16/02/2022
Labaran Safiyar Laraba 16/02/2022CE - 14/07/1443AH. Cikakkun labarai
Shugaba Buhari ya amince da nadin Muhammad Bello-Koko a matsayin Shugaban Hukumar tasoshin ruwa, NPA.
Kamfanin NNPC ya umurci wuraren tara Mai su rika aiki awa 24.
Kotu ta bai wa Hukumar EFCC damar karbe wasu ƙaddarori da kudinsu ya kai Naira bilyan 3.7
Gwamnatin Tarayya ta dukufa wajen ƙara yawan man fetur da gas da take sayar wa Turai.
Wani matashi ya kashe kansa saboda budurwarsa ta juya masa baya a Kano.
Kwamitin Amaechi ya wanke Hadiza Bala Usman Tsohuwar shugabar Hukumar NPA.
Wahalar man fetur ta sanya 'yan buburuntu suna sayar da lita kan Naira 600.
Wasu bayanai na nuna cewa ƙananan hukumomin Jibiya da Batsari da Safana da suke jihar Katsina na hannun 'yan bindiga.
EPL: Manchester United ta sami nasara a kan Brighton da ci 2:0 a wasan jiya.
UCL: PSG ta sami nasara a kan Real Madrid da ci 1:0 a wasan jiya.
UCL: Manchester City ta sami nasara a kan Sporting CP da ci 5:0 a wasan jiya.