Dolensa, Shin Anan Waye Ya 'Kra Shi?? Aka Ce; Allah (S.W.T),

Don Haka Duk Wanda Ya Tafi Makkah da Madina to ya tafi Mauludin Manzon Allah (S.A.W) Ne Na Makani, inji Shi babban Malamin.

Har walayau, acikin bayanan babban Malamin, yaka da baki inda yake cewa; Zai je ya ga Inda Aka Haifi Annahi (S.A.W), Ya Ga Masallacinsa, Ya Ga Gidansa ya ga Ababen Da Aannbi (S.A.W) Yayi Rayuwa Da Su, Koba komai ya tuna da Annabi Kuma hakan Shima maulidi ne.

A karshe Jagoran Mabiya darikar Tijjaniyya, ya karkare da fashin baki Kan Haka, don Haka Kenan Dole Ne Musulmi Yayi Maulidi ko na Makani Wato Zuwa Makka da Madina, Ko Na Zamani 'Din Wato Watan Rabi'ul Auwal.

Manyan Jami'an 'Yan Sanda 10 da s**a fi cin hanci a Afirka. 1. Rundunar Yansandan Najeriya 🇳🇬 2. Dr Congo Police Force 🇨...
30/09/2022

Manyan Jami'an 'Yan Sanda 10 da s**a fi cin hanci a Afirka.

1. Rundunar Yansandan Najeriya 🇳🇬
2. Dr Congo Police Force 🇨🇩
3. Rundunar 'yan sandan Kenya 🇰🇪
4. Rundunar 'yan sandan Uganda 🇺🇬
5. Rundunar 'yan sandan Mozambique 🇲🇿
6. Rundunar 'yan sandan Kamaru 🇨🇲
7. Rundunar 'yan sandan Saliyo 🇸🇱
8. Rundunar 'Yan sandan Habasha 🇪🇹
9. Rundunar 'yan sandan Madagascar 🇲🇬
10. Rundunar 'Yan sandan Zambiya 🇿🇲

Source - Transparency International

Yadda ake girbin auduga a arewacin Syria.
25/09/2022

Yadda ake girbin auduga a arewacin Syria.

Qasar Iran Kafin Islamic revolution da bayan...📹photos.
25/09/2022

Qasar Iran Kafin Islamic revolution da bayan...
📹photos.

Africa's Most Spoken Local Languages1. KiSwahili (200 million speakers)2. Hausa (120 million speakers)3. Amharic (57 mil...
21/09/2022

Africa's Most Spoken Local Languages

1. KiSwahili (200 million speakers)

2. Hausa (120 million speakers)

3. Amharic (57 million speakers)

4. Yoruba (50 million speakers)

5. Igbo (45 million speakers)

6. Fulani (41.6 million speakers)

7. Oromo (37.4 million speakers)

8. Berber (32 million speakers)

9. IsiZulu (28 million speakers)

10. Malagasy (20 million speakers)

Credit: Africa facts zone

Hadarin mutuwa don soyayya A Madagascar, matan glKabilar Betsileo ba sa neman kyawu ko kuɗi.  Suna Neman Jarumta da ƙarf...
21/09/2022

Hadarin mutuwa don soyayya

A Madagascar, matan glKabilar Betsileo ba sa neman kyawu ko kuɗi. Suna Neman Jarumta da ƙarfin zuciya.

Shekaru aru-aru, mazan Betsileo sun karbi bakuncin gasar kokawa ta “Savika” wato kokawa da bijimi.

Maza masu neman soyayya suna nuna jarumtaka da karfinsu ta hanyar kokawa da bijimai domin su mallaki zukatan mata.

Babbar kasa a Afirka da Ingila ta yi wa mulkin mallaka ita ce Najeriya.  Babbar ƙasar da Ingila ta yi wa mulkin mallaka ...
17/09/2022

Babbar kasa a Afirka da Ingila ta yi wa mulkin mallaka ita ce Najeriya.

Babbar ƙasar da Ingila ta yi wa mulkin mallaka a Asiya ita ce Indiya (wacce ta ƙunshi Pakistan da Bangladesh na yanzu). Lokacin da Birtaniya ta shigo Najeriya da Indiya, kamar sauran kasashen da s**a yi wa mulkin mallaka, sun kawo fasaharsu, addininsu (Kiristanci), da al'adunsu: sunaye, sutura, abinci, harshe, da sauransu.

A gefe guda kuma, Najeriya ta rungumi addinin Burtaniya, da al'adun Burtaniya - sunaye, sutura, abinci, da harshe - amma sun ƙi Amfani fasahar Burtaniya.

Bambance-bambancen da ke tsakanin ’yan Najeriya da Indiyawa shi ne, yayin da Indiya ke alfahari da al’adunta, Nijeriya ba ta da alfahari da abubuwan da ta gada, lamarin da ya shafi kishin kasa na ‘yan Nijeriya da ci gabanmu a matsayin kasa daya. Kafin zuwan Kiristanci Larabawa sun shigo da Musulunci ta Arewa ta Najeriya. Musulunci ya kuma shafe yawancin al'adun Arewacin Najeriya. A yau Arewa tana da kotunan Shari’a na musulunci Amma Babu kotunan gargajiya a kuduncin kasar.

Don haka tun daga Arewa har zuwa Kudancin Najeriya, Yammacin Duniya da Gabashin Duniya sun tsara rayuwarmu ta zama irin tasu kuma mun yi asarar da yawa ta yadda muka manta da al'adumu .

Gaskiyar baƙin ciki game da Afirka da aka nuna a taswirar duniya. Idan muka kalli taswirar duniya, kasashe kamar Kanada,...
17/09/2022

Gaskiyar baƙin ciki game da Afirka da aka nuna a taswirar duniya.

Idan muka kalli taswirar duniya, kasashe kamar Kanada, Amurka, Greenland, Rasha da sauransu. suna da girma sosai, kuma a matsayinmu na mutane muna samun ra'ayin kai tsaye: Girman ƙasa shike nuna mana ƙarfinta.

An koya muna a makaranta shi ne, duk wannan karya ce kuma taswirar duniya ba daidai ba ce. Idan muma kalli Greenland, tana da girma kamar nahiyar Afirka. A hakikanin gaskiya, Afirka ta fita girma sau 14.

Mutanen da s**a zana taswira a lokacin mulkin mallaka (shekaru 500 da s**a gabata waɗanda har yanzu ana amfani da su a wannan zamani) da gangan sun sanya Afirka ta zama Mafi KANKANTA da sauran nahiyoyi yayin da a zahiri ita ce mafi girma tare da Asiya.
Wannan ya kasance wata hanya ce ta juya tunanin mutane musamman 'yan Afirka da suyi ta tunanin cewa Turawa da Amurkawa sun fisu.

Nelson Mandela ya ba da lambar yabo ta KORA ga Micheal Jackson a Afirka ta Kudu a cikin Satumba 1999. Michael Jackson ya...
17/09/2022

Nelson Mandela ya ba da lambar yabo ta KORA ga Micheal Jackson a Afirka ta Kudu a cikin Satumba 1999.

Michael Jackson ya ba da gudummawar R1 miliyan, wanda ya kasance dala 163,000 sannan ga asusun tallafawa yara na Nelson Mandela.

Abubuwa 5 game da Lagos, Nigeria 1. Legas tana da mutane kusan miliyan 6300 2. An kiyasta GDPn Legas ya kai dala biliyan...
17/09/2022

Abubuwa 5 game da Lagos, Nigeria

1. Legas tana da mutane kusan miliyan 6300
2. An kiyasta GDPn Legas ya kai dala biliyan 145.141.
3. GDPn Legas ya kai kashi 26.7% na jimillar GDPn Najeriya
4. Yawan jama'a kusan miliyan 30
5. Lagos gida ce ga kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya [NSE]

Wata mata ta kai mijinta kara kotu a raba aurensu – saboda yayi yunkurin bude mata Nikaf ya kalli fuskarta  Wata mata ‘y...
17/09/2022

Wata mata ta kai mijinta kara kotu a raba aurensu – saboda yayi yunkurin bude mata Nikaf ya kalli fuskarta



Wata mata ‘yar kasar Saudiyya ‘yar shekara 50 ta kai karar mijin ta a kotu tana neman a raba aurensu saboda mijin nata ya bude mayafinta (Nikaf) a lokacin da take cikin barci domin ya kalli fuskarta.

Majiyar Taskar Labarai ta ruwaito tsawon shekaru 30 da aurensu, amma matar ba ta taba nuna fuskarta ga mijin nata ba, kamar yadda al'adar kauyensu a garin "Khamis Mushat" ta ke a kasar Saudiyya.

Taskar Labarai ta ruwaito a wannan al'adar miji baya ganin fuskar matarsa dole ne ta kasance a cikin nikabi a koda yaushe, "Saboda haka a karshe dai dole mijin ya nemi gafararta, ya yi alkawarin ba zai sake yin haka ba" a cewar kafar yada labarai ta NBC



https://www.facebook.com/100532736151658/posts/104463262425272/?app=fbl

16/09/2022

Ku kalli wannan Bidiyon kusha Mamaki😁😝




Bakar Fatan Dayake Zaune A Spain Ba Bisa Ka'ida BaJIBRIL Yana Zaune ba bisa ka'ida ba a birnin Valencia na kasar Spain. ...
16/09/2022

Bakar Fatan Dayake Zaune A Spain Ba Bisa Ka'ida Ba
JIBRIL Yana Zaune ba bisa ka'ida ba a birnin Valencia na kasar Spain. Ya tsinci Ambulan Dauke Da euro €4,250 kwatankwacin Naira N1,843,546.73 Kuma ya mayar da ambulan din.

Bayan sun tambaye shi takardunsa na shaidar zama sun gano cewa ba shi da katin zama da ke nuna cewa yana zaune a Spain bisa doka, don haka Basu Duba Kyakykyawar zuciyar sa ba s**a kore shi.

Muyi aiki tukuru domin sake Gina afirka da samun rayuwa ingantacciya.

Address


Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when ZTG Hausa Tv posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Shortcuts

  • Address
  • Alerts
  • Videos
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share