ALIYU Abdullahi DAN AGAJi

ALIYU Abdullahi DAN AGAJi Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from ALIYU Abdullahi DAN AGAJi, Magazine, Zaria.

•Wasu S**e: MAMA•Wasu S**e: UMMAH•Wasu S**e: INNAH    •Daga Lokacin Da Ta Samu CikiZaman Lafiya Ya Kare A Wurin Ta •Kull...
10/02/2023

•Wasu S**e: MAMA
•Wasu S**e: UMMAH
•Wasu S**e: INNAH


•Daga Lokacin Da Ta Samu Ciki
Zaman Lafiya Ya Kare A Wurin Ta
•Kullum Tana Kan Hanyar Asibiti
•Magunguna Su Zasu Zama Abincin Ta
•Kullum Tana Cikin Amsar Allura 💉
•Hakan Bawai Iya Na Sati Daya Bane Ko Kuma Sati Biyu

Har Wata Tara Za Tayi Cikin Wannan Hali
Sai Kuma Tafara Jin Nakuda
Daga Wannan Lokacin Har Zuwa Ta Haihu Allah Kadai Yasan Irin Azabar Da Take Sha
Bayan Kazo Duniya Sai Tasamu Damar Shiga "Next Level" Na Wahala Dakai 🤱
•Kayi Kashi Ta Wanke
•Kayi Fitsari Ta Wanke
•Kayi Tumbidi Ta Share
•Da Zarar Ka Fara Kuka Zata Dauke Ka Ta Baka Nono
Wani Lokaci Har Cizon Ta Zakayi
Idan Taji Zafi, Sai Ta Daga Hannu Zata Buge Ka
Sai Kayi Dariya
Dariyar Da Kayi Sai Itama Ya Bata Dariya !
Allah Sarki Mahaifiya💧
•Mahaifiya Ita Kadai Ce Take Ajiyar Danta Wata Tara Acikin Cikin Ta 🤰 Kuma Ta Aje Sa Har Abada Acikin Zuciyarta.
Allah ya jikan mahaifanmu Allah yasa Aljannace makomarsu👏Ameen muma intamu tazo Allah ya sa mudace da Aljannar Ameen ya Allah

10/02/2023

Duk wanda ya raba mace da baqin ciki lallai ya aikata babban aiki, domin suna binne baqin ciki a zuciyar su ne su yi ta rayuwa dashi. Allah ka bamu ikon farantawa iyayenmu da matanmu

10/02/2023

Ka girmama matarka, kar ka zalunce ta. Wata rana 'Yarka ko 'Yar'uwarka za ta je gidan wani.

Kiyi wa Mijinki biyayya; wanda ya umurce ki da Sallah da Azumi Shi yace kiyi masa biyayya.

Itama fa rayuwar aure akwai hisabi akan ta. Wasu mutanen suna rasa albarka da nasara a rayuwa ne sabo da danne hakkin Zamantakewar Aure.

Kulawa da hakkin Aure yana daga cikin Wasiyyar Manzon rahama (S)

10/02/2023

JAN HANKALI

Karka sake Maƙotanka su yi maka mummunan shaida akan waɗannan abubuwan:

1. Kar ka sake ayi maka shaidar rashin yin sallah ko ƙin zuwa masallaci matukar kana da lafiya.

2. Kar ka sake ayi maka shaidar baka yiwa mutane sallama ko in sun yi maka baka amsawa.

3. Duk rintsi duk wuya kar a sameka da laifin ƙin zuwa ta'aziyya, ko rashin duba maƙocinka yayin da bashi da lafiya.

4. Kar ka sake a kamaka da laifin zubawa maƙocinka kwata a ƙofar gidansa.

5. Ka yi iyaka ƙoƙarinka wajan barin matarka zuwa dubiya ko barkar suna a keɓantaccan lokacin da ka zaɓa mata.

6. Karka sake ka ci kuɗin maƙocinka, ko a yi maka shaidar zalunci.

7. Kar ka sake maƙocinka ya tambayeka wani abu ka hana shi matukar kana da shi ko yaya ya ke.

8. Ka zamanto mai nuna damuwarka yayin da maƙocinka ya ke cikin wani mawuyacin hali, karka koma gefe kana tseguminsa.

9- kar ka sake ayi maka shaidar mai nuna fariya ko nuna cewa ka fi kowa ilmi, kuɗi, matsayi, ko mukami.

10. Kar ka sake ka kwana cikin koshi yayin da maƙocinka ke cikin yunwa

Ya Allah ka sanya mu cikin salihan bayinka karka sanya mu cikin gafalallu.


Allah yasa muna daga ciki masu samu babba rabo ranar gobe kiyama. ameen

Ya Allah! Ka bamu kuɗi masu yawa, masu amfani kuma masu albarka
08/02/2023

Ya Allah!
Ka bamu kuɗi masu yawa, masu amfani kuma masu albarka

08/02/2023

Allah yasa mu tsira gada farkon mutuwa har zuwa tsallake siraɗi, Allah ya haɗa mu da habibuna Sallallahu alaihi Wasallama ❤️

08/02/2023

YIN ALWALA YAYIN KWANCIYA BACCI SABABI NE DAGA CIKIN SABUBBAN DAKE SA MALA'IKU SU NEMAWA BAWA GAFARA A WURIN ALLAH (ﷻ)

Alwala Yayin Da Mutum Zai Kwanta Bacci Tana Daga Cikin Al'amuran da Shari'a Ta Kwaɗaitar da Aikatasu; Don Hakane Hadisai Ingantattu S**a Tabbata Game da Falala da Mutum Yake Samu Yayin da Ya Kwanta Bacci Cikin Tsarki. Hakika Hadisi Ingantacce Yazo Manzon Allah (ﷺ) Yana Cewa Dangane da Kwaɗaitarwa Akan Alwala Yayin Kwanciya Bacci:

(إذا أتيت إلى فراشك فتوضأ وضوءك للصلاة)
{البخاري (٢٤٧)، مسلم (٢٧١٠).

“Idan Ka Isa Wurin Baccinka, To Kayi Alwala Irin Alwalarka Ta Sallah”.
(Bukhari: 247, Muslim: 2710)

Ibn Hajr (rh) Yana Cewa: “Mustahabbi Ne Sabunta Alwala Yayin da Mutum Zai Kwanta Barci Koda Kuwa Yana Cikin Tsarki Ne; Ballanta Kuma Ga Wanda Asali Ma Ba Cikin Tsarkin Yake ba”.

Yana Daga Cikin Gara6asa Da Bawa Zai Samu Yayin da Yayi Alwala Lokacin Kwanciya Barci, Abinda Ya Tabbata Daga Manzon Allah (ﷺ) Yana Cewa:

عن عبد الله بن عمر رضي الله عنه، عن رسول الله صلّى الله عليه وسلّم قال: (مَن بات طاهرًا بات في شِعارِه مَلَكٌ فلَمْ يستيقِظْ إلَّا قال المَلَكُ: اللَّهمَّ اغفِرْ لعبدِك فلانٍ فإنَّه بات طاهرًا)
[رواه إبن حبان]

An Karɓo Daga Abdullahi bn Umar (ra), Daga Annabi (ﷺ) Yace: “Duk Wanda Ya Kwana Cikin Tsarki, Zai Kwana a Tare Dashi Akwai Wani Mala'ika, Bazai Farka Ba Face Mala'ikan Yace: (YA ALLAH KA GAFARTAWA BAWANKA WÃNE, DOMIN YA KWANA NE CIKIN TSARKI)”.
(Ibn Hibbãn Ya Ruwaitoshi)

Har Ila Yau Hadisi Ya Tabbata Game da Samun Neman Gafarar Mala'iku Ga Wanda Ya Kwanta Bacci Da Alwala Inda Manzon Allah (ﷺ) Yake Cewa:

عَنِ ابْنِ عُمَرَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: (طَهِّرُوا هَذِهِ الْأَجْسَادَ طَهَّرَكُمُ اللهُ، فَإِنَّهُ لَيْسَ عَبْدٌ يَبِيتُ طَاهِرًا إِلَّا بَاتَ مَعَهُ مَلَكٌ فِي شِعَارِهِ لَا يَنْقَلِبُ سَاعَةً مِنَ اللَّيْلِ إِلَّا قَالَ: اللهُمَّ اغْفِرْ لِعَبْدِكَ فَإِنَّهُ بَاتَ طَاهِرًا)
[الطبراني في المعجم الكبير (١٣٦٢٠)]

An Karɓo Daga Ibn Umar (ra), Lallai Manzon Allah (ﷺ) Yace: “Ku Ts

08/02/2023

Ya Allah! Ka sanya mu a cikin Aljannah, ba don halinmu ba, ba kuma don ayyukanmu ba, sai don Jin Ƙanka da tausayinka.

07/02/2023
First Aid Group Initiative Fityanul Islam Of Nigeria join all other Islamic organization to say no to burkina Faso Heart...
07/02/2023

First Aid Group Initiative Fityanul Islam Of Nigeria join all other Islamic organization to say no to burkina Faso Heartless Act by killing our Tijjaniya brother's. to for our Tijjaniya brother's Innocent Souls Killed by Burkina Faso.

27/01/2023

"Ita mace itace jagorar jama'a, idan ta gyaru jama'a sun gyaru, idan ta ɓaci jama'a sun ɓaci. Ku yi iyakar yin ku wajen inganta tarbiyyar ƴaƴan ku mata"

WANNAN SAƘON ALLAH YASA YAJE GAREKA ABBA.Naci karo da wani video daga jiya zuwa yau na kalle shi a status ɗin mutane yak...
10/01/2023

WANNAN SAƘON ALLAH YASA YAJE GAREKA ABBA.

Naci karo da wani video daga jiya zuwa yau na kalle shi a status ɗin mutane yakai 30 ko fiye da haka. Kowa Abun Dariya yake bashi Amma wallahi Ni sam bahaka bane daga Gareni naji tausayin ta sosai Yadda naga soyayyar ka ABBA fall a fuskar ta ta kasa ɓoyewa.

Su kansu matan sai yawo suke da Video sunga Abun mamaki Don Allah koda wasa kada kabari Yarinyar nan tayi nadamar Auran ka kayi iya ƙoƙarin ka Domin tabbatar da wannan farin cikin da ta nuna Lokacin da taji An ɗaura Auran ku.

Irin yadda Aure ya zama a wannan zamanin Ance Rashin soyayya ne yasa ya lalace to kai wlh ABBA wannan soyayyar da yarinyar nan ta nuna maka a Iya bayyanar wannan farin cikin Abu ne mai wahala kasamu Irin haka Domin Ni ko a Films ban taɓa gani ba Don Allah kariƙe yarinyar nan Amana Mallam ABBA.

Allah Ya baku zaman Lafiya ya dauwamar da Farin ciki a fuskar ku, muma Allah ka barmu da masu ƙaunar mu.

09/01/2023

In kika duba ni'imar da rufun asirin da aure ya miki,tun daga ranar da aka daura aure an maida ke fa sabuwa kamar yau aka haife ki,an yaye miki zunubanki na baya da kika yi,saboda darajar aure
Kuma ko me kika yi a gidannan ladane,kiyi kwalliya lada,kiyi shara lada,kiyi girki lada,komai kika yi lada ne duk da amfanin kanki ne,in yaranki k**e kula dasu lada ne

09/01/2023

Kar ku ga ana ta zancen maza kullum basu da kirki basu da kaza basu da kaza,sunyi kaza sunyi kaza
Allah yana sane ya yi su a haka!

Ita fah Aljannah ba a samunta cikin sauqi!!
Hakurinku,da juriyarku Allah yake gwadawa,yana so yaga zaku yi masa biyayya akan abinda ya umarce ku

Amma mata basa ganewa,wata in ance tayiwa miji biyayya sai tace ay bashi da mutunci,yayi kaza yayi kaza

Wallahi duk hakurinki Allah yana kallo,kuma yana sane.

09/01/2023

Me k**e so bayan wannan
Allah yana sane da wanda zasu fara hakuri s**e sun gaji,sai yace fasbir,kayi hakuri,sabaran jameela,hakuri kyakkyawa
Kunga kenan akwai hakurin da bai cika hakuri ba ko?
In kince hakurin ki ya qare kin dauki mataki toh me kenan kikayi? Wahalar da kikai a banza kenan ta tashi.

09/01/2023

Ku kalli fa,sujjadar da Allah kadai ake yiwa amma ace wai da za'a yi wa wani,ba'ace annabi ba,ba'a ce iyayenki ba,ba'a ce malaminki ba sai aka ce miji,kinga kuwa lallai ana so a nuna miki ne bayan Allah da manzonsa babu wanda ya chanchanci biyayyaa da total devotion irin mijinki

09/01/2023

Da yawa mata na making mistake wai s**e su zasu qwatarwa kansu yanci da cin zarafin miji,da bijere masa da kin yi masa biyayya,to kin samu 'yanci kin rasa aljanna me kika yi kenan?

09/01/2023

Babu wani dalili ko hujja da Allah zai karba daga wurinki duk randa kika tsaya a gabansa da laifin cin mutuncin miji,rashin biyayya,cin amanarsa da wulakanta shi
Miji yana da girman da sai da manzan Allah s.a.w yace da za'a umarci wani yayi wa wani sujjada toh da an umarci mace da tayi wa mijinta

Kar ka damu a yayin mutuwarka!! Kar ka damu da gangar jikinka, Musulmai zasu yi abin d ya kamata. Zasu cire maka tufafin...
09/01/2023

Kar ka damu a yayin mutuwarka!! Kar ka damu da gangar jikinka, Musulmai zasu yi abin d ya kamata. Zasu cire maka tufafinka, su wankeka, zasu sanya maka likkafani, sa'annan su fitar da kai zuwa ramin da za a turaka a ciki.

Mutane zasu bar harkokinsu na yau da kullum don su halarci Janazarka. Wani yana da wani abu mai matuƙar muhimmanci amma zai bar shi.

Duk abin da ka mallaka zai zama Gadon wasu, idan ka samu waɗanda suke da tarbiyya; sune waɗanda zasu yi maka abin da zai rage maka wahalar Ƙabari

Ka sani Duniya ba zata tsaya b saboda mutuwarka, harkokin cinikayya da na tattalin arziki, abubuwan ka na yau da gobe duk wasu ne zasu cigaba da yi.

Dukiyar da ka tara (Halal ce ko Haram) zata koma hannun Magada,kai kuma za a yi maka Hisabi akan taro da sisi (ya ya ka samu? ya ya ka kashe?).

Mutanen da s**a sanka sama-sama zasu ce Allah sarki, abin tausayi, su wuce. Abokanka zasu ji babu daɗi na wani ɗan taƙaitaccen lokaci saannan kowa ya cigaba d sabgoginsa kamar da ɗai wani abu bai faru b. Danginka zasu kai sati ɗaya zuwa biyu suna jimaminka daga nan su watsaka cikin tarihi, kowa ya cigaba da harkokin gabansa.

Labarinka tsakanin mutane ya ƙare, yabonsu ba zai amfaneka ba, haka, zarginsu ba zai cutar da kai ba.

Yanzu labarin Lahira zai fara! Mai ka tanadar mata? wana irin guzuri ka yi..? Me ka shirya domin zaman Ƙabarin da ka tabbatar babu makawa sai kaje..?

08/01/2023
27/12/2022

Wad'anda Suke Son Aure Babu Halin Yi, mata da maza ALLAH Ka Azurtasu Ka Wadatasu Da Arziqi Mai Albarkah 🖤🤲🏻

27/12/2022

Mu daure mu kawo sunan ALLAH Koda d'aya 1 ne IN'SHA ALLAH ze zam silar ALKHAIRAI da dauke war damuwa gare mu
AL'HAYYU AL'QAYYUM

27/12/2022

Sun Tsaya a Gida Sun Tsare Mutuncinsu ☺

YA ALLAH KA aurar dasu Ga mazajen 'kwarai Masu addini cikin salama❣️🤲

27/12/2022

Mu masu laifi ne dare da Rana fili da 6oye Muna tuba tare da neman shiriya YA GAFFARU
ASTAGFIRULLAH 😥

27/12/2022

Don Girman ALLAH🙏
Kar ku wuce sai kunyi man addu'a
Ko da ba comment ba like
ALLAH YA AMSA MANA
NAGODE SOSAI

Allah kar ka rabamu da Annabi, a duniya da lahira.Sallallahu alaihi wasallam.❤️
24/12/2022

Allah kar ka rabamu da Annabi, a duniya da lahira.

Sallallahu alaihi wasallam.❤️

Address

Zaria

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when ALIYU Abdullahi DAN AGAJi posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category


Other Magazines in Zaria

Show All