05/12/2023
NIKO TESLA DAN BAIWA A BANGAREN FASAHA.
A ranar 7, January 1948 mai shekaru 86, Nikola Tesla ya mutu a dakin hotel dinsa na New York city. Tesla ya mutu ne a matsayin talaka kuma shi kadai, yana daya daga cikin muhimman mutanen da tarihin su ba zai goge a duniyar fasaha.
Nikola Tesla mutum ne da a kullum burinsa samar da abin da zai taimaka rayuwar mutane, dan baiwa ne shi da ba'a kara yin k**ar sa ba, haka zalika mawaki ne shi akan abubuwan da s**a shafi kimiyya, masanin lissafi, kwararren mai hasashen gaba, masanin kimiyyar physics haka zalika masanin yaruka har guda takwas da ya ke magana da su tamkar yaren sa na farko yarensa na Serbia da Croatia, English, Czech, French, German, Hungarian da kuma Latin, haka zalika mutum ne da ya ke da kyakkyawan hadda, don ya kan iya karanto littafin kimiyya, formulas, da wakoki duk da ha haddace batare da littafin a hannunsa ba.
Kafin mutuwar sa ya kirkiri abubuwa da dama fiye da kowanne dan Adam da ya taba Rayuwa a duniyar, Tesla induction motor, Tesla rotary converter, Tesla Phase system of power transmission, transformer, Steam and gas turbine, Tesla coil wato fasahar da ta ke rarraba Wutar lantarki wirelessly, da wasun su da dama na daya daga cikin abubuwan da ya kirkira,a bangaren fasaha da sauran bangarorin kimiyya don kuwa a kowanne bangare za ka iya samun kirkire-kirkiren Nikola duka a kokarin sa na saukakewa mutane rayuwar su.
Kari akan haka, Tesla induction motor a wannan lokaci daya ne daga cikin abubuwan da 90% na rayuwar mu ta ta'allaqa da shi, inda mu ke amfani da shi a kusan komai da komai na rayuwar mu, duk wasu kamfanunuwan da suke samar da wutar lantarki su na amfani ne da fasahar Nikola Tesla da kuma Fasahar da ya samar na tsarin rarraba wutar lantarkin.
Burin sa da mafarkinsa har ya mutu shine mayar da duk wasu abubuwan da ya kirkira zuwa Abu guda daya, wanda ya Kira wannan aikin da World Wireless System a manufar sa ta samar da wutar lantarki a duka fadin duniya komai nisan wuri batare da amfani da wata waya ba k**ar yadda har yanzu a ke yi, wanda hakan zai saukakawa mutane wajen samun wutar lantarkin cikin sauki, kuma da matukar karfi.
Amma duk da haka an dauki lokaci mai tsayi bayan rayuwar sa kafin tasirinsa da aikace-aikacensa su watsu a cikin duniya kowa ya sani, a karni na ashirin har an fi girmama Einstein da karrama shi akan Nikola Tesla.A cikin littafin The 48 laws of power, marubucin ya rawaito yadda aka yaudare shi, inda da farko yana aiki a kamfanin Edison da ke kasar Serbia wato kasar sa ta haihuwa, sai manager na kamfanin ya tura shi babban reshen kamfanin domin ya yi wani aiki, tare da alkawarin cewa idan ya yi aikin za'a biya sa wasu miliyoyin kudade na dalar amurka tun a wancan lokacin, sai dai bayan ya kammala sai aka ki bashi, ba don Kudi ya ke yi ba, don haka ya dakatar da aiki a wurin kuma ya cigaba da ayyukan sa, bayan wannan lokaci ne kuma ya gano abin da yanzu ake kira Wutar lantarki, A shekarar 1893 kamfanin GE ya saci blueprints na aikin nasa wanda Edison yana cikin su. Abu mafi muhimmanci game da Tesla shine ya sadaukar da rayuwar sa ne gaba daya wajen kirkirar abubuwan da s**a wuce lissafowa, wanda a wannan lokaci wadannan abubuwan duka wani bangare ne na rayuwar mu a yanzu, da ace za'a dauke abubuwan da Nikola Tesla ya kirkira da za ka samu cewa sai komai ya dakata a wannan duniya, shine ya gano wutar lantarki da tsarin da ake rarraba ta har zuwa wannan lokaci, AC, injin tafiyar lokaci, Tesla wave, wireless connection da mu ke amfani da shi wajen kira, bayan wadannan ya kirkiri abubuwa da dama, sannan ya hasaso wasu abubuwa da dama da ya so kirkira, sai dai rashin kayan aiki, da kuma kudi ya sanya bai kai ga cimma nasara ba, wasu kuma su ka ce lokacin kimiyyar nan bai zo ba da Tesla ya samu nasara.
Wannan kadan ne a cikin tarihin Nikola Tesla, zan cigaba da kawo muku wasu muhimman bayanai game da Abubuwan da ya kirkira, maganganunsa, abun da aka ce a kansa da sauran su, kai dai ka yi following wannan shafin, kuma ka gayyato abokanka su yi following, haka zalika ka yi sharing don wasu su amfana!
.