05/04/2024
Harkar Musulunci Ta Gudanar Da Muzaharar Quds A Nijeriya
Daga Cibiyar Wallafa
'Yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) sun gudanar da Muzaharar Quds a yau Juma'a 26 ga Ramadan 1445 (5/4/2024) a manyan garuruwan Nijeriya kimanin 30, ciki har da babban birnin Tarayya, Abuja.
Muzaharorin wadanda aka yi su don bayyana goyon baya ga Al'ummar Falastinawa, da kuma yin Allah wadai da haramtacciyar ƙasar Izra'ila da ke kashe su ba dare ba rana tsawon fiye da shekaru 70, a dukkan garuruwan ya samu halartan dubun dubatan al'umma.
Muzaharar ya kunshi dukkan bangarorin al'ummar Musulmi, Shi'a da Sunnah, a wasu garuruwan kuma, k**ar a Katsina, an gudanar da Muzaharar ne tare da wasu daga mabiya addinin Kirista, inda s**a bayyana cewa al'amarin Falastinawa ya shafi mutuntaka ne ba addini kawai ba, kuma in ma addini ne, Yahudawan Sahayina suna kashe har da Kiristoci ne a Gazza.
An gudanar da Muzaharar a birane da dama, inda aka yi ta da safe a garuruwan Katsina, Bauchi, Kaduna, Potiskum, Zariya da wasu garuruwan masu yawa, sannan kuma bayan sallar Juma'a, aka gudanar a Abuja, Kano, Jos, da wasu biranen, sannan aka yi kashi na biyu kuma a garin Zaria.
A dukkan garuruwan da aka gudanar da Muzaharorin, an yi an kammala lafiya, in banda a Jihar Kaduna, inda gamayyan jami'an tsaron Nijeriya s**a bude wa masu Muzaharar wuta a Kaduna da Zaria, sun jikkata mutane kimanin 30, tare da kashe mutum 4 a Kaduna, 1 a Zariya.
Ga hotunan yadda Muzaharar ta gudana a Abuja.
— Cibiyar Wallafa
26/9/1445 (5/4/2024)