Angon Dubu

Angon Dubu Newspaper

18/12/2022

Da 'dumi'dumi:

Muhuyi Magaji Tsohon shugaban hukumar Yaki da rashawa na Jihar Kano Ya sanya Jar-hula Mai nuni da Tafiyar Kwankwasiyya bisa jagorancin Engr Sanata Rabi'u musa Kwankwaso.

Barista Muhuyi Magaji ya rubuta a shafinsa na Facebook Yana Mai cewa Barkanku da safiya 'yan gidan Daraja.

Me Zaku ce?

MUTUWA MAI YANKAN KAUNA ALLAH YAJIKANKA MALAM MUTUWA TA RABAMU DA MASOYINMU MUNA ADDU'AR ALLAH YAJIKANSA KUN HADA BAKI T...
15/12/2022

MUTUWA MAI YANKAN KAUNA ALLAH YAJIKANKA MALAM

MUTUWA TA RABAMU DA MASOYINMU MUNA ADDU'AR ALLAH YAJIKANSA

KUN HADA BAKI TARE DA SAKA WASU MUTANE SU KASHE SHEIKH JA'AFAR MAHMUD ADAM ATINANINKU KU BAZAKU MUTUBA

LALLE HAUSAWA SUNYI GADKIYA DA S**ACE KARSHEN ALEWA KASA TA MALAM JA'AFAR TAYI KYAU

KAI DAKA CE ZAKUYIWA JAFARU KISA IRIN NA TSAKA GA IRIN NAKA KARSHEN NAN

ALLAH YARABU DA SAN ZUCIYA

15/12/2022

HUKUNCIN ABDULJABBAR:

An yanke wa Abduljabbar hukuncin kisa ta hanyar rataya.

An kwance littattafansa da ya gabatar. Zaa kai littattafan State Library.

Anyi umarnin gwamnatin Kano ta gaggauta kwace masallatan Abduljabbar.

An haramta sanya karatuttukansa da hotunansa a Rediyoyi, Talabijin, Da Shafukan Sadarwa.

Awaisu Al'arabee Fagge
Jibwis Social Media
Kano State.

The family ofAlh. Sabitu usaini direba                 And that ofLate Mal. Yusuf yahaya karefaSuna GAYYATAR Yan uwa da ...
15/12/2022

The family of

Alh. Sabitu usaini direba
And that of
Late Mal. Yusuf yahaya karefa

Suna GAYYATAR Yan uwa da abokan arzuka zuwa wajan DAURIN AUREN yayansu

Rchp Mukhatar sabitu usaini (captain or scientist)
&
Fa'iza Yusuf yahaya

Wanda zaayi kamar haka
20-dec-2022
Wajen haduwa tudun wada yayande road
Wajen daura aure karefa kofar gidan sarkin karefa

A iso lafiya

15/12/2022

"Bana neman afuwar ka, kai Ibrahim Sarki Yola, a wajan Allah nake neman sassauci, kuma ina bawa Almajiraina hakuri zanje Lahira a madaukaki."

Kalaman Shekh Abduljabar Nasir Kabara kenan yau a kotu, bayan lauyansa ya nema masa sassauci.

15/12/2022

Ba da yawuna Lauyana ya nemi a yi min sassauci ba - Sheikh Abduljabbar Kabara

Kai tsaye daga Kotun Ƙofar Kudu.

Kotu ta ce, ta samu Abduljabbar Kabara da laifin yiwa ma'aiki (s a.w) kage da cin mutumcin ma aiki da cewar yayi fyade ,
An same shi da laifi karkashin sashe na 382 (B)

Lauyan da ke kare shi Barrister Aminu Abubakar yace ayi masa sassauci saboda kuskuren fahimta ce tasa Malam Abduljabbar ya aikata wannan laifi.

Amma nan take malamin ya miƙe ya ce shi dai ba da yawunsa ba, Lauyana yake magana.

Malamin ya ce, baya neman sassauci, kuma yana neman a gaggauta yi masa hukunci domin zai yi mutuwa ta girma.

Ku ci gaba da bibiya, zamu ci gaba da kawo muku yadda take kasancewa.

Shari'ar Abduljabbar

Sashishiyar maganaAisha Buhari ta janye karar da ta kai Aminu Muhammad, lawyansa C.K. Agu ya shaida wa BBC.
02/12/2022

Sashishiyar magana

Aisha Buhari ta janye karar da ta kai Aminu Muhammad, lawyansa C.K. Agu ya shaida wa BBC.

SHIN KO INA AKA KWANA GAME DA BATUN Piπ NETWORK
25/11/2022

SHIN KO INA AKA KWANA GAME DA BATUN Piπ NETWORK

25/11/2022

Alhamdulillah bayan wasu kwanaki da haking account Dina yau nadamu nasarar dawo dashi Alhamdulillah

12/11/2022

MY CHOICE

PRESIDENT:- ASUWAJU (A.P.C)

GOVERNOR:- SHA'ABAN SHARADA (A.D.P)

HOUSE OF REPS :- RT HON ALASSAN ADO DOGUWA (A.P.C)

SENATOR KANO SOUTH:- KAWU SUMAILA (N.N.P.P)

HOUSE OF ASSEMBLY:- SULE SHUWAKI (A.P.C)

RA'AYINA KAI FA KEFA????

10/11/2022

ABINDA YA HANA NI AURE HAR YANZU! 🙆‍♂️

Farar mace bata taba burgeni ba, kuma gaskiyar magana bazan iya auren bakar mace ba, bazan iya auren mace me kiba ba, kamar yanda ko da wasa zuciyata ba zata iya son siririya ba,

Doguwar mace ta fita daga lissafin yan matan da nake mafarki, gajera kuwa tsakanina da ita saidai fatan alkairi, yan matan da aka haifa a 2004/2005/2006 yarinta tana damunsu, waɗanda s**a haura shekarunsu kuma sun fita daga tsarin lissafina,

Amma idan kuma akwai wacce take ganin zata iya jaraba rayuwa dani to saitazo mu gwada

Kotu ta yanke wa su Mubarak Pikin hukuncin bulala ashirin, da tarar dubu ashirin, da sharar kotu na wata gudahttps://nas...
07/11/2022

Kotu ta yanke wa su Mubarak Pikin hukuncin bulala ashirin, da tarar dubu ashirin, da sharar kotu na wata guda

https://nasararadio.com/kotu-ta-yanke-wa-su-mubarak-pikin-hukuncin-bulala-ashirin/

Home Uncategorized Kotu ta yanke wa su Mubarak Pikin hukuncin bulala ashirin Uncategorized Kotu ta yanke wa su Mubarak Pikin hukuncin bulala ashirin By Abubakar Lecturer - November 7, 2022 0 54 Facebook Twitter Pinterest WhatsApp Wata kotun majistare a jihar Kano ta yi wa wasu matasa masu wallafa ho...

Dubban mutane ne s**a fito domin zanga-zanga a birnin Accra Ghana inda suke kira ga shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankw...
06/11/2022

Dubban mutane ne s**a fito domin zanga-zanga a birnin Accra Ghana inda suke kira ga shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akofo da ya sauka ko su tsige shi, saboda gazawar gwamnati wajen farfado da tattalin arziki da hauhawan farashin kayayyaki da kuma faduwar darajar “Cedi” wato kudin kasar.

An Cire Kwamishinan ’Yan Sandan Kano Kan Zargin Rashawa.Wata biyu kacal da nada Abubakar Lawal a matsayin Kwamishinan ’Y...
06/11/2022

An Cire Kwamishinan ’Yan Sandan Kano Kan Zargin Rashawa.

Wata biyu kacal da nada Abubakar Lawal a matsayin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, an cire shi kan zargin rashawa.

Shugaban ’Yan Sandan Najeriya Usman Baba, ya mayar da Abubakar Lawal Jihar Ebonyi, bayan samun sa da laifin; nan take aka maye gurbinsa da takwaransa na Ebonyi, Aliyu Garba.

Wata majiya mai tushe ta shaida wa Aminiya cewa akwai zargi kan CP Lawal cewa tura shi Kano a watan Agusta ke da wuya, “Sai ya dauke duk wasu bincike da ke alamar tsoka zuwa ofishinsa.

“Sannan ya sanya harajin mako-mako ga duk muhimman sassan da manyan ofisoshin ’yan sanda ke karkashin rundunar — abin da ya fusta shugaban ’Yan Sandan Najeriya.”

Aminiya ta samu rahoto cewa mataimakan Kwamishinan ’Yan Sanda da aka sauya wa wurin aiki ne s**a aike wa shugaban ’yan sanda rahoton rashawar da ke gudana a karkashin sabon kwamishinan.

Bayan nan ne Hedikwatar ’Yan Sanda ta Najeriya ta sa a yo binciken kwakwaf a sirrance, wanda a karshe ya tabbatar da zargin da ake wa sabon kwamishinan.

Wata majiya mai tushe ta ce Shugaban ’Yan Sandan da kansa ya zauna da wasu daga cikin masu zargin, a lokacin binciken, da nufin gano gaskiya.

A watan Agusta ne dai aka tura CP Abubakar Lawal zuwa Jihar Kano, bayan magabacinsa, ya yi ritaya daga aiki.

Wakilinmu ya nemi karin bayani kan lamarin daga kakakin ’yan sandan Najeriya, Muyiwa Adejobi, amma ya ce ba shi da masaniya.

Amma mun samu gabin wani sako da Hedikwatar ’Yan Sanda ta aike a ranar Juma’a mai lamba, TH.5361/FS/FHQ/ABJ/V.T3/87, cewa sauyin wurin aikin ya fara aiki ne nan take.
A halin da ake ciki ranar Litinin sabon kwamishin da aka tura Kano, Aliyu Garba, zai fara shiga ofis.

Sabon Kwamishinan ’yan sandan Kano, a baya ya kasance Mataimakin Kwamishina mai kula da Walwala, Kudade da Gudanarwa a Hedikwatar Rundunar da ke Abuja

Liberty Redio

Canja fasalin Naira: Mu na fakon gwamnoni 3 bisa badaƙalar maƙudan nairori - EFCCHukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da r...
06/11/2022

Canja fasalin Naira: Mu na fakon gwamnoni 3 bisa badaƙalar maƙudan nairori - EFCC

Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta ce tana sa ido kan gwamnonin ƙasar uku sakamakon yunƙurinsu na halasta kuɗin haram da biliyoyin kuɗin da s**a tara ta hanyar biyan ma'aikata albashi a hannu - maimakon ta banki.

Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa ya faɗa wa jaridar Daily Trust cewa dakarunsa za su ci gaba da kai samame kan 'yan canji game da zargin ɓoye dalar Amurka wanda hakan ke sa darajarta na hauhawa.

Duk da cewa Bawa bai faɗi sunan gwamnonin ba, ya ce biyu daga cikinsu daga arewacin Najeriya suke, inda ɗayan yake a kudanci.

Ya ce bayanan sirri da s**a samu sun nuna cewa gwamnonin sun kammala shirin fito da kuɗin ta hanyar biyan ma'aikatansu na jiha da garin kuɗi maimakon ta banki kamar yadda aka saba.

"Bari ku ji, a rahoton sirri da na samu jiya...tuni wasu gwamnonin jiha da s**a ɓoye garin kuɗi a gidaje yanzu s**a fara ƙoƙarin biyan albashi a hannu a jihohin nasu," in ji shi. .

Da aka tambaye shi ko EFCC za ta yi wa gwamnonin sammaci, Bawa ya ce suna dai saka musu ido zuwa yanzu.

EFCC na ɗaukar matakan ne a baya-bayan nan bayan Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da shirin sake fasalin takardun naira na N200 da N500 da N1,000, inda ya ba da wa'adin kwana 47 ga 'yan ƙasar da su kai tsofaffin banki.

Wasu masana na ganin cewa hakan na da nasaba da ƙarin karyewar darajar nairar. CBN ya ce za a fara amfani da sabbin takardun kuɗin daga ranar 15 ga watan Disamban 2022.

📷 Liberty Redio

A.P.CP.D.PN.N.P.PA.D.PP.R.PL.PKARON FARKON DA MANYAN JAM'IYYU A WANNAN JAHA S**A FITAR DA YAN TAKARAR GOBNA DUKA A KWARY...
06/11/2022

A.P.C
P.D.P
N.N.P.P
A.D.P
P.R.P
L.P

KARON FARKON DA MANYAN JAM'IYYU A WANNAN JAHA S**A FITAR DA YAN TAKARAR GOBNA DUKA A KWARYAR CIKIN BIRNI.

A 2019 IDAN BAMU MANTA BA KWANKWASO YAYI AMFANI TARE DA NUNAWA JAMA'AR KANO CEWA GA ABBA DAN KUNE KUMA DAN CIKIN GARIN KANONE HAR YAYI IKIRARIN CEWA ANDADE BA'A SAMU WANI DAN TAKARA DAYA FUTO DAGA CIKIN KWARYAR BIRNI BA.

AWANNAN LOKACI WADANCAN KALAMAI DA TSOHON SANATAN YAYI ZASUYI TASIRI GA KANAWA KUWA? DUBA DA JAM'IYYUN SIYASAR JAHAR DUKA SUNFITAR DA YAN TAKARKARUNSU A CIKIN BIRNI.

YAKUKE GANIN ZATA KASANCE????

05/11/2022

BALAIFI BANE KA HADA GAJERUN MATA GUDA BIYU KAYI SOYAYYA DASU A MATSAYIN DOGUWAR MACE

Mata Kenan....Tana kwance akan shimfiɗar ajali ta ce, Habibina in na mutu zuwa yaushe zaka sake wani auren?Yana kuka ya ...
30/10/2022

Mata Kenan....

Tana kwance akan shimfiɗar ajali ta ce, Habibina in na mutu zuwa yaushe zaka sake wani auren?

Yana kuka ya ce, zuwa lokacin da ƙasar kabarinki zata bushe. Ta yi murmushi ta ce, ka yi alƙawari? Ya ce, ƙwarai ma kuwa.

Bayan ta rasu sai da ya shafe fiye da shekaru 5 ya na zuwa maƙabarta amma abin mamaki kabarin bai bushe ba.

Allahu Akbar, ya yi mamaki sosai kuma ya ƙudurce a ransa matarsa Waliyyiya ce.

Wata rana ya yi sammako don ziyarar kabarinta, sai ya ci karo da ɗan uwanta, s**a gaisa. Ya ce kazo ziyarar ƴar uwarka ke nan?

Sai ya ce na dai zo don cika wasiyyar da ta mutu ta bar mini. Ta yi mini wasiyyar kullum da sassafe nazo na jiƙa ƙasar kabarinta, hakan zai sanya ta kwanta cikin nutsuwa, shekara da shekaru kenan ina wannan aikin.🙆🏽‍♂️
Wani aikin sai mata...😁

mikiya

Tsohon Shugaban Kasa GoodLuck JONATHAN, yakai Ziyara Mahaifarsa ta Otuoke dake Bayelsa dan Jajantawa wadanda Iftila'in A...
28/10/2022

Tsohon Shugaban Kasa GoodLuck JONATHAN, yakai Ziyara Mahaifarsa ta Otuoke dake Bayelsa dan Jajantawa wadanda Iftila'in Ambaliyar Ruwa ya shafa.

📸 Goodluck Jonathan

CBN AIKIN HANKALI/AIKIN RASHIN TUNANI.AIKIN HANKALI: A Shekarar 2014 Zamanin Jonathan Gudluck a Lokacin Da Najeriya Ta C...
28/10/2022

CBN AIKIN HANKALI/AIKIN RASHIN TUNANI.

AIKIN HANKALI: A Shekarar 2014 Zamanin Jonathan Gudluck a Lokacin Da Najeriya Ta Cika Shekaru 100 Na Hade Kasar Tsakanin Kudu Da Arewa (Amalgamation) Gwamnati Ta Canja Fasalin Naira 100, Inda Ta fito da sabbi, Babban Bankin Najeriya Yace Za'a ci gaba da kashe Sabon Kudin Da Tsohon Kudin A Lokaci Guda Har Tsoffin Su Bace.

AIKIN HANKALI: Hakama A kayi a Shekarar 2010 Duka Dai a Zamanin Gudluck, A Lokacin Bikin Cikar Najeriya Shekaru 50 Da Samun Yanci Kan Najeriya, Babban Bankin Najeriya (CBN) Yayi Sauye-sauye A Takardar Kudi Ta Naira Hamsim, Hakanan (CBN) Yace Za'a Ci Gaba Da Kashe Tsohuwar Takardar Kudin Da Sabuwar Har Tsohuwar Takardar Naira 50 Din Ta Bace, Ma'ana Idan Ta Shiga Banki Bazata Sake Fitowa Ba.

AIKIN RASHI TUNANI: A Yanzu CBN ya ba da wa’adin kwana 47 a mai da tsoffin kudin da za a sauya banki. Wannan Canji Koda Yana Da Kyau Wadannan Kwanaki Sunyi Mutukar Kadan.

Haka Ya Faru A Lokacin Mulkin Soja Na Janar Muhammadu Buhari A Watan Fabrairu 1984, Babban Bankin Najeriya Ya Bayar Da Umarnin Sauya Kudin Na Naira A Sati Biyu Rak, Sannan Najeriya Nada Yawan Jama'a ( 81.45 million) Kawai A Yanzu Kuwa Najeriya Nada Yawan mutane (217,947,709).

A Lokacin Kudin Takardun Naira Ya Soma Daga Sulai Biyar TaTakarda Zuwa Naira 20, A Zamanin Mutane Sun Mutukar Shan Bakar Walaha Wasu kuwa Karyewar Arzikin su Kenan Har Abada.

Kamata Yayi Babban Bankin Najeriya (CBN) Ya Kara dogon Lokaci Tare Da Umarnin Karbar Sabon Kudin da Tsohon A Lokaci Guda, Kamar Yadda Yayi 2010/2014 Domin Kauce Wahallahalu Da Jama'a Ka Iya Fuskanta.

Hakika Duk Wanda Yasan Abinda Ya Faru A Watan Fabrairun 1984 Ko Yake Da Tarihin Abinda Ya Afku, Bazai Samu Natsuwa Da Wannan Canjin Kudin da Bayar da Wannan Takaitaccen Wa'adin Ba.

Saliadeen Sicey ✍️

Ko Yanzu Akan Talaka Zata Ƙare.!Daga Yusuf A-y KuryaMaganar sauya fasalin Kuɗi ba'a yiwa talaka adalci ba domin ko abaya...
28/10/2022

Ko Yanzu Akan Talaka Zata Ƙare.!

Daga Yusuf A-y Kurya

Maganar sauya fasalin Kuɗi ba'a yiwa talaka adalci ba domin ko abaya da kayi wannan sauyi,
kabar kakanninmu da tulin kuɗi a buhu wanda yazama silan talaucewar iyayen mu awannan lokacin.

Baba Buhari maigaskiya ka yiwa Allah da Annabi ka dakatar da wannan kudiri naka.

Saboda akan talaka abun nan zai kare

Sha'aban Sharaɗa ya ce, ko yau aka saka zaɓe a mazaɓar Abba Gida-gida to tabbas zai tiƙa shi da ƙasa.Meye ra'ayinku a ka...
28/10/2022

Sha'aban Sharaɗa ya ce, ko yau aka saka zaɓe a mazaɓar Abba Gida-gida to tabbas zai tiƙa shi da ƙasa.
Meye ra'ayinku a kai?

Batun Canza Fasalin Takardun Kuɗin NijeriyaDAGA Datti AssalafiyJiya Gwamnan Babban Bankin Nigeria ya fitar sanarwa cewa ...
27/10/2022

Batun Canza Fasalin Takardun Kuɗin Nijeriya

DAGA Datti Assalafiy

Jiya Gwamnan Babban Bankin Nigeria ya fitar sanarwa cewa zai canza launi da fasalin kudin Nigeria domin kudin sunyi yawa kuma a sake tsaftace kudin da ga na 'yan damfara wadanda suke buga jebu, a cewarsa.

Wani bawan Allah ya ce; duk wannan rubutun harafin Larabci 'Ajami' shine ya tsole musu ido, anyi nasaran cirewa a ₦5, ₦10, ₦20, ₦50 da ₦100; shiyasa yanzu suke son su sake cirewa.

Takardun kudaden Naira da canjin zai shafe sun hada da takardan Naira ₦200, ₦500 da Nair ₦1,000 sune 'notes' da s**a rage, masu rubutun 'Ajami' harafin Larabci na Musulunci a jikinsu, idan sun samu nasaran cire wannan a watan December yanzu sauran "نصر من الله" na jikin bajin sojojin Nigeria ya saura.

Kafin zuwan Turawa, yankin Hausawa, Musulmai, da 'script' na 'Larabci' suke amfani wajen rubuce-rubuce don isar da sako, wannan dalili ya sa aka rubuta ajami a jikin takaran kudin ₦aira.

Larabci harshe ne, eh! Kuma shi ne 'official language' na addinin Musulunci; amma ba shi ke nuna Musulunci ba, don akwai Larabawa da ba Musulmai.

Idan ba'a manta ba, watannin baya kadan wani Lauya Mikiyin Musulunci ya shigar da kara Kotu domin a cire harafin Larabci daga jikin takardun kudin Nigeria saboda kyamar da yake yiwa Musulunci.

Shi kuma Malam Adam Baba Yamani cewa yayi:

Haka gomnatin Buhari ta 1984 ta yaudari al'ummah ta chanza Naira cikin sati biyu, wanda hakan ya janyo hasarar dukiya ga wadanda ba su samu chanza kudaden da ke hannunsu ba, Naira ta rasa karbuwa da yawa a duniya kamar Dollar, kafin Buhari ya chanza Naira a 1984, Naira ta na yawo a ko ina cikin duniya, amma yana chanza ta, sai ta rasa karbuwa da kima.

An zo yanzu kuma a 2022 ya dawo ya sake chanza Naira domin ya kara nakasata, da ma kuma akwai aniyar karya darajar Naira zuwa 1000 ga Dollar America, yanzu za a tabbatar da wannan kudirin IMF akan 'yan Nigeria, duk wannan hauragiyar don a dafa masa ya gama mulki lafiya, shi bai damu da halin da Kasa da al'ummar

Turawa daga kasar Jamus sun mini Alkawarin Kudi har Naira Miliyan Dari da Talatin da biyu (132M) Amma naki amincewa da b...
27/10/2022

Turawa daga kasar Jamus sun mini Alkawarin Kudi har Naira Miliyan Dari da Talatin da biyu (132M) Amma naki amincewa da basu fasaha ta.

Nace idan har suna son na basu fasahar, sai sun dauki 'ya'yana Aiki Kuma Abasu Mukami a kamfanin, Sannan Adinga Cirewa Iyalansa Wani Shiya A kamfanin Kafun na yarda naje Kasar Jamus na basu Wannan Ilimin.

Malam Hadi kenan dattijon da ya kera Abun dafa Abinci Na zamani Mai Amfani da Ruwa, ba Gas ba.

Rohoton Madubi.

Islam is all about focus and dedicated. It's better for you as a Muslim to know what's good and what's bad in your five(...
27/10/2022

Islam is all about focus and dedicated. It's better for you as a Muslim to know what's good and what's bad in your five(5) daily prayer.

Prophet Muhammad [PBUH] He said that the first thing you'll be questioned on the day of judgment is Salah. If it's good you'll Winn, if it's not good you are in trouble.

May Allah help us and answer our five daily Salat, protect us from the torments of the grave.

May we collect our books with right hand side. Amin 😢🤲
...✍︎ 𝑈𝑧𝑎𝑖𝑟𝑢 𝐻𝑎𝑙𝑖𝑑𝑢 𝐽𝑎𝑛𝑖

Da idan Baba zai fita gaisuwa yake yi mana da jinjina. Amma yanzu in zai fita daƙuwa yake yi mana.Rawahul Bilbisy, Lawal...
27/10/2022

Da idan Baba zai fita gaisuwa yake yi mana da jinjina. Amma yanzu in zai fita daƙuwa yake yi mana.

Rawahul Bilbisy, Lawal Mamman

Amma fa ruwaya nayi da ma'ana ba da lafazi ba.

GASHIN FIYAYYEN HALLITA MANZON TSIRA ANNABIN RAHAMA.Kamar yadda aka Saba duk Shekara a  yammacin jiya Laraba Sheikh Kari...
27/10/2022

GASHIN FIYAYYEN HALLITA MANZON TSIRA ANNABIN RAHAMA.

Kamar yadda aka Saba duk Shekara a yammacin jiya Laraba Sheikh Karibullah Sheikh Nasir Kabara ya fito da gashi na Annabi Muhammad (SAW) Wanda ya nunawa alumma Kuma ya fadi Tarihin yadda ya gaji wannan gashin da Kuma falalarshi ga alumma Masoya Manzon Allah.

Kamar yadda Abdulwahab Said Ahmad ya wallafa yace zaman akanyi shi duk Shekara a gidan Kadiriyya.

📸

'Dan Asalin Kasar China nan Geng Quanrong da aka zarge shi da kisan Ummakulsum Sani Buhari a Jahar Kano bayan caccaka ma...
27/10/2022

'Dan Asalin Kasar China nan Geng Quanrong da aka zarge shi da kisan Ummakulsum Sani Buhari a Jahar Kano bayan caccaka mata wuka ya musanta zargin da ake masa a gaban Kotu.

Wannan na zuwa ne bayan da aka karanta masa Kunshin tuhumar da ake masa.

DA DUMI-DUMI: Nayi nadamar duka karuwancin da nayi a baya -Inji Muneerat AbdulsalamGa abinda ta rubuta a shafinta na Fac...
25/10/2022

DA DUMI-DUMI: Nayi nadamar duka karuwancin da nayi a baya -Inji Muneerat Abdulsalam

Ga abinda ta rubuta a shafinta na Facebook

"Oh ni Muneerat Abdulsalam haka ratuwata ta koma? Ko kudin sayan paracetamol bani dashi kuma ba mai bani, na zama abin kwatance a idon duniya, gani ga wane ya ishi wanne tsoron Allah, nayi nadaman duka karuwancinda nayi daga baya, da duka shashanci, da barikanci, wannan ai shi ake cewa hisabi tun baka mutu ba,

Toh kar ku kuskura ku sawa yaranku suna Munira, kuma inaso ku maidani abin kwatance ga yaranku da jikoki, ina cikin nadamar rayuwar danayi daga baya, Allah ka yafemin.

Address

Saban Gari
Tudun Wada
ABDULMAALIK

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Angon Dubu posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Angon Dubu:

Share


Other Media/News Companies in Tudun Wada

Show All