17/03/2022
Abubuwa damutum zai iya yin amfani dashi, domin su saukaka masa kamuwa dasamun raunin alaura daga cikin su sunhada :
1.Farar albas.
Hakika farar albasa tanada taasir sosai wajan magance matsala naraunin alaura, kuma tana magance matsaloli kamar karancin maniyyi, dakuma rashin kaurin sa, da ita dakuma zait lauz halawi.
Tayadda zaayi wannan magani Zaasamo farar albasa kamar kwara 2-3 sai ayayyakata azuba acikin nono ko madara, ko ruwa sai adora akan wuta mara karfi,daga cikin abinda aka hada aka tafasa ko maye akasamu to sai atace sai kuma azuba awani waje sai asha bayan ansha saikuma asha zuma babban cokali, to yana saukaka kamuwa dakuma garkuwa daga samun raunin da namiji.
2.TAFARNUWA, DA KANUN FARI.
Zaasamo tafarnuwa kwara uku kokuma garinta sai ahada da kanin fari dan kadan sai atafasa tare da nono ko madara kamar minti 10 bayan ansauke sai asha shima zaasami biyan bukata insha Allah.
3.LAUZ (NAMIJIN GORO)
Zaa iya samo namijin goro ayi garin sai adumama nono ko madara sai adebi garin cokali daya azuba zaasha kafin kwanciya, akace wannan yana kara shaawa kwarai dagaske.
4.KARAS.
Zaa hada karas da tafarnuwa, ko garinta, sai kuma ahada da shanmmar sai atafasa arika sha sau 2 arana. Kokuma arika sanya karasdin zalla maana ana yayyanka wa asanya aabinci, kokuma ayayyanka sai ahada daruwa atafasa bayan yatafasa sai atace arika shan ruwa.
Kuma idan anacinsa zalla shima yana taimakawa wajan hana samun raunin da namiji, domin riga kafi magani.
5.Ruman.
Idan akasamo ruman ana tafasawa anashan kofi daya to yana maganin samun rauni na mazakuta gada namiji.
6.DANYAN CITTA(ZANJABIL).
Ko asamo danyan citta atafasa, koko ayi garinta sai arika hadawa da kwai 1-2 sai ahada daruwan cittan bayan antafasa sai kuma azuba zuma sai asha wannan gawanda yasami tsananin raunin na alaura akalla zaiyi sati 2-3yanayi zaadace insha Allah.
Amma danyan citta kadai idan ana tafasawa atace azuba zuma ko suga damadara ko madara zalla anasha yana hana kamuwa dasamun raunin mazakuta, gakuma yakar kwayoyin cuta acikin jiki.
7.DABINO.
Idan akasamo dabino anacinsa, ko ayi garinsa arika sanya cokali daya anono ko madara anasha yana hana samun rauni dakuma kara kuzari ga da namiji insha Allah.
Akwai saura wasu hanyoyin 13 zankawo su insha Allah.
Dafatan Allah yasa mudace ameen...