Kima Global Concept

Kima Global Concept Peace Ambassador

JAMA'A MU SAKA SU ACIKIN ADDU'ADa Yawa A Cikin Yan Uwanmu Dalibai na Fama Irin wannan Yanayin Wasu kawai Basa Iya Fitowa...
10/02/2024

JAMA'A MU SAKA SU ACIKIN ADDU'A

Da Yawa A Cikin Yan Uwanmu Dalibai na Fama Irin wannan Yanayin Wasu kawai Basa Iya Fitowa Fili su Fada ne, Amma Halin da Talakan Kasar nan yake ciki Ta fannin Kayan Masarufi, Fannin Kiwon Lafiya, da Kuma Fannin Ilmi a Jigawa da Nigeria sai dai Muce "Innalillahi Wa'inna Ilaihir Raji'un".

Gwamnati tayi Alkawarin biyama wadannan Daliban School Fees, Amma yanzu k**ar ba a taba yin zance ba kodai Gwamnati ta Shafa'a ne, Ko Kuma Gwamnatin Ba zata Iya Biya musu ba, ko Kuma dai tana so waɗanda ba zasu iya Biya ba suyi Asarar Karatunsu Allahu A'alamu.

Muna Sane da irin Makudan Kudaden da Gwamnati ke warewa wurin Gudanar da Aiyukan da Basu Kai Biyama Daliban School Fees ba, Inji Bahaushe Wai "An bar Jaki Ana Dukan Taiki".

Allah ya karkato da Hankalin Gwamnatin Jigawa Akan Talakawan ta, Ta Gane cewar suna cikin Yanayi marar Dadi, Wanda Har Yakai ga Masana Sun fitar da Jigawa Itace ta Uku A Jihohin da S**a fi Talauci a Nigeria.

'Yan uwanmu Dalibai Kuma Allah ya kawo Mana Mafita na Alkairi gaba dayanmu.

✍️✍️
Ahmed Gwadabe Kawu
10-02-2024

Alhamdulillah
15/01/2023

Alhamdulillah

ADDU'A TA MUSAMMAN.-"Allah muke roƙo ya karemu daga abinda baza mu iya ba, wanda muke iyawa kuma Allah ka huwace mana, A...
16/06/2022

ADDU'A TA MUSAMMAN.
-
"Allah muke roƙo ya karemu daga abinda baza mu iya ba, wanda muke iyawa kuma Allah ka huwace mana, Allah ka bamu lafiya da zama lafiya da gamawa lafiya da abinda lafiya za ta ci"

"Masu tada waɗannan fitintinu in masu shiryuwa ne Allah ka shirya mana su, idan ba masu shiryuwa bane, Allah ka k**a su irin kamun adawa da samudawa, duk mutumin da ya fitine mu ya Allah ka fitine shi, wanda ya addabe mu Allah ka addabe shi, wanda ya hura mana wuta ya Allah ka hura masa"
-
"Duk mutumin da aikinsa kisan mutane ne Allah ka ɗora waɗanda za suyi ajalinsa, wanda ya hana mutane zaman lafiya Allah kada ka barshi lafiya, dukkanin wanda ya nemi mu lalace ya Allah ka mayar dashi na baya ga dangi sai dangi sunci su bashi"
(Shiekh Khamis Sa'id Al-misery)
-
Telegram channel
https://t.me/hausaislamicpicturesquotes
-
Biyo Instagram ɗinmu
https://instagram.com/hausa.islamic.pictures.quotes?igshid=11g6c9k6osqg5

Domin Karantarwa Abisa Koyarwar Magabata Na Ƙwarai, FISABILILLAHI. - https://mobile.facebook.com/Hausa-Islamic-Pictures-Quotes-304897013359792/?ref=opera_speed_dial - https://instagram.com/hausa.islamic.pictures.quotes?igshid=11g6c9k6osqg5

30/03/2022

Alhamdulillah ala kullu hal!!

Allah rufa Mana asiri duniya da lahira

07/03/2022

Sanarwa!Sanarwa!!Sanarwa!!!

Kungiyar Likitoti Wato IMAN Da Take Asibitin Malam Aminu Kano (Teaching Hospital) Tana Gayyata Yan Uwa maza Da Mata Zuwa Lacca Da Za’a Gabatar Kamar Haka:

Rana: Gobe Insha Allah 05-08-1443 Daidai Da 08-03-2022.

Mai Gabatarwa: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa (Hafizahullah).

Maudu’i: Kula Da Mara Lafiya a Lokacin Gargara A Mahangar Addinin Musulunci.

Lokaci: Karfe 2:00Pm Na Rana.

Waje: AKTH Conference Hall, Catering Department.

Allah Ya Kaimu Ya Bada Ikoh Zuwa Amin.

06/03/2022

Yau Lahadi in sha Allah, Malam zai fara karatun sabon littafi na Silatul-Arhaam (wato kyautatawa yan'uwa da masoya) na mawallafin littafin da aka kammala, wato Shaykh Saeed Bn Aliy Bn Wahab Al-Qahdaaniy (RH). Wannan Ya biyo bayan kammala littafin Birrul Waalidayn ne a cikin darasi 15.

A isar da sakon ga wadanda suke samun halartan karantu a Masallacin Annoor Wuse 2, Abuja.

Allah Ya sa mu dace, Ya sa karatun ya zama dalilin tsira gare mu duniya da lahira.

Signed: Management

02/03/2022

Nigeria zata kashe
Naira Biliyan Uku
wajen kwaso
'Ya'yanta daga Ukraine

19/02/2022

IDAN KAJI ANA ZAGIN MALAMI. TO WA'AZINSA NE YAJE INDA AKE DA BUƘATAR ZUWANSA.
-
❝Duk sanda kaji ana zagin wani malamin sunnah mai da'awa ta gaskiya zuwa ga tafarkin Allah a cikin wa'azozi na'sa, ko wani ɓangare na wa'azinsa, to haƙiƙa ya cancanci ya zuba ruwa a ƙasa ya sha sabida murna da tsananin godiya ga Allah maɗaukakin sarki, domin haƙiƙa wa'azinsa ya'je inda yake da buƙata yaje, ya rage ga ma'abota jin wa'azin na'sa suyi amfani dashi ko kuma suyi biris dashi, amma shi dai ya sauke haƙƙinsa na wa'azantarwa❞
-
"Dukkanin wani malami na gaskiya kuma mai tsoron Allah, bazai faɗi abin da yasan zai fusata Allah domin ya farantawa mutane ba, sai dai idan yayi kuskure a matsayin sa na ɗan adam, domin shima ai baifi ƙarfin yin kuskure ba a cikin kalamansa"
-
"Amma tabbas yana daga cikin alamun nasarar mai yin wa'azi game da wata ɓarna da ake yawan yinta a ban-ƙasa, shi ne: idan ya yi wa'azin sai mutane su dinga zaginsa, tabbas wannan ke tabbatar masa da cewa haƙiƙa wa'azinsa ya na zuwa gurin da ya da'ce yaje"
-
Muhammad Umar Baballe.
Abu Amatullah.

19/02/2022

RAYUWAR DA BA DAƊEWA ZA AYI BA.
-
"Rayuwar da ba daɗewa za ayi ba, to menene ya kawo haɗama a cikin ta, menene ya kawo son duniya fiye da lahira, menene ya kawo wasu suke halaka wasu domin su su dauwama a cikin ta?. Tabbas dukkanin wanda ya ruɗu da wannan duniyar, to haƙiƙa za ta kaishi ta baro shi a inda bai yi tsammani ba, tabbas Allah yana iya yafe laifin da ke tsakanin sa da bawa, amma baya taɓa yafe laifin da yake a tsakanin bawa da bawa har sai sashen su ya yafewa ɗayan sashen"
-
"Da yawan mutane s**an riƙi wannan duniyar tamkar wata madauwamiya a garesu, ba sa taɓa yin tunanin mutuwa a cikinta, s**an saɓi Allah ne ta yadda s**a so, s**an bi dukkanin wata hanyar da za ta faranta musu rai ne koda kuwa za su saɓawa mahaliccin su Allah, to lallai ne Allah yana nan a madakata, kuma da sannu zai sakankawa dukkanin wata rai a bisa abin da ta kasance tana gabatarwa a wannan duniyar"
-
"Mallam rayuwar nan fa ba ta da tsayi, kawai kayi ƙoƙari ka bautawa Allah, wannan ita ce kaɗai hanya mai ɓullewa a gareka"
-
Biyo Instagram ɗinmu
https://instagram.com/hausa.islamic.pictures.quotes?igshid=11g6c9k6osqg5
-
Telegram channel
https://t.me/hausaislamicpicturesquotes

20/01/2022

Kakakin 'yan sandan jihar Kano yayi bayanin yadda aka gano gawar Hanifa yarinyar da Malamin makarantarsu yayi garkuwa da ita ya kuma kashe ta

Address

Dutse

Telephone

+2348166623405

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kima Global Concept posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share

Category

Nearby media companies