Ibrahim Suleiman Tsamiya Babba

Ibrahim Suleiman Tsamiya Babba Nigerian journalist
Media consultant
Sports Analysis
Reporter
Newscaster
Programme presenter
(1)

Da Dumi-Dumi Shugaba Buhari ya umurci ‘yan Najeriya su ci gaba da amfani da tsohuwar takardar Naira 200 sannan ya bukaci...
16/02/2023

Da Dumi-Dumi

Shugaba Buhari ya umurci ‘yan Najeriya su ci gaba da amfani da tsohuwar takardar Naira 200 sannan ya bukaci su kai tsofaffin 500 da 1000 ga bankin CBN.

Shugaba Buhari ya bai wa 'yan Najeriya haƙuri kan halin da ake ciki sak**akon canjin ƙudi.
16/02/2023

Shugaba Buhari ya bai wa 'yan Najeriya haƙuri kan halin da ake ciki sak**akon canjin ƙudi.

YANZU-YANZU: Kotun Koli ta dage ci gaba da sauraron karar da Jihohi uku s**a shigar kan sabbin kudi zuwa ranar Laraba, 2...
15/02/2023

YANZU-YANZU: Kotun Koli ta dage ci gaba da sauraron karar da Jihohi uku s**a shigar kan sabbin kudi zuwa ranar Laraba, 22 ga watan Fabrairun 2023.

Saudiyya ce za ta karɓi baƙuncin gasar kofin duniya ta ƙungiyoyiAn zaɓi ƙasar Saudiyya a matsayin ƙasar da za ta karɓi b...
15/02/2023

Saudiyya ce za ta karɓi baƙuncin gasar kofin duniya ta ƙungiyoyi

An zaɓi ƙasar Saudiyya a matsayin ƙasar da za ta karɓi baƙuncin gasar kofin duniya ta ƙungiyoyi a karon farko.

An bayyana matakin ne kwana uku bayan da Real Madrid ta ɗauki kofin a Morocco, bayan da ta casa Al- Hilal da ci 5-3, ƙungiyar Saudiyya ta farko da ta kai wasan ƙarshe a gasar.

Saudiyya da za ta kasance ƙasa ta shida da ta ɗauki baƙuncin gasar tun bayan ɓullo da ita a shekarar 2000.

Ministan wasanni na ƙasar ya ce ɗaukar nauyin gasar alama ce da ke nuna cewa ''karanmu ya kai tsaiko''.

A 'yan shekarun baya-bayan nan dai ƙasar Saudiyya na ta zuba jari a ɓangaren wasanni, lamarin da ya sa wasu ke zarginta da zubar da martabar ƙasar.

Haka kuma ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam ciki har da Amnesty International na zargin ƙasar da take haƙƙin bil adama.

Kotun Koli ta dage sauraron karar da wasu Gwamnoni s**a shigar kan canjin kudin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi zu...
15/02/2023

Kotun Koli ta dage sauraron karar da wasu Gwamnoni s**a shigar kan canjin kudin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi zuwa ranar Laraba mai zuwa.

Yau kotun ƙoli za ta saurari ƙarar da jihohi su ka shigar kan soke wa'adin daina amfani da tsoffin kuɗiA yau Laraba ne a...
15/02/2023

Yau kotun ƙoli za ta saurari ƙarar da jihohi su ka shigar kan soke wa'adin daina amfani da tsoffin kuɗi

A yau Laraba ne ake sa ran kotun ƙolin Najeriya za ta saurari dukkanin ɓangarori a ƙarar da wasu gwamnonin johohi s**a shigar domin hana Babban Bankin Najeriya aiwatar da wa’adin amfani da tsofaffin takardun kuɗin naira na 1,000, da 500, da kuma 200.

Gwamnatocin jihohin Kaduna, da Zamfa da kuma Kogi ne s**a shigar da ƙarar, inda tun farko kotun ta bayar da umurnin jingine wa’adin daina amfani da takardun kuɗin na 10 ga watan Fabrairu, wanda bankin ya bayar a farko.

BBC ta rawaito cewa mutane dai a Najeriya sun shiga ruɗani a kan ko za su iya ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗin na naira 1,000, da 500, da 200 duk da umurnin da kotu ta bayar na jingine wa’adin na 10 ga watan Fabrairu.

Haka nan rahotanni daga wurare da dama sun nuna cewa bankuna sun daina karɓar tsofaffin takardun kuɗin, suna bayar da hujjar cewa umurni ne s**a samu daga Babban Bankin na Najeriya.

Haka nan ma wasu masu ƙananan sana’o’in da dama sun daina amsar tsofaffin kuɗaɗen.

Jama'ar ƙasar na sanya ido kan abin da kotun za ta ce a zamanta na yau, wanda zai iya yin tasiri kan halin da al'ummar ke ciki na ruɗani game da ci gaba ko kuma daina amfani da tsofaffin kuɗaɗen.

CBN ya ce duk wanda aka k**a yana sayar da kuɗi ko yana wulanta ta su hakan ka iya ja masa hukuncin biyan tara ko kuma z...
02/02/2023

CBN ya ce duk wanda aka k**a yana sayar da kuɗi ko yana wulanta ta su hakan ka iya ja masa hukuncin biyan tara ko kuma zaman gidan yari.

YANZU -YANZU: CBN ya umarci  bankuna da su riƙa bada sabbin kuɗi ba ta ATM kawai baBabban Bankin Najeriya CBN ya umarci ...
02/02/2023

YANZU -YANZU: CBN ya umarci bankuna da su riƙa bada sabbin kuɗi ba ta ATM kawai ba

Babban Bankin Najeriya CBN ya umarci bankunan kasuwanci da su fara biyan kudaden da aka sauyawa fasali a kan kanta, idan har bai haura Naira dubu 20 ba a kowace rana ba.

Daraktan Sadarwa da watsa labarai na babban bankin, Osita Nwanisobi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya kara da cewa babban bankin zai hada gwiwa da hukumar ‘yan sandan Najeriya da hukumar tara haraji ta tarayya FIRS sai hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC da kuma sashin kula da harkokin kudi na Najeriya NFIU, don hukunta masu masu sayar da sabbin kuɗi a bankuna.

Ya ce: “Babban Bankin Najeriya CBN ya lura, tare da nuna matukar damuwa, ganin yadda mutane ke sayar da sabbin takardun kudi da aka yi wa gyaran fuska lamarin da ya jefa al’umma cikin mawuyacin hali.

01/02/2023

A nan Kano dai daga tsohon kudin har sabon babu. Ya abun yake a wuraren ku?

01/02/2023

EFCC

Hukumar EFCC ta ce, a Litinin din nan jami'anta sun je har gida sun k**a dan takarar Sanatan Kano ta tsakiya na jam'iyyar APC Alh. Abdussalam Abdulkarim Zaura.
Sannan ta gurfanar da shi a gaban Kotu sai dai lauyansa bai bayyana ba, daga baya kuma aka sanya shi a hannun beli.
Kakakin hukumar ta EFCC a Kano Idris Muhammad ya yiwa Freedom Radio karin bayani.

01/02/2023

Kotu ta umarci a kamo Abdullahi Abbas bisa zargin barazanar ga rayuwa da tada hankali

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta bayar da umarnin a gaggauta k**a shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, da kuma gurfanar da shi a gaban kuliya, bisa zargin laifin barazana ga rayuwa, tada hankali da kuma kalaman ɓatanci.

Mahmoud Lamido, ɗan gwagwarmaya a jihar Kano kuma shi ne abin ya shafa, ya garzaya kotu ta hannun lauyansa, Bashir Tudunwazirirchi, ya na neman a gaggauta k**a shugaban jam’iyyar ta APC Abdullahi Abbas, bisa zarginsa da yi masa barazana ta wayar tarho, ta hanyar cewa "sai na batar da kai".

Mai shari’a, S.A. Amobeda na babbar kotun tarayya mai zamanta a Kano ya bayar da wannan umarni tare da ɗage zaman zuwa ranar 16 ga watan Fabrairu domin sa ido kan ko za a bi umarnin.

Da ya ke mayar da martani kan lamarin a cikin wata sanarwa, kakakin jam'iyyar adawa ta NNPP, Sanusi Dawakin Tofa ya ce wannan ne karo na biyu a jere da alkalai daban-daban s**a bayar da irin wannan umarnin kotu, domin tilasta wa kwamishinan 'yan sandan k**awa tare da gurfanar da Abbas a gaban kuliya kan batutuwan da s**a shafi tashin hankali, tsoratarwa da barazana ga rayuwa.

"Muna fatan wannan zai zama darasi ga duk wani dan siyasa da ya zabi hanyar tashin hankali, maimakon inganta zaman lafiya a Kano da Nijeriya," in ji Mista Dawakin Tofa.

DA ƊUMI-ƊUMI: Bankuna za su ci gaba da karɓar tsoffin kuɗaɗe har bayan ƙarewar wa'adi - EmefieleGwamnan Babban Bankin Ƙa...
31/01/2023

DA ƊUMI-ƊUMI: Bankuna za su ci gaba da karɓar tsoffin kuɗaɗe har bayan ƙarewar wa'adi - Emefiele

Gwamnan Babban Bankin Ƙasa, CBN, Godwin Emefiele, ya ce bankuna za su ci gaba da karbar tsoffin takardun kudi na Naira har bayan wa’adin musanya wa da sabbin kudi ranar 10 ga Febrairu.

A ranar Lahadi ne babban bankin ya kara wa’adin rufe karɓar tsoffin takardun Naira na 1,000 da 500 da kuma N200, biyo bayan korafin ‘yan Najeriya.

Sai dai a yayin da Emefiele ya bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilai kan sabon tsarin sauya fasalin Naira ,da kuma canjin naira a yau Talata, shugaban na CBN ya ce har yanzu bankuna za su karbi tsoffin takardun har bayan wa’adin.

Emefiele ya ce idan aka yi la’akari da sashe na 20, karamin sashe na 3 na dokar CBN ta 2007, ko da wa'adin amfanin tsoffin kuɗaɗe ya cika, CBN za ta ci gaba da karbar su.

Emefiele ya ce dole ne bankunan kasuwanci su karbi kudin ko da bayan wa'adin 10 ga watan Fabrairu ne.

Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya Bude  Soron Ingila, Wanda  Sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayero ya Sabunta.Soron Ingila gud...
30/01/2023

Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya Bude Soron Ingila, Wanda Sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayero ya Sabunta.

Soron Ingila gudane daga cikin Fadojin dake da Tsohon Tarihi a Masarautar.

Hotunan Tashar Tsandauri kenan wato (Dala Inland Dry Port) wanda aka kaddamar a yau Litinin 30/01/2023 bisa Jagorancin S...
30/01/2023

Hotunan Tashar Tsandauri kenan wato (Dala Inland Dry Port) wanda aka kaddamar a yau Litinin 30/01/2023 bisa Jagorancin Shugaban Kasa Muhammad Buhari tare da jagoranci Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR.

An kaddamar ta tashar wacce take hadin gwiwa ne tsakanin Gwamnatin tarayya data Jihar Kano a unguwar zawaciki dake karamar hukumar kumbotso.

Ginin Tashar Tsandaurin ta Dala Inland Dry port zai saukakewa yan kasuwa wajen shigowa da fitar kayayyakin kwantaina kai tsaye daga duk inda aka dauko zaizo Kano ba tare da an sauke a Lagos ko Cotonou ba inda hakan zai kara bunkasa harkokin kasuwanci a Jihar Kano ta cigaba ta rike kanbun ta na cibiyar kasuwancin yammacin Africa.

Aminu Dahiru
SSA Photography 📸

Yadda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sauka a tashar tsandauri da ke Zawaciki a Jihar Kano domin kaddamar da wasu muhi...
30/01/2023

Yadda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sauka a tashar tsandauri da ke Zawaciki a Jihar Kano domin kaddamar da wasu muhimman ayyuka da Gwamnatin Tarayya da ta Jihar s**a aiwatar.

Ta cikin shirin ‘Zube Ban Kwarya’ na ranar Lahadi 29 ga watan Janairu na shekarar 2023, zamu karbi bakuncin ɗan takarar ...
29/01/2023

Ta cikin shirin ‘Zube Ban Kwarya’ na ranar Lahadi 29 ga watan Janairu na shekarar 2023, zamu karbi bakuncin ɗan takarar majalisar tarayya na yankin ƙananan hukumomin Gezawa da Gabasawa cikin jam'iyyar APC wato Hon. Mahmoud Muhammad Santsi.

Zai yi bayanin manufofinsa idan al'ummar yankunan s**a zabe shi a zaben 2023.

Zaku iya kallonmu kai tsaye a shafinmu na Facebook, sannan zaku iya turo mana tambayoyin da kuke so muyi masa.

Muna dakon ku.

Gwamnatin Najeriya ta tsawaita wa‘adin karbar tsoffin kudi zuwa 10 ga watan Febrairu.
29/01/2023

Gwamnatin Najeriya ta tsawaita wa‘adin karbar tsoffin kudi zuwa 10 ga watan Febrairu.

28/01/2023

Mista Emefiela ya ce ''hakika ina ɗauke da sako maras daɗi ga wadanda suke tunanin za mu ƙara wa'adin, don haka ina mai bayar da haƙuri kasancewar hakan ba zai yiyu ba''.

Pedri scores a crucial winner for Barcelona on his 1️⃣0️⃣0️⃣th appearance for the club to remain top of LaLiga 👏
28/01/2023

Pedri scores a crucial winner for Barcelona on his 1️⃣0️⃣0️⃣th appearance for the club to remain top of LaLiga 👏

28/01/2023

Yadda Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya ta yi bikin yaye dalibanta su 35,758 tare da bayar da Digirin Girmamawa ga wasu mutum hudu.

📸: Abubakar Sadiq Mohd

28/01/2023

Cibiyar Horas da Aikin Hajji da NITDA sun haɗa gwiwa don kawo fasahar zamani a harkokin Hajji

A kokarin daƙile matsaloli wajen gudanar da shirye-shiryen aikin Hajji a Nijeriya, Cibiyar Horas da Aikin Hajji ta Najeriya (HIN) wata cibiya da ke karkashin kulawar Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), da aka kafa ta kwanan nan, ta nuna sha’awarta na yin hadin gwiwa da Hukumar Bunkasa Fasaha ta Ƙasa, NITDA akan kawo fasahar a shirye-shirye na aikin Hajji.

A wani taro da su ka yi a hedikwatar Hukumar NITDA da ke Abuja a jiya Juma'a, NITDA da HIN sun amince cewa irin wannan hadin gwiwa tsakanin kungiyoyin biyu zai taimaka wajen karfafa aikin Hajji a kasar.

A nasa jawabin, babban daraktan hukumar NITDA, Kashifu Inuwa, CCIE, ya bayyana kafa cibiyar a matsayin muhimmaci wajen ilimantar da maniyyata, da kuma daidaita hanyoyin da za a bi wajen inganta shirye-shirye na aikin hajji a ƙasar.

Ya bayyana kafa Cibiyar HIN a matsayin wani al'amari a lokacin da ya dace da masu niyyar zuwa aikin Hajji ke bukatar a ilimantar da su, inda ya kara da cewa, “sabuwar cibiya an kafa ta a lokaci ne da ya dace da ku tsara dabarun ku, irin bukatun da ku ke son cimma. Ana buƙatar amfani tunani da basira wajen tafiyar cibiyar."

Ya ce tsarin haɗin gwiwa tsakanin NITDA da Cibiyar wata babbar dama ce domin ƙungiyoyin biyu su na da buri ɗaya na ƙididdige ayyuka a cikin ƙasar da kuma samun amfani da fasahar zamani

Tun da fari, shugaban Cibiyar ta HIN, Farfesa Nasiru Muhammad Maiturare, ya ce abin da ya mayar da hankali a kai shi ne yin amfani da fasahar zamani wajen samar da hidimomi, musamman a halin yanzu da aka mayar da tsarin aikin Hajji ya zama na fasahar zamani.

28/01/2023

Najeriya: Ko me ya sa Gwamna Abdullahi Ganduje daukar matakin soke ziyarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya shirya kai wa jihar Kanon don kaddamar da wasu aiyukan raya kasa?

28/01/2023

(NRC)

Hukumar Kula da Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC) ta dakatar da jigilar fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna sak**akon gocewa daga layin dogo da wani jirgi ya yi ranar Juma’a.

27/01/2023




Gwamnatin Kano Karkashin Jagorancin Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje tayi Wani zaman gaggawa da Malaman Jihar Kano da s**a futa daga bangarorin Qadiriyya da Tijjaniya da Izala kan karancin sabon Kudi da yadda abun ya shafi rayuwa da kasuwanci a Jihar.

Gwamnati da Malaman sun bukaci Babban Bankin 'kasa na CBN daya Kara wa'adin daina karbar Tsohon Ku'di saboda rashin wadatar Tsohon a Kano baki 'daya.

26/01/2023

Allah gabamu shuwa gabanni nagari masu tausayin mu

26/01/2023

Gwamna Abdullahi Ganduje ya Sanya hannu wajen Sallamar Barista Muhyi Magaji Rimin Gado daga Kujerar Hukumar Karbar Korafe Korafe.

Cikin Takardar da Sakataren Gwamnatin Kano Malam Usman Alhaji ya Sanyawa hannu yace an sauke Muhyin ne bisa dogaro da matsayar da Majalisar Jihar Kano ta dauka akansa tun a Lokutan baya.

Address

Tsamiya Babba, Gezawa
Kano
TSAMIYABABBA

Telephone

+2348069251302

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ibrahim Suleiman Tsamiya Babba posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Ibrahim Suleiman Tsamiya Babba:

Share

Nearby media companies


Other Broadcasting & media production in Kano

Show All

You may also like