06/01/2024
-Yazo A Hadisil Qudisi, Daga Amintaccen Allah Mala’ika Jibrilu (AS) Yace; “Ya Muhammad.(S)! Allah ta'ala Wanda Girmansa Ya Girmama Yana Cewa: "Ba Don Na Halicci Ali (AS) Ba, da Fatima (AS) Bata da (Kufu’i) Ma'ana Sa’an Yin Aure A Duk Doron Ƙasa, Tun Daga Annabi Adamu (as) Har abin Dake Gabaninsa.”
-Allahu Akhbar! Ƴa’ƴan Sayyida Fatima Sune Imam Hasan da Husaini (AS), Sune Waɗanda Manzon Allah (S) Yake Cewa Dangane da Haƙƙinsu da Darajarsu Cewa: "Sune Shugabannin Samarin Aljanna.
-Manzon Allah (S) Yace: Su Shine, Shi Sune, Kuma Yace: su Ƴa’ƴansa Ne, Daga Gareshi Suke, Kuma Duk Abinda Ya Cutar Dasu Yana Cutar Da shi.
-Kuma Ya Ƙara da Cewa Su Shugabanni Ne A Duniya da Lahira, Kuma Su Jagorori Ne Tare da Sun Riƙe Muƙami Ko Basu Riƙe Ba.
-Ya Kai Ɗan Uwana Musulmi Ka Tsaya Ka yi Tunina da Basirar da Allah Ta'ala Ya Baka, Shin Suwa Ka Riƙe A Matsayin Jagororinka Zuwa ga Allah, Shin Ka Miƙa Wulayarka inda Manzon Allah (S) Yace Ka Miƙa?
-Saboda Maƙiya Sun Zalunci Annabi (S) Sun Cutar da shi Sun Cutar da Saƙonsa, Ku Kula Kar Ku Faɗa Hannun Ƴan Sari.
-Allah Ka Raba Mu da Ɓata Cikin Shiriya.