#TafiyaMabudinIlmi# Ko kun san gada irinta ta farko a duniya da aka yi amfani da hasumiyoyi biyu da karafa wajen riketa? Cikin wannan shiri, Fa’iza Mustapha ta ziyarci wannan, sai mu bita mu sha kallo.
Yanzu haka ana gudanar da bikin baje kolin CIIE a birnin Shanghai. Inda daga ran 5 zuwa 10 ga watan nan, za a baje kolin dubban sabbin kayayyaki da fasahohi da hidimomi. Ga irin wainar da ake toyawa a wajen bikin
Ana gudanar da bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin karo na biyar (CIIE) a birnin Shanghai na kasar Sin daga yau Asabar 5 zuwa 10 ga watan Nuwanban wannan shekara.
A matsayinsa na bikin baje kolin kasa da kasa na farko a duniya, mai taken shigo da kayayyaki, bikin na CIIE ya kasance wani muhimmin dandali na saye da sayarwa na kasa da kasa, da inganta zuba jari da musaya tsakanin al’ummomi da na al’adu, da hadin gwiwar dake shafar kowa da kowa tun lokacin da aka fara gudanar da shi a shekarar 2018. A yayin bukukuwan CIIE guda 4 da aka gudanar a baya, yawan darajar kwangilolin da aka kulla ta kai dalar Amurka biliyan 272.3.
Kalmar da zan koya muku ita ce进博会 jìnbóhuì, ma’ana bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin ko CIIE a takaice. Bikin baje kolin CIIE, shi ne irinsa na farko a duniya, wanda wata kasa ke gudanarwa da nufin hallara masu shigo da hajoji daga waje, wanda kuma ke gudana a birnin Shanghai na gabashin kasar Sin duk shekara, tun daga shekarar 2018. An ce wakilai daga kasashe 145 za su shiga a dama da su, a baje kolin a bana, Ana sa ran bude sabon sashen baje kolin hajoji, daga kamfanonin samar da irin shuka, da na fasahohin kwaikwayon tunanin bil Adama, baya ga daruruwan sabbin masu sayayyar albarkatun gona, da hajojin fasaha, da sauran ayyukan hidima.#KoyonSinanciASaukake#
Auduga a Xinjiang
Assalamu alaikun, masu kallonmu. Jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta dake arewa maso yammacin kasar Sin wuri ne da ta fi samar da yawan auduga a duk fadin kasar Sin. A halin yanzu ana girbin auduga ba dare ba rana a jihar, kuma an kammala kashi 80 bisa dari na ayyukan ta hanyar amfani da injuna.
Kwadon Baka Promo EP25
Shin kun damu ku san yaya noman zamani da ake amfani da naurori yake da kuma yadda ake gudanar dashi? Shin kayan marmarin da aka samar ta hanyar noman zamani na da dandano mai dadi? Ku kalli kadan daga ciki kuga yadda zai kayatar daku!
STORY 2 - A SINGLE MOM AND HER RAILWAY STORY
Labarin mahaifiya da hanyar dogo a kasar Kenya
Ana shirya bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin (CIIE) karo na biyar a birnin Shanghai.