10/07/2024
DARASI DAGA SHIRIN LABARINA SERIES ,,,
WANNE DARASI KAƊAUKA A SHIRIN LABARINA 👇👇
Dama a zahirin gaskiya, wanda yafi kusanci da kai ya fi samun saukin cutar da kai. Mafi kusanci da kai ya fi yi maka hassada da son ganin bayanka. Wannan ita ce gaskiya mai daci kuma mai wahalar yarda. Abunda Jamila tayi da abunda ta fada na cewa tana jin bakin cikin ganin Aminiyarta Maryam da Mainasara cikin nishadi da walwala, shi ne yanayin da mafi yawan mutane ke rayuwa a cikinsa.
Alpagu a Destan yayi wata magana yake cewa idan kaji an soke ka ta baya, kar ka fara tunanin makiyinka ne, ka fara kawo cewa wani wanda kake zaton yana sonka ne kuma ka kyautata masa zato. Duk inda kaga an hada kai an cutar da wani, babu makawa an yi amfani da makusantansa ne ko ma mafi kusancin mutane a wajensa. Don babu wanda zai cutar da kai sai wanda yake da bayanai a kanka. Wanda bashi da bayanai a kanka kuma bashi da masaniya akan inda kake da gazawa balantana yayi amfani da wannan har ya cutar da kai.
Jamila da abubuwan da tayi, darussa ne manya. Kuma hakika ce ta rayuwa da dukkan mu muke cikinta!
Allah yasa Mudace 🤲🏽
H Dacter Nakøwa 💯