Hausa Daily News

Hausa Daily News Sahihan Labarai
(2)

KAFA TARIHI A CHAMPIONS LEAGUEGa 'Yan wasan da s**a fi kowa cin Champions league inda s**a kafa tarihin lashe kofin zaka...
01/06/2024

KAFA TARIHI A CHAMPIONS LEAGUE

Ga 'Yan wasan da s**a fi kowa cin Champions league inda s**a kafa tarihin lashe kofin zakarun Turai har sau shida.

Toni Kroos
Dani Carvajal
Luka Modric
Nacho

AN K**A WANDA YA SAYAR DA ’YARSA KAN NAIRA MILIYAN 1.5 A BAUCHIRundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta k**a wani mutum da ...
01/06/2024

AN K**A WANDA YA SAYAR DA ’YARSA KAN NAIRA MILIYAN 1.5 A BAUCHI

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta k**a wani mutum da ake zargi da yunƙurin sayar da ’yar cikinsa mai shekara biyar a duniya kan kuɗin Naira miliyan 1.5.

Wanda ake zargin mai suna Yusuf Umar mai shekara 49, ya bayyana cewar yana aiki da ƙaramar huk*mar Warji ne.

A cewar rahoton ’yan sandan, Umar, ya riga ya shirya miƙa yarinyar ga wani mutum, sai dai ya yi rashin sa’a wanda zaj sayi yarinyar jami’in ɗan sanda ne da ke aiki a sirri.

“A ranar 26 ga watan Mayu, 2024, wanda ake tuhuma ya ɗauki yarinyar ’yar shekara biyar daga wajen mahaifiyarta a ƙaramar huk*mar Warji kan cewar zai kai ta wajen ’yar uwarsa da ke garin Bauchi.

“Mahaifiyar ba ta da masaniyar cewar ya shirya miƙa yarinyar ga waniutum, ba tare da sanin cewa shi jami’in ’yan sanda ne ba,” in ji Kwamishinan ’yan sandan Jihar Bauchi, Auwal Mohammed.

Ya ce an k**a wanda ake zargin ne a wani otal da ke Bauchi.

SAMUN 'YANCIKalli Hotunan Yadda Dakataccen Matai Makin Kwamishinan 'Yan Sanda Abba Kyari A Hadu Da Iyalansa Bayan Da Aka...
01/06/2024

SAMUN 'YANCI

Kalli Hotunan Yadda Dakataccen Matai Makin Kwamishinan 'Yan Sanda Abba Kyari A Hadu Da Iyalansa Bayan Da Aka Bada Belinsa Daga Gidan Gyara Hali Dake Kuje, Abuja

GWAMNATI BA ZA TA IYA BIYAN MAFI KARANCIN ALBASHI  NA NAIRA 494,000 BA  - MINISTAGwamnatin tarayya tace ba za ta iya biy...
01/06/2024

GWAMNATI BA ZA TA IYA BIYAN MAFI KARANCIN ALBASHI NA NAIRA 494,000 BA - MINISTA

Gwamnatin tarayya tace ba za ta iya biyan naira 494,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ba, k**ar yadda ƙungiyar ƙwadagon ƙasar ta buƙata.

Ministan yaɗa labarai Mohammed Idris ne ya bayyana hakan inda yace biyan buƙatar ƴan ƙwadagon na nufin gwamnati za ta kashe naira tiriliyan tara da rabi wajen biyan albashin ma'aikata, lamarin da ya ce zai jefa walwalar ƴan Najeriya fiye da miliyan 200 cikin barazana.

Da yake jawabi a wani taron manema labarai a babban birnin tarayya Abuja, ministan ya ce gwamnatin tarayya ta amince da biyan naira dubu 60 a matsayin mafi ƙarancin albashi, wanda ke nufin ƙarin kashi 100 ke nan na ƙarancin albashin, k*ma tuni kamfanoni masu zaman kansu s**a amince da hakan.

Ya ce: “Gwamnatin tarayya ta yi ƙarin kashi 100 na mafi ƙarancin albashin ma'aikata na 2019, amma ƙungiyar ƙwadago na buƙatar a biya naira 494,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

“Akwai buƙatar ƴan Najeriya su fahimci cewa gwamnatin tarayya tana da niyyar biyan wadataccen albashi ga ma'aikata, amma a gefe guda, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya na ƙoƙarin kauce wa yanayin da zai sa mutane da dama su rasa ayyukansu, musamman daga kamfanoni masu zaman kansu, waɗanda ba lallai su iya biyan mafi ƙarancin albashin da ƴan ƙwadagon ke bukata ba.”

Akarshe Ministan ya buƙaci kungiyoyin ƙwadagon su koma teburin tattaunawa da gwamnati domin samar da mafita a kan lamarin.

Yanzu Yanzu!!!Real madrid ta doke Burossia Dortmund Da ci 2 da nema inda ta lashe gasar champions league karo na 15.
01/06/2024

Yanzu Yanzu!!!

Real madrid ta doke Burossia Dortmund Da ci 2 da nema inda ta lashe gasar champions league karo na 15.

OBASEKI YA FARA BIYAN MAFI ƘARANCIN ALBASHI NA NAIRA 70,000 Gwamna Jihar Edo, Godwin Obaseki wanda a yayin bikin Ranar M...
01/06/2024

OBASEKI YA FARA BIYAN MAFI ƘARANCIN ALBASHI NA NAIRA 70,000

Gwamna Jihar Edo, Godwin Obaseki wanda a yayin bikin Ranar Ma’aikata ta 2024 ya ƙara wa ma’aikata albashi mafi ƙaranci daga Naira 40,000 zuwa Naira 70,000, ya cika alƙawarin da ya yi don daƙile illolin da taɓarɓarewar tattalin arziki ke yi wa al’ummar jihar.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Sadarwa da Wayar da Kan Jama’a na jihar, Chris Nehikhare ya fitar.

Kwamishinan ya ce biyan mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000 ga ma’aikata, ya ƙara nuna irin sadaukarwar da gwamnatin Gwamna Godwin Obaseki ke yi na kyautata jin daɗin ma’aikatan Edo.

Ya ce, “Gwamnatin jihar ta biya mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000 a watan Mayu, wanda hakan ke nuna yadda aka aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashin.

“Wannan cika alƙawarin da Gwamna Godwin Obaseki ya yi ne a farkon watan Mayu, a wani ɓangare na ƙoƙarin daƙile ƙuncin da al’umma ke fuskanta sak**akon cire tallafin mai da sauran matsalolin tattalin arziki.”

Kwamishinan ya buƙaci ma’aikatan jihar su jajirce wajen gudanar da ayyukansu, tare da bayar da gudunmawa yadda ta k**ata domin saka wa gwamnatin jihar a kan na kyautata rayuwarsu.

HAJJ 2024: NAHCON TA GARGADI MANIYYATA KAN SAYAR DA KAYAN SUHuk*mar alhazai NAHCON ta gargadi maniyyatan kasar kan sayar...
01/06/2024

HAJJ 2024: NAHCON TA GARGADI MANIYYATA KAN SAYAR DA KAYAN SU

Huk*mar alhazai NAHCON ta gargadi maniyyatan kasar kan sayar wa wadanda ke zaune a Saudiyya domin neman kudi da aka fi sani da 'takari' tufafin da huk*mar ta dinka musu domin gudanar da ayyukan hajjin.

Daraktan Da'awah na huk*mar ta NAHCON reshen jihar Kebbi, Sheikh Aminu Hassan ne ya bayyana haka lokacin da yake yi wa maniyyatan jhar jawabi bayan isarsu kasa mai tsarki.

Akwai zarge-zargen cewa takarin na sayen tufafin wasu maniyyatan musamman mata da kudi masu yawan gaske, tare da yin bad da bami domin shiga cikinsu da fakewa da aikin hajjin wajen aikata abubuwan da ba su dace ba.

Sheikh Aminu Hassan ya ce sayar da tufafin babban laifi ne da zai iya janyo wa duk wanda ya aikata hukunci mai tsanani, don haka ne ya gargadi maniyyatan su kauce wa wannan mummunar dabi'a.

Ya ce hakika za ka iya samun kudi masu yawa a wajen takarin, musamman ku mata, to amma ku tuna cewa za su yi amfani da tufafin ne wajen aikata barna, sannan ku sani cewa za a danganta barnar da Najeriya da ma jihar Kebbi musamman.

Daraktan ya kara da cewa ''ku tuna cewa tufafinku alama ce ta kasa da jihar da kuka fito, don haka ku kiyaye duk wani abu da zai bata wa kasarku suna''.

CHAMPIONS LEAGUE: YAU ZA'A YITA TA KARE TSAKIN REAL MADRID  BORUSSIA DORTMUND A yau Asabar kungiyar kwallon kafa ta Real...
01/06/2024

CHAMPIONS LEAGUE: YAU ZA'A YITA TA KARE TSAKIN REAL MADRID BORUSSIA DORTMUND

A yau Asabar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid za ta buga wasan karshe a gasar zakarun Turai ta Champions League inda zata kece raini da Borussia Dortmund a wasa na Wembley dake Ingila.

Wannn shi ne karon farko da Real Madrid da Borussia Dortmund za su kara a wasan karshe a babbar gasar tamaula ta Turai, amma karo na 15 da za su fuskanci juna a gasar.

To sai dai Dortmund na fatan ɗaukar Champions League na biyu a wasan karshe karo na uku da za ta buga a gasar a tarihi.

Ƙungiyar da Edin Terzic ke jan ragama ta kai wannan matakin, bayan da ta kai zagaye na biyu daga rukuni na shida, sannan ta fitar da PSV a zagayen ƴan 16.

Haka k*ma Dortmund ce ta yi waje da Atletico Madrid a zagayen quarter-finals, sannan ta yi nasara a daf da karshe a kan Paris St Germain gida da waje.

Ranar Asabar 1 ga watan Yuni, Real Madrid na shirin buga wasan karshe karo na 18 a Champions League, bayan da ta lashe kofi 14 daga ciki.

Ita ce kan gaba a yawan zuwa karawar karshe a babbar gasar tamaula ta zakarun Turai, k*ma ita ce kan gaba a yawan lashe kofin a tarihi.

Real ta fara daukar kofin farko zuwa na biyar tare da jagorancin Di Stefano tsakanin 1956 zuwa1960.

Ƙungiyoyin da ta doke a lokacin sun hada da Reims 4-3 da Fiorentina 2-0 da Milan 3-2 da Stade de Reims 2-0 da k*ma Eintracht Frankfurt 7-3.

Bayan da Real Madrid ta yi rashin nasara a hannun Benfica da k*ma Inter a 1962 da k*ma 1964, daga nan ta dauki na shida da ake kira La Sexta a 1966 bayan nasara a kan Partizan 2-1.

A 1981, Madrid ta kasa daukar Champions League, bayan rashin nasara a hannun Liverpool.

Daga lokacin k*ma ta dunga lashe dukkan karawar da ta kai wasan karshe ta k*ma doke Juventus ta dauki La Séptima a Amsterdam a 1998, bayan cin 1-0.

Haka k*ma ta dauki na La Octava bayan doke Valencia 3-0 a Paris, sai ta ɗaga La Novena a wasan da ta doke Bayer Leverkusen 2-1 a Glasgow a 2002, shi ne lokacin da Zidane ya ci ƙwallo mai kayatarwa.

A kakar 2014 tare da Ancelotti a kan ragama ta dauki La Decima a Lisbon da cin 4-1 har da ƙwallo mai kayatarwa da Ramos ya ci.

A 2016 Real Madrid ta doke Atletico ta dauki La Undecima a birnin Milan.

Haka k*ma Real Madrid ta ɗauka a 2017, wato La Duodécima a birnin Cardiff bayan nasara a kan Juventus da cin 4-1.

A 2018, Real ta doke Liverpool da cin 3-1 ta lashe La Decimotercera.

Sai k*ma a 2022, Real Madrid ta kara yin nasara a kan Liverpool da cin 1-0 a Paris ta dauki na 14 jimilla, wato La Decimocuarta.

SARKI SANUSI YA JAGORANCI SALLAR JUMA'AMai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu ya ce babu wanda zai iya rokon A...
01/06/2024

SARKI SANUSI YA JAGORANCI SALLAR JUMA'A

Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu ya ce babu wanda zai iya rokon Allah ya yi masa bayani kan kowace irin lamari.

Sarkin ya bayyana haka ne a cikin hudubarsa a babban masallacin kofar Kudu da ke Kano, inda ya jagoranci sallar Juma’a.

Hudubar ta ta'allaka ne kan imani da Allah, muhimmancin hakuri da k*ma wajabcin karbar kaddara a matsayin daya daga cikin abubuwan imani.

Sanusi yace “Duk wanda ya yarda cewa Allah ne kadai ke bayar da komai, dole ne ya dauki matakinsa da zuciya daya. Babu mai tambayar Allah dalili akan komai.

“An gaya mana cewa duk wanda bai yarda cewa kaddara daga Allah take ba, imaninsa bai cika ba. Ya k**ata mutum ya kasance mai godiya a yanayi mai kyau da mara kyau. Dole ne mu yi imani cewa duk abin da ya faru da mu kaddara ce k*ma abin da ba za mu iya samu ba daga Allah ne.

“Muna gab da kusantar Zhul Hijja, wanda ke da fa’ida sosai; k*ma mu kiyaye addu'a a kwanakin nan."

Daga baya sarki ya jagoranci sallar juma'a kafin daga bisani ya koma fadarsa.

Anasa bangaren, Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero shi ma ya yi sallar Juma’a a karamar huk*mar Nasarawa, tare da dimbin magoya bayansa.

Tun da farko dai, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta yi watsi da rahotannin da ke cewa Aminu Ado Bayero zai jagoranci sallar Juma’a a babban masallacin Kofar Kudu da ke Kano, tareda sarki Muhammadu Sanusi.

Sanusi da Aminu Ado Bayero duk sun yi da’awar zama kan karagar mulki, lamarin da ya haifar da rudani a cikin birnin kano.

MATASHI M***I YAKS YA RASUMatashi Abdullateef Aliyu Maitaki wanda aka fi sani da M***i Yaks ya riga mu gidan gaskiya. Ma...
01/06/2024

MATASHI M***I YAKS YA RASU

Matashi Abdullateef Aliyu Maitaki wanda aka fi sani da M***i Yaks ya riga mu gidan gaskiya.

Matashin wanda ya rasu a daren jiya ya yi ƙaurin suna wajen kwaikwayar salon karatun shahararren malamin nan M***i Menk, inda daga nan ne ya samo na shi sunan na M***i Yaks.

Za a gudanar da jana'izarsa a gidansu da ke unguwar Dutsen Kura Gwari a garin Minna.

NLC DA TUC SUN TSUNDUMA YAJIN AIKI AKAN MAFI KARANCIN ALBASHI Kungiyoyin Kwadago na NLC da takwararta ta TUC sun ayyana ...
01/06/2024

NLC DA TUC SUN TSUNDUMA YAJIN AIKI AKAN MAFI KARANCIN ALBASHI

Kungiyoyin Kwadago na NLC da takwararta ta TUC sun ayyana shiga yajin aikin gama gari tun daga Litinin 3 ga watan Yuni mai k**awa, sak**akon gazawar kwamiti mai kusurwa 3 wajen samun matsaya akan batun mafi karancin albashi da karin kudin lantarki.

Shugaban Kungiyar Kwadago ta TUC, Festus Usifo ne ya ayyana shiga yajin aikin a yayin wani taron manema labarai daya gudanar tare da shugabannin kungiyar kwadago ta NLC a Abuja a yau Juma'a.

A cewar Shugabanin Kwadagon, shawarar ta biyo bayan karewar wa'adin bukatar da s**a gabatarwa gwamnatin tarayya tunda fari na kammala tattaunawa akan batun mafi karancin albashi kafin karshen watan Mayu.

Hadaddiyar kungiyar kwadagon ta taba ficewa daga tattaunawar tare da yin fatali da tayin gwamnatin tarayya har sau 2, wanda na baya-bayan nan ya kasance naira dubu 60, inda su k*ma s**a dage akan Naira dubu 497 a matsayin mafi karancin albashi.

Sak**akon lamuran dake faruwa, shugabannin kwadagon sun bijiro da dimbin matakai da s**a hada da sabon mafi karancin albashi da nau'ukan hanyoyin sufuri da mak**antansu domin rage radadin janye tallafin man fetur.

TINUBU ZAI TSAGA NAJERIYA ZUWA YANKI - YANKI A wani sabon salon jeka da halinka da Gwamnatin Shugaban Najeriya Bola Tinu...
01/06/2024

TINUBU ZAI TSAGA NAJERIYA ZUWA YANKI - YANKI

A wani sabon salon jeka da halinka da Gwamnatin Shugaban Najeriya Bola Tinubu ke shirin mika kudurin gaban majalisar wakilai da ta dattawa shine zai baiwa ko wani yanki yancin damar cin gashin kai wajen dogaro da abinda suke samu a yankinsu wajen rike kansu da kansu.

Misali : mutanen da su fito daga yankin Naija Delta zasu dogara da ɗanyen man fetur wajen dogaro da yankinsu.

Mutanen da su fito daga yankin Legas da jihohin dake kunshe da Legas zasu dogara da kansu da abinda ake samu ta hanyar jigilar kaya ta ruwa.

Arewa maso gabashin Najeriya zata dogara da noma ko bodojin yankin.

Wannan tsarin baya nufin an cireta daga Najeriya a'a yana ƙarƙashin Najeriya sai dai zai bawa ko wani yanki damar amfana da abinda yake samu wajen ciyar da kansa maimakon sai an turawa ko wacce jiha ko yanki da kasonsa daga gwamnatin tarayya.

ZANEN BARKWANCI AKAN RIKICIN SARAUTAR KANODaga Shafin facebook na BULAMA
26/05/2024

ZANEN BARKWANCI AKAN RIKICIN SARAUTAR KANO

Daga Shafin facebook na BULAMA

ZANGA-ZANGA TA BARKE A MASARAUTAR GAYA DAKE KANORahotanni daga Kano sun ce Yanzu haka ana zanga-zanga a titunan Gaya day...
26/05/2024

ZANGA-ZANGA TA BARKE A MASARAUTAR GAYA DAKE KANO

Rahotanni daga Kano sun ce Yanzu haka ana zanga-zanga a titunan Gaya daya daga cikin masarautu biyar da Majalisar dokokin jihar Kano ta rusa.

Jam’iyyar NNPP mai rinjaye a majalisar dokokin jihar ne ta soke dokar da tsohon gwamna Abdullahi Ganduje ya yi amfani da shi wajen tsige Alhaji Muhammadu Sanusi II a shekarar 2020.

Yayin da ya ke amincewa da dokar a ranar Alhamis, Gwamna Abba Yusuf ya sanar da rusa karin masarautu hudu da Ganduje ya kafa da s**a hada da Rano, Gaya, Karaye da Bichi.

Gwamnan ya k*ma umurci dukkan sarakunan da s**a hada da Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir Sarkin Gaya da su mika wa Kwamared Abdulsalam Gwarzo mataimakin gwamna wanda ke kula da ma’aikatar kananan huk*momi da masarautu.

Mazauna garin sunce Sarkin da aka tsige ya bar fadar ne da tsakar daren ranar Alhamis.

To sai dai ya zuwa yanzu babu wata alamar tashin hankali ko turjiya a garin kasancewar an jibge jami'an tsaro dauke da mak**ai.

Da safiyar Lahadin nan ne mazauna garin s**a yi dafifi kan tituna domin nuna kin amincewa da rusa masarautar.

Masu zanga-zangar dauke da alluna sun rika rera wakokin nuna adawa da gwamnati, inda s**a yi zargin rashin adalci, suna masu cewa rusa masarautan na da alaka da siyasa.

JIRGIN KASAN ABUJA ZUWA KADUNA YA SAKI HANYA Rahotanni sun bayyana cewa wani jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja ya kauce han...
26/05/2024

JIRGIN KASAN ABUJA ZUWA KADUNA YA SAKI HANYA

Rahotanni sun bayyana cewa wani jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja ya kauce hanya da safiyar yau Lahadin.

Jirgin wanda ya baro Kaduna ya kauce hanya ne da misalin karfe 9:30 na safiya a daidai yankin Jere da ke Ƙaramar Huk*mar Kagarko ta Jihar Kaduna.

Bayanai sun ce wannan lamari dai ya katse hanzarin gomman fasinjojin da jirgin ya dauko.

Kawo yanzu dai ana ci gaba da kokarin gyara jirgin wanda kusan taragonsa guda uku s**a sauka daga hanya.

Tuni dai jami’an tsaro da s**a hada da sojoji da ’yan sanda s**a isa wurin da jirgin ya yi hatsari da ke tsakanin wasu duwatsu.

SERAP TA BUƘACI TINUBU YA GAGGAUTA BAYYANA KADARORINSA Ƙungiyar Dake mai Fafutukar Yaƙi da cin Hanci a Najeriya SERAP  t...
26/05/2024

SERAP TA BUƘACI TINUBU YA GAGGAUTA BAYYANA KADARORINSA

Ƙungiyar Dake mai Fafutukar Yaƙi da cin Hanci a Najeriya SERAP ta buƙaci shugaba Bola Tinubu ya yi amfani da bikin cikarsa shekara guda a kan mulki wajen wallafa takardun kadarorin da ya mallaka.

ƙungiyar ta bayyana bukatar hakan ne a cikin wata buɗaɗdiyar wasiƙa da ta aike wa shugaban ƙasar, inda ta ce wannan dama ce da shugaban ƙasar zai nuna wa 'yan ƙasar yadda yake son ci gaba dimokraɗiyya da nuna tsantseni da rashin rufa-rufa a gwamnatinsa.

Kazalika ƙungiyar ta buƙaci shugaban ƙasar, ya umarci mataimakinsa da ministoci da gwamnonin jihohin ƙasar domin su wallafa nasu takardun kadarorin da s**a mallaka.

SERAP ta ce: “Muna so ka wallafa takardun mallakar kadarorinka, sannan ka umarci sauran jami'an gwamnati su ma su yi haka, saboda hakan zai ƙarfafa samar da cikakken tsarin gwamnati maras rufa-rufa a duka matakai.''

“Yin abubuwa a bayyane ba tare da rufa-rufa ba, k**ar yadda yake ƙunshe cikin takardun bayyana kadarori, zai inganta tsarin dimokraɗiyya tare da tsantseni a duka matakan gwamnati'', in ji SERAP.

Ƙungiyar ta k*ma buƙaci shugaban ƙasar ya gaggauta bijiro da buƙatar yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar kwaskwarima ta yadda za a saka dokar wallafa takardun mallakar kadarorin masu riƙe da muƙamai kafin su hau mulki da k*ma idan suna kan mulki da bayan saukarsu.

HAJJIN BANA: HUKUMA AIKIN HAJI TA KASA TA KAI MANIYYATA 19,700 KASAR SAUDIYYAHuk*mar alhazan ta kasa, NAHCON, ta ce ta k...
26/05/2024

HAJJIN BANA: HUKUMA AIKIN HAJI TA KASA TA KAI MANIYYATA 19,700 KASAR SAUDIYYA

Huk*mar alhazan ta kasa, NAHCON, ta ce ta kammala jigilar maniyyatan jihohin biyar a jigilar maniyytan da take yi zuwa ƙasa mai tsarki.

Cikin wata sanarwa da huk*mar ta wallafa a shafinta na X, ya nuna ce kawo yanzu huk*mar ta kammala kwashe maniyyan jihohin Kogi da Nasarawa da Edo da Oyo da k*ma jihar Ogun.

Haka k*ma huk*mar ta ce ta kammala kwashe maniyyatan da s**a biya ta huk*mar rundunar sojin Najeriya.

Kawo yanzu dai maniyyatan fiye da 19,700 huk*mar ta yi jikilar su, sai dai ta kara da cewa tana dab da kammala kwashe maniyytan jihohin Yobe da Banchi da Osun da Legas da Kebbi da k*ma Birni Tarayya Abuja.

TINUBU ZAI KADDAMAR DA AYYUKA A LEGASShugaban Kasa Bola Tinubu zai fara bikin murnar cikarsa shekara guda a kan karagar ...
26/05/2024

TINUBU ZAI KADDAMAR DA AYYUKA A LEGAS

Shugaban Kasa Bola Tinubu zai fara bikin murnar cikarsa shekara guda a kan karagar mulkin da buɗe wasu muhimman ayyukan gwamnatin Tarayya a Legas da aka kammala a lokacin mulkinsa.

Cikin wata sanarwa da mai mataimakawa masa na musamman ga kan kafofin yaɗa labarai na zamani, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce a yau Lahadi shugaba Tinubu zai buɗe wani babban titin da aka yi da kankare zuwa manyan tasoshin jiragen ruwa na Apapa da Tin Can a birnin na Legas.

Haka k*ma shugaba Tinubu zai buɗe fitacciyar gadar nan ta 'Third Mainland' da aka zamanantar da ita''.

Kana k*ma zai ƙaddamar da katafaren aikin titin da ya tashi daga Legas zuwa Calaba da aka yi ƙiyasin cewa zai laƙume kusan naira tiriliyan 15, T**i ne da zai ratsa jihohin kudancin aƙalla tara''.

Bayo Onanuga ya kara da cewa shugaban Tinubu zai ƙaddamar da aikin sake gina tituna har 330 a duka faɗin ƙasar.

TSOHON SHUGABAN EFCC IBRAHIM LAMORDE YA RASUTsohon shugabana Huk*mar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya, EFCC, Ibr...
26/05/2024

TSOHON SHUGABAN EFCC IBRAHIM LAMORDE YA RASU

Tsohon shugabana Huk*mar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya, EFCC, Ibrahim Lamorde ya rasu.

Wata majiya mai kusanci da Lamorden ta tabbatar wa BBC labarin rasuwar tasa a ƙasar Masar inda yake jinyar wata rashin lafiya.

Tsohon mataimakin Sifeton 'yan sandan Najeriyar, mai shekara 61, ya jagoranci huk*mar EFCC daga shekarar 2011 zuwa 2015.

Da farko tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ne ya naɗa shi a matsayin shugaban riƙo na huk*mar a watan Nuwamban 2011, bayan sauke Farida Waziri.

Sai k*ma a watan Fabrairun 2012, Mista Jonathan ya tabbatar da shi a matsayin cikakken shugaban huk*mar bayan amincewar majalisar dattawan ƙasar.

Ibrahim Lamorde - ɗan asalin jihar Adamawa - ya kasance mutum na uku a jerin waɗanda s**a jagoranci huk*mar EFCC tun bayan kafuwarta.

A shekarar 2015 ne wani kwamitin Majalisar Dattawan Najeriya ya ƙaddamar da bincike kan zargin karkatar da dala biliyan biyar, da wasu kadarori da EFCC ta ƙwato a lokacin da yake jagorantar huk*mar.

To sai dai a lokacin Ibrahim Lamorde ya musanta zargin yana mai cewa shure-shure ne kawai, kasancewar a lokacin EFCC ta gurfanar da mutumin da ya yi zargin.

A watan Nuwamban 2015 ne, tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya sauya shi da Ibrahim Magu.

AMINU ADO BAYERO ZAI TAFI BABBAR FADAR SARKIN KANOAn shiga ruɗani a Kano bayan Sarkin Kano na 15 ya fara shirye-shiryen ...
25/05/2024

AMINU ADO BAYERO ZAI TAFI BABBAR FADAR SARKIN KANO

An shiga ruɗani a Kano bayan Sarkin Kano na 15 ya fara shirye-shiryen zuwa Babbar Fadar Sarkin Kano ta Gidan Rumfa, daga karamar fadar da ke Nassarawa.

Yanzu haka dai za'a iya cewa sarakuna biyu ake dasu a Jihar Kano, inda Sarki Muhammadu Sanusi II yake zaune a Fadar Sarkin ta Gidan Rumfa.

Wannan dai na zuwa ne bayan Aminu Ado Bayero ya gana da tawagar Jami'an tsaro.

SARAUTAR KANO: ZAMU TABBATAR DA UMURNIN KOTU - JAMI'AN TSAROHadakar Jami'an tsaro a Kano sun sha alwashin bin umarnin ko...
25/05/2024

SARAUTAR KANO: ZAMU TABBATAR DA UMURNIN KOTU - JAMI'AN TSARO

Hadakar Jami'an tsaro a Kano sun sha alwashin bin umarnin kotu tare da samar da cikakken tsaro a faɗin jihar.

Sun bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai na hadin guiwa da s**a gabatar a shalkwatar 'yan sanda da ke Bompai.

Da yake jawabi kwamishinan 'yan sanda na jihar, CP Usaini Gumel ya ce jami'an tsaron suna biyayya ne da umarnin da kotun tarayyar da ke Kano ta bayar.

Idan za'a iya tunawa Kotun tarayya ce dai ta bayar da umarnin dakatar da soke masarautun jihar bayan shigar mata da ƙorafi kan hakan, sannan ta saka ranar 3 ga watan Yuni domin fara sauraron ƙasar.

Acewar Gumel jami'an 'yan sanda tare da haɗin gwiwar sojoji da sauran jami'an tsaro za su yi aiki tare domin samar da cikakken tsaro k**ar yadda kundin tsarin Najeriya ya tanadar.

Kwamishinan 'yan sandan ya k*ma yi kira ga mazauna birnin Kano da su kwantar da hankula tare da bai wa jami'an tsaro hadin kai, musamman yadda ya ce an san al'ummar jihar wajen bin doka da oda, kafin kotu ta yanke hukunci kan batun ranar 3 ga watan Yuni.

Kazalika ya gargaɗi duk wanda ya yi yunƙurin karya doka a jihar da cewa zai fuskanci fushin jami'an tsaro.

Akarshe ya bada tabbacin cewa jami'an tsaron sun baza komarsu a faɗin birnin Kanon domin tabbatar da zaman lafiya da bin doka.

kalli hotunan yadda Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II Ya yi hawa, ya k*ma fara zama fadarsa.
25/05/2024

kalli hotunan yadda Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II Ya yi hawa, ya k*ma fara zama fadarsa.

SOJOJI SUN ZAGAYE GIDAN AMINU ADO BAYERO DOMIN BASHI KARIYA An tura sojoji zuwa karamar fadar tsohon Sarkin kano Alhaji ...
25/05/2024

SOJOJI SUN ZAGAYE GIDAN AMINU ADO BAYERO DOMIN BASHI KARIYA

An tura sojoji zuwa karamar fadar tsohon Sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero, wanda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauke a ranar Alhamis.

Matakin na zuwa ne bayan Abba Gida ya bayar da Umurnin k**a shi.

A ranar Juma'a ne maitaimakawa Aminu Ado kan yada labarai Abubakar Balarabe Kofar Naisa ya yi kira ga Al'umar jihar Kano musamman masoya Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero cewa yau Asabar 25/05/2024 Tsohon sarkin zai dawo Kano bayan kammala ziyarar aiki.

Acewarsa zai sauka a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da Karfe 8:00am na Safe.

Saboda haka wannan sanarwa tana gayyatar dukkannin masoya suyi dafifi domin tarar mai Martaba Sarki domin rakashi zuwa gidan Dabo.

Inda ya Umurci masoyansa su fito cikin ladabi da nutsuwa da biyayya da da'a ayi a tare shi lafiya a gama lafiya.

A yayinda Sojojin s**a Isa Gidan dai sun cimma Daruruwan magoya bayan Basaraken sun yi Dafifi a kofar Gidan.

Tun da farko wasu Hotuna da s**a karade shafukan sada zumunta sun nuna yadda Sarkin kanon na 15 ya Isa Fadar Sarkin dake Nasarawa, wanda hakan ya tabbatar da dawowansa Birnin Kano.

MAYAR DA SARKI SANUSI A MATSAYIN SARKIN KANO NACI GABA DA TADA KURA A ranar Juma'ar da ta gabata ne Gwamnan Kano Abba Ka...
25/05/2024

MAYAR DA SARKI SANUSI A MATSAYIN SARKIN KANO NACI GABA DA TADA KURA

A ranar Juma'ar da ta gabata ne Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya mika wa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II takardar dawo dashi a Matsayin Sarkin Kano.

Da yake gabatar da wasikar a ranar Juma’a, gwamnan ya ce, “Mun mayar da Sanusi ne saboda zargin an ci zarafinsa a shekarar 2019.

"Muna k*ma mayar da shi a matsayin Sarkin Kano, domin ya ci gaba da gudanar da ayyukan alheri da yake yi domin amfanin al'ummar Kano."

Dangane da tsarin majalisar da ya kai ga dawo da Sanusi, Abban kanawa yace, "Da zarar an rattaba hannu kan kudirin doka, ya zama doka k*ma babu wanda zai iya canza hakan."

Kazalika Gwamnan bukaci Sanusi da ya hada kan iyalan Ibrahim Dabo sannan k*ma ya kara himma wajen ganin an hada kungiyoyin Musulunci a matsayin masu bautar Allah daya.

Sa'o'i bayan karbar takadar k**a aikin nasa ne Sarkin Kano Muhammad Sunusi na biyu ya shiga Fadar Masarautar Kano tare da mataimakin gwamna da sauran kusoshin gwamnatin Kano s**a yiwa Sarkin rakiya zuwa gidan Dabo

Da fari dai an yi ta hasashen cewar Sarki Aminu Ado Bayero yana hanyar shiga gidan bisa la’akari da umurnin da kotu ta bayar na dakatar da rushe masarautun kanon.

wannan dai baya rasa nasaba da wata sanarwa da Mai taimakawa tsohon sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayero Kan harkokin yada labarai Abubakar Balarabe Kofar Naisa ya fitar a daren juma'a.

Sanarwar tace "Ina sanar da al'umar jihar Kano musamman masoya Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero cewa ranar Asabar 25/05/2024 mai martaba sarki zai dawo Kano bayan kammala ziyarar aiki"

"Kuma zai sauka a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da Karfe 8:00am na Safe insha Allahu"

Saboda haka wannan sanarwa tana gayyatar dukkannin masoya suyi dafifi domin tarar mai Martaba Sarki domin rakashi zuwa gidan Dabo.

"Muna Kira ga masoya a fito cikin ladabi da nutsuwa da biyayya K**ar yadda aka sammu da da'a ayi tare lafiya a gama lafiya" In ji Abubakar Balarabe Kofar Naisa

To sai a wani mataki na mayar da martani da safiyar Yau Asabar Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya bai wa kwamishinan ‘yan sandan jihar umarnin k**a Sarki Aminu Ado Bayero, bisa abin da ya kira yunkurin tayar da tarzoma.

Tun da farko an jiwo Gwamnatin Kano na zargi Shugaban Jam'iyar APC k*ma tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da mai ba Shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu da neman tada zaune tsaye a Kano ta hanyar dawo da Aminu Ado fada da karfin tuwo.

Mataimakin Gwamnan jihar Kano ya tabbatar da cewa Nuhu Ribadu shine ya bawa tsigaggen sarkin Kano Aminu Ado Bayero jirgi biyu tare da jami'an tsaro dan su banƙara a shigar da shigar dashi masarautar Kano.

Yace k*ma Ganduje ne yaje wajan mai bawa shugaban kasar shawara kan harkar tsaro wato Nuhu Ribadu domin aikata wannan mummunan aiki.

A cewar mataimakin Gwamnan duk abinda za muyi zamuyi dan mu tabbatar haka bata faru ba, muna gidan Sarki dukkanin mu jami'an Gwamnati.

Muke da iko da jihar Kano, muke da iko da cire sarki ko naɗawa babu wanda ya isa yai mana shan kai.

Muna kira ga masoya a kwantar da hankali, k*ma a fito ai dafifi a nunawa sarki ƙauna, kowa ya naɗe kafar Wandon sa dan ganin mun hana yi mana wannan cin kashin ba a Kano.

Rahottani daga Jihar kano sunce yanzu haka magoya bayan tsohon Sarkin Kano sun zagaye Gidansa domin bashi kariya bayan gwamnan kano ya bayarda Umurnin k**a shi.

YANZU YANZU!!!Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bada Umurnin a K**a tsohon Sarkin Kano Aminu Ado Bayero a duk inda aka Ga...
25/05/2024

YANZU YANZU!!!

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bada Umurnin a K**a tsohon Sarkin Kano Aminu Ado Bayero a duk inda aka Ganshi a Jihar ta Kano.

12/05/2024

YANZU-YANZU: Ƴan bindiga na harbe-harbe cikin daren nan, a garin Ƴarmalamai da ke ƙaramar huk*mar Faskari ta jihar Katsina.

AN RAGE KUDIN WUTAR LANTARKI A NAJERIYAHuk*mar Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta sanar da rage kudin wutar ga masu am...
06/05/2024

AN RAGE KUDIN WUTAR LANTARKI A NAJERIYA

Huk*mar Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta sanar da rage kudin wutar ga masu amfani da layin Band A.

NERC ta umarci kamfanonin rararba wutar lantarki da su rage kudin kowane kilowatt daga Naira 225 zuwa N206 ga kwastomomin da ke kan layin Band A.

Umarnin na daga cikin matakan da huk*mar ta dauka da nufin tabbatar da samun wutar lantarki ta akalla awa 20 a kullum ga ’yan Band A.

Sanarwar da Kamfanin Rarraba Lantarki na Legas ya fitar ya ce ragin zai fara aiki ne daga ranar 6 ga Mayu, 2024, amma bai shafi kwastomomin da ke kan layin lantarki na Band B, C, D da k*m E ba.

Ragin N19 da aka yi wa ’yan Band A na zuwa ne kimanin wata guda da ta yi musu karin kudin kilowatt daga N68 zuwa N225, wanda ya sha Allah-wadai daga al’umma da mahukunta.

Ina Kira ga Rara,  Ado Gwanja,  Da Hamisu Breaker Da Su yi Koyi Da Naziru Sarkin Waka Wajan Bai wa Iyayen Annabi S.A.W. ...
05/05/2024

Ina Kira ga Rara, Ado Gwanja, Da Hamisu Breaker Da Su yi Koyi Da Naziru Sarkin Waka Wajan Bai wa Iyayen Annabi S.A.W. Kariya Ta Hanyar Waka --- Sheikh Abulfatahi.

GWAMNATIN KANO TA MUSANTA HARBIN DAN JARIDA A GIDAN GWAMNATIAna Zargin Wani harsashi da ba a san daga inda ya fito ba ya...
04/05/2024

GWAMNATIN KANO TA MUSANTA HARBIN DAN JARIDA A GIDAN GWAMNATI

Ana Zargin Wani harsashi da ba a san daga inda ya fito ba ya raunata wani Ɗan jarida a gidan gwamnatin jihar Kano.

Bayanai sunce Alburushin ya farwa Ɗan jaridar mai suna Naziru Idris Ya'u wanda ke aiki da gidan talabijin na Abubakar Rimi (ARTV) ne a lokacin da yake cikin harabar gidan gwamnatin Jihar Kano.

Yanzu haka dai 'ƴan sanda sun fara gudanar da bincike kan lamarin mai cike da ruɗani.

To sai dai Mai magana da yawun gwamna jihar Kano Sunusi Bature dawakin tofa ya karyata labarin inda yace ba harbin Dan jaridar aka yi ba, hasalima yace baraguzan gini ne ya taba Dan jaridar har ya jimasa rauni.

SANI DANJA DA MANSURA ISAH ZASU AURAR DA 'YARSUShahararren Dan Wasan Kannywood, Sani Danja zai aurar da ya a wajan sa Ri...
04/05/2024

SANI DANJA DA MANSURA ISAH ZASU AURAR DA 'YARSU

Shahararren Dan Wasan Kannywood, Sani Danja zai aurar da ya a wajan sa Riziqat Sani Danja.

Za'a ɗaura Auren ne ranar Asabar 18 ga watan May a masallacin juma'a na Tudun Wada dake karamar huk*mar Nasarawa Kano.

Rizkat Sani Danja zata amarce da angon ta Abdulsalam Abdlhameed ne a Ranar 18 ga Watan Mayu a Birnin Kano

Allah ya basu zaman lafiya

Address

Otako Abuja
Abuja

Telephone

+2348124905058

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausa Daily News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Hausa Daily News:

Videos

Share


Other Abuja media companies

Show All

You may also like