23/08/2021
بسم الله الرحمن الرحيم
🏴🏴🏴🏴🏴
HAR YANZU A HANA SHEIK ZAKZAKY FITA NEMAN MAGANI !?
Yau Lahadi 13 ga Al-Muharram 1443 (22/8/2021) Kwana 25 da Fitan Jagora Sheik Ibraheem Zakzaky(h) da matar sa Malama Zeenatu daga Kurkuku Azzalumai ! Amma Gwamnatin Buhari sun hana Malam(h)da Matarsa fita waje neman magani kamar yadda shi Shugaban kasa yake fita don neman magani na ciwon da yake damun shi! Wannan wani irin zalinci ne ? Ku kufita neman magani amma kuma ku hana shi fita bayan kun raunata su da harbi! harsasai na jikin su! kun tsare su na kusan shekara 6 suna ta fama da lalurori daban daban na rashin lafiya amma kuma ku hana su fita naman magani ! Ku kuma kuna fita! Ashe wannan ba tauye hakkin dan kasa bane ?!Wannan ba zalinci bane ?!
Bamu manta da irin kisan kiyashi da Gwamnatin Buhari da Gwamnan kaduna su kayi ba fa! Don bamu yafe ba kuma baza mu yafe ba !! Muna kara rokon Allah Ta'ala da yabi mana hakkin mu !
A ba wa Malam(h) da mai dakin sa pasport din su don su fita neman magani !
- A sako mana Sauran yan'uwan mu da suke hanun Gwamnati !
- A bamu gawarwarkin yan'uwan mu da Gwamnati ta kashe !!
Allah ya kara wasu Malam Ibraheem Zakzaky Lafiya da kariya ya tabbatar masa da muradin sa na ganin alumma sun komo kan tafarkin gaskiya da adalci.
Allah ya daukaki Gaskiya da Ma'abota Gaskiya a duk inda suke.
Godiya ga Allah mara iyaka ! Alhamdu Lillah.
🏴🏴🏴🏴🏴