Muryar Al'ummar Zone C

Muryar Al'ummar Zone C Domin sanin muhimman cigaba da abubuwa da s**a shafi yankin jahar neja maso AREWA dama kasa Baki daya
(1)

29/05/2024

jamaa ga fa sabon national anthem na Nigeria 😄😄😄 kowa yyi kokari ya haddace

Innalillahi wainna ILAIHI rajiun. Allah yayima Jarumar Kannywood Fati Slow Motion, rasuwa a Habasha a daren jiya Litinin...
28/05/2024

Innalillahi wainna ILAIHI rajiun. Allah yayima Jarumar Kannywood Fati Slow Motion, rasuwa a Habasha a daren jiya Litinin.

Da wanne Film za ku iya tunawa da ita?

Thanks for being a top engager and making it on to my weekly engagement list! 🎉 Nasir Izalah, Halliru Yakubu Makeri, Mod...
28/05/2024

Thanks for being a top engager and making it on to my weekly engagement list! 🎉 Nasir Izalah, Halliru Yakubu Makeri, Modi Mai Shadda Kontagora, Abdul M Dangware Adogo

Zanga Zanga-zanga Tabarke A Babban Birnin Tarayya Abuja Kan Dawo Da Sunusi Lamido Sunusi A Matsayin Sarkin Kano Da Gomna...
24/05/2024

Zanga Zanga-zanga Tabarke A Babban Birnin Tarayya Abuja Kan Dawo Da Sunusi Lamido Sunusi A Matsayin Sarkin Kano Da Gomnatin Jihar Kano tayi .

Menene rashin ku akan hakan?

Ana wata ga wataKotu ta Dakatar da Rushe Masarautun Kano Babbar kotun tarayyar mai zama a Kano ta bayar da umurnin dakat...
24/05/2024

Ana wata ga wata

Kotu ta Dakatar da Rushe Masarautun Kano

Babbar kotun tarayyar mai zama a Kano ta bayar da umurnin dakatar da gwamnatin Kano daga aiwatar da matakin rushe masarautun jihar.
Wannan mataki ya biyo bayan karar da guda daga cikin manyan hakiman da matakin ya shafa Alh Aminu Babba Dan Agundi Sarkin Dawaki Babba ya shigar a gaban kotu domin kalubalantar matakin rusa masarautu da majalisar dokokin Kano ta yi, wanda gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya rattaba hannu na amincewa da kudurin.

Kotun Karkashin Justice AM Liman ta sanya ranar 3 ga watan Yuni domin sauraran karar.

Mene ne ra’ayin ku kan wannan turka-turkan

DW hausa

Ɗan Social Media! Ƙasurgumin INFORMER, USAMAN ANKA Ya  Cikin Waɗanda Yanzu Haka Ake Tsare Dasu Bayan Bankaɗo Asirinsu  D...
22/05/2024

Ɗan Social Media! Ƙasurgumin INFORMER, USAMAN ANKA

Ya Cikin Waɗanda Yanzu Haka Ake Tsare Dasu Bayan Bankaɗo Asirinsu Da Ta'adin Da S**ayi Na Kisan Mutane Tare Da Haɗin Baki Domin Garkuwa Da Mutane Domin Amsar Kuɗin Fasa a Yankin Ƙauran Namoda Da Jahar Zamgara.
Shine Yayi Bayanu Dalla Dalla Yadda S**a Kitsa Sache Babban Ma'aikachin Tajj Bank Dake Garin Gusau....

Daga Basharu Altine Guyawa Isa

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN: Wasu Bata-gari sun hallaka hakimi har lahira a Jihar Neja.Al'ummar Garin Pandogari d...
20/05/2024

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN: Wasu Bata-gari sun hallaka hakimi har lahira a Jihar Neja.

Al'ummar Garin Pandogari dake Masarautar Kagara ta karamar hukumar Rafi sun shiga cikin tashin hankali a cikin daren nan.

Bayan da wasu mutane s**a biyo hakimin Ringa Alhaji Samaila Shekarau har gida s**a sassarashi har sai da s**a tabbatar baya motsi.

Daya daga cikin Ya'yan shi mai suna Yariman Ringa ne ya shaidawa Limamin Tsalle Daya wannnan mummunar labari, Yace suna zargin Yan sakai dake aikin tsaro na sakai ne da aikata aika-aikar.

Anyi kokarin jin ta bakin Shugaban Karamar Hukumar yankin amma bai dauki waya ba, Sak**akon kila yayi bacci.

Credit:- Nura Daza 👍

Mu ƙaru da juna, ina masanan gidan nan, don Allah wannne man fetur din ne ya fi kyau anan Jan ko farin ?
19/05/2024

Mu ƙaru da juna, ina masanan gidan nan, don Allah wannne man fetur din ne ya fi kyau anan Jan ko farin ?

A BIRNIN JOSWannan matashi da kuke gani ba addininmu daya ba, daga ganinsa zaku fahimci bangaren da ya fito a JosYa daur...
14/05/2024

A BIRNIN JOS

Wannan matashi da kuke gani ba addininmu daya ba, daga ganinsa zaku fahimci bangaren da ya fito a Jos

Ya daura bàma-bámaí a kunkuminsa, yaje wani banki a Jos zai tàrwat$a mutane asirinsa ya tonu, yanzu yana hannun 'yan sanda

Hakika Allah Ya takaita faruwar wani mummunan al'amari jiya a birnin Jos, watakila da yanzu labari marar dadi muke ruwaitowa daga garin, saboda abinda makiya Musulunci suke jira kenan ya faru su cutar da 'yan uwa

Allah Ka tona asirin 'yan ta'adda da masu daukar nauyin ta'addanci a tsakanin mu.

14/05/2024

Bayanin Bello Turji gameda yin sulhu tsakanin gwamnati da makiyaya

NHMMM alamarin saidai mu cigaba da Addu'a

Cin Amana! Matashi Ya Hallaka ‘Yar Uwarsa 'yar shekara 6 Bayan Ya Yi Garkuwa Da Ita, Ya Turbudeta A Kango An k**a wani m...
13/05/2024

Cin Amana!

Matashi Ya Hallaka ‘Yar Uwarsa 'yar shekara 6 Bayan Ya Yi Garkuwa Da Ita, Ya Turbudeta A Kango

An k**a wani matashi Abdulazeez Idris, mazaunin unguwar Jama’a da ke ƙaramar hukumar Maƙarfi a Jihar Kaduna, kan zargin sace ‘yar uwarsa ‘yar shekara 6 tare da kashe ta da kuma turbude gawarta a kango.

Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!! 😥😥Abun tausayi kwarai da gaske wallahi 🥹🥹Shi yasa aka ce Allah baya gama halitta h...
11/05/2024

Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!! 😥😥

Abun tausayi kwarai da gaske wallahi 🥹🥹

Shi yasa aka ce Allah baya gama halitta har sai randa ya dauki ran ka.

K**ar yadda kuka sani sunan ta Maryam wacca ake kira da Lailah a Film din Labari na

Sunyi hatsari a kwanaki 3 da s**a gabata tare da Mijin ta da kanin mijin ta da yaronta

Da ita da Mijin ta suna kwance a asibiti, shi kuma kanin mijin nata ya rasu tun a ranar da s**a yi hatsarin, a safiyar yau kuma Allah Ya ɗauki ran yaron ta wanda hatsarin shima ya rutsa da shi 🥹🥹

Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un 🥹
Halin da ake ciki yanzu shi ne Maryam ta rasa rabin fuskar ta k**ar yadda naji daga majiya mai tushe.😭

Ta rasa ido 1 👀
Ta rasa kunne 1 👂
Ta rasa rabin hancin ta 👃
Ta rasa rabin bakin ta 👄

Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un 🥹

Rabin face din yayi damage fa. La Haula 💔😭🥹.

Allah Ya gafarta wa Kanin Mijinta Ibrahim da kuma yaronta, Allah kuma Ya bata lafiya ita da Mijin ta.🙏😭🙏

10/05/2024

Ya amshi kudi har miliyan uku domin bada offer Amma bai Bayar ba, Kuma ya kashe Wanda ya karbi kudin sa.

Innalillahi Wa'innah Illaihi Raji'un😭Ya shiga har gida ya kashe abokinsa akan miliyan uku ya dauka motar mamacin tareda ...
09/05/2024

Innalillahi Wa'innah Illaihi Raji'un😭

Ya shiga har gida ya kashe abokinsa akan miliyan uku ya dauka motar mamacin tareda sa gawarsa ya jefar ya gudu da motar anyi nasarar k**ashi Allah ka rabamu da aikin dana sani da mummunar qaddara Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un 😭😭 ya baka aron kudi akan Karka bashi ka kashe shi ga kunyar dunia ga kunyar haduwa da Allah 😭

ALLAH KA SHIRYAR DA BARAYIN WAYAWannan yarinya ta hadu da sharrin barayin waya, s**a càka mata wúka a bayanta, s**a kwac...
28/04/2024

ALLAH KA SHIRYAR DA BARAYIN WAYA

Wannan yarinya ta hadu da sharrin barayin waya, s**a càka mata wúka a bayanta, s**a kwace wayanta s**a gudu

Wannan zalunci ya faru a anguwar Jerusalem dake birnin Damaturu jihar Yobe

Yanzu haka yarinyar 'yar shekara 24 tana kwance a Specialist Hospital Damaturu Likitoci na kokarin bata agajin gaggawa

Shawara:
Idan tsautsayi ya rusa da kai barayin waya sun tareka a inda ba zaka iya gudu ko samun agaji ba, to ka mika musu wayan ka tsira da rayuwanka ina ganin hakan yafi

Yawanci mutanen da barayin waya s**a caka wa wuka su kan nemi suyi gardama ne da jayayya idan barayin sun bukaci karban wayan a hannunsu, don haka rayuwa yafi waya daraja a fahimtata

Bursunoni Sun Tsere Daga Gidan Gyaran Hali na Suleja Cikin Daren Nan......Wani lamari ya faru cikin daren nan, A Gidan G...
25/04/2024

Bursunoni Sun Tsere Daga Gidan Gyaran Hali na Suleja Cikin Daren Nan......

Wani lamari ya faru cikin daren nan, A Gidan Gyaran hali (Prison) ta Suleja dake Jihar Neja yayin da Bursunoni s**a tsere ana cikin tafka ruwan sama.

Wani Ma'aikacin Gidan ya shaidawa Limamin Tsalle Daya ta wayar tarho cewar, Lamarin ya faru ne sanadiyyar rushewar Katanga ana tsaka da ruwan sama inda Bursunonin s**a yi amfani da damar s**a ringa fecewa.

Ya kuma ce suna ta yankin Madalla a cikin daren nan, Inda suke cigaba da kamo wasu daga cikin su domin mayar dasu Gidan.

~ daga:- Tsalle Daya

24/04/2024

Ibrahim Ya Mika Hakkin Umar Bush Ga Iyayensa

"Wannan da Kuke Gani Dauke da Kudi Shine Mahaifin Umar Bush Na Gefansa Kuma shine Yayan Mahaifinsa

"A Gaban Shaidu dük Wani Hakkı Na Umar Bush Wanda Akai Niyar Siya masa Wata Kadara Wace Zai dogara da Ita Tare da Umarnin Magaifin Sa da Kuma Yayan Mahaifin Sa Allah Beyi Ba Har Zakazo Aka Samu Wannan Sabanin

"Yanzu Cikin ikon Allah Ga Hakkin Umar Nan dama dük Abinda Yake Samu dağa kan Nera Goma Zuwa Muliyan daya sai An Rubuta a Takarda Cikin ikon Allah Gashi nan An Danka Hakkin Umar a Hannun Mahairin Umar da Yayan Mahaifin Sa Tare da Shaidu da Kuma Lauyoyi 👇🏼👇🏼

"Duk wani Karin Bayani Kuma Ibrahim Abdullahi Zaizo Muku Dashi". Cewar Sadeeq Tarda Ungogo

INDA RANKA: Nafisa Salisu daga Rafin Guza a Kaduna ta sa a ka$he mijinta saboda ya ranta mata kudi tayi kasuwanci sai ta...
16/03/2024

INDA RANKA: Nafisa Salisu daga Rafin Guza a Kaduna ta sa a ka$he mijinta saboda ya ranta mata kudi tayi kasuwanci sai ta kashe kudin yanzu kuma ya zo yana tuhumarta ina kudi... saboda haka sai ta yanke shawarar sakawa a ka$he mata shi....

Sai dai sun kai masa hari amma basu samu nasara ba...

YA KUKE GANIN WANNAN HUKUNCIWasu fusatattun matasa sun kashe wanda ake zargin barawon mashin ne a garin Kwantagora, lama...
15/03/2024

YA KUKE GANIN WANNAN HUKUNCI

Wasu fusatattun matasa sun kashe wanda ake zargin barawon mashin ne a garin Kwantagora, lamarin ya faru ne a daren talatar makon nan daidai gadar makarantar sakandare ta jeka-ka-dawo (Government Day Secondary School).

Binciken da aka gudanar an gano cewar mamacin ya yi yunkurin sace mashin din ne a hannun dan kabu-kabu har ya kai ga yanke masa yatsa, sak**akon hakan ne, sai dan kabu-kabun ya yi ihu! domin jawo hankalin jama'a inda s**a kawo masa dauki.

Bayan sun yi nasarar kwace mashin din da ceto dan kabu-kabun; sai jama’a s**a dauki hukunci a hannunsu inda s**a auka wa wanda ake zargin da duka wanda hakan ne ya yi sanadin ajalinsa kafin zuwan jami'an tsaro.

Wani shugaban ‘yan kabu kabun da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce mafi akasarin ‘yan kabu-kabu sun fada irin wannan tarko da ya yi sanadin hasarar rayukansu da baburansu.

Ya dai nemi ‘yan kabu-kabu a duk inda suke da su zama masu kiyaye wuraren da suke shiga da irin jama'ar da suke dauka, domin al’amarin tarkon miyagu ba wanda ya isa ya kauce masa sai a tabbatar ana kiyayewa.

Innnalillahi WA inna ilaihi Raji un matan sirri Kinga wani rashin imani 😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭Wani mara imanı yawa yarinya yar 9 ...
15/03/2024

Innnalillahi WA inna ilaihi Raji un matan sirri Kinga wani rashin imani 😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭

Wani mara imanı yawa yarinya yar 9 years fyade kuma ya rataye ta da cable ta mutu, a layin Isiyaka Gwanna jos. Allah ya Isa Ubangji Allah ya tona asirinsa da duk msu hali irin nasa, Ubngj Allah Dan wannan wata Mai Albrk Ka tarwasa rayuwarsa , Innalillahi wa inna ilaihi rajiun 😭💔💔💔💔💔💔😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭💔😭

'Yan sanda Sun Kai Samame Rugar Fulani, Sun  K**a 'Yan Fashi, Sun Gano Bindugun Ak47 A Jigawa A ranar 7 ga watan Maris d...
14/03/2024

'Yan sanda Sun Kai Samame Rugar Fulani, Sun K**a 'Yan Fashi, Sun Gano Bindugun Ak47 A Jigawa

A ranar 7 ga watan Maris din 2024 ne jami’an ‘yan sanda tare da hadin gwiwar jami’an tsaron sa-kai na yankin, s**a kai samame a sansanin Fulani na Dangoli da ke karamar hukumar Kiyawa ta jihar Jigawa tare da k**a wani Musa Babangida dan shekara 18 da Bello Usman mai shekaru 20.

'Yan sandan sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyu daga hannun wadanda ake zargin dauke da harsashi 68 da sarkar kafa daya, da babur daya, da wayoyin salula 8, batura 8, layin SIM guda 5, da na’ura mai amfani da hasken rana daya, da fasfo da tsabar kudi Dubu Dari Biyu da Ashirin da Daya, Dari Biyar da Goma (N221,510).

Wadanda ake zargin dai sun dade suna aikata munanan ayyukan fashi da makami, a tsakanin shiyoyi da dama.

YANZU-YANZU: Wannan mutumin wasu marasa tsoron Allah ne s**a shaƙe shi, a dai dai gidan Gwamnatin jihar Kano, babu alamu...
11/03/2024

YANZU-YANZU: Wannan mutumin wasu marasa tsoron Allah ne s**a shaƙe shi, a dai dai gidan Gwamnatin jihar Kano, babu alamun rai tare dashi.

Yanzu haka an garzaya da shi zuwa asibitin Nasarawa da ke Kano.

Dan Allah kuyi share ko yan uwan sa za su gani

Hoton Mutumin Da Ya Jagoranci 'Yan Uwansa Askarawan Zamfara S**a Yi Wa Limami Yankan Rago Na Yawo A Soshiyar Midiya Wann...
11/03/2024

Hoton Mutumin Da Ya Jagoranci 'Yan Uwansa Askarawan Zamfara S**a Yi Wa Limami Yankan Rago Na Yawo A Soshiyar Midiya

Wannan wanda ake zargin ya jagoranci 'yan uwansa askarawan Zamfara, s**a yiwa malamin addinin Musulunci Limamin masallacin garin Mada, Shugaban Majalisar Malammai na kungiyar Izala ta ƙasa reshen karamar hukumar Gusau, Sheikh Imam Abubakar Hassan mada, Yankan Rago a garin mada dake jihar Zamfara.

Al'ummar garin sun sanya ido ga Hukumomi da Gwamnatin jihar Zamfara, don ganin An gurfanar da su gaban kotu, domin ya fuskanchi Shari'ah.

RAMADAN MUBARAKYanzu yanzu Kasar saudiya ya sanar da ganin jinjirin wata, Wanda insha Allah ake sa Ran zaa fara azumin w...
10/03/2024

RAMADAN MUBARAK

Yanzu yanzu Kasar saudiya ya sanar da ganin jinjirin wata, Wanda insha Allah ake sa Ran zaa fara azumin watan Ramada na wannan shekara a gobe littinin idan Allah ya kaimu.

Muna yiwa Al'ummar mabiya wannan shafi fatan zaa shiga wannan wata Mai alfarma cikin aminci.

NIGER STATE 2024 RAMADAN TAFSEERSUNAYEN MALLAMAI MASU TAFSIRIN RAMADAN A KARKASHIN  JIBWIS  JAHAR NEJA 1445/20241-AGWARA...
08/03/2024

NIGER STATE 2024 RAMADAN TAFSEER

SUNAYEN MALLAMAI MASU TAFSIRIN RAMADAN A KARKASHIN JIBWIS JAHAR NEJA 1445/2024

1-AGWARA L G.

Mallam Umar Mukhtar Da Alrm Abubakar Abubakar
Wurin Tafsir- Agwara

2-BIDA L G
Sheikh Abdulqadir Sulaiman
Wurin Tafsir- Bida

3- BORGU L G
Sheikh Aliyu Libata da Alrm Nasiru Abubakar Sk
Wurin Tafsir -New Bussa

Sheikh Muhammad Gidado
Wurin Tafsir- Malale

4-CHANCHAGA L G

Sheikh Muhammad Awwal Umar Rijau
Wuri Tafsir - Minna Tudun Fulani

Sheikh Muhammad Sani Abubakar da Alrm Suhail Muhammad Sani
Wuri Tafsir- Minna Tayi Village

Sheikh Abubakar Rabi'u Beji da Alrm Idris Muhammad
Wurin Tafsir- State Secretariat Minna

Mall Yahaya Aliyu Koko
Wurin Tafsir- Masjid Sahaba Minna

5- EDATI L G

Mall Abdullahi Imam Enagi
Wurin Tafsir- Enagi

6- GBAKO
Mall Muhammad Salisu
Wurin Tafsir- Lemu

7- GURARA
Mall Abbas Muhammad
Wurin Tafsir- Lambata

8- KONTAGORA

Mall Muhammad Bello Musa Da Alrm Muhammad Kabir
Wurin Tafsir- Uthman Bn Affan Kontagora

Alkali Usman Abubakar Da Alrm Nasiru Mahmud Uthman
Wurin Tafsir- Sabuwar Kasuwa

Mall Awwal Marafa Da Alrm Imrana Mariga
Wurin Tafsir- Kawo

Mall Attahiru Koko Da Alrm Bardizba Ashafa
Wurin Tafsir- Masallacin Sani Hussain

Mall Bukhari Zakariyyah Da Alrm Umar Idris
Wurin Tafsir- Tsohon Kasuwa

Mall Shehu A Tudun Wada Da Alrm Ibrahim M Bangi
Wurin Tafsir- Masallacin Shukura

9- MARIGA L G

Mall Abubakar Sanyinnah Da Alrm Salmanu Aliyu
Wurin Tafsir- Kamfanin Bobi

Mall Yakubu Aliyu Da Alrm Muhammad Baba Dikko
Wurin Tafsir- Bangi

Mall Abubakar Muhammad Yahuza Da Alrm Yusuf Adam Yauri
Wurin Tafsir- Shadadi

Mall Suleiman Abubakar Kontagora
Wurin Tafsir- Gulbin Boka

10- MAGAMA L.G

Mall Yusuf Sulaiman
Wurin Tafsir- Auna

Mall Umar Sulaiman Jabo
Wurin Tafsir- Ibeto

Mall Awwal Karaye
Wurin Tafsir- Salka

11- MASHEGU L G

Mall Abdussalam Ibrahim Gbajibo Da Alrm Awwal Abubakar B/Rami
Wurin Tafsir- Sabon Rijiya

Mall Alhassan Idris Da Alrm Iliyasu Abubakar
Wurin Tafsir- IBBI

Mall Aliyu Nuhu Mariga Da Alrm Bashiru Uthman
Wurin Tafsir-Zugurma

Sheikh Ahmad Adam Gwada Da Alrm Khamis Tahir Kontagora
Wurin Tafsir- Kaboji

Sheikh Saidu Jibrin Wushishi Da Alrm Ismail Abubakar
Wurin Tafsir-Sabon Pegi

Sheikh Mahmud Abdullahi Mokwa Da Alrm Mustafa Umar Makera
Wurin Tafsir- Makera

Sheikh Khidir Hashim Da Alrm Abdur Rahman Abdulaziz
Wurin Tafsir- Babban Rami

12- MOKWA L G

Mall Muhammad S Kele Da Alrm Hassan Uthman Lapai
Wurin Tafsir- Gbajibo

Mall Dahiru Wara Da Alrm Shafi'u A Suleja
Wurin Tafsir- Mokwa

13- MUNYA L G

Mall Nasir Abdullahi Sarkin Pawa Da Alrm Ishaq Gwada
Wurin Tafsir- Sarkin Pawa

14- PAIKORO L G

Seikh Umar Dada Paiko
Wurin Tafsir- Paiko

Mall Sani Kasuwan Garba Da Alrm Abdullahi Abubakar Kagara
Wurin Tafsir- Kaffin Koro

15- RAFI L G

Mall Hudu Abdullahi Kagara Da Alrm Yakubu Zakariyyah
Wurin Tafsir- Kagara

16- RIJAU L G

Sheikh Ibrahim Garba Kawo
Wurin Tafsir- Dukku

Mall Salihu Alkutubi
Wurin Tafsir- Chibadi

17- SHIRORO L G

Mall Ismail Sulaiman Kainji Da Alrm Jamilu Sale Galadima
Wurin Tafsir-Zumba

Mall Rabi'u Abdullahi Gombe
Wurin Tafsir- Gwada

18- SULEJA L G

Mall Muhammad Bauchi
Wurin Tafsir- Madalla

19- TAFA L G

Mall Alhassan Idris Da Alrm Mubarak Tafa
Wurin Tafsir- GAURAKA

Mall Ahmad Sambo Da Alrm Muhammad Nura
Wurin Tafsir- Sabon Wuse

20- WUSHISHI L G

Mall Musa Isah Erana
Wurin Tafsir- Wushishi

Mall Misbahu Zungeru Da Alrm Hassan Mahmud
Wurin Tafsir- Zungeru

Mall Umar Maikifi Da Alrm Zayyanu Qasimu Makera
Wurin Tafsir- Tungan Sayyadi

JAN HANKALI : AN GARGADI MALLAMAI MASU TAFSIRIN DA SU KIYAYI YIN TSOKACI AKAN TSARO, SAI DAI ADDU'A , ALLAH YA BADA ZAMAN LAFIYA A KASA

AAMEEN

ZILAL MUHAMMAD SANI
JIBWIS NIGER STATE
MEDIA AND PUBLICITY

25/02/2024

A CIKIN GARIN KONTAGORA

HMMMM, shin wannan lamarin akan su wa zaa daura alhakin hakan.

To mudai saidai muce Allah ya kiyaye na gaba Kuma ya bamu shugabnni Mafi alkhaairi.

21/02/2024

Niger state government and Niger state NLC executive before starting today meeting.

21/02/2024

Shugaban kungiyar kwadago na jahar neja kenan Comrd IDREES Lafene yayin da yake jawabi ga manema labarai Jim kadan bayan fitowa daga hutun takaitaccen lokaci na zaman tattaunawa da ya gudana d a gwamnatin jahar neja, dangane da yajin aikin da ma'aikatan jahar s**a tsunduma ayau.

Wanda hakan yasa aka rufe makarantun, asibitoci da duk masana'antu gwamnati dake fadin jahar.

Menene raayinku game da wannan yajin aiki


20/02/2024

MAZA DA FATAN ZAKU DAUKI GYARA 😄😄😄

SHIN YA DACE HAKAN?MATSIN RAYUWA: Wani Mutum Ya Cire Fara Rufin Kwanon Masallacin Da Ya Gina Shekaru 30 Da S**a WuceAl'a...
20/02/2024

SHIN YA DACE HAKAN?

MATSIN RAYUWA: Wani Mutum Ya Cire Fara Rufin Kwanon Masallacin Da Ya Gina Shekaru 30 Da S**a Wuce

Al'amarin ya faru ne a Birnin Kudu dake jihar Jigawa, lamarin da ya razana al'umma.

Shi dai wannan bawan Allah wanda aka sakaya sunansa shine ainihin wanda ya gina Masallacin tsawon shekaru talatin da s**a shuɗe, sai yanayin matsin rayuwa tasa ya ga ya dace ya gina shaguna a wani ragowar filin harabar Masallacin, lamarin da mutane s**ace basu san wannan ba, tunda ya riga ya gina Masallacin ya barwa al'umma.

Dalilin haka ya fusata ya hau ya fara cire rufin kwanon Masallacin da zummar ya fasa yin Masallacin.

Address

Minna
AWARENESS/EDUCATING

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Muryar Al'ummar Zone C posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share

Nearby media companies


Other Digital creator in Minna

Show All

You may also like