Northern Mirror Hausa

Northern Mirror Hausa Page for fresh Hausa News

Majalisar Wakilai Taki amincewa da kudirin dakatar da Sabon Harajin internet da Babban bankin Najeriya Ya Buƙaci bankuna...
08/05/2024

Majalisar Wakilai Taki amincewa da kudirin dakatar da Sabon Harajin internet da Babban bankin Najeriya Ya Buƙaci bankuna Su fara

A zaman na Yau Laraba, Hon. Mansur Manu Soro ya nuna damuwarsa, inda ya nuna cewa shirin karbar harajin bai dace ba, musamman idan aka yi la’akari da kalubalen da ‘yan Najeriya da dama ke fuskanta a halin yanzu.

‘Yan majalisar sun bayyana imanin cewa bai k**ata alhakin sarrafa kudaden da aka tara ya kasance ƙarƙashin kulawar mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ba.

Kakakin majalisar Tajudeen Abbas ya bukaci dan majalisar ya janye kudirin, tare da baiwa shugabannin majalisar damar tattaunawa kan lamarin tare da tantance matakin da ya dace.

KBC Hausa

Sama Da Ɗalibai 200 Yan Jihar Kastina da suke Jami'ar Usman Ɗan Fodio Sokoto s**a amfana da Tallafin kuɗin Makaranta Dag...
08/05/2024

Sama Da Ɗalibai 200 Yan Jihar Kastina da suke Jami'ar Usman Ɗan Fodio Sokoto s**a amfana da Tallafin kuɗin Makaranta Daga Gidauniyar Lado Development Foundation

Dalibai ƴan asalin jihar Katsina masu karatu a jami'ar Ɗan fodiyo da ke birnin Sokoto
sama da 200 sun amfana da tallafin kuɗin karatu a fannoni da dama na ilimi

Daliban dai sun samu wannan tallafi ne daga gagarumar Gidauniyar nan ta Lado Development Foundation saboda duba da matsin tattalin arziki da al'umma suke ciki yasa wannan Gidauniya ta duƙufa domin Ganin Dalibai yan Asalin Jihar Katsina sun cigaba da karatun su a ko'ina a faɗin Najeriya ba tare da fuskantar matsala ba

Bugu da ƙari wannan Gidauniya tayi kaurin suna wajen tallafawa Al'ummar jihar Katsina ta kowanne fannin cigaban rayuwar su, Wadda s**a haɗa da fannin lafiya, ilimi, tallafin kuɗi hannu, da dai sauransu, sannan wannan gidauniya tana bawa Matasa, Mata, Tsofaffi da ƙananan yara muhimmanci sosai domin matsayin su a cikin al'umma, Ko a kwanakin baya Gidauniyar ta tallafawa dalibai masu dimbin yawa a jami'o'i da dama da s**a haɗa da na cikin jihar da wajen ta.

Wannan ne ma ya sa kungiyar Ɗaliban jihar Katsina Reshen Jam'iar Ɗan fodiyo dake Sokoto s**a karrama Gidauniyar da lambar Yabo na Musamman Saboda ƙoƙarin Gidauniyar a ɓangaren ilimi a jihar Katsina a lungu da saƙo

kuma duk wannan ayyukan suna daga cikin Burin Gidauniyar na ganin al'ummar jihar Katsina sun samu Cigaba ta fannoni da dama ta yadda jihar Katsina za ta zama abin kwatance a duk faɗin Najeriya

Lado Development Foundation

Gidauniyar Lado Development Foundation Ta Tallafawa Majinyata Fiye Da Dubu Goma 10,000 Inda Kowanne Mutum ɗaya yasamu Ta...
24/03/2024

Gidauniyar Lado Development Foundation Ta Tallafawa Majinyata Fiye Da Dubu Goma 10,000 Inda Kowanne Mutum ɗaya yasamu Tallafin Dubu 10,000

A Jiya Asabat 23 Ga watan March 2024. Gidauniyar Lado Development Fondation A ƙarƙashin Jagorancin Mai Dakin Sen Yakubu Lado Ɗan Marke Hajiya Hauwa Yakubu Lado Sun ziyarci wasu Daga cikin ƙananan Hukumomi da Suke Shiyyar Kastina Ta Kudu Domin Tallafawa marasa lafiya Duba da halin da ake ciki na Yau da kullum Musamman Talakawa a wannan lokacin suna fuskantar Wahalhalu dama musamman Hauhawar farashin kayyyaki iri daban-daban. Wanda ya Sanya Talakawa da dama basa iya biyan kuɗin jinya a asibitoci da dama.

Ga jerin Ƙananan Hukumomin da s**a Amfana da Tallafin

Kankara
Bakori
Funtua
Faskari
Sabuwa
Danja
Kafur
Malumfashi

Gidauniyar Lado Development Fondation Ta shiga lungu da sako a Shiyyar Kastina Ta kudu Duk da ana fama da Matsalar Tsaro Musamman a Shiyyar Kastina Ta Kudu Hakan bai hana Gidauniyar Ta shiga domin sanya farin ciki a zukatan al'umma musamman marasa Galihu.

Waɗanda s**aci Gajiyar Tallafin Sun nuna farin cikinsu matuƙa akwai Hajara Mohammed A ƙaramar Hukumar Sabuwa. Inda Ta Bayyana cewa "Garin mu Yana daga cikin garuruwa da suke fama da matsanancin Rashin tsaro Wanda hakan ya sanya ba Kowanne Mutum bane yake shigowa domin Ya Tallafawa al'ummar Mu. "Amma Gashi Muna zaune wannan Gidauniyar ta Tallafa man da kuɗaɗe Bazan Misalta farin cikin da na samu kaina ba a cewarta.

A ɗaya Ɓangaren Kuma Mal Yahya Dake ƙaramar Hukumar Faskari ya bayyana farin cikinsa da Tallafin Kuɗin magani da aka bashi Wanda Yace bazai taɓa manta wa da Irin alherin Lado Development Fondation a Rayuwarsa Saboda an Taimake shi a lokacin da Yake buƙatar taimako.

"An kwantar da matata Asibiti bani da ko sisi na rasa yadda zan saka kaina na Naime a bani A ron Kuɗi Daga hannun Abokaina "Amma saboda Wahalhalu da ake Fuskanta Hakan bai Sanya na samu ba ina zaune kwastam sai ga Tallafin kuɗaɗe daga Gidauniyar Lado Development Fondation A Gaskiya na samu Farin ciki Marar misaltuwa.

Dukkanin Mutanen da s**a amfana da Tallafin sun bayyana farin cikinsu Tare da Addu'oin Fatan Alheri A Gidauniyar Lado Development Fondation A Bisa namijin ƙoƙari da s**ayi na Tallafawa marasa Galihu.

Shugaba Tinubu Ya Bada Umarni Ga EFCC Tayi Bincike Dangane Da Kasafin Kuɗin Ma'aikatar Harƙoƙin Jinkai Kimanin Tiriliyan...
09/01/2024

Shugaba Tinubu Ya Bada Umarni Ga EFCC Tayi Bincike Dangane Da Kasafin Kuɗin Ma'aikatar Harƙoƙin Jinkai Kimanin Tiriliyan Biyu 2.38 Daga Shekarar 2020 Zuwa 2024.

2020: N453.3bn

2021: N456.1bn

2022: N507.9bn

2023: N426bn

2024: N532.5bn

Shugaba Bola Tinubu ya umurci hukumar EFCC da ta kaddamar da cikakken bincike kan Harƙoƙin kudi na ma'aikatar jin kai da yaki da fatara.

Northern Mirror Hausaa

Wannan Shine Shugaban Yansa kai na Jihar Borno Wanda Ake Ƙira Lawan Ja'afar Shine Mutum na Farko daya fara K**a Boko Har...
03/10/2023

Wannan Shine Shugaban Yansa kai na Jihar Borno Wanda Ake Ƙira Lawan Ja'afar Shine Mutum na Farko daya fara K**a Boko Haram da Hannunsa Shine Ya fara ɗaukan Sanda yake bin Masu Bindiga

Dalilinsa Aka Ƙirkiri Kungiyar sakai Wata Civilian JTF Anje Yaƙi Dashi iri iri Kuma Yayi Nasara iri iri sai dai Akwai Masu Hassada Dashi Kasan Cewar Allah yadaukakashi Su Kuma Makiya ba haka s**asoba Anata ƙoƙarin Sai An Gano laifinsa Domin a Rabashi da Al ummar Jahar Ko kuma Gwamnatin Jihar Amma Allah bai nu faba Sai Yanzu s**a fito da Wannan makirci Kuma Shima bai Samu karɓuwaba Allah Ya shiga Tsakanin Nagari da mugu

Daga S Baba Shatan Gabas

01/10/2023
Takaitaccen Tarihin! Sabon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN Muhammad Sani DattijoMuhammad Sani Abdullahi, W...
15/09/2023

Takaitaccen Tarihin! Sabon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN Muhammad Sani Dattijo

Muhammad Sani Abdullahi, Wanda aka fi sani da Dattijo, Kwararren Ma'aikacin Gwamanti Ya na da ƙwarewa a fannin ci gaban kasa da kasa, inda ya yi aiki a Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma Gwamnatin Najeriya.

Dattijo ya kammala karatun sa ne a Jami’ar Manchester da Jami’ar Ahmadu Bello. Hakanan yana da takaddun shaida daga Makarantar Tattalin Arziki ta London, Jami'ar Columbia, da Jami'ar Oxford.

Kafin ya fara aiki da Gwamnatin Najeriya, Dattijo ya yi aiki a matsayin mai ba da shawara ga babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki-Moon. Ya kasance memba a ƙungiyar haɓaka Manufofin Ci Gaba mai Dorewa (SDGs).

A Shekarar 2015 ne aka nada Dattijo kwamishinan Kasafin kudi da tsare-tsare a jihar Kaduna. A wannan aikin, shi ne ya dauki nauyin bunkasawa da aiwatar da kasafin kudin jihar. Ya kuma kasance mai fafutukar Tabbatar da Gaskiya da rikon amana a Cikin Gwamnati.

Dattijo tauraro ne mai tasowa a fagen ci gaban kasa da kasa. Shi mai ba da shawara ne mai ƙoƙarin Ganin an tabbatar da adalci ga zamantakewa da damar tattalin arziki. Haka kuma haziki a wajen magana da rubutu. Akwai kyakkyawan fatan da yakinin cewa zai ci gaba da bayar da Gagarumar Gudunmawa a fagen Tattalin Arziki da cigaban ƙasa.

KBC Hausa News

Darajar Ƙwarewa Wani jirgin ruwa ya taɓa samun wata matsalaMatsalar ta fara ne lokacin  da injin jirgin ya fara wata ƙar...
13/09/2023

Darajar Ƙwarewa

Wani jirgin ruwa ya taɓa samun wata matsala

Matsalar ta fara ne lokacin da injin jirgin ya fara wata ƙara wanda ba'a saba jin ta ba.
Amma su mamallakan jirgin sai s**a yi burus da abinda suke ji.

Saboda Suna tunanin wata karamar matsala ce da za ta tafi da kanta.

Amma ana nan ana nan wata rana, kwatsam injin ya daina aiki gaba ɗaya.

Masu jirgin sun kasance cikin matsananciyar damuwa. Ba su san abin da za su yi ba. Sun kira kowane makanike(Mai gyara) a garin, amma babu wanda zai iya gyara injin.

Suna cikin nema sai s**a ji labarin wani ƙwararren injiniya wanda ya ke da ƙwarewa a fannin injinan jiragen ruwa ta tsawon shekaru 40.

Aka masa magana. Washegari injiniyan ya iso ya duba injin a hankali. Ya kalli kowane bangare, daga sama zuwa ƙasa. Bayan 'yan sa'o'i, ya sa hannu cikin jakarsa ya ciro wata karamar guduma. Ya buga wani abu a hankali, kawai sai yace ya gama gyaran.

Masu jirgin sun yi mamaki sosai!. Sun kasa yarda cewa injiniyan ya gyara injin daga buga guduma a waje ɗaya kawai.

S**a tambaye shi nawa ne kuɗin aikin sa. Injiniyan ya amsa da cewa, "buga gudumar: dala biyu ne $2. Sanin inda za a buga da kuma sanin yanayin ƙarfin da za a yi amfani da shi: dala dubu tara da ɗari tara casa'in da takwas $9,998. Saboda haka kuɗin sa gaba-daya dala dubu goma" $10,000. Masu jirgin s**a ƙi yarda su biya haka.

S**a ce "Iya buga wani guri fa kawai kayi da guduma!" "Abin da ka yi kenan fa!" Injiniyan ya yi murmushi. "Eh, haka ne Amma na ɗauki shekaru 40 kafin in koyi insan inda zan buga da yawan ƙarfin da zan yi amfani da shi."

Masu jirgin Kawai sai s**a sallama masa s**a biya shi Kuɗin sa, kuma su ka ma sa godiya da gyara injin jirgin su da ya yi.

Sun koyi darasi mai mahimmanci game da ƙimar ƙwarewa.

Wannan labarin Injiniyan abin tunatarwa ne cewa kwarewa ba abu ne da za a iya saya ko sayarwa ba.

Abu ne da ake samu a tsawon lokaci, ta hanyar aiki tukuru da sadaukarwa.

Injiniyan ya shafe shekaru 40 yana koyo a game da injuna, kuma wannan ilimin ya fi kowane adadin kuɗi.

Duk Lokacin da ka fuskanci wata matsala mai wuya, kada ka ji tsoron neman wanda ke da kwarewa.

Wataƙila zai iya taimaka maka magance matsalar cikin sauri a kuma sauƙake, hakan zai yi saurin magance matsalar ba tare da ɓata lokaci mai tsawo da kuɗi mai yawa ba.

Darajar gwaninta ba ta iyakance ga duniyar fasaha ba kawai ba. A'a Hakanan tana da mahimmanci a wasu fannonin rayuwa, k**ar kasuwanci, alaƙa ta yau da kullum da sauran alamura.

Duk Lokacin da ka fahimci kana da gogewa a wani fanni, ta yadda kana da zurfin fahimtar yadda abubuwa ke aiki a wannen ɓangaren. Kuma Ka san abin da za a iya fuskanta, kuma ka san yadda za a magance su. Wannan na iya ba ka wata babbar dama ko fa'ida akan waɗanda ba su da ƙwarewa k**ar ta ka a wannan fannin,

ka ga Don haka idan kana son samun nasara a rayuwa, kada ka raina darajar ƙwarewa.

MK Adam

Wanene Muhammad Ali? Kashi na farko (01)Me ya sa ya shahara?  Me ya sa yake da sunaye biyu, Cassius Clay a shekarunsa na...
13/09/2023

Wanene Muhammad Ali?

Kashi na farko (01)

Me ya sa ya shahara? Me ya sa yake da sunaye biyu, Cassius Clay a shekarunsa na farko, daga baya kuma Muhammad Ali?

Muhammad Ali ya kasance, ba shakka, shahararren dan dambe ne, zakaran duniya. Amma ya yi yaƙi don baƙaƙen fata Amurkawa, Mohammad Ali Ya daina dambe a 1981 saboda rashin lafiya. Amma har ya rasu ya kasance yana fafutukar ganin an samu zaman lafiya a duniya.

Keken mai launin ja da fari (🔴⚪)

Labarin ya fara ne da wani sabon keke mai launin ja da fari na wani yaro.

A shekarar 1954 wani mai suna Joe Martin dan sanda ne a garin Louisville Kentucky, amma yana koyar da dambe a dakin motsa jiki da maraice.

Wata rana wasu samari bakar fata guda biyu s**a shigo dakin motsa jikin. Daya daga cikinsu yana ganin Joe.

Yace "kayi hakuri." "Kai ne Joe Martin, dan sanda?"

"Haka ne." Joe ya ce. "Mene ne matsalar ku?"

Sai yaron ya ce "Sabon kekena ne, mai launin ja da fari 🔴 ⚪ a gaban ginin nan kuma yanzu ban ganshi ba"

Yaron ya faɗi haka cikin damuwa da kuma fusata sosai.

Sannan yaron ya cigaba da fadin cewar
"Zan nemo yaron da keken nawa, sai na masa dukan tsiya!"

Joe Martin ɗan sanda yana kallon ikon Allah kawai yana murmushi.
Yaron dai duka-duka bai fi shekara goma sha biyu ba. Dogo ne da dogayen kafafu, kuma sirara.

"Zaka iya dambe?" Joe ya tambayi yaron,

"A'a, ba zan iya dambe ba," yaron ya ce, "Amma ina so in yi wa yaron dukan tsiya."

Joe ya sake murmushi "To idan haka ne kuwa ya k**ata ka fara zuwa nan dakin motsa jiki da farko. Watakila zan iya koya maka yadda ake dukan."

"Ok" yaron yace. "Ina son hakan."

"Na gode," in ji Joe. "Menene sunnan ka?"

Ya ce "Cassius," ya kara cewa. "Cassius Clay."

Joe bai san cewa a cikin shekaru goma kacal masu zuwa wannan matashin bakar fata zai zama zakaran damben duniya ba!

Bayan haka, Cassius ya fara zuwa wurin motsa jiki na Joe Martin kwanaki shida a mako. Ya kasance mai ƙarfi da kuma zafin Nama sannan yana da matukar sauri a yadda yake jujjuya ƙafafunsa, ana nan har ya fara dambe tare da sauran samari a cikin dakin motsa jikin. Ya kasance baya yin damben kudi, Yana yin dambe ne saboda yana so da sha'awar sa. Kuma ya kanci Nasara sosai a damben da yake yi.

Amma shi ba ya daga cikin dalibai masu hazaƙa sosai a makaranta. Ya sami matsaloli da yawa. Ya kasance yaro nagari daga gida nagari. Ya kasance yana da haba haba da kowa kuma malamansa suna son shi. Amma karatu a makaranta yana masa wuya. Abin da ya fi muhimmanci a wajen sa a duniya a lokacin shi ne dambe.

A cikin shekaru shida, ya yi fafatawa 108 kuma ya ci nasara a guda 100 daga cikinsu.

Sannan a shekara ta 1960, ya je Roma ya yi dambe domin wakiltar Amurka a gasar Olympics.

Gasar Olympics 1960

A 1960, Cassius yana da shekaru goma sha takwas kawai. Ya kasance a Roma don gasar Olympics. Ya doke dukkanin abokan hamayyarsa kuma ya ci lambar yabo ta Olympics ga Amurka. Ya kasance zakaran damben Olympic. Kuma bai cire lambar yabon ta Olympics ba na makonni dare ko rana kodayaushe yana yawo da abar sa a rataye 😊

A gida a garin da ya ke na Louisville, ya shahara. Amma ya kasance shi baƙar fata ne. Kuma a garin Louisville a cikin shekarun 1960s akwai wuraren zama na fararen fata da wuraren baƙar fata.

A yawancin otal-otal, gidajen wasannin kwaikwayo, shaguna, da motocin bas bas, baƙar fata ba sa zama tare da fararen fata.

Wata rana Cassius yana so ya sayi abin sha a cikin kantin "fararen fata". Ashe hakan da matsala, S**a ce masa baza su sayar masa ba sai "fararen fata kawai."

Cassius ya fusata sosai yace,
"Amma ni ne zakaran damben Olympic - na shahara, sosai kowa ya sanni" in ji shi.

"Farare kawai muke saidawa" s**a sake ba shi amsa. Sannan s**a ce masa
"tafi kabar nan!"

Cassius bai ji dadin hakan ba.

"Zan zama zakaran duniya," in ji shi. "Zan zama mai mahimmanci, sannan turawa za su zauna tare da ni kuma dole su saurare ni."

Bayan gasar Olympics Cassius ya fara dambe domin kudi. Dambe ba wasa ko sha'awa bane kaɗai yanzu. A'a Aikinsa ne.

Ya tashi daga Louisville zuwa Miami. Ya je ya samu wani sabon dakin motsa jikin a Miami,

kuma ya haɗu da sababbin abokai da masu bashi horo. Daya daga cikinsu shi ne

Angelo Dundee. Ya yi aiki tare da Cassius a dakin motsa jiki kuma koyaushe yana tare da shi a dukkan damben da zai yi.

✏️ MK Adam

Peter Obi Ba zai taɓa Zama Shugaban ƙasa ba Muddin Ina Raye - Reno OmokriReno Omokri, Tsohon mai Taimakawa Tsohon Shugab...
07/09/2023

Peter Obi Ba zai taɓa Zama Shugaban ƙasa ba Muddin Ina Raye - Reno Omokri

Reno Omokri, Tsohon mai Taimakawa Tsohon Shugaban ƙasa Goodluck Jonathan kan Harƙoƙin yada labarai, Yasha alwashin cewa ba zai taɓa Bari Ya kuma kalli Peter Obi, Ɗan Takarar Shugaban kasa na jam'iyyar Labour, LP, ya zama Shugaban ƙasar Najeriya ba.

Omokri ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tweeter A jiya Laraba.

Yayi nuni da cewa ko da za ta kai shi kashe duk wani abu da yake dashi, zaiyi Hakan ne Don Ganin Obi bai ci Zaɓen Shugaban ƙasa a Najeriya ba.

Omokri ya Rubuta, “Peter Obi, ina jiranka a 2027 da 2031. Allah ya tsawaita rayuwata.

“Saboda abin da mutanen ku marasa da’a s**a yi wa ‘yata ’yar Shekara daya da sauran dangina, Mun sha alwashin baza ku taɓa jin ƙamshin Shugabancin ƙasar ba.

Zan kashe duk abin da nake dashi, Don Ganin Cewa Nijeriya batayi kuskuren zaɓen ku a Matsayin Shuwagabannin mu, Yanzu da kuma har abada abadin!”

Like Northern Mirror Hausa

YANZU-YANZU: Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓe Shugaban ƙasa Ta Kori ƙarar Atiku Abubakar na Kalubalentar Nasarar Bola Tinu...
06/09/2023

YANZU-YANZU: Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓe Shugaban ƙasa Ta Kori ƙarar Atiku Abubakar na Kalubalentar Nasarar Bola Tinubu A Zaɓen da Ya Gabata

Kotun Ta Bayyana cewa Babu wata hujja Da ta nuna an tafka Aringizon Kuriu A zaɓen da Aka Gudanar na Shugaban ƙasa A faɗin Najeriya baki ɗaya

DA ƊUMI-ƊUMI Kotu Ta Karɓe Kujera Daga Hannun LP Zuwa APC A Jihar Abia Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓe A jihar Abia ta ko...
06/09/2023

DA ƊUMI-ƊUMI Kotu Ta Karɓe Kujera Daga Hannun LP Zuwa APC A Jihar Abia

Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓe A jihar Abia ta kori Dan Takarar jam'iyyar Labour Party (LP), Cif Amobi Ogah, Tare da bayyana Dan Takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Hon. Nkeiruka Onyejeocha, a Matsayin Wanda ya lashe Zaɓen Mazabar Tarayya na Isiukwuato/Umunneochi a Jihar Abia.**

Kotun ta yanke hukuncin ne a yau Laraba, 6 ga Satumba, 2023, Bayan ta amince da karar Onyejeocha na kalubalantar sak**akon zaben. Kotun ta Gano cewa an samu kura-kurai da kura-kurai a zaɓen, Wanda ya shafi sak**akon zaben.

Onyejeocha, Wadda kwanan nan ne shugaba Tinubu ya nada a matsayin Ƙaramar Minista a ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi, ta bayyana jin dadin ta ga kotun da ta yanke hukuncin. Ta ce tana da yakinin cewa ta ci zabe cikin adalci kuma za ta yi wa al’ummar mazabarta hidima Gwargwadon iyawarta.

Shi kuwa Ogah ya sha alwashin ɗaukaka kara kan Hukuncin da Kotun ta yanke. Yace yana da yakinin cewa zai yi Nasara a Kotun ɗaukaka kara.

Matakin kotun dai wani babban koma-baya ne ga jam'iyyar LP, wadda ta yi fatan samun Gagarumar nasara a babban zaben kasar na 2023. Sai dai wannan mataki na kara karfafawa jam'iyyar APC mai mulki a mazabar Isiukwuato/Umunneochi na tarayya.

Hukuncin kotun ya kuma tunatar da cewa har yanzu tsarin zabe a Najeriya ba shi da kura-kurai, don haka akwai buƙatar a yi gyare-gyare domin Tabbatar da an gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci.

Gamayyar Matasa Masu Kishin Jihar Kaduna Sun Roƙe Shugaba Tinubu Ya Ɗauki Muhammad Sani Dattijo A Matsayin Minista Daga ...
13/08/2023

Gamayyar Matasa Masu Kishin Jihar Kaduna Sun Roƙe Shugaba Tinubu Ya Ɗauki Muhammad Sani Dattijo A Matsayin Minista Daga Jahar Kaduna.

Tun Bayan da Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Elrufa'i Ya Janye batun karɓar Minsta A Gwamnatin Bola Tinubu Wanda Hakan Ya Haifar da cecekuce Musamman Zaɓo Wanda zai maye Gurbin Nasiru Elrufa'i A Matsayin Wanda Zai Zama Minista Daga Jihar Kaduna.

Gamayyar Ƙungiyoyin Matasa Masu Kishin jihar Kaduna, Sun roƙe Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa Sen Kashem Shettima Dasu miƙa Kujerar Ministan Jihar Kaduna A Muhammad Sani Dattijo Tsohon Shugaban Ma'aikata A Gwamnatin Malam Nasiru Elrufa'i Wanda Ya taka Rawar Gani wajen iya aiki da kawo cigaba a jihar Kaduna.

Comr AA Abubakar Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Matasan Ya bayyana Cewa Muhammad Sani Dattijo Matashi ne mai ƙwazo wanda ya dukufa wajen Ganin ya ƙoƙarta an Samar da cigaba a tsawon lokaci da yayi yana aiki a ma'aikatu daban-daban Cike da wajen kasar nan.

Comr AA Ya ƙara da Cewa Saboda Kwarewarsa da Sanin mak**ar Aiki Tsohon Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Elrufa'i Ya dawo dashi Najeriya Daga ƙasar waje Domin Ya Bada Gudummawar sa A Jiha da ƙasa baki ɗaya, Ina Ganin ire-iren waɗannan Matasan bai k**ata a barsu haka ba Yak**ata a basu dama domin su bada Gudummawar su ta hanyar Samar da Cigaba Mai ɗorewa a ƙasar mu Najeriya.

Sakataren Kungiyar Matasan AMB Sulaiman Buhari Ya Buƙaci Al'ummar Jihar Kaduna dasu Cigaba da yin kiraye-kiraye na Ganin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu Ya Zaɓi Muhammad Sani Dattijo A Matsayin Wanda zai naɗa Minista Daga Jihar Kaduna Domin hakan ba ƙaramin cigaba bane Ga ƙasar mu da Jihar mu baki ɗaya.

Daga ƙarshe Gamayyar ƙungiyoyin Sunyi Fatan Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu Ya duba kiraye-kirayen su da Idon basira Domin Samarwa jihar Kaduna da ƙasa baki ɗaya Cancanta da Dacewa.

Wannan ƙira ne Daga Dandazon Matasa Masu Kishin Jihar Kaduna Da Kasa baƙi ɗaya.

Majalisar Dattawan Najeriya taci karo da Matsaloli Wajen Tabbatar Da Malam Nasir El-Rufai, Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna T...
07/08/2023

Majalisar Dattawan Najeriya taci karo da Matsaloli Wajen Tabbatar Da Malam Nasir El-Rufai, Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Tare da Wasu Ministoci biyu, Bisa Dalilin tsaro.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya Gabatar da Sunayen Mutane 48 a matsayin ministoci, daga cikin 45 aka samu nasarar tabbatar dasu.

Bayan tabbatar da Sunayen Mutane 45 na farko, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Obot Akpabio ya bayyana cewa, Malam Nasir El-Rufai da wasu ‘yan takara biyu ba su samu amincewar tsaro ba.

Akpabio ya bayyana cewa, "Binciken tsaro bai wanke El-Rufai da wasu Mutane biyu ba."

Mutanen da ba a tabbatar da sun hada da Malam Nasir El-Rufai (Kaduna), Stella Okotete (Delta), da Danladi Umar (Taraba).

Ƴan Najeriya Da Kansu S**a Zaɓawa Kansu Tsadar Rayuwa- Sule LamidoTsohon Gwamnan Jihar Jigawa Suke Lamido A Hirar da aka...
07/08/2023

Ƴan Najeriya Da Kansu S**a Zaɓawa Kansu Tsadar Rayuwa- Sule Lamido

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Suke Lamido A Hirar da akayi dashi A Gidan Jaridar BBC Hausa ya bayyana cewa yan Najeriya suni s**a jefa kansu Cikin Halin da suke ciki,

Sule Lamido Ya bada misali Da cewa masu kada kuri'a ba Mahaukata bane Kasan APC kasan PDP Kasan Yan Takarar su, Kasan Wanda Yadace kasan wanda bai dace ba, Sannan da hannun ka zaka jefa kuri'a a Ranar zaɓe. Saboda haka Ni a nawa tunanin yan Najeriya suni s**a jefa kansu Cikin Halin da suke ciki A yanzu.

Sule Lamido Ya Kara Da cewa batun korafe-korafe da Yan Najeriya Suke ba afita bane su Cigaba da Addu'ar Allah ya basu ikon Gyara kuskuren da s**ayi na zaɓar jam'iyyar da bata dace dasu ba

Daga ƙarshe Ɗan jaridar Ya Tambaye Sule Lamido Cewar Tinubu ya taɓa tuntuɓar sa Domin Bashi shawarwari Domin A daƙile Wahalhalun da Al'ummar Najeriya suke fama dashi, Ya Bayyana Cewa ba'a naime shi ba Kuma Yasan baza'a naime shi ba Domin Ba'a ɗauki layin aiwatar da hakan ba.

Hukumar ICPC Ta Fara Bincike Kan Zargin cin Hanci da Rashawa Da ake Yiwa Tsohon Ministan Shari'aHukumar yaki da cin hanc...
07/08/2023

Hukumar ICPC Ta Fara Bincike Kan Zargin cin Hanci da Rashawa Da ake Yiwa Tsohon Ministan Shari'a

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ta ICPC a hukumance ta tabbatar da fara Gudanar da bincike a hukumance kan zargin cin hanci da rashawa da ya shafi Tsohon Babban lauyan Gwamnatin tarayya kuma Ministan shari’a, Abubakar Malami. Anyi cikakken bayanin wannan bincike ne, A cikin wata sanarwa mai kwanan watan Yuli 19, 2023, Wanda H.S. Folaranmi Ya Fitar.

A yayin da take mayar da Martani kan koken da cibiyar albarkatun ƙasa ta Human and Environmental Development Agenda (HEDA), Wata ƙungiya mai zaman kanta ta Najeriya ta shigar Gaban, ICPC ta bayyana kudurinta na magance matsalolin da aka taso. Shugaban ƙungiyar, Olanrewaju Suraju, ne Ya miƙa buƙatar A Ranar 10 Ga Watan Yuli, 2023.

Takardar koken ta kawo misalai daban-daban na Rashin da’a da Kuma rashin bin ka’ida da s**a shafi Abubakar Malami a lokacin da yake riƙe da muƙamin Babban lauya Kuma Ministan shari’a. Waɗannan zarge-zarge sun kunshi batutuwa da dama, Da s**a haɗa da rabon kyaututtukan Motoci, Gwanjon jiragen Ruwa da aka k**a, da katsalandan a bincike, Da kuma zargin hannu a ayyukan damfara.

HEDA ta Bayyana damuwar ta Sannan ta Buƙaci a Gudanar da cikakken bincike kan waɗannan munanan zarge-zarge don tabbatar da bin doka da oda da kuma Tabbatar da bin diddigin masu riƙe da muƙamin Gwamnati.

Matakin da ICPC ta ɗauka na fara Gudanar da bincike ya nuna irin yadda ta dage wajen Tabbatar da Gaskiya, Da kuma adalci a cikin sassan Gwamnatin Najeriya. Wannan matakin na nuna muhimmancin Tabbatar da cewa anyi nazari sosai kan zarge-zargen cin hanci da Rashawa da kuma cin zarafi na ofis da kuma magance sahihancin cibiyoyin Gwamnati.

Ɗan Majalisar Jihar Daga Jihar Bauchi Ya Bada Naira Miliyan 23 Domin Taimaka Al'ummar da Yake Wakilta A Ɓangarori Daban-...
31/07/2023

Ɗan Majalisar Jihar Daga Jihar Bauchi Ya Bada Naira Miliyan 23 Domin Taimaka Al'ummar da Yake Wakilta A Ɓangarori Daban-daban.

Ɗan Majalisar Jiha Mai Wakiltar Karamar Hukumar Jama'are Alhaji Mubarak Haruna Mai Rakumi yayiwa kwamitocinsa rabon kudi da zasu k**a aiki harna Tsawon Shekara Ɗaya.

A yayin jawabinsa yaja hankalin ko wanne Chirman na kwamiti da yayi aiki tukuru da kudin da aka bashi ta Hanyar Daya dace domin kuɗin al'umma ne kuma su s**a kawoshi wannan Kujerar.

Wannan sune Kwamitin da aka Basu kuɗi domin k**a aiki.
1. Kwamitin kula da Ruwan sha 2 million naira.
2. Kwamitin kula da lafiya 1.4 million naira.
3. Kwamitin empowerment Maza da mata 6 million naira.
4. Kwamitin wassanni 1 million naira.
5. Kwamitin Agajin Gaggawa 1.25 million naira.
6. Kwamitin Yan makarantar High education 1.25 million naira.
7. Kwamitin nemawa Yan makaranta Admission 500k naira.
8. Kwamitin Yan makarantar primary da secondary school 1.4 million naira.

Ya Rabawa wayannan kwamitin kyautar kudi a Wajen Taron.

Health 100,000
Education 450,000
Sports 450,000
Emergency 250,000
Higher Edu. 1,300,000
Admission 250,000
Marriage Comm. 150,000
Water 1,100,000
Mai Rakumi T.V 95,000
Media Comm. 700,000
Special List 92,000

Ida ba'a Manta Ba dai Hon Mubarak Mai Rakumi Shine Ɗan Majalisar jiha ɗaya Tilo daga jihar Bauchi da Ya lashe Zaɓen Ɗan Majalisa a Jam'iyyar NNPP a zaɓen da Ya Gabata, Nasarar sa a bakuwar Jam'iyya yanuna tasirin sa da Samun Amincewar mutanen ƙaramar Hukumar sa. Na yakinin zai gudanar da adalci Wajen Sahihancinsa.

KBC Hausa News

Shari'a: Hon Farouk Mustapha Ya Bada Shaida Ta Karshe Daga Ɓangaren PDP Kan Zaben Gwamnan jihar Bauchi A 2023.Kotun Saur...
13/07/2023

Shari'a: Hon Farouk Mustapha Ya Bada Shaida Ta Karshe Daga Ɓangaren PDP Kan Zaben Gwamnan jihar Bauchi A 2023.

Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe Dake jihar Bauchi A Yau Alhamis 13 Ga Watan July Ta Cigaba da Sauraren ƙarar da Jam'iyyar APC da Ɗan Takarar ta na Gwamna Air Marshall Sadik Abubakar s**a Shigar na Kalubalentar Nasarar Gwamnan Jihar Bauchi Sen Bala Abdulkadir Mohammed Kauran Bauchi A Zaɓen da Ya Gabata.

Babban Daraktan Yaƙin neman Zaben Gwamnan Jihar Bauchi Hon Farouk Mustapha Ya Zama shaida na ƙarshe da Jam'iyyar PDP Da Kauran Bauchi s**a Gabatar a Matsayin wanda zai bada shida akan zaben Gwamnan jihar Bauchi da Ya Gabata. Ta ɓangaren su.

Farouk Musapha Ya bayyana wa Mai Shari'a cewar nasarar su nasara ce Mai inganci wacce al'umma s**a fito s**ayi zaɓe ba tare da Magudi ba. Kuma ya bayyana cewar Zaɓen jihar Bauchi zaɓe ne da ya Kasance Sahihi Mai inganci Wanda ba'a taɓa Irinsa ba a Jihar Bauchi.

A Halin Yanzu Jam'iyyar APC Sun Kammala Gabatar da Hujjojin Su A Gaban Kotu Yayinda Jam'iyyar PDP S**a kammala Kariyar su.

Mai Shari'a Ya ɗage Shari'ar Zuwa Ranar 16 Ga Watan Agusta Domin Cigaba da Sauraren Ƙarar.

KBC Hausa News

Hon Muhammad Sani Dattijo Tsohon Kwamishinan kasafi da tsare-tsare A Jihar Kaduna, Ya saki Sabon littafinsa na farko, Ma...
08/07/2023

Hon Muhammad Sani Dattijo Tsohon Kwamishinan kasafi da tsare-tsare A Jihar Kaduna, Ya saki Sabon littafinsa na farko, Mai Suna "Dole A Rushe A: Sake Tunanin Mulki Ga Talaka,

Wannan littafi na farko ya shiga cikin lamarin Gaggawa na kafa Gwamnatin da zatafi bada Muhimmanci Ga Rayuwar masu rauni a cikin al'ummarmu.

Abubuwan da suke Cikin Littafin Shine samar da canji mai mahimmanci da cimma daidaiton zamantakewa na Gaskiya. Ta hanyar tambayar hikimar al'ada Game da Mulki, Littafin Yana Gabatar da dabarun juyin juya hali don biyan buƙatun Talakawa Yadda Ya k**ata. Karku rasa damar mallakar kwafin wannan Gagarumin littafin. Sayi kwafin ku Domin kara fahimtar Mahimman batutuwa da s**a shafi ƙasar mu Najeriya.

Wuraren da aka wari Domin sayar da littattafai A jihohi daban-daban Gasu k**ar Haka👇

A babban Birnin Tarayya Abuja:
2nd Floor, City Center Plaza,
Port Harcourt Crescent, Garki II,
Abuja.

A jihar Kaduna:
Fasaha Cafe 21,
R***a Street, Off Isa Kaita,
Kaduna.

A Jihar Legas Legas:
Shafi kantin sayar da littattafai,
1st Floor, Ibilola Nelson House,
Allen Avenue, Ikeja,
Legas.

KBC Hausa News

SEN. ABDULAZIZ YARI NE YAFI DACEWA DA JAGORANCIN MAJALISAR DATTAWA NA 10.Ƙungiyar Atiku Door to Door Mobilisation Forum ...
11/06/2023

SEN. ABDULAZIZ YARI NE YAFI DACEWA DA JAGORANCIN MAJALISAR DATTAWA NA 10.

Ƙungiyar Atiku Door to Door Mobilisation Forum na kasa, A taron da s**a kira na yan Jaridu, Sun Gabatar da Goyon bayan Kungiyar Ga Sen. Abdulaziz Yari don Yazama Shugaban Majalisar Dattawa na kasa karo na Goma.

Shugaban Ƙungiyar na Kasa, Amb. Imran Abdullahi Idris (Barden Samarin Najeria) Shine yayi wannan kira, A lokacin daya jagoranci zaman, Ya bayyana Sen. Yari a Matsayin gogaggen ɗan siyasa, Wanda ya rike muƙamai daban-daban a jam'iyyance, Dama matakin tarayya, Tun Daga Shugaban jam'iyya na jiha har na ƙasa, yayi ɗan Majalisar Tarayya, Gwamna har sau biyu, Sannan yaci zaɓen Sanata a 2019, Wanda hakan yanuna gogewarsa, kuma zai bashi daman iya Jagorancin Majalisar.

Amb. Imran yayi kira Ga sauran Sanatocin, Da suyi amfani da damansu donsu zaɓa wa kansu dama kasa baki daya shugabanni nagari, Ta Hanyar zaban Sen. Yari a Matsayin Shugaban su, don Samun kyakyawan Shugabanci A Majalisar Dattawa Karo na Goma.

ATIKU DOOR TO DOOR MOBILISATION FORUM
MEDIA TEAM
11/06/2023

Abubuwan al'ajabi ba za su ƙare ba. Allah ɗaya gari banban Wasu makwabtan juna guda biyu sun yi musayar matansu na aure ...
05/06/2023

Abubuwan al'ajabi ba za su ƙare ba.

Allah ɗaya gari banban

Wasu makwabtan juna guda biyu sun yi musayar matansu na aure a kotu

"Mun gaji da bin Matan juna" maƙwabtan da kayi musayar matan nasu sun ba da dalilin abin da s**a aikata. Waɗannan mutane maƙwabta biyu ne waɗanda s**a zama aminai. Haka s**a dinga ziyartan juna har s**a fara soyayya da matan juna. Da farko suna zagayawa har daga ƙarshe s**a cimma matsaya kan musayar matansu ta hanyar shari'a. Sun yi haka kuma matan sun tafi gidajen mijinsu tare da ’ya’yansu.

Hon Zuwaira Gambo Tayi Ƙoƙari Wajen Samar Da Cigaba A Fannin Mata A Lokacin Da Take Riƙe Da Matsayin Kwamishinar Mata.Ho...
04/06/2023

Hon Zuwaira Gambo Tayi Ƙoƙari Wajen Samar Da Cigaba A Fannin Mata A Lokacin Da Take Riƙe Da Matsayin Kwamishinar Mata.

Hon Zuwaira Gambo Tsohuwar Kwamishinar Mata a jihar Borno Ta bada Gudummawa sosai Wajen Samar da cigaba Mai ɗorewa a ɓangaren Mata. Samarwa da Mata jari Domin su dogara da kansu a ƙananan hukumomi 27 da Suke jihar Borno babu karamar Hukumar ta Bata samar da cigaba ba. Ƙarƙashin Mai Girma Gwamna Babagana Umara Zulum

An kwashe Tsawon Shekaru a jihar Borno Mata suna riƙe da muƙamin. Amma ba'a taɓa samun wacce tayi ƙoƙarin Samar da nagartattun abubuwa k**ar Zuwaira Gambo ba. Lungu da Saƙo a jihar Borno Ba Yadda sunanta bai shiga ba. Saboda jajircewar da take akan al'umma.

Dubban Mata ne suke addu'a ba dare ba rana. Akan Mai Girma Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum Akan Yadawo da ita kan Kujerar ta Domin ta ɗora Daga Yadda Ta saya na Taimakon marayu da marasa Galihu na jihar Borno da kewaye.

Wannan kira ne Daga Kungiyoyi Mata Masu kishin Jihar Borno

A Tarihin Jihar Borno Ba'a Taɓa Samun Shugaban Karamar Hukumar Da Yayi Ayyukan Da S**a Daca K**ar Hon Ibrahim Haruna Ibs...
03/06/2023

A Tarihin Jihar Borno Ba'a Taɓa Samun Shugaban Karamar Hukumar Da Yayi Ayyukan Da S**a Daca K**ar Hon Ibrahim Haruna Ibsy

Ƙungiyar Matasa masu Kishin Karamar Hukumar Biu Sun Bayyana cewa a tarihin ƙaramar Hukumar ba'a taɓa samun Jajirtaccen da yayi aiki Tukuru Don Gina Ƙaramar Hukumar K**ar Hon Ibrahim Haruna (IBSY) Muna Kira Ga Mai Girma Gwamnan da Ya Duba Wannan Bawan Allah Yabashi dama domin cigaba da kawo ayyukan alheri a karamar Hukumar mu ta Biu.

Gwamanan Jihar Borno Babagana Umara Zulum ya kasance Mutumin kirki wanda yake Kaunar aiki da mutanen kirki muna Fatan a wannan sabuwar Gwamnati da za'a kafa. Zulum ya dauki ire-iren su IBSY Domin kawo cigaba Mai ɗorewa a jihar mu ta Borno.

Shanun Buhari sun ragu saboda kyauta'Tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya miƙa takardar da ya cike da ke ƙunshe...
03/06/2023

Shanun Buhari sun ragu saboda kyauta'

Tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya miƙa takardar da ya cike da ke ƙunshe da bayanan kadarorin da ya mallaka ga hukumar ɗa'ar ma'aikata CCB bisa tanadin shafi na shida na Kundin tsarin mulkin ƙasa.

A yau ne hukumar ta CCB ta tabbatar da karɓar fom din tsohon shugaban ƙasar.

Takardar bayanan ta nuna cewa kadarorinsa da za a iya sauyawa wuri ba su ƙaru ba - a gida da kuma wajen Najeriya.

Sannan bai buɗe wani sabon asusun banki ba, baya ga wanda yake da shi a bankin Union a Kaduna.

Bayanan sun ƙara da cewa, tsohon Shugaban bai karɓi bashi ba kuma adadin shanunsa sun ragu saboda ya bayar da wasu kyauta cikin shekara huɗu da ta gabata.

©BBC Hausa

Address

London

Telephone

+2347067289098

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Northern Mirror Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share

Category

  • 457Games

    457Games

    92 the larches, Palmers Green