15/10/2023
ASALIN RIKICIN FALASDINAWA DA YAHUDAWA (4) .
JUYIN JUYA HALIN FARANSA DA SAMUN 'YANCIN YAHUDAWA A KASASHEN TURAI .
A shekarar 1789 miladiyyah aka fara zanga-zangar juyin juya halin Faransa (French Revolution) wanda shine irinshi na farko a kasashen Turai . Wannan juyin juya hali tawaye ne ga sarakunan Faransa da mulkin sarauta shi kanshi , watau tsarin mulukiya .
Tsarin mulukiya , watau tsarin sarauta , an ginashi ne a kan cewar akwai wadanda sune s**a gaji mulki , duk sauran mutane talakawansu ne . Haka kuma mutane da abinda s**a mallaka gaba daya duk na Sarki ne .
Kafin wannan juyin na Faransa dukkan kasashen Turai karkashin mulkin sarauta suke . Juyin Faransa ya jawo aka kashe Sarki da Sarauniya na kasar , da masu rike da sarauta da yawa . Bore ne da talakawa s**a yiwa sarauta .
Juyin juya hali da ya faru a Coci (Reformation) a kasashen Turai da Amerika, inda aka yiwa mazhabar katolika (Catholic) tawaye shine ya haifar da wannan juyin na siyasa a Faransa . Don haka ne ma juyin Faransa ya ari akidunshi da yawa daga akidun cocunan Protestant .
An gina manufofin juyin Faransa a kan abubuwa guda uku , sune : " Liberty , Fraternity , Equality" , ('Yanci , Zumunta , Daidaito) . Ma'ana dukkan mutane kowa na da 'yancin yin rayuwar da ya zaba ,tare da 'yancin mallakar abinda ya mallaka , da 'yancin zama shugaba , ya zaba ko a zabeshi . Sannan kowa daidai da kowa yake babu sarki da talakka , sai dai zumuntar zama kasa daya .
Da wannan ne Faransa ta zama "Republic" , watau (Jumhuriya) , inda kowa na da damar ya zama shugaba in dai shi dan kasa ne . Haka aka tabbatar da rabe addini daga siyasa , da tabbatar da hakkokin dan Adam .
Shugabannin juyin Faransa sun kuma yi aro daga juyin Coci cewa Yahudawa suma 'yan kasa ne , 'yan uwan zama tare ne , ba za a ci gaba da kiyayya da su ba ko a nuna masu bambanci ko a hana masu wani hakki nasu na zama 'yan kasa . Wannan ya kara karfafa fahimtar juna da ta fara samuwa tsakanin kirista da yahudawa a Turai sakamakon juyin Coci