A.S.U Media TV

A.S.U Media TV Dan isar da sakonni tareda fitar da sahihan labarai, Da kuma tallace-tallace wa kamfanoni da sauransu
(43)

Wasu Ma’aikatan YOROTA A Jihar Yobe Su Aure Junansu
12/12/2023

Wasu Ma’aikatan YOROTA A Jihar Yobe Su Aure Junansu

Da alamu kungiyar NLC za ta sake tsunduma yajin aiki a kwanakin nan.Kungiyar ta yi barazanar ce bayan Tinubu ya dakatar ...
12/12/2023

Da alamu kungiyar NLC za ta sake tsunduma yajin aiki a kwanakin nan.

Kungiyar ta yi barazanar ce bayan Tinubu ya dakatar da biyan dubu 35 ga ma'aikata.

Wannan na zuwa ne bayan shugaban ya biya kudaden ma'aikatan Gwamnatin Tarayya na wata daya kacal.

CIGIYA: Barayi Sun Ƙwace Wannan Motar A BauchiMuna cigiyar wannan mota da barayi s**a kwace a wurin Bauchi club da daren...
12/12/2023

CIGIYA: Barayi Sun Ƙwace Wannan Motar A Bauchi

Muna cigiyar wannan mota da barayi s**a kwace a wurin Bauchi club da daren jiya, duk wanda ya ga ko ya ji an samu mota ga hoton ta nan,

Ku kira wannan number k**ar haka; 09064414455

Mun gode, Allah ya toni asirin su.

Wani matashi mai suna Sadiq Idrissu ya harbe mahaifiyarsa har lahira bisa zargin cewa ita mayya ce.Sadiq, mai shekara 30...
12/12/2023

Wani matashi mai suna Sadiq Idrissu ya harbe mahaifiyarsa har lahira bisa zargin cewa ita mayya ce.

Sadiq, mai shekara 30, daga ƙauyen Boga na ƙaramar hukumar Gombi ta jihar Adamawa, ya harbe mahaifiyarsa ce har lahira a ranar 5 ga watan Disambar da muke ciki.

Matashin, wanda ya amince da kashe mahaifiyar tasa, ya ce bai yi nadamar hakan ba, Saide ma, ya jajanta wa mahaifinsa bisa aure da kuma zama da ita.

"Na kashe mamata ce saboda ina daukanta a matsayin mayya. Mutane sun zarge ta da maita shekaru biyu da s**a gabata. Da gaske ne, saboda wani abu na tsoratar da ni musamman ma da dare, in ji Sadiq.

Matashin, wanda ke shan wani abu da ake kira 'zuƙa ka mutu' wato 'suck and die' a turance, ya ce mahaifiyarsa tana fito masa a mafarki matsayin mayya, kuma tana sanya masa tsoro, da kuma hana shi bacci da daddare.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Adamawa, SP Sulaiman Yahaya Nguroje, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ana kan bincike a kai.

Tasiu Hassan

Fasinjoji 10 sun kwanta dama a wani mummunan hatsarin mota a titin Legas-Ibadan.Hukumar FRSC ta tabbatar da lamarin, ind...
12/12/2023

Fasinjoji 10 sun kwanta dama a wani mummunan hatsarin mota a titin Legas-Ibadan.

Hukumar FRSC ta tabbatar da lamarin, inda ta ce wasu mutum bakwai na kwance a asibiti.

Kwamandan FRSC ya nuna damuwa kan yadda haɗarin ya auku, a cewarsa akwai ganganci.

Shararren Mahaddacin Al-Qur'anin Nan Sheikh Afif Zai Ziyarci Jihar KatsinaShahararren matashin mahaddacin Al-Qur'anin na...
12/12/2023

Shararren Mahaddacin Al-Qur'anin Nan Sheikh Afif Zai Ziyarci Jihar Katsina

Shahararren matashin mahaddacin Al-Qur'anin nan, Sheikh Afif Muhammad Taj, ɗan ƙasar Habasha zai halacci gagarumin bikin yaye ɗaliban makarantar Al-Falah Model Qur'anic Academy GRA Katsina, wanda s**a samu nasarar Saukewa da Haddace Al-Qur'ani Mai Girma.

Wanda za ayi ranar Lahadi 17 ga watan Disamba 2023 da ƙarfe 9 na safe, a babban ɗakin taro na jami'ar Umaru Musa 'YarAdua.

Sanarwa Daga
Abubakar Afif bin Hussain
Shugaban ƙungiyar Nigerian Supporters Sheikh Afif Muhammad Taj na ƙasa

Alhamdulillah APC,n Jihar Bauchi Zatadawo da Tagomashinta Nasara Natasamuwa Chikin Ikon Allah Ansamu Nagartaccen Shugaba...
12/12/2023

Alhamdulillah APC,n Jihar Bauchi Zatadawo da Tagomashinta Nasara Natasamuwa Chikin Ikon Allah Ansamu Nagartaccen Shugaba Adali Mutumin kirki Alhaji Muhammad Hassan Tilde...........

Daga Shafin Sani Bala ( Siyasar katagum) Auditor na Jam'iyyar APC a Jihar Bauchi.

Rundunar sojin saman Nigeriya ta yi ajalin wasu kasurguman 'yan ta'adda a jihar Niger.Daga cikin wadanda su ka mutun akw...
12/12/2023

Rundunar sojin saman Nigeriya ta yi ajalin wasu kasurguman 'yan ta'adda a jihar Niger.

Daga cikin wadanda su ka mutun akwai Ali Alhaji Alheri da aka fi sani da 'Kachalla Ali Kawaje'.

Har ila yau, sojin sun hallaka manyan kwamandojin Dogo Gide yayin harin a jiya litinin.

Aljihun wani matashi da ke tuka tsadaddiyar mota a turai na kuka.Matashin wanda ya mallaki mota kirar motar Benz C Class...
12/12/2023

Aljihun wani matashi da ke tuka tsadaddiyar mota a turai na kuka.

Matashin wanda ya mallaki mota kirar motar Benz C Class Coupe ya ce duk wata yana kashe N1.4m don kula da ita.

Ya gargadi matasa da ke sha’awar irin rayuwarsa cewa tana da tsada sosai.

Mako ɗaya bayan jefa bam kan masu Maulidi, yan bindiga sun sake kai hari yankin Igabi a Kaduna.Yayin harin, sun sace mut...
12/12/2023

Mako ɗaya bayan jefa bam kan masu Maulidi, yan bindiga sun sake kai hari yankin Igabi a Kaduna.

Yayin harin, sun sace mutum 30 ciki har da mata, yara da jariran da ba su haura shekara 2 ba.

Har yanzu hukumar ƴan sanda ba ta ce komai ba amma mazauna sun faɗi abinda ya faru.

Kimimiya Da Fasaha...Wadannan pipe din kuke gani hanyoyi ne da dalibai suke bi su tafi lectures ko hostels a jami'ar Tec...
12/12/2023

Kimimiya Da Fasaha...

Wadannan pipe din kuke gani hanyoyi ne da dalibai suke bi su tafi lectures ko hostels a jami'ar Technical University dake birnin Munich a kasar Germany.

Ba kuma bin hanyoyin akeyi ba da kafa ana tafiya, a'a, super akeyi suuuuuu a zaune saboda yafi sauri maimakon mutum yabi matakalan bene.

Daga bene hawa uku ko hudu, kana zama a bakin pipe din, suuuuu a seconds kadan zaka zo kasa.

Yanzu idan zakaje, Makabartar Bauchi, dole ka tsaya ka sayi Blocks.Domin babu Katakon da ake amfani da shi wajen Bisne G...
12/12/2023

Yanzu idan zakaje, Makabartar Bauchi, dole ka tsaya ka sayi Blocks.

Domin babu Katakon da ake amfani da shi wajen Bisne GAWA.

Allahuakbar, 😭😭😭

Daga: Abdulrahaman Bala katsinawa.

Tinubu na da kyawawan tsare-tsaren farfaɗo da martabar Najeriya a idon duniya - Hon Abdulmumin Jibrin KofaHon Abdulmumin...
12/12/2023

Tinubu na da kyawawan tsare-tsaren farfaɗo da martabar Najeriya a idon duniya - Hon Abdulmumin Jibrin Kofa

Hon Abdulmumin Jibrin Kofa, dan Majalisar Wakilai na mazaɓar Kiru/Bebeji, Kano, kuma shugaban Kwamitin Harkokin Waje na majalisar, ya yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya ƙara kuɗafen da ya ware wa Ma’aikatar Harkokin Waje domin cim ma kyawawan ƙudurorin da yake da su na harkokin waje, musamman ɓangaren bunƙasa Dimokuraɗiyya da ci gaba.

Ɗan majalisar ya yi kiran ne lokacin zaman haɗin gwiwa na kwamitocin Harkokin Waje na majalisun tarayya yayin kare kasafin kudin ma’aikatar wanda ya jagoranta tare da shugaban kwamitin na Majalisar Dattawa, Sanata Abubakar Sani Bello a ranar Litinin.

Kwamitocin dai sun bi diddigin kasafin kudin ma’aikatar na 2023, sannan s**a tace tare da tsefe kasafinta na 2024.

Yayin zaman dai, Ministan Harkokin Waje, Amb. Yusuf Maitama Tuggar, ya yi ƙarin haske a kan kasafin ma’aikatar na 2024 sannan ya yi bayani daki-daki kan manufofin Shugaban Kasa kan ƙasashen waje.

Sai dai kwamitin haɗin gwiwar ya ce bisa la’akari da waɗancan kyawawan manufofin na Shugaban Ƙasa, kasafin kuɗin da aka ware wa ma’aikatar a 2024 ya yi ƙaɗan wajen aiwatar da su.

Daga nan ne sai kwamitin ya bayar da shawarar ƙara wa ma’aikatar kuɗaɗe a kasafin, inda ya yi alkawarin tattaunawa da Shugaban Majalisar Dattijai da Kakakin Majalisar Wakilai da ma kwamitocin kasafin kuɗi na majalisun biyu, ko da hakan zai kai ga tattaunawa da Shugaban Ƙasa domin yi masa bayani a kan haka.

Ba abinda na fi so a duniya illa ci-gaban jihar Kano, domin ni dan Kano ne, in ji fitaccen mawakin siyasa a Kannywood, D...
12/12/2023

Ba abinda na fi so a duniya illa ci-gaban jihar Kano, domin ni dan Kano ne, in ji fitaccen mawakin siyasa a Kannywood, Dauda Kahutu Rara.

12/12/2023

Sakon Godiya wa Gwamnan Jihar Bauchi da tallafin da ya bawa masu Sana'ar wankin muta ta hannun kwamishinan kananan hukumomi Aliyu Ahmad Jalam Daga Daya daga cikin jagororin Kungiyar Masu Sana'ar wankin Mota na Jihar.

Najeriya Ta Kudiri Aniyar Samar da Cibiyoyin Lafiya Kimanin Dubu 17,000 A faɗin Najeriya Gwamnatin Najeriya ta dauki wan...
12/12/2023

Najeriya Ta Kudiri Aniyar Samar da Cibiyoyin Lafiya Kimanin Dubu 17,000 A faɗin Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta dauki wani gagarumin mataki na kawo sauyi ga tsarin kiwon lafiyarta, inda ta bayyana shirin samar da a kalla cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko Guda Dubu 17,000 a fadin kasar.

Wannan jajirtaccen shiri, Wanda ya zo daidai da Ranar bayar da tallafin kiwon lafiya ta duniya (UHC) a Ranar 12 ga watan Disamba. Yana wakiltar ƙaƙƙarfan ƙuduri don tabbatar da daidaito da kuma samun lafiya ga duk 'yan Najeriya.

Rana24 ta ruwaito Farfesa Ali Pate, Ministan Lafiya da Ci gaban Jama'a, ya bayyana jajircewar Shugaba Bola Tinubu wajen ganin ya samu nasarar UHC. Ya jaddada cewa Gwamnati na da niyyar isar da “mafi kyawun sak**ako” ga kowane dan kasa, ba tare da barin kowa a baya ba.

Wannan kyakkyawan aikin yana nuna canji mai ban mamaki daga cibiyoyin kiwon lafiya na farko Guda 8,000 na yanzu. Ta fiye da ninka wannan adadin, Gwamnati na da niyyar inganta haɓaka hanyoyin samun sabis na kiwon lafiya, Musamman a cikin al'ummomin da ba su da hidima.

Shirin ya nuna sabon zamani na hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da Hukumomin jihohi. A ranar Talata, jami'ai za su hada hannu da abokan aikin ci gaban kiwon lafiya don rattaba hannu kan wata yarjejeniya, Tare da karfafa kudurin su na tuki ayyukan UHC. Wannan ruhun haɗin kai yana da mahimmanci don tabbatar da nasarar wannan babban aiki.

Dole Ne 'Yan Najeriya Su Ɗauki Harin Bom Na Tudun Biri A Matsayin Ƙaddara Daga AllahShugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya b...
12/12/2023

Dole Ne 'Yan Najeriya Su Ɗauki Harin Bom Na Tudun Biri A Matsayin Ƙaddara Daga Allah

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana haka ya yin da ya kaiwa Shehun Borno Alhaji Abubakar Garbai, ziyara a ranar Litinin, bayan ya ƙaddamar da motocin zirga-zirga wanda gwamna Zulum ya samar a jihar.

Me za ku ce?

12/12/2023
Wasu majiyan na cewa Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Engr Abba Kabir Yusuf ta Shiga rudani, biyo bayan da bank...
12/12/2023

Wasu majiyan na cewa Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Engr Abba Kabir Yusuf ta Shiga rudani, biyo bayan da bankuna s**a Hana Hana Gwamnatin taba kudaden Jihar ta hanyar rurrufe akwatunan asusun ajiyan na Jihar Kano Baki Daya.

Shin ya kuke ganin wannan lamarin?
Sannan Mai dalilin yin hakan ?

12/12/2023

Ameenullah Shatima ya ja hankalin masu hannu da shuni kancewa sudinga kokarin Kula da makabartu wajen bada Gudummawar kudi ko kayan aiki da a dinga bada kyakkyawar kulawa wa makabartun dake Jihar Bauchi.

Sannan ya yabawa Alh Ibrahim Ago Shugaban matasan Jam'iyyar adawa ta APC bisa namiji kokarin da yayi da bada katakai da luru da ayyukan makabartan.

Assalamualaikum Warahmatullahi Wa Barkatuh. Jama-a Muna Cikiyar Wannan Dalibar Makarantarmu Dake Sabon Unguwar Railway M...
11/12/2023

Assalamualaikum Warahmatullahi Wa Barkatuh.
Jama-a Muna Cikiyar Wannan Dalibar Makarantarmu Dake Sabon Unguwar Railway Makarantar Ikhlas Litilawatil Qur'an Waddirasatil Islamiya Sabon Unguwar Railway Bauchi.
Dan Allah Duk Wanda Yaji Labarinta Ya Tuntube Mu A Lambar Wayarmu Dake Kasa.

08134870799

11/12/2023

ZAMFARA DAI:
'Yan ta'adda sun kashe mutum uku, sun arce da mata da ƙananan yara bayan banka wa rumbunan hatsin talakawa wuta a yankin Zurmi

Allahu Akbar ....Allah ya Kara mana karfin Imani da tsoron sa.
11/12/2023

Allahu Akbar ....
Allah ya Kara mana karfin Imani da tsoron sa.

Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya yi abin a yaba bayan raba muk**ai har guda 64.Sanatan da ke wakiltar Sokoto ta Kudu ya b...
11/12/2023

Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya yi abin a yaba bayan raba muk**ai har guda 64.

Sanatan da ke wakiltar Sokoto ta Kudu ya ba da muk**an ne na hadimansa na musamman a mazabarshi.

Sanatan ya bayyana dalilin raba muk**an inda ya h**e su da aiki tukuru.

A kokarin rage tsadar mak**ashin girki da jama’a ke amfani da shi a Najeriya, gwamnatin kasar da soke batun biyan harajı...
11/12/2023

A kokarin rage tsadar mak**ashin girki da jama’a ke amfani da shi a Najeriya, gwamnatin kasar da soke batun biyan harajın VAT da ma karbar kudin fito daga dillalan da ke shigo da iskar daga kasashen waje.

Ko kuna ganin hakan zai sauko da farashin gas din na girkin a kasuwanni?

Tsohon Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya ziyarci Tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a gidansa da ke Da...
11/12/2023

Tsohon Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya ziyarci Tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura a jihar Katsina.

11/12/2023

Mun k**a kifi inji Ali Baba.
Yayin da yake stegunta wa Dr Ganduje Cewar wani Sanata zai Sauya sheka zuwa Jam'iyyar su ta APC.

Tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya roki kungiyar ECOWAS da ta cire wa Nijar takunkuman da ta kakaba mata. ‘Yan Ni...
11/12/2023

Tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya roki kungiyar ECOWAS da ta cire wa Nijar takunkuman da ta kakaba mata.

‘Yan Nijar sun fada matsi tun bayan da ECOWAS ta kakaba wa kasarsu takunkumai sak**akon juyin mulkin da sojoji s**a yi a kasar a watan Yulin da ya gabata.

Takunkuman sun hada da rufe iyakokin Nijar da kasashen mambobin ECOWAS da katse mata wutar lantarki daga Nijeriya.

YANZU-YANZU: ‘Yan Nijar sun roki Buhari ya sanya baki a bude boda Wasu 'yan fafitikar farar hula na jihar Damagaram ciki...
11/12/2023

YANZU-YANZU: ‘Yan Nijar sun roki Buhari ya sanya baki a bude boda

Wasu 'yan fafitikar farar hula na jihar Damagaram ciki har da Sadat iliya Dan Malam da Moustapha Adam Obama sun ziyarci tsohon shugaban kasar Najeriya Muhamadu Buhari

Domin rokon shi ya saka baki don ECOWAS ta sassuta takunkumin da ta kakabawa Nijar Sak**akon A halin Yanzu suna Cikin ƙunci

Me zaku ce?

11/12/2023

Kalaman Sarkin Kano Akan Malam Isah Ali pantami.

Allah Ya taimaki Sarkin Kano!
Allah Ya sa Aljannah ce makomar mu gaba daya.

SANATA SHEHU BUBA UMAR YA HALARCI BIKIN YAYE DALIBAN HUKUMAR LEKEN ASIRI NA KASA________Mai girma Sanatan Bauchi ta Kudu...
11/12/2023

SANATA SHEHU BUBA UMAR YA HALARCI BIKIN YAYE DALIBAN HUKUMAR LEKEN ASIRI NA KASA
________

Mai girma Sanatan Bauchi ta Kudu Kuma kuma shugaban kwamitin tsaro da leken Asiri a Majalisar dattijan Nijeriya. Shehu Buba Umar ya halarci wurin bikin yaye daliban hukumar leken asiri ta kasa, a Abuja.

Taron wanda mataimakin Shugaban kasa Kasheem Shatema ya Halarta,Shima Ministan Foreign affairs Amb Yusuf Maitama Tuggah ya samu halartan Taron tare da sauran kusoshin Gwamnatin tarayyar Nijeriya.

Sanata Shehu Buba na cikin wanda s**a gabatar da jawabi ga Daliban yanda ya nemi su zama yan kasa nagari domin kare martaba Nijeriya ta fuskan tsaro.

11/12/2023

Wadanda aka kora daga filin tantacewa na niman Shiga aikin dan sanda .

Sababbin hotonan Jarumar Tiktok Murja Ibrahim Kunya Wanda ta wallafa a shafinta na Facebook a safiyar nan.
11/12/2023

Sababbin hotonan Jarumar Tiktok Murja Ibrahim Kunya Wanda ta wallafa a shafinta na Facebook a safiyar nan.

BABU JIHAR DA TA SAMU ALKHAIRAN DA MUKA SAMU A TARON ƊUMAMAR YANAYI NA DUNIYA, CEWAR KWAMISHIN MUHALLI NA JIHAR ZAMFARAK...
11/12/2023

BABU JIHAR DA TA SAMU ALKHAIRAN DA MUKA SAMU A TARON ƊUMAMAR YANAYI NA DUNIYA, CEWAR KWAMISHIN MUHALLI NA JIHAR ZAMFARA

Kamar yadda majiyar mu ta ruwaito, mai girma kwamishinan muhallai da albarkatun ƙasa na Jihar Zamfara, Alhaji Mahmud Muhammad Abdullahi, ya bayyana cewa Jihar Zamfara ta samu nasarar cimma yarjeniyoyi da manyan kamfanonin Duniya za shigo Jihar Zamfara su tallafawa al'ummar Jihar ta fuskar samar da murahun girki masu sauƙin cin itace da kuma samar da wutar lantarki a garuruwa da dama.

Tunda farko kwamishin ya fara ne da cewa: "Mu ma muna da matsalolin da ke damunmu k**ar sauran ƙasashen Duniya, kuma mun samu taimako muna kuma sa ran samun ƙarin wani tallafin a taro na gaba wata shekarar. Zuwan ya yi mana amfani sosai, mun yi abubuwa da dama da za mu samu taimako daga waɗanda su ke da halin taimakawa.

Kwamishin ya bayyana cewa daga cikin tarin alkhairan da Jihar ta samo a taron sun haɗa da:

1. An samu nasarar ƙulla alaƙa da kamfanin GGI za su shigo Jihar Zamfara a watan Fabarairu, za su taimakawa Jihar wajen samar da kundin tsari wanda zai taimakawa Jihar wajen samun tallafin kuɗaɗe da haɗin-gwiwa da manyan kamfanoni da ƙungiyoyi masu bada agaji na Duniya kan ɗumamar yanayi.

2. An samu nasarar ƙulla alaƙa da kamfanin da ke samar da mak**ashi wanda zai tallafawa Jihar Zamfara da Naira (Biliyan 25), ita ma Jihar za ta ƙara nata kason domin a samarwa ƙauyuka wuta mai amfani da hasken rana.

3. Gwamnan Jihar Zamfara ya tsara raba murhu ga gidaje(2,000) a Jihar Zamfara, kuma an tallata tsarin a wurin taron, a sanadiyyar hakan kamfanin samar da murahu masu ƙarancin cin itace, (Green Cooking Alliance) na ƙasar Amurka ya yi alƙawarin zai shigo Jihar Zamfara shi ma ya bada tasa gudunmawar.

Da ya ke tsokaci game da alfanun murhun kuwa, kwamishin ya bayyana cewa: "Murhun ɗan ƙarami ne zai iya dafa abinci na wata shida. Koda ba a yi amfani da ice ba, in aka saka gawayi biyu ko uku zai iya dafa abinci. Zai zamto ba a samun hayaƙi da ya ke cutar da mutane

11/12/2023

Kalaman Malam Nappa Hotoro Gameda wadanda aka kashe da bam a yayin da suke taron Maulidi na Garin biri dake Jihar Kaduna.

A madadin Kamfanin A.S.U Media And General Services tana Mika sakon Taya murnan zagayowan Raman Haihuwa wa Tsohon Gwamna...
11/12/2023

A madadin Kamfanin A.S.U Media And General Services tana Mika sakon Taya murnan zagayowan Raman Haihuwa wa Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi H,E M•A Abubakar SAN.
Tar da masa fatan Alkhairi da gamawa lafiya, Allah ya Karo dimbin nasarori da shekaru masu Albarka.

Daga Kamfanin A.S.U Media and General Services.

11/12/2023

Tsohuwar ajiya.
Kalaman tsohon Gwamnan Jihar Bauchi
H,E M•A Abubakar SAN.

Duk wani Mai rai sai ya Dan dani mutuwa.Allah yajikanki da rahamarsa.
10/12/2023

Duk wani Mai rai sai ya Dan dani mutuwa.
Allah yajikanki da rahamarsa.

Juma'at MubarakHon Salisu Tanko YakasaiDawisun Kanawa .
08/12/2023

Juma'at Mubarak
Hon Salisu Tanko Yakasai
Dawisun Kanawa .

Address

Bauchi

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when A.S.U Media TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to A.S.U Media TV:

Videos

Share


Other Media/News Companies in Bauchi

Show All