22/07/2022
Yajin aikin ASUU: Gwamnatin tarayya ta roƙi NLC da ta janye zanga-zangar da ta ke shirin yi
Gwamnatin tarayya ta yi kira ga Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa, NLC da ta janye zanga-zangar da ta ke shirin yi a fadin kasar nan domin nuna goyon baya ga kungiyoyin kwadago a jami’o’in gwamnati da sauran su a faɗin ƙasar nan.
Ministan Ƙwadago da Samar da Ayyukan yi, Chris Ngige ne ya yi wannan roƙo a wani taro da shugabannin ƙungiyar NLC a ofishinsa a jiya Alhamis a Abuja.
A tuna cewa NLC ta yanke shawarar shiga Zanga-zangar ta Kasa ne a taronta na Majalisar Zartarwa, NEC, a watan Yuni.
Ƙungiyar ta shirya gudanar da zanga-zangar ta kasa ne a ranakun 26 da 27 ga watan Yuli domin tabbatar da cewa ɗalibai sun koma makaranta da kuma goyon bayan kungiyoyin kwadago a jami’o’in gwamnatin Najeriya dake fafutukar neman ilimi mai inganci.
Sa sai kuma a wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami'in hulda da jama’a na ma’aikatar, Olajide Oshundun, Ngige ya ce gwamnatin tarayya ta yi kokari matuka wajen ganin an shawo kan tabarbarewar harkokin jami’o’in, inda ta ce har yanzu ana ci gaba da kokarin.
Ya kuma tunatar da shugabannin NLC cewa ya shigar da su cikin sulhun bangarorin uku da ke gudana a ma’aikatar sa.
Ngige ya kara da cewa NLC na sane da kokarin gwamnati na ganin an shawo kan matsalar, don haka bai kamata ta gudanar da wani gangami ko zanga-zanga ba.
Ya ci gaba da cewa majalisar zartaswa ta tarayya, FEC, ta umarce shi da ya sanar da NLC din mummunar illar da za ta shafi tsaro idan ta gudanar da zanga-zangar da ta shirya yi.