Ahlin gidan sheik Aleeyu namangi zaria

Ahlin gidan sheik Aleeyu namangi zaria Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Ahlin gidan sheik Aleeyu namangi zaria, Magazine, Zaria city, Zaria.

03/05/2021

TAKAITACCEN TARIHIN GIDAN SU DR ALIYU NAMANGI DA SANADIYANR RASA IDANUNSA
KASHI NA FARKO (1)
Bincike ya nunar da cewa asalin garin Kakannin Aliyu Namangi shi ne Jibiya da ke cikin Jahar Katsina a yanzu. Sun taso sun komo kasar Zazzau ne a zamanin mulki sarkin Zazzau Hammada, wato a wajen shekara ta dubu daya da dari takwas da arba'in da shida, 1846. Masihiyya. Malam Muhammudu Attammu, wato Kakan Aliyu Namangi shi ne ya fara zuwa Zariya da zama.

Zuriyar Muhammudu Attammu, wato Kakan Aliyu Namangi suna daga cikin magadan sarautar Jibiya. Saboda kalubale da surkulle da ke cikin neman sarauta shi ne ya sabbaba masu bari garin Jibiya inda s**a watsu cikin duniya. Wasu sun nufi wajen Kano wasu kuwa s**a danno zuwa Zariya. A cikin wadanda s**a nufo Zariya har da Kakan Aliyu Namangi Muhammudu Attammu. A yayin da s**a iso Zariya sun zauna ne a Anguwar Limanci a cikin birnin Zariya.

Ba wani abu ya dawo da Iyayen Aliyu Namangi, garin Mangi da zama ba, illa nadin da aka yi wa Kakan Aliyu Namangi, wato Muhammudu Attammu da sarkin Mangi mai ci a wancan lokacin ya yi masa a matsayisa sarkin yara Magajin gari Mangi, Mangi na wannan lokacin mai mulki ana kiransa Magaji Daudu.

Mahaifin Aliyu Namangi Malam Ishaka ya sami sarautar Mangi bayan an fitar da Magajin Mangi wanda ya gaji Daudu, wato Isa. Sarkin Zazzau Yero ne ya nada shi a matsayin Magajin Mangi.

Malam Ishaka mahaifin Aliyu Namangi bayan da ya yi aure ya dauki tsawon lokaci, Allah bai ba shi haihuwa ba. Wannan ya sa Malam Ishak ya damu kwarai da gaske saboda rashin haihuwa matarsa. A matsayisa na dan sarki kuma ga shi magajin gari, in har ba shi da dan lallai zai kasance ba shi da magaji kenan a nan gaba.

Akwana a tashi wata rana sai wani bako ya ziyarci Malam Ishak. Saboda rashin dan sai Malam Ishaka ya rinka yi wa bakon nan hidima da kansa a cikin gida a matsayinsa na magajin gari. Bayan wani lokaci sai malamin nan ya lura da cewa bai ga yara suna Zirga-Zirgan a cikin gidan Malam Ishaka ba, kamar yadda ake yi a sauran gidan masu sarauta. Sai bakon Malamin nan ya ce Wai babu yara a gida nan ne? Sai Malam Ishaka ya ce ai ni Allah bai taba ba ni haihuwa ba. Sai Malamin ya ce Allah Sarki, akwai wata Addu'a wacce idan na yi ta da yardan Allah matarka za ta dauki ciki. Sai Malam Ishaka ya ce To Malam ai sai a taimaka mana, Malami ya ce To za a kokarta a cikin dare da yardar Allah.

Bayan da gari ya waye sai Malam Ishaka ya kawo wa bakon nan abincin karyawa. Bayan da ya gama kalaci sai ya tambayi Malamin nan Malam ko an sami damar yin addu'ar kuwa? Sai Malamin ya ce lallai kam na yi addu'a kuma za ka sami dan da yarda Allah amma kuma abin da aka nuna mani makaho ne Allah zai ba ka A lokacin da ake yi wa Malam Ishaka wannan bushara ta samun dan makaho suna tare da wani abokinsa ne. Sai wannan abokin nasa ya budi ya ce Yallabai me za ka yi da makaho?

Sai Malam Ishaka ya ce Ni a wurina in dai makahon nan mai albarka ne, to na gode wa Allah. Bayan kwana yan kwanaki sai Malamin nan ya koma inda ya fito.

A kwana a tashi ran nan sai matar Malam Ishak Huraira ta sami ciki bayan wata tara sai ta haifi danta namiji sambalele. Koda aka duba sai aka gan shi da idanuwansa guda biyu tangararan. Sai Malam Ishak ya ce Allah da ikonsa Malamin nan ya ce Za a haifi makaho amma ga shi an sami mai gani, Da rana ta kewayo aka rada wa jariri suna Aliyu.

21/05/2020
Allah yajikan Dr Aleeyu namangi allah kaga furta mai kayi masa rahama ka azar ta ziriar shi da soyayyar manzon allah s. ...
24/08/2019

Allah yajikan Dr Aleeyu namangi allah kaga furta mai kayi masa rahama ka azar ta ziriar shi da soyayyar manzon allah s. a.W

Address

Zaria City
Zaria
JAMEEL

Telephone

+2349034057076

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ahlin gidan sheik Aleeyu namangi zaria posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category


Other Magazines in Zaria

Show All