El-Jareedah Newspaper Hausa

El-Jareedah Newspaper Hausa News and entertainment

20/03/2024

DAGA WAZIRIN EL-JAREEDAH

Waziri yace muna neman afuwa ga masu bibiyarmu wajan karanta labaranmu saka makon rashin sakawa kwana biyu .to yanzu muna san zamu cigaba da sakawa don haka muna kara godiya ga duk wanda suke sauraranmu.
Sai waziri yace gaskiya jamma'a suna cikin wani yanayi na rashin kudi don suna kasa biyawa kansu bukata karama ko babba .sakamakon rashin kudi da muka sami kanmu aciki.
Waziri ya kara cewa gaskiya ya dace muzama masu taimakawa junanmu don kara samun fahinta tsakaninmu.
Yace munsani wasu suna taimakawa,wasu basasan suzama masu taimako ga alumma musamman yan uwanmu musulmi.
Yace ya dace masu bada duk wani taimako s**ara don darajar wannan watan da muke ciki watan da ubangiji (Allah) madaukakin sarki yake ninka maka lada idon kayi abin ladan.
Yace yanzune lokacin da duk wanda yake da wata dama don yaga ya taimakawa jamma'a,kuma shima (Allah) zai taimaka masa don haka inna kara kira ga wanda yake san yayi taimako ta yanda zai bada taimako
Yace ya wasu kasashen idon kaga yanda suke bada taimako sai kayi mamaki musamman kasashen larabawa da suke duniya.
Yace 1- ya dace ciyarwa da shayarwa ya dace Sosai.2- ya dace katara jamma'a kaciyar dasu kashayar dasu don kara Neman yardar (Allah) madaukakin sarki
3- yace awannan watan na ramadan yace mukara neman kusanci ga ubangiji madaukakin sarki .don gaskiya duk wanda yake da wata dama cikin wannan watan to yayi amfani da wannan dama don karuwar sace to nizan cigaba da wannan fadakarwa ko kuma yinkira da fatan alhairi ga dukkan yan uwa muslmi da suke fadin duniya ya (Allah) kasamu dace darabo.

11/03/2024

DAGA ZAINAB UMAR MAMMAN KANO
A Yau litinin 11-3-2024 hijirata 1447 muka tsunduma cikin azumin watan ramadana wanda al-umma da dama suketa hada hadarsu ta yau da kullum
Inda na hangi dandazon mata akofar wani gida suna tsaitsaye domin jiran wani Abu.koda na karasa sai naji cewar suna zaman jiran mai gidanne domin Samun abinda zasu saka abakin salati idan lokacin sharruwa yayi.
Malama habiba tace muna zuwa wannan guri aduk lokacin da watan Ramadan ya Kama.s**anzo domin neman taimakon kayan abinci kamar irinsu masara,shinkafa,da kuma abinci da faffe lokacin buda baki da kunun tsamiya.
Daga karshe dai tayi godiya da kuma jinjina ga mai wannan gida domin yana kokari sosai samun irinsa acikin al-umma yana wahala .tace ya kamata masu hali suyi koyi da dabi'u irin na wannan bawan Allah.domin ya cika jan gwarzo kuma jajur tacce don samun irinsa yana da matukar wahala.

20/02/2024

MASU KUDI KUBADA ZAKKA DUKIYA TA ZAUNA LAFIYA.
DAGA YAU SANI GARBA K.GODA.
Malam Auwalu Wanda yake zaune a cikin birni,a fegin sunusi Malam yace fidda zakka ya zama dole Iran Kanada kudi ,Dukiya bata da asara sai dai tadinga daukaka bazaka ga wata asaraba sam don kana kiyaye ka'ida ta fidda zakka.
Malam yace wasu wanda sukeda dukiya suna ganin sune s**a bawa Kansu ,don tsananin nemansu shine yasa s**a tara dukiya .basa tunanin cewa Allah ne yabasu don haka basu taimaki kowaba babu ruwansu da kowa babu taimako.
Malam yace gaskiya wasu daga cikin masu kudi basa zuwa hajji,basa umara,basa sanyin ibada

13/02/2024

JAMMA'AR NIJERIYA SUNA NEMAN TAIMAKON (ALLAH) DON HAKA SAI ADDU'A MUCHANJA HALINMU.
DAGA ZAINAB UMAR MAMMAN KANO
"Yan najeriya da da mane s**a koka don ganeda halin yinwa da fatarar da ake ciki,musamman mata da yara,su abin yafi shafa .
Wata baiwar (Allah) mai suna Amina tayi kira ga gwamnatin tarayya ,data taimaka wajen ganin tasa malamai sudage da addu'a,domin samun saukin rayuwar da muke ciki .
Wallahi a yau sai mutum yayi kwana 2 bai ciba kuma ga yara.ta kara da cewa maganar dubu 8 baitasoba .ataimaka abude boda asami abinci .
Ta Kara da cewa tununbu kaifa musulmine.

08/02/2024

MATA DA KANANAN YARA SUNA WANI HALI ACIKIN NIJERIYA.
DAGA ZAINAB UMAR MAMMAN KANO
Mata na cikin wani yanayi a najeriya mata da yara suna cikin matsanancin hali a najeriya,duba da tsadar rayuwa da ake fama da ita ,maza nashan wahalar samo abinci,wanda hakan nataka muhimmiyar rawa wajen lalacewar yara da zawarawa.dama gurbacewar tarbiyya.zainab Umar mamman kano tayi nazari ga rahoton,data hada mana.
Tsadar rayuwa ta dugun zuma mata da yara wajen ganin sunfita naiman abin sakawa abakin salati.
Na zanta da wani yaro mai suna kamalu inda ya shaida mana cewa,yana fita gwangwanne ,inyasiyar yaci abinci ,tunda bako yaushe yake samowaba.
Ya kara da cewa wasu lokutanma ko yaje makaranta baya iya karatun saboda yunwa.haka kuma yayi kira ga wanda abin ya shafa dasu da surika fadakar da gwamnati da "yan kasuwa ,tunda duk abinda katara anan zaka barshi.
Kubiyomu shiri na gaba.

08/02/2024

WANI DATTIJO YAJA HANKALIN AL'UMMA GAMEDA TSADAR RAYUWA.
DAGA ZAINAB UMAR MAMMAN KANO
Malam baba yace turda halayyar wasu mutane .
Ambayyana tsadar rayuwa da rashin kwanciyar hankali,da rikicewar al'amuran Kasa,dacewa,cin'amana ,da kashe kashe,da rashin gaskiya ne ya haifar dasu .kiran ya fitone tabakin wani dattijo mai shekaru(90),malam baba ya tabbatar da cewa duk maishekaru irin nasa ayau yana Cikin tashin hankalin ganin rayuwar da ake ciki .
Ya kara da cewa ayau mutane sunacin amanar Allah da manzonsa, inda zakaga matan aure da zawara suna naiman mazan daba nasuba .mazama suna neman maza "yan uwansu,
Inada da janhankulanmu da tuba da komawa ga Allah.

07/02/2024

Ajiyan sharada yace tuni ya dace jammaa muyi tunani ya dace mukoma ga Allah madaukakin sarki don ganin yanayin damuka sami kammu aciki ,wannan yanayi matasa sun sami kansu cikin tabarbarewar tarbiya .wasu daga cikin matasa maza da mata sunanan da yawa sosai wasu kuwa sai son barka ,wasu kana ganinsu sai kai sha'awarsu.
Ajiya yace gaskiya wani yanayi da mata suke ciki yanzu gaskiya wallahi sai du'ai kawai ,tuni dama matsalar tarbiya gunsu yada dukkanninmu iyaye mukara saka ido mukula sosai yanda ya kamata mukara samun kulawa guntarbiyyar iyaye gaskiya kusani cewa dukkannin "ya"yanmu da matanmu dukkanninsu amanane gunmu sai Allah ubangiji ya tambayemu yanda muka zauna dasu kula dasu ,tarbiyyarsu kowa sai yayi bayani yanda ya kula dasu sai kayi bayanin haka ,don kuwa ya dace mukula mukara kulawa sosai don rikon Amana.
Yace duk matsalar da ta ubace da uwarsa suna karkashin uba Kai kuma uba kada kazama mai sakaci ga duk wanda suke karkashinka kada Kamanta .cewa Allah yananan zai tambayeka Kuma sai muntsaya Gaban Allah mai kowa mai komai don haka kowa yadace ya gasgata wannan rana don zata zowa kowa.
Yace Wanda yayi imani da wanda bai imaniba sunyi bayani sai kasanar da duk yanda kayi sannan idon kayi firi shikenan taka tafusheka idon kasami matsala to wannan kaita shafa kada kai kuka da kowa kayi dakanka.
Yace gaskiya jamma'a muna wasa da lamarin ubangiji madaukakin sarki,musani cewa shi ubangiji baya wasa kuma baihalil cemu don yinwasaba kowa ya dace ya gasgata haka to ya muke ko inkula da wannan lamari muji tsoron allah dame zamu gani cikin wannan Lamari.

06/02/2024

GWAMNONI KUTAINAKAWA JAMMA'A DAKE CIKIN YANKUNANKU.
DAGA. Wazirin el-jareedah hausa Kano Nigeria.
Ni waziri zandora daga inda natsaya to gaskiya ya kamata Mai girma shugaban kasa ya Samarda wani kwamitin dazai tuhumi duk wani gwamna dabai bada taimako ga alummarsaba
Yace gaskiya mata da maza suna shan wahala don haka gwamnoni kutaimaka don cigaba kokuma kumaida kudin tunda bazakuba yarba don anbaku don kutaimaka badon kujeku ajiyeba,kada gwamnatin tarayya ta bayar.
Wannan shine karshen bayani nabada taimako na gwamnoni bazasu bayar ga mutanansu
Ni wazirin el-jareedah na Kano karshen wannan bayani sai nakuma zuwa ga wani labarin da zaikuma zama cigaba ga dukkannin alummar da suke nijeriya.

06/02/2024

GWAMNONIN AREWA KUTAIMAKI AL'UMMA MUNA CIKIN WANI YANAYI.
DAGA ZAINAB UMAR MAMMAN KANO
Gwamnonin arewa kuji tsoron Allah domin nauyine Allah ya Dora muku na al'umma akanku yaku shuwagabanninmu,
Muna cikin wani hali nakuncin rayuwa da matsi,da wahala.rashin abinci,yaku shuwagabanninmu dan allah kutausaya mana kuji tsoron Allah kusama mana Mafita.
Ga matasa babu aikinyi ya Allah kaka womana dauki kasa sutausaya mana.

Allah yayiwa Malam (yahaya Mai tamsiri) Dandago rasuwa ,ya rasu bayan wata gajeriyar jinya.        Yarasu ranar litinin ...
29/01/2024

Allah yayiwa Malam (yahaya Mai tamsiri) Dandago rasuwa ,ya rasu bayan wata gajeriyar jinya.
Yarasu ranar litinin 29-1-2024 Wanda yayi dai dai da 17 ga watan rajab.
Ya rasu yana da shekara 104
Ya bar yara maza da mata da jikoki da dama Allah yaji kansa ameen

11/12/2023

MUSAN KANMU MATA
DAGA MAIMUNATU NA SIDI
Mata musani allah yai mana daraja da kima kuma ya girmamamu saboda haka kada muwulakanta kanmu ,musani babu addinin daya girmama mace kamar musulunci. Idan muka koma tarihi a lokacin jahiliyya wato kafin zuwan musulunci "ya mace ba'a bakin komai takeba domin bata da "yancin walwala, ba'a bata gado,bata gada sai dai a rabata acikin kayan gado .kamar inda za',a raba saniya ,ba'abata sadaki, bata da damar fadin ra'ayinta ko ai shawara da ita .akwai kasashen da in mijinta ya mutu sai dai a binnesu tare da ranta.akwai lokacin da idan aka haifawa mutum "ya mace zai fara bakin ciki kamar inda allah ya bamu labari acikin alkur'ani .
Idan akayiwa dayansu bushara da mace sai ya bata rai yana bakin cikin abinda akayi masa bushara dashi yana tunanin ya riketa a wulakance koya binneta da ranta.
Kenan "ya"ya mata ada ko "yancin rayuwa basu dashi domin binnesu ake .
Bayan zuwan musulunci ya bawa mata "yancin su rayu ya hana a binnesu yace kar'atabasu sai anbada sadaki idan an auresu su zauna a inuwa a fita a nemo abasu idan makusan tansu sun mutu a basu gado. Idan sunyi aikin alkhairi za'a basu lada su shiga aljanna kamar inda za'aba maza allah yace 'wanda yai aikin alkhairi maza da mata allah zai saka masa da abinda ya aikata'.kai wani abin dadima akwai aiyukan da in akayiwa mata allah yake bada aljanna.kamar wanda ya tarbiyyantar da "ya"ya mata uku harya aurar dasu zai shiga aljanna ,wanda yayiwa mahaifiyarsa biyayya zai shiga aljanna ,kuma wani tuntube ma duk aikin ladan da kai a irin tukuicin da allah zai maka a gidan aljanna shine a baka matan hurul ini a duniya mace tana daga cikin cikamakon dadin zaman duniya .manzan allah (s.a.w) yace duniya wurin jin dadi ne amma mafi alkhairi jin dadin duniya a baka mace ta gari.
A biyoni anan gaba donjin wacece mace ta gari? A ina ake samota? Maye halayenta? Ya kamata ayi tarbiyyarta harta zama ta gari ?

MUTARI DANDAGO YA KARA JINJINAWA GWAMNAN KANO.     Tsohon mai shari'a dake a jihar kano alhaji mutari garba dandago ya b...
10/10/2023

MUTARI DANDAGO YA KARA JINJINAWA GWAMNAN KANO.
Tsohon mai shari'a dake a jihar kano alhaji mutari garba dandago ya bawa mai girma gwamnan kano alhaji abba kabir yusuf yanda ya dage don kawo cigaba a jihar kano.
Tsohon mai shari'ar yace gaskiya munyi sa'ar jajir tacce ,dama kano irinku take bukata masu sanyin aiki da taimako ga dukkannin al'ummarku don haka ya zama dole muyaba masa bisa chanchanta da dacewarsa da yake da ita.
Mutari dandago ya kara cewa gashi mungani kuma ma'aikata sunsani cewa 25-7-2023 ya fara biyan duk wani ma'aikaci albashinsa babu wani jinkiri gameda biyan albashi kowa ya sheda haka .
Dandago yace don haka jamma'a muyita yimasa addu'a da kara yimasa fatan alhairi gameda yanda ya zama jajir tacce wajan salan iya mulki ,ya dace sauran gwamnoni suyi koyi dashi wajan kamanta sanyin adalci ,jamma'a sungani sun kara gani.
Yace (allah) mun godemaka kabamu wannan gwamna da kayi ajihar kano don haka mai girma gwamna kakara zama jajir tacce gameda ayyuakan da kakeyi a kano sosai abba na kowa.

09/10/2023

KOWA SAI YA GYARA
DAGA EL-JAREEDAH HAUSA KANO
NI wazirin zan dora daga inda natsaya kan labarina na kowa sai ya gyara
Gaskiya ni wazirin el-jarida gaskiya matasa maza da mata kanana da manya suna cikin rashinyin biyayya ga iyayansu da yawan wadansu matasan sune suke saka iyayansu cikin wani nau'in bala'in da suke shiga ciki wasu iyayan basason laifinsu basasan wani ko wata suyi fada ga dansu sai ransu ya baci sosai don kauna da soyayya da suke yiwa yaransu.
Gaskiya ni waziri nasani cewa da yawan wasu matasan mata da maza basasan ayi musu fada don basu saba da ayi musu fadaba duk wanda yayi musu fada to wannan mutumin ko kuma wannan matar wannan matashi ya sata cikin makiya nasa don tayi masa fada kawai sai bamai yimasa fada don baisa bajin fadaba.
Wasu daga cikin matasa maza da mata idon kai musu fada suna jin dadi suna girmamaka duk inda s**a ganka sai sun girmamaka sai dai su irin wannan matasan basu da yawa cikin matasa maza da mata sai da shawarar bazan bawa duk wani matashi namiji koma ce dukkannin al'umma wallahi muji tsoron allah musani akwai ranar karshe tananan tana zuwa sai kowa ya sami kansu cikin wannan rana.
Gaskiya niwazirin el jarida inna matukar bada shawara wallahi mukoma ga (allah) tun wuri da wuri don gano mana duk wata gaskiya tsakanin maza da mata da suke cikin addinin musulunci muda mukayi imani da ranar gobe alkiyama.

DAGA LUBABATU  SANI GARBA   Cikin makon daya gabata nazanta da wata malama mai suna maimunatu yakubu dandago inda take c...
09/10/2023

DAGA LUBABATU SANI GARBA
Cikin makon daya gabata nazanta da wata malama mai suna maimunatu yakubu dandago inda take cewa inna san nayi amfani da wannan dama na kara kira ga dukkannin iyayan yara maza da mata damu zama masu karin sa'ido gun mu'amalar yaranmu.
Malama maimunatu ta kara cewa gaskiya wasu iyayan yaran suna da sakaci wajan kulawa da tarbiyar yaransu suna gani sunayin abinda bai daceba suna kauda kai duk wanda yayiwa wannan yara magana to sai kaga iyayan basuso wannan lamarinba.
Maimuna tace tuni wasu iyayan sune s**a bada matsala wajan gurbacewar tarbiyar wasu daga cikin yaranmu ,kada uba ko uwa kowanda ya isa yayi magana yace zaizira ido yana gani yace shi bazayyi maganaba gaskiya yin haka kuskurene don haka inna sanmu gane cewa duk wani uba ko uwa ko wani wanda yake wakili neshi musani cewa sai (allah) ya tambayemu yanda muka kula dasu.
malama ta kara da cewa gaskiya matasa suna da karancin tarbiya maza da mata wasu idon kaga yanda sukeyi sai kaji tsoran lamarin .mata ko maza idon kagani kare bazai ciba sai kaji kunya sai kace basu da masu tsawa tardasu.
Tace matasa mata da maza kuji tsoran (allah) kukyau tata don ganta karku da duk kannin al'umma da suke kasarnan gaskiya al'umma bamajin dadin ganin abubuwan da sukeyi to don haka yaku matasa kukara lura gameda baki na dukkanin jamma'a.
Malama maimunatu tace tuni ya dace kowa yasan abinda ya kamata yadingayi ga reshi kuma matasan da suke da sana'a komai kankantarta kurike ta sosai kada kuyi wasa da ita .
Daga karshe maimuna tayi fatan alhairi ga dukkannin matasa maza da mata da (allah) yasa duk suzama daga cikin nagari mata da maza.

19/09/2023

KUNGIYAR GWAMNONIN NIJERIA KISA BAKI DON KADA ASAMAR DA YAJIN AIKI AKASAR NIJERIYA BAI KAMATABA.
Daga wazirin el-jarida hausa Kano nigeria to niwazirin na kuma da wowa da wani labarin wanda ya shafi kowa da kowa gameda lamarin yajin AIKI.
Waziri yace gaskiya ya dace dukkannin gwamnonin nijeriya susaka baki gameda wannan yajin aiki da kungiyar kwadago ta ambata cewar zasuyi yajin aiki na duk kasa,dama ga yanayin da al'umma s**a Sami kansu ciki to gaskiya wannan bai kamata dukkannin gwamnoni susaka Idoba .gameda wannan labarin.
Waziri ya kara cewar yin yajin aiki zai kara saka dukkannin al',Umma cikin wani saban lamari don haka kungiyar gwamnoni kasarnan Tamu ta nijeriya ta saka baki don kada afara.wannan yajin aikin bazai zama alhairi ga duk wani Dan nijeriyaba Sam tashin yinsa shine dai dai.

19/09/2023
19/09/2023

DAGA EL-JAREEDAH NEWS PAPER HAUSA KANO NIGERIA.
Amadadin wanda yake wannan gidan Jarida muna kara murnar zagayowar watan haihuwar fiyayyan halitta manzon (allah) (s.a.w)annabi muhammad (s.a.w) muna kara godiya ga (allah) ubangiji madaukakin sarki daya nuna Mana wannan watan na rabiyi Auwal shekarar (1445)bayan hijirarsa.
Daga el-jarida tace wannan watane wanda dukkannin musulmi suke kara murna tare da farin cikinsa da kara yiwa annabi hiduma don kara nuna soyayya ga fiyayyan halitta (allah) ya kara Mana soyayyar ma'aiki annabi muhammadu(s.a.w.)
El-jarida tace daga karshe za'ayi shagul gulan maulidi lafiya ,akuma gama lafiya muna fatan haka sosai.
Yace kanawa da sauran jihohi munsanku da nuna kwazo da nuna kauna ta manzon (allah) (s.a.w.)to mukara dagewa sosai.

18/09/2023

DAHIRU SANI DAKE KATSINA STATE YACE BANA MUNSAMI DA MUNA MAI ALBARKA.
DAGA WAKILINMU DAKE JIHAR KATSINA MUSBAHU GARBA.
Nazanta da wani mutun kuma manomi Malam DAHIRU SANI yace gaskiya bana munsami da muna mai albarka sai daimu jihar katsina muna da matsala ta wasu guraran bamu Sami yinnomaba da lilin haka munshiga cikin tashin hankali .
Don haka don (allah)gwamnatin jihar muta katsina kitaimakawa wanda basuda basusami yinnomaba don gaskiya bana munsami ruwan Sama sosai yanda ya Kamata.
Yace gaskiya muna cikin damuwa kan wasu bangaran da basuyi nomaba don gaskiya muna bukatar taimakon gwamnati ta taimakawa dukkannin bangaran da basuyi nomaba don suna cikin wani yanayi kan samun taimakon.
Gaskiya kuma wasu daga cikin manoma wanda s**a Sami amfanin gona ,bana gaskiya munsami da muna mai tsafta don haka don (allah,) muji tsoron (allah) mutau sayawa jamma'a wanda suke sayan kayan abinci don suyi amfani dashi don cinsa ya dace mutausaya.
Don gaskiya dukkan wani nau'in kayan abinci Yana tsada .wannan bai daceba tsakanin musulmi da musulmi don haka saimun duba sosai yanda ya Kamata tsakaninmu.
Don haka don (allah,) jamma'a mudinga tausayawa junanmu ko munsami falalar ubangiji madaukakin sarki don haka jamma'a muyi taimako ga junanmu don Samar da hadin kanmu donmu kuma samun tsira garemu.

Address

Ja'in Yamma A, Gwale LGA
Kano
700103

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when El-Jareedah Newspaper Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share

Category