Martaba FM

Martaba FM An online News Platform. online media
(1)

02/04/2024

Matashin ɗan Badan wanda ake zargi da yi wa wani abokin faɗansa yankan Rago da Zarto a unguwar Ɗorayi da ke birnin Kano, ya ce lokacin da ya aikata kisan sai da imaninsa ya fita.

Tini dai rundunar Ƴansandan Kano ta k**a matashin wanda ya yi yunƙurin tserewa zuwa ƙasar Nijar.

Bidiyo: Abdullahi Haruna Kiyawa/Facebook

Wasu al'umma mazaunan jihar Kebbi sun  daka wawa ga kayan abinci, bayan sun afka cikin wani gidan ajiyar kaya na gwamnat...
01/04/2024

Wasu al'umma mazaunan jihar Kebbi sun daka wawa ga kayan abinci, bayan sun afka cikin wani gidan ajiyar kaya na gwamnati a unguwar Bayan Kara cikin Birnin Kebbi, da kuma fasa shagunan ƴan kasuwa, inda s**a wawashe buhunhunan kayan abincin da ke ciki,

Rahotanni sun ce mutanen sun bijire wa jami'an tsaron da aka jibge a gidan ajiyar, inda s**a saci kayan abinci.

Shugaban ɗariƙar Qadiriyya ta Afrika Sheikh Qaribullah Nasiru Kabara, ya zargi mawaƙan Hipop da rugurguza tarbiyar ƴaƴan...
31/03/2024

Shugaban ɗariƙar Qadiriyya ta Afrika Sheikh Qaribullah Nasiru Kabara, ya zargi mawaƙan Hipop da rugurguza tarbiyar ƴaƴan Musulmi a jihar jihar Kano.

29/03/2024

Yadda al'ummar musulmai ke halartar tafsirin Alƙur'ani mai girma a fadar Sarki Kano tsawon kwanakin Azumin watan Ramadan.

"Address Food Crisis now" - Obi tells FG, Says the Terror and Bandits Effect is worrisomeRead more https://tinyurl.com/5...
29/03/2024

"Address Food Crisis now" - Obi tells FG, Says the Terror and Bandits Effect is worrisome

Read more https://tinyurl.com/5n7p8bau

Wata babbar kotun jihar Kano ta yankewa ɗan ƙasar china, Mr. Frank Geng Quarong, hukuncin kisa ta hanyar tataya, a sak**...
26/03/2024

Wata babbar kotun jihar Kano ta yankewa ɗan ƙasar china, Mr. Frank Geng Quarong, hukuncin kisa ta hanyar tataya, a sak**akon samun da da laifin kashe budurwar sa Ummulkhulsum Sani Buhari, wanda aka fi sani da Ummita.

25/03/2024

Abinda ya sa na yi waƙar "na samu fara, mulkin Tinubu"- Mawaƙi Usman.

Mawaƙin wanda ɗan asalin jihar Bauchi ne mazaunin birnin Kano mai suna Usman Ahmad Adam wanda aka fi sani da Usman A Faggo, ya ce, a cikin waƙar tasa akwai darasi.

Mawaƙin ya kuma ce, ba ya yin adawa da gwamnatin Bola Ahmad Tinubu shugaban ƙasar Najeriya, amma ya ce, akwai buƙatar al'ummar ƙasar su gyara halayensu.

Me za ku ce?

25/03/2024

Rukunin kamfanonin M.Abba Trading Company da M.Abba Gallery da kuma M.Abba Textiles, M.Abba Perfume Incense, suna yi muku barka da Azumin watan Ramadan da fatan za kammala lafiya, tare da yin idaba karɓarɓiya.

25/03/2024

Murja Kunya Ta Yi Nadama, Ba Za Ta Bijirewa Sharuɗan Bayar Da Belinta Ba- Rahoto.

25/03/2024

Ayyukan Da Manzon Tsira Annabi Muhammad S.A.W Ke Yi A Kwanaki Goman Ƙarshen Watan Ramadan- Saƙon Mai Azumi.

24/03/2024

"Kasuwancin Zamani" sabon shiri ne za mu dinga kawo muku shi, zai dinga mayar da hankali kan kasuwanci da taltalin arziƙi na zamani.

Yau ta cikin shirin mun tabo batun yadda kudin Internet za su danne na takarda a duniya, sai kuma batun Kirfto.

Ku biyo mu cikin shirin.

Hotunan ɗaliban makarantar Kuriga ta jihar Kaduna su 137 da sojojin Najeriya s**a ceto a daren lahadin nan a jihar Zamfa...
24/03/2024

Hotunan ɗaliban makarantar Kuriga ta jihar Kaduna su 137 da sojojin Najeriya s**a ceto a daren lahadin nan a jihar Zamfara.

23/03/2024

Ƴan Arewacin Najeriya Ba Sa Yin Amfani DA Social Media Yadda Ya Kamata- Kwararre.

Mujaheed Ibrahim wanda kwararren mai amfani da kafafen sada zumunta ne ya bayyana mana yadda ya k**ata a yi amfani da su.

Ku kalli karin bayanin sa.

23/03/2024

Kaf jam'iyyar NNPP babu wanda ya yi aikin da Aliyu Sani Madaki ya yi, ko Gwamna bai kai shi aiki ba.- Aliyu Zangina.

Ƴa'ƴan Jam'iyyar NNPP Kwankwasiyya a ƙaramar hukumar Dala na ci gaba da kokawa kan karbar wasu tshoffin kansiloli da jagororin jam'iyyar APC da s**a fice zuwa mai kaya marmari.

Aliyu Muhammad Zangina ya ce da sake a lamarin, ga abinda ya shedawa shirin siyasa na "Inda Ba Ƙasa".

Me za ku ce?

Ƴan Arewacin Najeriya Ba Sa Yin Amfani DA Social Media Yadda Ya Kamata- Kwararre.Yau Asabar Da Ƙarfe GomanDare Agogon Na...
23/03/2024

Ƴan Arewacin Najeriya Ba Sa Yin Amfani DA Social Media Yadda Ya Kamata- Kwararre.

Yau Asabar Da Ƙarfe Goman
Dare Agogon Najeriya Za Mu
Kawo Muku Hira Ta Musamman
Kan Yadda Ake Amfani Da Social Media.

Ƙungiyar Da Ke Kare Namun Daji Da Shi Kansa Gandun Dajin Da Kyautata Muhalli A Jihar Bauchi.
23/03/2024

Ƙungiyar Da Ke Kare Namun Daji Da Shi Kansa Gandun Dajin Da Kyautata Muhalli A Jihar Bauchi.

Ƙungiyar Da Ke Kare Namun Daji Da Shi Kansa Gandun Dajin Da Kyautata Muhalli A Jihar Bauchi. ...

23/03/2024

An samun ƙaruwar mabuƙata ya yin da ake ci gaba da fuskantar tsadar rayuwa a Najeriya.

Shugaban wata gidauniya a jihar Bauchi Malam Ibrahim Muhammad Inuwa, ne ya bayyana wa Martaba FM hakan a wata zantawa da shi.

23/03/2024

Mai yin fushi ko harsala zai iya samun matsala a cikin Azuminsa.

Malam Aminu Adamu Muhammad, na'ibin limamin masallacin Juma'a na Alfurƙan da ke birnin Kano, ya yi mana karin bayani kan illar fushi ga mai Azumi.

Saƙon Mai Azumi

Ƙasar Nijar Ta Buɗe Iyakokinta Da Najeriya Sama Da Mako Guda Bayan Najeriya Ta Buɗe Nata.
22/03/2024

Ƙasar Nijar Ta Buɗe Iyakokinta Da Najeriya Sama Da Mako Guda Bayan Najeriya Ta Buɗe Nata.

Ƙasar Nijar Ta Buɗe Iyakokinta Da Najeriya Sama Da Mako Guda Bayan Najeriya Ta Buɗe Nata. ...

22/03/2024

Yau ta cikin shirin Saƙon Mai Azumi Malam Umar Ɗahiru Soron Ɗinki, Ya Yi Mana Ƙarin Bayani Kan Karatun Alƙur'ani mai girma a lokacin Azumi.

21/03/2024

Manufofinmu sun yi daidai na gwamnatin jihar Kano, za mu kawo sauyi ga yadda ake tafiyar da ƙaramar hukumar Dala- Aminu Mamman Yaro.

Aminu Mamman Yaro, shugaban ƙungiyar Kwankwasiyya Dubai kuma ɗan takarar shugaban ƙaramar hukumar Dala da ke jihar Kano a Jam'iyyar NNPP ya bayyana mana manufofinsa na fitowa takara.

Ku kalli cikakkiyar hirarsa da mu ta cikin shirin "Inda Ba Ƙasa".

Me za ku ce?

Yau Alhamis ƙarfe goman dare agogon Najeriya Za mu kawo muku hira da Aminu Mamman Yaro, shugaban ƙungiyar Kwankwasiyya D...
21/03/2024

Yau Alhamis ƙarfe goman dare agogon Najeriya Za mu kawo muku hira da Aminu Mamman Yaro, shugaban ƙungiyar Kwankwasiyya Dubai kuma ɗan takarar shugaban ƙaramar hukumar Dala da ke jihar Kano a Jam'iyyar NNPP.

Za ku iya bayyana mana ra'ayoyin ku yanzu.

21/03/2024

Malamin addinin Musuluncin wanda limamin masallacin Juma'a ne a Kano ya bayyana mana cewa akwai buƙatar a ƙara zage dantse wanjen ayyukan alkairi a wannan goma ta biyu da masu Azumi s**a shiga.

La'akari da tsadar rayuwa da ake fama da shi a Najeriya, Dakta Yahaya Khamis Idiris, ya ce Zai yi kyau a ƙara matsawa da addu'a domin neman sauƙi.

Kai Gwauro Waye Ya Ke Tashin KaYin Sahur?
21/03/2024

Kai Gwauro Waye Ya Ke Tashin Ka
Yin Sahur?

Jerin sunayen masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Najeriya da gwamnatin tarayya ta fitarƘarin bayani: https://tinyurl.com/5y...
20/03/2024

Jerin sunayen masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Najeriya da gwamnatin tarayya ta fitar

Ƙarin bayani: https://tinyurl.com/5yxxdp4p

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya ce yana ganin k**ar baƙi daga ƙetare ne s**a hallaka sojojin Naj...
19/03/2024

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya ce yana ganin k**ar baƙi daga ƙetare ne s**a hallaka sojojin Najeriya 17 a Jihar Delta.

Shugaban majalisar ya bayyana hakan ne a lokacin da suke tattaunawa a zauren majalisar kan kisan kiyashin da aka yi wa zaratan dakarun a makon jiya.

Akpabio ya ce, “Mutanen Delta, mutanen kirki ne, ba na tunanin za su iya aikata irin wannan mummunan aiki.

“A ganina waɗansu ne baƙi daga ƙetare ne s**a kitsa wannan abin takaicin kuma s**a aiwatar, ba na so in yarda cewa jama’ar Delta ne.”

Sanata Akpabio ya buƙaci a kafa wani kwamiti mai karfin gaske da zai binciki faruwar wannan abin baƙin cikin da ya samu Najeriya.

Shugaba Bola Tinubu ya ce wadanda s**a kashe dakarun soji 16 a yankin Okuoma da ke Karamar Hukumar Ughelli a Jihar Delta...
17/03/2024

Shugaba Bola Tinubu ya ce wadanda s**a kashe dakarun soji 16 a yankin Okuoma da ke Karamar Hukumar Ughelli a Jihar Delta, za su ɗanɗana kuɗarsu.

A ranar Alhamis ne wasu bata-gari s**a yi wa wasu dakarun soji kisan gilla lokacin da suke kokarin sulhunta rikici tsakanin ƙabilar Okuama da Okoloba a Jihar Delta.

Bata-garin sun hallaka Kwamandan soji daya, Manjo biyu, Kyaftin daya, sojoji 12 da kuma wani mutum daya.

Tinubu cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, ya bayyana kisan a matsayin “jahilci” da cewa dole a hukunta wadanda suke da hannu a lamarin.

Ya kuma mika ta’aziyyarsa ga iyalan sojojin da aka kashe tare da bayyana aniyar gwamnatinsa na hukunta wadanda ke da hannu a kisan sojojin.

Aminiya

Hardship: Obi berates AG's office Workshop in London, says it's insensitivity to the plight of NigeriansRead More:  http...
17/03/2024

Hardship: Obi berates AG's office Workshop in London, says it's insensitivity to the plight of Nigerians

Read More: https://tinyurl.com/2rx7wkmv

Address

Murtala Mohammed Way
Bauchi

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Martaba FM posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Martaba FM:

Videos

Share


Other Media/News Companies in Bauchi

Show All