15/06/2023
Takaitaccen tarihin Janar Sani Abacha
An haifi janar Sani Abacha ranar 20 ga watan Satumbar shekarar 1943 a cikin garin Kano.
Ya yi makarantar Firamari ta City Senior Primary School, Kano, Government College, Kano, 1957-1962, Kwalejin horas da sojoji ta Kaduna Najeriya, 1962-1963.
Sannan ya wuce kwalejin Horas da Sojoji ta Aldershot dake Ingila, 1963, Kwalejin horas da dakarun kasa ta Warminster, ta Birtaniya 1966, 1971 Kwalejin sojoji ta Jaji dake Kaduna Najeriya, 1976, Kwalejin nazarin manufofi da tsara dabarun mulki ta Kuru, Jos, 1981, ya yi kuma wasu kwasa-kwasai da s**a shafi harkar tsaro a Canada, Amurka a shekarar 1982.
Tun daga juyin mulki na farko a Najeriya a shekarar 1966 janar Sani Abacha ke taka rawar gani sai wanda aka yiwa Shagari da na Babangida da kuma wanda yaiwa Cif Ernest Shenakon.
Allah ya yiwa janar Sani Abacha rasuwa ranar 8 ga watan Yuni shekarar 1998 yana da shekaru 54 da haihuwa sakamakon ciwon zuciya.
Ya mutu ya bar mata daya Hajiya Maryam Abacha da 'ya 'ya tara mata uku da maza shida.