Na'ebtv

Na'ebtv Nae'ebTV, Hausa Online Television that brings You News and Current Affairs across Nigeria and Africa at large.

Labaran Safiyar Laraba 5 ga watan Augusta 2020.An sami karin mutane 304 wadanda s**a kamu da Coronavirus a Najeriya, jim...
05/08/2020

Labaran Safiyar Laraba 5 ga watan Augusta 2020.

An sami karin mutane 304 wadanda s**a kamu da Coronavirus a Najeriya, jimilla 44,433.

Gwamnonin Najeriya za su gudanar da wani taro a yau don tattaunawa kan matsalolin tsaro.

Gwamnatin jihar Jigawa ta umurci dukkanin ma'aikatan jihar su koma bakin aiki a yau.

'Yan kasuwa na son kara farashin litar man fetur zuwa N150 a cikin wannan wata ta Agusta.

Gwamnatin tarayya ta yi wa dokar kalaman kiyayya gyaran fuska, inda za a ci tarar wanda ya yi Naira milyan 5.

Gwamna El-Rufai na jihar Kaduna ya ce cikin shekaru 5 sun kashe Naira bilyan 16 kan harkar tsaro.

Gwamnan jihar Kano, Ganduje ya samu lambar yabo kan yaki da cutar Covid-19 daga kasar Senegal.

Shugaba Buhari ya umurci hukumar NDDC ta biya Dalibansu kudaden tallafin karatunsu.

Hajji 2020: Kasar Saudiyya ta yi asarar Dala Bilyan 12 saboda rage yawan mahajjata.

Kasar Pakistan na yunkurin sulhunta Iran da Saudiyya.

Taliban ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta a lokutan bukukuwan sallah.

04/04/2020

: Coronavirus gaskiya ce
Yana da kyau mubi umarnin Gwamnatin tare shawarwarin ma'aikatar lafiya wajen kokakarin ta dakile cutar ta Coronavirus wacce aka sauya mata suna da Covid 19.

Sako daga dan majalisa mai wakiltar Katsina ta tsakiya wato sanata Kabiru Abdullai Barkiya.

APC ta gargadi masu neman EFCC ta binciki TinubuKungiyar wayar da kan matasan ta jam’iyyar APC a Najeriya ta yi kira ga ...
14/11/2019

APC ta gargadi masu neman EFCC ta binciki Tinubu

Kungiyar wayar da kan matasan ta jam’iyyar APC a Najeriya ta yi kira ga babbar jam’iyyar hamayya wato PDP da ta yi wa ya yanta gargadi kan su daina huro wuta ko zabani hakkan, wanda suke ikirarin cewa a binciki Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Kungiyar ta APC National Awareness for Youth Vanguard ta fitar da sanarwar ne a ranar Laraba 13 ga Watan Nuwamba 2019, inda ta soki kiran da ake yi wa hukumar EFCC ta bi ta kan Jagoranta.

Shugaban kungiyar ta wayar da kan matasan APC Alhaji Mukhtar Abubakar, ya bayyana cewa ana neman EFCC ta binciki Bola Ahmed ne saboda ya bada gudumuwa wajen lallasa PDP a 2019. Wata kungiya mai zaman kanta, ta bukaci EFCC ta binciki abin da ya kai motar kudi cikin gidan Bola Tinubu a lokacin zaben da aka gudanar na shekara da muke ciki.

Sai dai Abubakar ya bayyana cewa , abun da ke faruwa shine, akwai wasu mutane da dama wayanda ke neman suna tare da sun haddasa fitina, kuma basu son hadin kan matasan Najeriya sobada wata bukatar su wacce baza ta amfanawa al’ummar kasar tamu da komai ba.

“Irin wayannan ne ke fitowa suna yin zargin a kan daya daga cikin ‘yan siyasan da ake ganin darajar a Najeriya a yau.”

Abubakar ya shaidawa OakTV cewa , neman EFCC ta binciki Jagoran jam’iyyar APC saboda ya ajiye motar kudi a gidansa, tun kafin ayi nisa ba zai kai ga zuwa ko ina ba, kuma ikirari hakkan bai da wani ma tabbata,domin babu wani wanda ya taba zargin hanyar arzikin na jagoran APC saboda da kansa ya miki kansa gaban Hukumar ta EFCC har sau 2 a lokacin da ya tsaya takarar gwamnan jahar Legas, bayan gabatar da kadarorinsa a lokacin da ya ke mulkin jahar Legas.

A karshe Alhaji Muktar Abubakar yace, duk wani kamfani da dan siyasar Najeriya ya mallaka to babu shakka al’ummar Najeriya suna sane da shi.

01/10/2019
27/09/2019

Yan mata masu zuwa biki a dinka kula..Akwai Cc fa!

27/09/2019

Kalli Aliko Dangote tare da yarsa Fatima suna rawa

Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu wato Kabiru Gaya na murna zagayuwar shekarun haihuwar sa.A ganin ku zai kai shekara naw...
16/09/2019

Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu wato Kabiru Gaya na murna zagayuwar shekarun haihuwar sa.

A ganin ku zai kai shekara nawa?

04/09/2019
Xenophobia: Abunda ya haddasa rikici tsakanin yan Najeriya da Afrika ta Kuduwani mazaunin Najeriya  wanda ke saune a bir...
04/09/2019

Xenophobia: Abunda ya haddasa rikici tsakanin yan Najeriya da Afrika ta Kudu

wani mazaunin Najeriya wanda ke saune a birnin Johanasbag dake Afirka ta Kudun, mai suna Ibrahim Bitrus ya bayyana halin da 'yan kasashen waje ke ciki a wata hira da yayi da BBC.

Rikicin ya samo asali ne a lokaicn da wani dan kasar Tanzania ya tafi wata unguwa domin sayar da wasu kwayoyi masu sa maye.

Ya ce, Kwayoyi ne da matasa kan nuka, su saka cikin taba sauna sha. To wasu direbobin motocin tasi a unguwar sun hana yaron zuwa unguwar, amma ya ki".

To da s**a k**a shi ne sai kawai s**a dake shi. Shi kuma sai ya tafi gida ya dauko bindiga ya harbi wani daga cikin wadanda s**a doke shi", inji Ibrahim Bitrus.

Ya kuma bayyana wa BBC cewa a sanadin haka ne aka dora wa 'yan Najeriya wannan laifin, kuma daga nan aka fara kai musu hare-hare.

Ya kuma ce wutar rikicin ta fara ne daga babban birnin kasar Pretoria, kafin daga baya ta bazu zuwa birnin Johannesburg.

03/09/2019

Hmmm...Ana wata fa ga wata😷Allah yasa mu dace

03/09/2019

: Yadda dan majilisar jahar Kebbi yayi rabon motoci guda 7 a mazabar sa

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Na'ebtv posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Na'ebtv:

Videos

Share

Nearby media companies


Other Broadcasting & media production in Kano

Show All