16/02/2024
BARKA DA JUMU'A!
DAGA HAƊAƊIYAR ƘUNGIYAR SAKKWATAWA MAZAUNA ABUJA!
YIN MAGANA, HIRA KO CINIKAYYA IDAN LIMAMI NA HUƊUBAR JUMA'A LAIFINE
Idan Liman yana huɗuba, ba a magana. Wannan karatu ne da ya kamata a ce, an jima da wucewa, amma har yanzu da sauran gyara; musamma a tsakanin matasa.
Zaka sha mamakin ganin dandazon matasa, su zo masallacin Juma'a a makare (late), kuma su kafa dabar hirar, alhalin limamin Juma'a na huɗuba.
An ruwaita daga Abu Hurairah, Ubayy ibn Ka’b da Abu’l-Darda’ (رضي الله عنهم) cewa, Manzon Allah ﷺ Ya yi hani mai matsanani a kan yin zance, ko shagala a lokacin da limamin Juma'a ke gabatar da huɗuba. Har Ya siffanta mai yin zance a lokacin da liman ke huɗuba da 'mai lagawu' (yarfaffen zance), koda kuwa wani ka so yiwa magana, kan ya daina surutu. [Bukhaari, 892; Muslim, 851 & Ibn Majah 1111].
Ba a yin hira, cinikayyar kasuwanci, ko wasu abubuwa na shagala a lokacin da liman ke huɗubar Juma'a [Al-Juma'ah, aya ta 9], haka na bayuwa mutum ya rasa wani sashe na Juma'arsa, koma ya rasa Juma'ar baki ɗaya.
Al-Imam Ibn Qudaamah رحمه الله yana cewa: "Wurare da aka aminta, aka bada uzuri, mai halartar Juma'a ya yi magana, shi ma in ya zama lalura, sune, sai in limamin ne ya maka magana, kuma yana buƙatar ka bashi amsa, ko kuma sanar da shi wani muhimmin al'amari [Mugni 2/83], ko amsawa liman sallama, ko ta'amini (cewa amin) in liman ya yi addu'a, ko faɗakar da wanda wata halaka ke ƙoƙarin afka masa, kamar makaho da zai faɗa rami, kamar yadda Ibn Uthaimin ya ambata cikin Al-Sharh Al-Mumti’.
Amma dai, kuskure ne babba, yin zance a lokacin da limamin Juma'a ke huɗuba.
(✍️Nura Sa'idu Danchadi PRO)
(Dr. Bashir Aliyu)