Gaskiya Jari

Gaskiya Jari Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Gaskiya Jari, Media, Gyallesu T/dawa zaria, Zaria.

ABIN TAKAICIMawakin jam'iyyar APC mai mulki wanda kwanannan Uwarsa ta kubuta daga hannun 'yan ta'adda bayan ya biya kudi...
26/07/2024

ABIN TAKAICI

Mawakin jam'iyyar APC mai mulki wanda kwanannan Uwarsa ta kubuta daga hannun 'yan ta'adda bayan ya biya kudin fansa Miliyoyin Naira

To amma duk da haka bai ji ba a jikinsa, gashi nan yana cewa wai butulci ne kawai zaisa dan Arewa ya yiwa Tinubu zanga-zanga

Hakika naji zafin wannan magana da Rarara yayi, bana zagi da tsinuwa, amma yadda zuciyata ke tafasa saboda wannan kalamai nasa na rashin imani, ji nake kamar na dura masa buhun ashar hadi da tsinuwa

Yaa Allah mun kawo karan Rarara gareka, Ya Allah bawanKa ne, Ka jarrabeshi jarraba mai girma Yaa Allah 🙏

DA ƊUMI ƊUMI: An Fitar Da Jadawalin Yadda Zanga-zanga Zai Kasance A Birnin Zariya.Al'Ummar dake yanki kamar Haka: (1)- T...
26/07/2024

DA ƊUMI ƊUMI: An Fitar Da Jadawalin Yadda Zanga-zanga Zai Kasance A Birnin Zariya.

Al'Ummar dake yanki kamar Haka:

(1)- Tsarin fitowarmu Zanga zanga" karfe 6:00Am na safe.

(2)- Alummar yankin
Kofar Doka Ku rufe Titin Jos 60:00am na safe.

(3)- Alummar dake Dan Magaji Ku rufe hanyar zuwa Kano. 6:00am na safe.

(4)- Alummar dake Sabon Gari da Dogarawa Ku rufe hanyar Zuwa Sokoto 60:00am na safe.

(5)- Alummar dake Kofar Kuyanbana da Gwargwaje Ku rufe Hanyar Zuwa Kaduna 6:00 am na safe.

Daga nan zamuje gidan Mai Martaba Sarkin Zazzau da sauransu.

DOKA! DOKA!! DOKA!!!

(1)- Babu mākāmî.
(2)- Babu taba kayan kowa.
(3)- Babu fada ku cin zarafin wani.
(4)- kowa ya fito da rubutu na kokensa a jikin kwali.
(5)- idan da hali kowa yayi shigar farar riga da bakin wanda, ko kuma duk shigar da kaga dama amma shiga mai ma'ana.

Taimako! Taimako!! Taimako!!!

(1)- masu halin cikinmu su dafo abinci.
(2)- wasu su taimako da ruwan sha da kuma magani.
(3)- mu taimaki duk wanda yake bukatar taimako ko wana iri" uwa daya uba daya.

Bamu daukewa kowa ba" daga kan Dan shekara 18 zuwa sama" matasa maza da mata" Dattijai da tsofaffi" kowa ya fito domin ceto kasar mu daga halin da shugabanni s**a jefata na tsananin yinwa da tsaradar rayuwa da kuma rashin tsaro.

ABINDA MUKE BUKATA SHINE,

(1)- A bude bodojin Arewa baki daya domin ashigo da abinci kamar yadda yake a baya da kuma kaiyade masa farashi.

(2)- A dawo da tallafin man Fetir ya dawo 200 duk lita.

(3)- Duk yan kunan dake fama da rashin tsaro a Arewa a dawo da zaman lafiyar yankin domin cigaba da noma da kiyo.

(4)- A dawo da tallafin karatu domin Dan Talaka ya yaki Jahilci.

(5)- A samarwa matasa maza da mata aiyukan dogaro dakai domin gujewar aikata munanan laifuka.

(6)- A dawo da tallafin wutar lantarki, domin karfafar masana'antu manya da kanana

Lokacin fitowa karfe 60:00Am na safe zuwa 60:00Pm na yamma.

Kafin afito kowa ya karanta duk wata addu'a wanda ya iya domin neman taimakon Ubangiji ya bamu ikon fita lfy mu daw

'YAN SIYASA SUNA KARA ZUBAR DA KIMAR RUNDINAR SOJIN NIGERIAJiya Babban Supeta janar na 'yan sandan Nigeria yace zasu baw...
26/07/2024

'YAN SIYASA SUNA KARA ZUBAR DA KIMAR RUNDINAR SOJIN NIGERIA

Jiya Babban Supeta janar na 'yan sandan Nigeria yace zasu bawa masu zanga-zanga kariya matukar ta lumana ce

Yau kuma sanarwa daga Babban Hafshin Sojojin Nigeria yace ba zasu bari masu zanga-zanga su wargaza kasa ba (amma kuma an bari 'yan ta'adda suna cigaba da wargaza mana kasa ai) abin kunya kawai

Abu na farko: Zanga-zanga ba laifi bane a tsarin mulkin Demokaradiyya, kuma ya zama wajibi ga 'yan sanda su bawa masu zanga-zanga kariya kamar yadda yake a doka

Abu na biyu: Rundinar 'yan sandan Nigeria ita ne wanda kundin tsarin mulkin Kasa na Constitution ya daura mata alhakkin kula da harkokin tsaron cikin gida, sai idan lamarin tsaron cikin gida yafi karfinta kafin nan sai Sojoji su kawo mata agaji

Idan an fahimci wannan, to bai kamata rundinar Sojin Nigeria tayi wannan gargadi ga masu shirya zanga-zanga ba domin ba huruminta bane, zanga-zanga civil matter ne, sam bai kamata a shigo da Sojoji ba cikin wannan hayaniya

Yanzu da Sojoji s**a fitar da wannan sanarwa, sai kuma ya kasance masu zanga-zanga sun fito, shin hakan ba zubar da kima da kwarjinin rundinar Sojin Nigeria bane?

Ko da wasa bai kamata rundinar Sojin Nigeria ta bari 'yan siyasa suna rage mata mutunci da daraja ba a idon 'yan kasa saboda biyan bukatun 'yan siyasar, wannan yana kara dagula harkokin tsaron kasa gaba daya

Ita rundinar Sojin Nigeria itace rundina mafi karfi, an samar da ita ne don tayi yaki ta kare Kasa ta sama da kasa da ruwa daga mahara ketare ko kasashen waje, itace last hope a fannin tsaro, shiyasa bai kamata soja yayi mu'amala da fararen hula ba

Kuma bai kamata Soja ya shiga harkokin tsaron cikin gida ba, domin ba akan haka ya samu horon aiki ba, abinda aka horar da Soja shine yayi harbi ya kashe abokin gaba, 'yan sanda kuma aikin su shine su kare rayukan 'yan kasa da dukiyoyinsu, sannan suyi bincike kan masu aikata laifuka

Amma abin takaici yau mun wayi gari miyagun 'yan siyasa sun lalata mana rundinar Sojin Nigeria,

DA ƊUMI ƊUMI: Mahukunta Ƙasar Chadi sun yi shelan kāryā farashin aure a ƙasar, inda s**a nema da al'umma daga maƙwafta d...
25/07/2024

DA ƊUMI ƊUMI: Mahukunta Ƙasar Chadi sun yi shelan kāryā farashin aure a ƙasar, inda s**a nema da al'umma daga maƙwafta dasu su shigo su aura ƴan matansu.

25/07/2024

Irin halin da mutanan G@za ke ciki kenan, Amma maki¥a addinin mu$lumci basu so a y@da. Ya Allah muna tawassali da kyawawan sunayen ka muna Kuma tawassali da annabi Muhammad (S A W) Allah ka Kai musu dauki.

Ayi following din mu Dan kawo muku
Labarai na gaskiya.

25/07/2024

Something that you'll not see in newspaper or social medias

An rantsar da Janar Brice Nguema a matsayin shugaban mulkin soji a ƙasar Gabon.Hakan na zuwa ne bayan ya hamɓarar da gwa...
04/09/2023

An rantsar da Janar Brice Nguema a matsayin shugaban mulkin soji a ƙasar Gabon.

Hakan na zuwa ne bayan ya hamɓarar da gwamnatin Ali Bongo a makon da ya gabata bisa zargin rashin cika sharuɗɗan zaben shugaban kasar da aka yi.

Address

Gyallesu T/dawa Zaria
Zaria

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Gaskiya Jari posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share

Category

Nearby media companies


Other Media in Zaria

Show All