15/06/2024
Labaran Yammacin Asabar 09/12/1445AH - 15/06/2024CE Ga Takaitattun Labaran.
Shugaba Tinubu ya bukaci babban daraktan hukumar sa ido a harkokin saye saye na gwamnati, BPP, Mamman Ahmadu ya yi murabus.
Rundunar Sojoji Kasa ta yaye sabbin sojoji 5,937 daga makarantar horas da kuratan sojoji da ke zariya a yau Asabar.
NDLEA reshen Jihar Kano ta ce ta k**a kwayoyin Tramadol guda 230,600 da kuma wasu mutane 106 da ake zargi da hannu a fataucinsu a jihar Kano.
Rundunar 'yan sanda za ta sake nazarin sunayen sabbin 'yan sanda da za a ɗauka aiki.
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya zargi gwamnatin Ganduje da raba kan gidan dabo.
Hukumar Kula da 'yan Najeriya mazauna ƙetare NIDCOM, ta ce an mayar da 'yan matan ƙasar kimanin 10 da aka yi safararsu zuwa Ghana.
Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero ya bayyana cewa ya hakura da hawan Sallah ne dan a samu zaman lafiya a fadin jihar.
Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya aike da saƙon fatan alheri ga Shugaba Tinubu da Gwamna Abba Kabir Yusuf, sak**akon bikin babbar sallah.
Gwamnan jihar Zamfara ya fadawa alkalai yadda ake hada-kai da kotu ana sakin ‘yan bindiga.
Duk da halin rashin tsaro a Najeriya, aƙalla sojoji 197 ne zasu tafi domin wanzar da zaman lafiya a kasar Gambia.
Kocin Super Eagles Finidi George ya yi murabus daga mukaminsa bayan rashin katabus a kungiyar.
An k**a wasu mutum sama da 100 da ake zargin sun shigo Saudiyya ba tare da izinin gwamnati ba.
Hukumomi a ƙasar Saudiyya sun bayyana cewa aƙalla maniyyata miliyan 1,833,164 ne s**a halarci aikin Hajjin 2024.
Alƙalin Alƙalan Kenya ya ce alƙaliyar da ɗan sanda ya harba a lokacin da take tsaka da jagorantar shari'a a mutu a asibiti.
Dakarun rundunar sojin Sudan sun kashe kwamandan RSF a al-Fasher.
Kotu a Jamhuriyar Benin ta jefa ƴan Nijar 3 da ta k**a kurkuku.
An sake zaɓar Ramaphosa a matsayin shugaban Afirka ta Kudu.
An buɗe taron zaman lafiyar Ukraine a Switzerland ba tare da wakilcin Rasha ba.
Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta sanar da mutuwar tsohon dan wasanta, Kevin Campbell bayan fama da jinya.
Euro: Switzerland ta sami nasara akan Hungry da ci 3:1 a wasan yau.