Jaridar Kabawa

Jaridar Kabawa JARIDAR KABAWA

Acikin Photo:- Yadda gobara taci dabbobi da tarin abinci a Garin BAWADA  mazaɓar kambaza dake ƙaramar hukumar mulki ta G...
26/11/2024

Acikin Photo:- Yadda gobara taci dabbobi da tarin abinci a Garin BAWADA mazaɓar kambaza dake ƙaramar hukumar mulki ta Gwandu jihar Kebbi.

A shirye Nike tsaff in Auri (Hamdiya Sidi Shareef) in har tana buƙatar hakan. Cewar Sama'ila Umar Mazauni  Ɗakin gari da...
26/11/2024

A shirye Nike tsaff in Auri (Hamdiya Sidi Shareef) in har tana buƙatar hakan. Cewar Sama'ila Umar Mazauni Ɗakin gari dake Jihar Kebbi.

YADDA MAMACI ZAI GANE SHI MATACCE NE,mamaci ba zai gane shi matacce ba ne a karon farko, saboda abun zai masa k**ar a ma...
25/11/2024

YADDA MAMACI ZAI GANE SHI MATACCE NE,
mamaci ba zai gane shi matacce ba ne a karon farko, saboda abun zai masa k**ar a mafarki, zai ga yana kuka yana shure shure yana kaiwa da komowa har ya kai ga anamishi wanka, a kuma ɗaukeshi zuwa magabarta duk zai na ganin abun k**ar a mafarki,

Bai yadda cewa ya zama gawa ba,
sai bayan an bun ne shi yanaji ana cewa kutura ƙasa ta ɓangaren can, ganan baiji ƙasa ba, ku kawo ɗanyan kasa ta bangarennan, a wannan lokacin zai ringa cewa mutane mai kuke kokarin yi ne,

Bayan kowa ya bar maƙabarta, anbarshi shi ka dai a cikin kasa, sai Allah yasa a dawo masa da ransa ya ɓude idon sa ya farka a cikin matattu,

Daga lokacin zai fara murna ya farka daga mummunan mafarki,

A Wannan lokacin sai ya godewa Allah
ya yi yun ƙurin miƙewa sai yaji ansuturtashi, an daddamkeshi da wata riga marar hannu, babu aljihu ba wuya, sai ya fara mamaki da tambaya a karon farko,

A ina nake haka? Ina ne nan? ba wutar lantarki, ba AC, ba fanka, an rufeni ta kowani ɓangare,

Mai na ke yi a nan ?

To a nan ne zai gane lallai yana cikin kasa,zai kuma tabbatar cewa lallai yanzu ba mafarki bane mutuwace ta gaskiya,

A wannan lokacin zai yi wani sauti mai karan gaske, yana kiran yan uwansa k**ar yadda ya ke yi anan duniya
idan yana bukatar dauki

Zairinka kiran sunayen ƴan uwansa,
Amma zai ji babu mai amsa masa, to daga nan zai soma fahimtar cewa allah ne ka ɗai zai agaza masa, to a lokacin zai din ga fadan astagfirullah,

Allah natuba ka agaza mini kaji kaina,

Ya na furta haka a cikin tsoro mai tsanani,

Idan mutumin kirki ne a lokacin mala'iku biyu zasu bayyana a gareshi cikin kyakkyawan fuska, sai su tallafeshi s**e kwantarda hankalinka daga nan zai fara samun kyakkyawan agaji,

Jama'a mu tuba zuwa ga Allah, mu gyara ayyukan mu, musani cewa babu makawa sai mun riski mutuwa, ya Allah ka sa mu cika da imani amin.

Dattijiwa ƴar shekaru 130 tarasu bayan watanni uku data karɓi addinin Musulunci.
24/11/2024

Dattijiwa ƴar shekaru 130 tarasu bayan watanni uku data karɓi addinin Musulunci.

Waye gwanin ku acikin waɗannan gwamnoni a jihar Kebbi, waye yafi kawo ci gaba a faɗin Jihar Kebbi karkara da birane?
14/11/2024

Waye gwanin ku acikin waɗannan gwamnoni a jihar Kebbi, waye yafi kawo ci gaba a faɗin Jihar Kebbi karkara da birane?

AIKIN ALHERI: Malama Hajara ƴar ƙabilar Yoruba ta Gina Sabon Masallaci a Wani kauye Dake Jahar Niger State.🥰Allah Yakara...
21/10/2024

AIKIN ALHERI: Malama Hajara ƴar ƙabilar Yoruba ta Gina Sabon Masallaci a Wani kauye Dake Jahar Niger State.🥰

Allah Yakara Ɗaukaka Musulunci 🙏

Jami'an tsaron Soji sun Sami Nasara Sheke wasu Yan Bindiga tare da k**a masu Kai masu Mak**ai a Jahohin Sokoto katsina d...
19/10/2024

Jami'an tsaron Soji sun Sami Nasara Sheke wasu Yan Bindiga tare da k**a masu Kai masu Mak**ai a Jahohin Sokoto katsina da Zamfara.

An samu wannan Nasara k**a waɗannan a Jihar Plateau yau . Jama'a ku dubi tsohonnan har furfura a geme sannan ku dubi wannan mata tayi shiga ta k**ala amma dukkansu zuciya babu kayau 😭

Mark Bazai Bari mu Dora maku Hutunan Mushen wadanda aka shekeba amma zamu edit mu tura

Muna Addua Allah Ya ci gaba da taimakon jami'an tsaron mu Ya Kuma Kara Tsare Muna Alu'mmar mu daga Sharin miyagun bayi Amin.

A Jihar kebbi, Al'ummar Garin Yauri Sunyi Nasarar Kashe Wata  Dorina Wacce Ta Addabi Mutanan Yankin.
07/10/2024

A Jihar kebbi, Al'ummar Garin Yauri Sunyi Nasarar Kashe Wata Dorina Wacce Ta Addabi Mutanan Yankin.

Subhanallah: Yan bindiga sun yi wa jami'an Community Watch Corps kwantan bauna a hanyar Yankara zuwa Faskari sun kashe j...
04/10/2024

Subhanallah: Yan bindiga sun yi wa jami'an Community Watch Corps kwantan bauna

a hanyar Yankara zuwa Faskari sun kashe jami'an Dikko 4 yan bijilante 2 dake karamar hukumar Faskari jihar Katsina

Allah Ubangiji ya jiƙansu da rahama 😢🙏

16/09/2024

Alhamdulillahi Zamu Dawo Bakin Aiki Insha Allah

Kotun Koli ta yanke hukunci a ci gaba da amfani da tsoffi da sabbin kuɗi har sai  yadda hali ya yi
29/11/2023

Kotun Koli ta yanke hukunci a ci gaba da amfani da tsoffi da sabbin kuɗi har sai yadda hali ya yi

Rundunar sojoji tare da haɗin guiwar ƴan banga sunyi nasarar kuɓutar mutane shida (6) da akayi garkuwa dasu a ƙaramar hu...
27/11/2023

Rundunar sojoji tare da haɗin guiwar ƴan banga sunyi nasarar kuɓutar mutane shida (6) da akayi garkuwa dasu a ƙaramar hukumar mulki ta Shanga dake Jihar Kebbi:

Daga Sani Twoeffect Yawuri

Nasarar hakan tazo a wani harin da rundunar sojojin da ta ƴan bangan s**a kai ranar juma'a 24/11/2023 a dajin shangan bayan wani rahoto da s**a samu.

Waɗanda aka kuɓutar mutane shida (6) maza k**ar yadda daraktan harkokin tsaro na cabinet office Abdulrahman Usman ya bayyana.

Haka kuma ya bayyana wadanda aka kuɓutar din suna cikin koshin lafiya inda tuni aka haɗasu da iyalansu.

An dai yi nasarar kuɓutar da mutanen ne a dajin Kogon Damisa dake Saminaka a ƙaramar hukumar mulki ta Shanga wanda dajin shine kan iyakar Jihar Kebbi da Jihar Neja.

Muna addu'ar Allah ya kara baiwa jami'an tsaron kasar mu nasara kuma ya bamu zaman lafiya a fadin duniya baki daya

Najeriya Zata Daina Shigo da Man Fetur Daga 2024 ~ NNPCLA wani Gagarumin Nasarar da Najeriya ta samu na samun ‘yancin ci...
24/11/2023

Najeriya Zata Daina Shigo da Man Fetur Daga 2024 ~ NNPCL

A wani Gagarumin Nasarar da Najeriya ta samu na samun ‘yancin cin Gashin kai, Manajan Darakta GMD na Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC), Mele Kyari, ya yi kakkausar murya ya bayyana cewa shigo da mai zai daina wanzuwa a Najeriya nan da shekarar 2024.

Wannan sanarwar da aka bayyana ta nuna wani muhimmin lokaci mai muhimmanci. A cikin tarihin al'ummar kasar, Wanda ke nuni da cewa an sauya sheka daga dogaro da man fetur Da ake shigowa dashi Daga ƙasar waje zuwa Najeriya

Hannun jarin da kamfanin mai na NNPC zai yi a matatun mai na zamani da ke warwatse a fadin kasar nan, zai kara karfafa samar da mai a cikin gida. Waɗannan ƙananan matatun mai, waɗanda ke da ƙarfin haɗin gwiwa sama da 50,000 bpd, za su taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ci gaba da samar da man fetur A cike da wajen kasar

Bugu da ƙari Kuma, Matatar Mai ta Dangote, matata mafi girma a nahiyar Afirka, tana gab da kammala aikinta, inda ta ke shirin shigar da ƙarin 650,000 a cikin man kasar. Wanda aka shirya zai fara aiki a shekarar 2024, Zai zama mai kawo sauyi ga yanayin man Najeriya.

KBC News

Mai Girma DSP Sen. Barau I Jibin Maliya CON Yabiwa Mara Lafiyar Nan Dan karamar Hukumar Kunchi Kundin Aiki da za,a yimas...
23/11/2023

Mai Girma DSP Sen. Barau I Jibin Maliya CON Yabiwa Mara Lafiyar Nan Dan karamar Hukumar Kunchi Kundin Aiki da za,a yimasa a asibiti
Ayau 23/11/2023

An k**a yaro dan shekara 16 bayan ya yi wa kananan yara mata 2 yan shekara 6, 5 fyade a Badariya jihar Kebbi
22/11/2023

An k**a yaro dan shekara 16 bayan ya yi wa kananan yara mata 2 yan shekara 6, 5 fyade a Badariya jihar Kebbi

Da Duminsa: Ɗaya daga cikin yan matan jami'ar FUDMA dake Dutsinma da yan bindiga s**a sace a ɗakin kwanansu ta kubutaƊal...
21/11/2023

Da Duminsa: Ɗaya daga cikin yan matan jami'ar FUDMA dake Dutsinma da yan bindiga s**a sace a ɗakin kwanansu ta kubuta

Ɗalibar ta ɓullo ta kauyen Ƙuncin-Kalgo ta jihar Zamfara

Bayan share sama da kwanaki 45, a hannun yan bindiga, ɗaya daga cikin yan mata 5 na Jami'ar gwamnatin tarayya dake Dutsinma ta kubuta.

Kamar yadda Shugaban Jami'ar Farfesa Arma'yau Bichi ya tabbatar wa majiyar Katsina Daily News ta BBC, ya ce yan bindigar sun sako ɗaya daga cikin daliban da s**a sace, inda ta bullo a kauyen Ƙuncin-Kalgo dake yankin karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

Ya ce duk da har yanzun ɗalibar ba ta kai ga isowa ba, amma tana kan hanyar dawowa gida yanzun haka.

Sai dai ya bayyana cewa ba a biya ko sisin kwabo wajen sako ɗalibar ba, suna dai ta rokon yan bindigar da su taimaka su saki daliban.

Dandazon magoya bayan Gwamnan jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf kenan lokacin da ya kai ziyara kasuwar Kantin Kwari a yau...
21/11/2023

Dandazon magoya bayan Gwamnan jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf kenan lokacin da ya kai ziyara kasuwar Kantin Kwari a yau.

📷Salisu Mohammed kosawa.

Address

Shanga
Birnin-Kebbi

Telephone

+2348161236022

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jaridar Kabawa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Jaridar Kabawa:

Videos

Share

Nearby media companies


Other Media/News Companies in Birnin-Kebbi

Show All