27/11/2021
KASHEDINKA DA GAFALA DA LOKACIN SALLAR ASUBAHI DA LA'ASAR,
NA FARKO-
ﻗﺎﻝ ﷺ : ﻣﻦ ﺗﺮﻙ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻌﺼﺮ ﺣﺒﻂ ﻋﻤﻠﻪ . ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ
Manzon Allah (saw) Yace:
Wanda Yabar Sallar La'asar Aikinsa ya Baci,
NA BIYU-
ﻗﺎﻝ ﷺ : ﺍﻟﺬﻱ ﺗﻔﻮﺗﻪ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻌﺼﺮ، ﻛﺄﻧﻤﺎ ﻭﺗﺮ ﺃﻫﻠﻪ ﻭﻣﺎﻟﻪ . ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ
Manzon Allah (saw) Yace:
Wanda Sallar La'asar Ta Kubuce Masa, Kamar Wanda Yayi Hasarar Iyalansa, Da Dukiyarsa Ne
NA UKU-
ﻗﺎﻝ ﷺ : ﻣﻦ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﺒﺮﺩﻳﻦ ﺩﺧﻞ ﺍﻟﺠﻨﺔ . ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ
Duk Wanda Ya Sallaci Sanyi Biyu, Asubahi Da La'asar Zai Shiga Aljannah.
Asubahi Tana Dauke da Sanyin Dare La'asar Tana Dauke da Sanyin Rana.
TAMBIHI-
Mutane da Yawa S**an Gafala da Sallar La'asar da Asubahi Akan Lokacin Su Ba Tare da Wani Nuna Damuwa ba.
Wanda Hakan Ke Nuni ga Rashin Sanin Mahimmancin Su,
MANZON ALLAH (SAW) YACE:
ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
ﻣﻦ ﺻﻠﻲ ﺍﻟﻔﺠﺮ ﻓﻲ ﺟﻤﺎﻋﺔ ﻛﺎﻥ ﻓﻲ ﺯﻣﺔ ﺍﻟﻠﻪ ( ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ
Duk Wanda Ya Sallaci Sallar Asubahi Acikin Jam'i Zai Kasance Cikin Kulawar Allah,
Wanda Ya Kasance Cikin Kulawar Allah, Zai Samu Kariya daga Dukkan Sharri, Duk Wanda Ya Zalunce Shi Kuma, Allah Ya Daukan Masa Fansa,
Koda kuwa bai Roqi hakan daga Gurin Allahn ba.
SA'ANNAN Allah (swt) Yace:
ﻗﺎﻝ ﺗﻌﺎﻟﻰ :
ﺣَﺎﻓِﻈُﻮﺍ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟﺼَّﻠَﻮَﺍﺕِ ﻭَﺍﻟﺼَّﻠَﺎﺓِ ﺍﻟْﻮُﺳْﻄَﻰٰ ﻭَﻗُﻮﻣُﻮﺍ ﻟِﻠَّﻪِ ﻗَﺎﻧِﺘِﻴﻦَ
Ku Kiyaye Salloli Da Sallar Tsakiya, (La'asar) Ku Tsayu ga Allah Kuna Masu Biyayya da Qanqan da Kai.
Me Yasa Bayan Allah Ya Ambaci Kiyaye Salloli Gaba Dayan Su, Sai Kuma Ya Ware Daya daga Cikin Su ? AMSA= Don Girman Sha'anin ta.
SA'ANNAN-
Hatta Mala'ikun da Aka Wakiltasu Akan Duba Ayyukan Mu, Suna Yin Canjin Aiki Ne Alokacin Salloli biyu,
Asubahi da La'asar.
Wannan Yasa Duk Lokacin da S**a Kusanto Sai Kaji Zakara Yayi Cãra.
Manzon Allah (saw) Yace:
Zakara Yana Ganin Mala'iku, Duk Sanda Kuka ji yayi Cãra Ku Roqi Allah daga Falalar Sa Domin Yaga Mala'ikun Rahama ne,
ATAQAICE DAI-
SALLAR LA'ASAR, DA SALLAR ASUBAH DA KUKE GANI-
Suna Qunshe da Wasu Abubuwa Na Alkairai Masu Yawan Gaske ga Duniyar Dan Adam da Lahirar Sa,
DAN HAKA-
Ku daina Wasa Da Lokutan Su.
Yaa Allah Kasanya Mu daga Cikin Masu Fifita Lokutan Sallah Akan Lokutan Ayyukan Mu.
# Fatan_Alkairi