05/08/2020
Labaran Safiyar Laraba 5 ga watan Augusta 2020.
An sami karin mutane 304 wadanda s**a kamu da Coronavirus a Najeriya, jimilla 44,433.
Gwamnonin Najeriya za su gudanar da wani taro a yau don tattaunawa kan matsalolin tsaro.
Gwamnatin jihar Jigawa ta umurci dukkanin ma'aikatan jihar su koma bakin aiki a yau.
'Yan kasuwa na son kara farashin litar man fetur zuwa N150 a cikin wannan wata ta Agusta.
Gwamnatin tarayya ta yi wa dokar kalaman kiyayya gyaran fuska, inda za a ci tarar wanda ya yi Naira milyan 5.
Gwamna El-Rufai na jihar Kaduna ya ce cikin shekaru 5 sun kashe Naira bilyan 16 kan harkar tsaro.
Gwamnan jihar Kano, Ganduje ya samu lambar yabo kan yaki da cutar Covid-19 daga kasar Senegal.
Shugaba Buhari ya umurci hukumar NDDC ta biya Dalibansu kudaden tallafin karatunsu.
Hajji 2020: Kasar Saudiyya ta yi asarar Dala Bilyan 12 saboda rage yawan mahajjata.
Kasar Pakistan na yunkurin sulhunta Iran da Saudiyya.
Taliban ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta a lokutan bukukuwan sallah.