31/10/2020
ALHAMDULILLAH TATTALIN ARZIKIN KASAR FARANSA YA DURKUSHE
Minstan Kudi na Kasar Faransa Bruno Le Maire ya bayyana cewa Kasar zata fuskanci mummunar karayar tattalin arziki har zuwa karshen wannan shekara ta 2020 saboda cutar Coronavirus da ta sake bulla Kasar a karo na biyu, a dai-dai lokacin da hukumar kididdigar Faransa ke cewa tattalin arzikin Kasar ya fadi da kashi 18 cikin 100 a yanzu haka saboda halin da Kasar ke ciki
Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da kayayyakin masarufi da Faransa ke samarwa a kasashen Larabawa (yankin Golf) sakamakon kauracewa sayan kayan Faransa saboda nuna bacin rai da kasashen Musulmai s**a nuna tare da kiran kauracewa kayayyakin na Faransa gaba daya sakamakon shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron yana goyon bayan masu zanen bataci ga Annabi Muhammad (SAW)
A Kasar Kuwait, manyan shaguna 60 s**a fitar da kayayyakin Faransa, yayin da wasu kamfanonin shirya tafiye-tafiye s**a dakatar da Faransa daga cikin jerin kasashen da ake ziyarta.
Khalid Hussain manajan daya daga cikin shuganun da s**a kauracewa kayayyakin Faransar, ya shaidawa AFP cewar sunyi haka ne, soboda taba Annabi (SAW) wanda shine mafi girman tsokana da zaโayi wa addinin Musulunci kenan.
A Kasar Qatar ma, Al-Meera, wani babban kamfani dake rarrabawa manyan shuganu kayayyaki ya dakatar da kayan Faransa cikin kayayyakinsa, yayin da wasu majiyoyi biyu na gwamnati s**a shaidawa AFP cewar, Qatar za ta kaurace wa taron tattaunawar zaman lafiya wanda Paris zata karbi bakwanci ranar 11 ga watan Nuwamba, haka batun yake a kasar Saudiya da Hadeddiyar Daular Larabawa da sauransu. ~Sashin Hausa na gidan Rediyo Faransa ya hada rahoton
Yaa Allah Ka durkusar da tattalin arzikin Faransa
Allah Ka tsinewa Emmanuel Macron albarka
Allah Ka wulakantashi har sai alade yafishi daraja
Allah Ka watsa al'amarinsa Amin