Kalli yadda mazauna Zariya ke fama da matsalar ruwan sha
Bidiyo: Aliyu Baban karfi Zariya
Yadda masu Tsire da Balangu ke kuÉ—ancewa a Abuja
Sana’ar Tsire da Balangu wata daɗaɗɗiyar sana’a ce da aka san mazauna ƙasar Hausa da ita.
To amma ya sana’ar take a Abuja?
Wane irin alhairai da ƙalubale ake samu a yayin gudanar da sana’ar a Abuja?
Wannan bidiyo yana ɗauke da bayani dalla-dalla dangane da yadda sana’ar ke gudana a Abuja.
Dabarun Rabauta Da Kwanaki 10 Na Ƙarshen Ramadan
A wannan bidiyon, mun kawo muku waɗansu dabarun kasancewa cikin karkashi da ƙoshin lafiya yayin gudanar da ibadar kwanaki goman ƙarshe na watan Ramadan mai albarka
Yadda tsohon Shugaban Najeriya Obasanjo ya diro daga dandamali bayan kammala jawabi a bikin baje-koli da aka gudanar a Lagos
🎥: X/Pooja
Yadda ruwan sama ya sauka a masallacin Annabi da ke Madina yayin da ake tsaka da huɗubar Juma’a.
🎥: Haramain Sharifain
Musabbabin ayyukan zunubi a Ramadan
Al’umma na zaton cewa la’akari da ɗaure shaiɗanu da aljanu da ake yi a cikin wannan wata na Ramadan kamar yadda aka sha jin hakan daga bakunan malamai, don haka ba zai yiwu a sami wani ya aikata ayyuka na sabo ba.
Aminiya ta tattauna da Sheikh Muhammad bin Uthman ga kuma irin bayanin da ya yi game da wannan fahimta.
Wata Sabuwa: 'Yan fim sun karrama Gwamnan Kano
'Yan Kannywood sun karrama Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf a ranar Talata kan gudunmawar da suka ce yana bayarwa wajen ci gaban jihar.
Taurarin dai sun karrama Gwamnan ne, yayin liyafar buɗa-baki da ya shirya domin ganawa da mawaƙa da ‘yan fim karkashin jagorancin Shugaban Hukumar Tace Fina-Finai da dab’i na Kano, Abba Al-Mustapha.
Taurarin Zamani: Ummusalma Sadiq Gezawa
Ummusalma dai ta fara ayyukanta a Kannywood a bayan fage kafin daga bisani ta fito a matsayin jaruma.
Ta ce tana da muradin ci gaba da kasancewa a matsayin mai shirya fim ko bayar da gudunmawa idan ta yi aure.
A gefe guda kuma, ta ce tabbas ƙananan jarumai na fuskantar babban ƙalubale a masana’antar, amma ita Allah Ya yi mata gyaɗar dogo, ba ta faɗa hannun ɓata-gari ba.
Yadda Shugaba Tinubu da gwamnonin Kano, Delta, Kogi, Imo, da Bayelsa suka halarci jana’izar sojoji 17 da aka yi wa kisan gilla a Jihar Delta.
Bidiyo: Idowu Isamotu
Yadda na rasa 'ya'yana uku da mijina a aikin soja - Mahaifiyar marigayi Laftanar Kanar A H Ali
Hajiya Hassana Hasan a yanayi na kaduwa yayin tattaunawarta da Aminiya ta bayyana yadda ta ji a ranta dangane da labarin rasuwar É—anta na karshe.
Ta ce mutuwarsa babban rashi ne a wajenta, domin shi ne wanda ke daukar dawainiyar rayuwarta
Yadda Gwamna Abba Kabir ya yi dirar mikiya wani wajen dafa abincin buÉ—a baki da gwamnati ta ware, inda ya nuna É“acin ransa kan irin abincin da ya gani.
Ba mu kama Kirista ko É—aya a kamen gandaye ba - Hisbah
A makon da ya gabata ne, Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ta fitar da sanarwar kama wasu matasa da ke cin abinci da tsakar rana a lokacin Ramadan.
Sai dai bayan kamen sai wani batu ya taso, inda wasu ke zargin cewa hukumar ta kama wadanda ba Musulmai ba, tare da tilasta musu yin azumi.
A jawabin Darakta Janar na hukumar, Abba Sa'idu Sufi, ya ce Hisbah Musulmai kawai ta ke kamawa, ba ruwanta da wanda ba Musulmi ba.
Wata Sabuwa: Ba daidai ba ne sukar malamin da ke tafsiri da mai dakinsa - Amdaz
Fitaccen tauraron Kannywood Abdallah Amdaz ya bayyana farin cikinsa da samun malamin da ke tafsiri tare da mai dakinsa da aka yi a Jihar Kaduna, inda ya ce ba karamin ci gaba ba ne ga addinin Musulunci.
Taurarin Zamani: Zainab Nasir Ahmad
Zainab matashiya ce da ke amfani da Soshiyal Midiya, kuma ta yi ƙaurin suna musamman kan batun babu wata riba a aure.
Matashiyar ta ce ta fuskanci kalubale a Soshiyal Midiya, musamman lokacin da ta yi batun aure, ta ce ta sha zagi da suka, amma ta ce da yawa sun mata gurguwar fahimta.
A gefe guda kuma, ta ce batun auren ya sa ta yi shura a Facebook da sauran kafafen sada zumunta.
Kalli cikakkiyar hirar da shirin Taurarin Zamani ya yi da ita.
Dalilin cikar masu Umrah a watan Ramadan ya sa an fara ɗawafi a kan gadar da ke da’irar rufin Masallacin Harami da motoci na musamman.
🎥: Haramain Sharifain
BIDIYO: Kalli yadda Peter Obi ya halarci tafsirin Ramadan a Masallacin Suleja da ke Jihar Neja.
Tasirin Azumi ga lafiyar jiki
Bayan kasancewarsa ibada mai girma da tarin falala da Allah Madaukakin Sarki Ya ce naSa ne kuma Shi Ya ke bada ladansa, Azumi kan taka rawa wajen inganta lafiyar jikin dan Adam.
Azumi yana zaizaye kitse da daidaita magudanan jini da sauransu.
Kalli wannan bidiyon domin jin falalar da ke tattare da Azumi tare da Sheikh Muhammad Bin Uthman
Mai ƙafa ɗaya da ke sana’ar haƙa rami
A wannan bidiyon za ku ji irin gwagwarmayar da Idris Abdulraheem ya yi da kuma ƙalubalen da ya fuskanta tun bayan rasa ƙafarsa guda ɗaya, musamman ma wajen neman aikin da zai ba shi damar samun abun da zai sa wa bakin salati, da kuma ɗaukar nauyin iyalansa.
Yadda Gwamna Ahmad Aliyu ya yi buÉ—a-baki tare da Almajirai a Jihar Sakkwato.
Ma’anar kalmar Ramadan da asalinta a Shari’a
Galibi Azumi ya kan zo a yanayi na tsananin zafi da rana, inda hakan ke ƙara tsananta ƙishirwa da galabaitar mai yi.
Shin ko a zamanin baya haka al’amarin yake?
A cikin wannan bidiyon fitataccen malamin addinin musulunci, Sheikh Muhammad Bin Uthman, ya zayyano mana ma’ana da asalin kalmar Ramadan da kuma ma’anar Azumi a luga da shari’a da kuma falalarsa.