Daily 24 Hausa

Daily 24 Hausa Daily 24 Hausa Kamfanin Jarida ne da zai cigaba da kawo maku Sahihan Labarai Masu Inganci. Mun gode da Ziyara
(2)

An Ɗaure Sam Bankman-Fried Sarkin Yan Crypto Shekaru 25 A Gidan YariBankman-Fried fitaccen ɗan kasuwa ne da babu irinsu ...
28/03/2024

An Ɗaure Sam Bankman-Fried Sarkin Yan Crypto Shekaru 25 A Gidan Yari

Bankman-Fried fitaccen ɗan kasuwa ne da babu irinsu da yawa - ya yi shahara mai ƙarfi a kafafen sada sumunta, abin da ya sa ƙanana da matsagaitan masu hada-hadar crypto ke bin shafinsa.

Manyan masu zuba jari sun amince da shi, saboda yadda kasuwanci ke haskakawa kuma ya samu karbuwa a duniya, dalilin da ya sanya s**a sanya miliyoyin suƙinsu kenan a kamfaninsa.

Yana yawan nuna kansa a matsayin kwararre kuma ɗan baiwa a lissafi wanda bai damu da tara duniya ba.

Biloniyan ya taɓa tuka wata motar iyalai da ta rakwakkwaɓe kuma ya sha kwana kan buhun waje a ofishinsa. Yana da burin taimakawa ƙungiyoyin baimakawa al'umma.

Kamfaninsa na musayar kuɗi na crypto ya bunƙasa ya sama na biyu mafi girma a duniya inda suke hada-hadar dalar Amurka biliyan 10 zuwa 15 a rana.

Kamfanin Samuel Hapak ya wakilci masu zuba jari 200 a zaan kotun waɗanda s**a yi asarar kuɗi da s**a kai dala miliyan 35 lokacin da kamfanin FTX ya bayyana yana daf da durkushewa.

Shugaban kamfanin samar da manhajar kwamfuyuta na Wincent ya shaida wa BBC cewa ɗaurin da aka yi wa Sam na shekara 25 ya yi daidai.

Kamfanin Wincent ya yi asarar rabin jarinsa kimanin dala miliyan 70 - kashi 25 na hannun jarinsa, Hapak ya shaida wa BBC.

BBC Hausa

YANZU YANZU: An fara gudanar da tafsiri na watan Ramadan a gidan Bobrisky, inda ta samu Malamin da zai riƙa yi k**ar yad...
28/03/2024

YANZU YANZU: An fara gudanar da tafsiri na watan Ramadan a gidan Bobrisky, inda ta samu Malamin da zai riƙa yi k**ar yadda ya bada cigiya.

Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi, ya bawa mutane 27 jarin miliyan Goma-Goma, domin suyi sana'ar siyar da kayan tuk...
27/03/2024

Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi, ya bawa mutane 27 jarin miliyan Goma-Goma, domin suyi sana'ar siyar da kayan tuka-tuka.

Muhammad Isma'el
SA Publication and Photography.

Kudurorin Majalisar Zartaswa Ta Jihar Jigawa A taron Majalisar Zartaswa ta jihar Jigawa na ranar Litinin (25/3/2024) an ...
27/03/2024

Kudurorin Majalisar Zartaswa Ta Jihar Jigawa

A taron Majalisar Zartaswa ta jihar Jigawa na ranar Litinin (25/3/2024) an amince da ƙudurori k**ar haka:

1. Majalisar Zartaswa ta duba Rahoton Kwamitin Tantance Rahoton Kwamitin Bincike akan Manyan Makarantun Koyar da Ayyukan Kiwon Lafiya na jiha, inda ta umarci Ofishin Babban Akanta na jiha da ya aiwatar da shawarwarin da wannan kwamiti ya bayar tare da ɗaukar waɗannan matakai:

I. Sauke shugabannin Kwalejin Koyon Aikin Jinya ta Birnin Kudu da s**a haɗa da Provost, Bursar da Registrar tare da umarnin su kai kansu Ma’aikatar Lafiya, Ofishin Shugaban Ma’aikata da Babban Akanta.

II. An sauke daraktocin Makarantun Koyon Aikin Jinya na Birnin Kudu, Hadejia da Babura daga muƙamansu kuma za su kai kansu Ma’aikatar Lafiya.

III. Daraktocin Birnin Kudu, Hadejia da Babura za su biya kuɗaɗen da s**a bayar da ba’asi akansu.

IV. An sauke Provost, Bursar da Registrar na Kwalejin Kiwon Lafiya ta Jahun daga muƙamansu sannan kuma za su kai kansu Ma’aikatar Lafiya, Ofishin Shugaban Ma’aikata da Babban Akanta.

V. Provost na Kwalejin Kiwon Lafiya zai bayar da dalilai kan ɓacewar kuɗaɗen shiga na kwalejin da waɗanda aka samu daga gwamnati waɗanda ba a bayar da ba’asinsu ba.

VI. Dukkan jami’an da suke karɓar albashin da bai k**ata su karɓa ba sannan kuma ba a makarantun suke aiki ba amma sunayensu s**a kan jadawalin albashi na makarantun, za su mayar da kuɗin da s**a karɓa wanda ba haƙƙinsu ba ne.

VII. Ma’aikatar Lafiya za ta sabunta gine-gine da kayan aiki a Makarantun Koyon Aikin Jinya na Birnin Kudu, Hadejia da Kwalejin Kiwon Lafiya ta Jahun.

VIII. Ma’aikatar Lafiya za ta ɗauki ƙarin ma’aikata domin cike giɓin ƙarancin malamai a waɗannan makarantu biyu.

IX. Gwamnati za ta kafa Hukumomin Gudanarwa na waɗannan makarantu biyu.

X. Ma’aikatar Lafiya za ta ƙara kuɗin abinci na ɗaliban Kwalejin Kiwon Lafiya ta Jahun.

2. Samar da ƙarin rancen kuɗi ga JASCO domin sayen buhunan takin zamani 90,000

(motoci 150) na NPK don kakar noma ta shekarar 2024 wanda za a sayar ga al’ummar jihar Jigawa. Za a sayo takin naira Biliyan Biyu (N2,000,000,000.00).

3. Gina gidajen kwana na ma’aikatan Ungozoma guda 7 tare da zagaye su a ƙananan cibiyoyin kiwon lafiya na: Abaya PHC a Dutse, Koya PHC a Miga, Kanzan PHC a K/Hausa, Madachi PHC a Kirikasamma, Yar’ Sara PHC a Roni, Chakwaikaiwa PHC a Taura da kuma Amanga PHC a Sule Tankarkar. Za a yi wannan aiki ne akan kuɗi naira N305,674,439.11.

4. Sabunta kwangilar samar da lantarki mai aiki da hasken rana (solar) a Babban Asibitin birnin Dutse daga naira N172,754,158.00 zuwa naira N252,849,395.50.

Lamarin kasar nan fa sai Addu'a Wani Boka ya koma Nika.🤣
26/03/2024

Lamarin kasar nan fa sai Addu'a Wani Boka ya koma Nika.🤣

Shin Ya Sunanta Kuma Wane Fim Ku Ka Tuna?
26/03/2024

Shin Ya Sunanta Kuma Wane Fim Ku Ka Tuna?

Abincin ciyarwar Azumi da Gwamnatin jihar Jigawa take rabawa al-ummar jihar. Shin yaya na jiharku yake?
25/03/2024

Abincin ciyarwar Azumi da Gwamnatin jihar Jigawa take rabawa al-ummar jihar. Shin yaya na jiharku yake?

ALHAMDULILLAH: An Yi Nasarar Kuɓutar Da Dukkanin 'Yan Makarantar Da Aka Sace A Garin Kuriga Su 137 A Jihar Zamfara
24/03/2024

ALHAMDULILLAH: An Yi Nasarar Kuɓutar Da Dukkanin 'Yan Makarantar Da Aka Sace A Garin Kuriga Su 137 A Jihar Zamfara

Jihar Jigawa ce kan gaba wurin jagorantar kokarin samar da abinci a Najeriya, inji Gwamnan jihar Jigawa. Jihar Jigawa ta...
23/03/2024

Jihar Jigawa ce kan gaba wurin jagorantar kokarin samar da abinci a Najeriya, inji Gwamnan jihar Jigawa.

Jihar Jigawa ta zuba jarin noman Alk**a, Shinkafa, Sesame, da gum Arabic na taka rawar gani wajen samar da wadataccen abinci a Najeriya.

Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya ce jiharsa ce ke jagorantar kokarin samar da abinci a Najeriya ta hanyar zuba jari a fannin noma.

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar fadar shugaban kasa a gidan gwamnati dake Dutse, a jiya Alhamis.

Tawagar ta samu jagorancin ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris, kuma ta kunshi hadiman shugaban kasa Bola Tinubu kan harkokin yada labarai da shugabannin hukumomin yada labarai.

Gwamna Namadi ya ce jihar ta sanya hannun jari a fannin noman Alk**a, Shinkafa hibiscus, sesame, da da gum Arabic, kuma tana taka rawa sosai a tafiyar da Najeriya ke yi na samar da abinci da wadatar tattalin arziki.

Gwamna Namadi, ya yi karin haske kan yadda jihar ke noma wanda ya yi nuni da cewa ya sanya gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin bunkasa alk**a na kasa a jihar a watan Nuwamban da ya gabata.

Ya yi nuni da cewa, gwamnatin tarayya za ta noma hekta 100,000 na alk**a a bana, a matsayin wani bangare na ajandar sabunta harkar na Shugaba Tinubu.

Gwamnan ya kara da cewa jihar Jigawa ta ware hekta 40,000 na fili ga shirin noman alk**a, wanda gwamnan ya ce ya yi daidai da ajandar gwamnatinsa mai dauke da abubuwa 12.

“Abin farin ciki ne mu nuna irin ci gaban da muka samu a fannin noma da samar da abinci domin tallafa wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen samun wadatar abinci a fadin kasar.

"Muna farin cikin ganin yadda gwamnatin Tarayya ta kaddamar da "Fadama Radio", gidan wayar da kan manoma a Auyo, a matsayin wani bangare na sadaukar da kai ga ilimin aikin gona da karfafawa. Tare da yalwar filayen noma da jagoranci mai himma, jihar Jigawa a shirye take ta jagoranci kokarin samar da abinci a Najeriya,” in ji Mista Namadi.

Minista Idris, a nasa jawabin, ya ce ya gamsu da nasarar shirin noman rani na gwamnatin tarayya a Jigawa.

Ministan ya ce tawagarsa ta ziyarci karamar hukumar Auyo ne domin ganin kokarin da manoman shinkafa da alk**a ke yi na tabbatar da samar da abinci a kasar.

“Ba don komai ba ne shugaban kasa ya canza sunan ma’aikatar noma da raya karkara zuwa ma’aikatar noma da samar da abinci domin sai da ka samu wadatar abinci ne za ka samu kowane irin tsaro a kasar nan, inji Idris.

Ya ce ziyarar da ya kai jihar Jigawa ya nuna karara na jajircewar Shugaba Tinubu wajen magance matsalolin da ke tattare da samar da abinci, inda ya ce tawagarsa ta kuma a Auyo domin tabbatar da cewa an yi amfani da ayyukan gwamnatin tarayya k**ar yadda aka tsara.

Ya yi kira ga ’yan Najeriya da su koma gona su ci gajiyar tallafin da gwamnatin tarayya ke ba su a duk tsarin darajar noma don samar da abinci mai yawa a kasar nan.

“Kuna sane da irin kokarin da gwamnatin tarayya ke yi ta ma’aikatar noma da samar da abinci ta tarayya ta fannin tallafa wa kayayyakin masarufi, rancen lamuni da duk wani abu da manoma ke bukata domin su samu dogaro da kansu.

Wace Kujera Ku Ke Ganin Malam Nasir El-Rufai Ya Kamata Ya Nema A Zaben Shekarar 2027 Idan Allah Ya Kaimu?
22/03/2024

Wace Kujera Ku Ke Ganin Malam Nasir El-Rufai Ya Kamata Ya Nema A Zaben Shekarar 2027 Idan Allah Ya Kaimu?

An Gurfanar Da Shugaban Miyetti Allah Kautal H**e, Bodejo A Gaban Kotu Kan Zargin Ta’addanciGwamnatin Nijeriya ta gurfan...
22/03/2024

An Gurfanar Da Shugaban Miyetti Allah Kautal H**e, Bodejo A Gaban Kotu Kan Zargin Ta’addanci

Gwamnatin Nijeriya ta gurfanar da shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal H**e, Bello Bodejo a gaban kotu kan zargin aikata laifukan ta’addanci.

An gurfanar da Bodejo a gaban wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja kan zarginsa da kafa da kuma tallafa wa kungiyar ‘yan bindiga ta ‘Kungiya Zaman Lafiya’ ba bisa ka’ida ba.

An gurfanar da Bodejo ne a ranar Juma’a a kan tuhume-tuhume guda uku da ofishin babban mai shari’a na kasa ya shigar, inda ake tuhumarsa da karya dokar ta’addanci ta shekarar 2022.

Bodejo ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da ake yi masa a lokacin da aka karanto masa tuhumar a gaban kotu, daga nan ne mai shari’a Inyang Ekwo ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi a hannun hukumar leken asiri ta DIA.

Mai shari’a Ekwo ya dage ci gaba da sauraron shari’ar har zuwa ranar 27 ga watan Mayun 2024.

Idan za ku tuna kwanakin bayan an k**a shugaban na Miyetti Allah a jihar Nasarawa, bayan kungiyar ta kaddamar da wata kungiyar ‘yan banga mai suna Kungiyar Zaman Lafiya.

A lokacin bikin kaddamar da kayan Fulani na mutum 1,144 a ranar 17 ga watan Junairu, 2024, Bodejo ya ce, an dauki wannan matakin ne don magance matsalar ‘yan fashi da satar shanu da ma duk wani nau’in rashin tsaro da yake addabar jihar Nasarawa.

Bayan k**a shi, shugaban na Miyetti Allah, ya shigar da kara a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja domin kalubalantar tsare shi da aka yi.

A martanin da babban Lauyan gwamnatin tarayya, Lateef Fagbemi (SAN), a ranar 5 ga watan Fabrairu, ya shigar da kara a gaban kotu, inda ya bukaci a ci gaba da tsare Bodejo har sai an kammala bincike tare da gurfanar da shi a gaban kotu.

Mai shari’a Inyang Ekwo, wanda ke sauraron karar Bodejo, ya bai wa gwamnatin tarayya izinin tsare shi na tsawon kwanaki 15 a hannun hukumar leken asiri ta tsaro.

Daga bisani, alkalin ya umurci gwamnatin tarayya da ta gurfanar da shugaban na Miyetti Allah, ko kuma ta sake shi ya ci gaba da harkokinsa.

Leadership Hausa

Tsohan Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai  Ziyarci Helkwatar Jam'iyyar SDP Dake Abuja, Jiya Laraba
21/03/2024

Tsohan Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai Ziyarci Helkwatar Jam'iyyar SDP Dake Abuja, Jiya Laraba

Yadda Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi, yake kokarin ganin ya magance matsalolin da s**a addabi jihar Jigawa.Wato ...
20/03/2024

Yadda Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi, yake kokarin ganin ya magance matsalolin da s**a addabi jihar Jigawa.

Wato duk wanda yake son ganin zahirin abin da ake nufi da gina al’umma, samar da aikin yi da kuma magance matsalar al’umma, to ya kalli Jihar JIGAWA.

Don Allah mu kalli yadda gwamnan jihar Malam Umar Namadi ya jefi tsuntsaye da yawa da dutse ɗaya tak a fannin samar da ruwan sha ta gyaran famfunan tuƙa-tuƙa a gaba ɗayan sassan jihar.

Da farko dai, sanin kowa ne cewa babbar matsalar famfunan tuƙa-tuƙa a yankunanmu na karkara ba wai samar da famfunan ba ne kawai, a’a matsalar ita ce yadda za a cigaba da kula da kuma gyara su idan sun sami tangarɗa – wanda kuma hakan tamkar ruwan dare ne. Za ka ga an gina tuƙa-tuƙa mutane suna murna ruwan ya samu a ƙauye ko unguwarsu, amma da zarar ya lalace, to an shiga matsala kenan, domin wataƙila kafin a samu a gyara shi sai an ji jiki an wahala tukuna. Dole sai wani mai aljihu da kauri ya samo wani mai gyara da kayan aiki daga wani wurin daban kafin a iya magance wannan matsala ta rashin ruwa.

To abin da Gwamnan ya yi a nan shine: da farko sai a ɗauko mutum ɗai-ɗai daga kowace mazaba a dukkan faɗin jihar inda aka kai su s**a sami horo kan aikin gyara da haɗa famfunan tuƙa-tuƙa na tsawon watanni. Bayan kammala koyon, sai aka samarwa kowannensu kayan aiki, har ma da mashin na hawa, sannan aka tura su yankunan da s**a fito a matsayin ma’aikatan gyaran tuƙa-tuƙa da zimmar cewa duk wata matsalar tuƙa-tuƙa da ta zama tamkar ruwan dare a kowace mazaɓa, to an sami mai magance ta. Bugu da ƙari, shi kuma mai gyaran ka ga an sama masa aikin yi kenan.

Daga nan kuma sai gwamnati ta sake ɗauko mutane 27 - wato kenan mutum ɗaya daga kowace ƙaramar hukuma cikin ƙananan hukumomin jihar 27 – inda za a ba su horon sanin mak**a na tsawon mako guda.

To su kuma me za suyi?

Wato kowanne zai koma yankin ƙaramar hukumarsu ne inda zai buɗe shagon sayar da kayan aiki da gyaran tuƙa-tuƙa, wanda hikimar a nan itace: su waɗancan masu gyaran tuƙa-tuƙa na kowace mazaɓa za su riƙa sayen kayan gyara da aikin famfunan a shagunan waɗannan mutane a sauƙaƙe a yankinsu, ba tare da sun sha wahalar yin doguwar tafiya zuwa wasu garuruwa masu nisa ba.

Su kuma waɗannan masu shaguna gwamnati ce za ta ba su jari na wannan kasuwanci da za su shiga, wanda kuma babu ɗaya daga cikinsu da zai sami ƙasa da naira miliyan goma na jarin da za a ba shi, sannan za a haɗa su da kamfanin da zai riƙa ba su waɗannan kaya cikin sauƙi da rahusa. To su ma waɗannan ka ga ba kawai sana’a aka samar musu ba, masu kuɗi aka mayar da su (millionaires)!

Sa’annan kuma, wani alfanun daga wannan shine ita kanta al’ummar an sauƙaƙa mata matsalar rashin ruwa da kan faru a sak**akon lalacewar tuƙa-tuƙa inda ake ɗaukar tsawon lokaci kafin a samu a gyara shi.

To, ka ga kenan a Jigawa harkar famfon tuƙa-tuƙa ta zama nagge daɗi goma, kowa sai ya ci amfaninta. Wannan ne ake cewa multiplier effect da turanci.

Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi Ya Kaddamar Tare Da Ganawa Da ‘Yan Kasuwar Sayar Da Kayan Gyaran Fanfuna A Fadin ...
19/03/2024

Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi Ya Kaddamar Tare Da Ganawa Da ‘Yan Kasuwar Sayar Da Kayan Gyaran Fanfuna A Fadin Jihar Jigawa.

Mai Girma Gwamnan Jihar Jigawa Gwamna Mallam Umar A Namadi FCA A Cikin Shirinsa Na Samar Da Mutane 150 A Matsayin Attajirai A Fadin Jihar Jigawa A Yau 19/3/2024 Ya Kaddamar Da Rukunin Farko Na Mutane 27 Daga Kowacce Karamar Hukuma Tareda Masu Taimaka Musu 27 Jimulla 54 A Harkokin Kasuwancin Sayar Da Kayan Gyaran Fanfo.

Taron Wadda Ya Gudana A Dakin Taro Na MDI Dake Dutse, Wadda Aka Dauko Mutum Guda (1) Daga Kowacce Karamar Hukuma Yayinda Aka Koyar Dasu Ilmin Harkokin Kasuwancin Gyaran Fanfo.

Ana Sa Ran Kowanne Dan Kasuwa Daga Cikin Su Zai Samu Kudi Kimanin Naira Miliyan Goma, Haka Kuma An Umarci Kowanne Daga Cikinsu Da Samo Mutum Daya A Matsayin Wadda Zai Tayashi Gudanar Da Harkokin Kasuwancin Musamman Wajen Tattara Bayanai Dakuma Yadda Kasuwanci Zai Tafi Cikin Tsari.

Haka Zalika Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Nemo Hamshakin Dan Kasuwar Da Yake Harkar Sayan Kayayyakin Na Gyaran Fanfo Kai Tsaye Daga Kamfani Wadda Shima Dan Asalin Jihar Jigawane Domin Sayen Kayayyakin Kai Tsaye, Tareda Saukakawa Yan Kasuwar Samun Kayayyakin Cikin Sauki.

Haka Kuma Gwamnatin Jihar Jigawa Sanya Hannu Da Shugabannin Kananan Hukumomi Ta Ma’aikatar Kananan Hukumomi Domin Sayen Kayyakin Aikin Gyaran Fanfunan A Wurin ‘Yan Kasuwar Dake Kowacce Karamar Hukuma A Fadin Jihar Jigawa A Matsayin Doka.

Idan Ba’a Manta Ba A Kwanakin Baya Das**a Gabata Gwamnan Ya Kaddamar Da Yaye Mutane Kimanin 250 Daga Kowacce Mazaba A Matsayin Injiniyoyin Gyaran Tuka Tuka Wadda Aka Basu Horo Na Musamman Dakuma Kayayyakin Aikin Gyaran Fanfunan, Daga Bisani Aka Umarci Kowacce Karamar Hukuma Domin Saya Musu Sabbin Babura Domin Gudanar Da Ayyukan Nasu Cikin Sauki Tareda Dorasu Akan Turbar Dogaro Da Kai.

Gwamnan Yayin Wani Jawabi Daya Gabatar Mai Ratsa Jiki Inda Yake Tabbatarwa Da Yan Kasuwar Cewa Allah Ubangiji Yaga Niyyarsa Ta Fara Dora Jihar Jigawan Dakuma Kokarin Fitarta Daga Cikin Jihohin Masu Fama Da Talauci A Nigeria, Kuma Yace Yana Fatan Zasu Rike Amana Dakuma Buda Kasuwanci Nasu Har Suma A Samu Wasu Attajiran Daga Cikinsu Tareda Sake Buda Kasuwancin Nasu Zuwa Wasu Daga Cikin Sabbin Harkokin Kasuwanci.

A Karshe Gwamnan Ya Tabbatar Da Aniyarsa Ta Cigaba Da Shirin Zakulo Mutane Daban Daban Daga Sassan Jihar Jigawa Domin Basu Jari Tareda Koya Musu Dabarun Kasuwancin Wadda Hakan Ka Bada Dama Samun Nasarar Attajirai 150 Da Gwamnan Ke Shirin Samarwa Wadda Ke Kunshe A Cikin Kudirori Goma Sha Biyu (12Points Agender) Na Gwamnatinsa.

Yanzu yanzun Anzabi Comrade Tajuddeen Bashir Baba Matsayin Shugaban Kungiyar yan kwadigo na Ma’aikatan Gona da Abubuwa d...
19/03/2024

Yanzu yanzun
Anzabi Comrade Tajuddeen Bashir Baba Matsayin Shugaban Kungiyar yan kwadigo na Ma’aikatan Gona da Abubuwa da s**a shafi haka na Kasa wato (Nigerian Union of Agriculture and Allied Employees (NUAAE) National President

A taronsu na kasa da kasa dayawa wakana a Jahar Benue inda Baki daya delegates na wanan kungiyar ta kasa s**a zabeshi a matsayin shugaba. Comr Tajudeen Bashir Baba Dan Jahar Kano ne Nigeria.

Mal Abdul Danja
Daga Jahar Benue,Nigeria.
19/03/2024.

JIYA BA YAU BA: Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sir Abubakar Na Uku Kenan Cikin Raha Da Anna Shuwa Yayin Da Ya Halar...
17/03/2024

JIYA BA YAU BA: Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sir Abubakar Na Uku Kenan Cikin Raha Da Anna Shuwa Yayin Da Ya Halarci Taron Festac A Garin Kaduna A Cikin Shekarar 1977.

Allah Ya Gafarta Masa Da Dukkan Magabatan Mu.

Daga Shafin Lugude

YANZU-YANZU: Yaro mafi ƙarancin shekaru da ke jan baƙi ya yin Tafsirin Al-Ƙur'ani mai girma a garin mararrabar gurku da ...
12/03/2024

YANZU-YANZU: Yaro mafi ƙarancin shekaru da ke jan baƙi ya yin Tafsirin Al-Ƙur'ani mai girma a garin mararrabar gurku da ke jihar Nasarawa.

Masu karatu wane fata zaku yi masa?

Shahararren ɗan Daudun nan mai suna Idiris, wanda aka fi sani da Bobrisky ya bayyana cewa zai riƙa ciyar da mutane 500 k...
12/03/2024

Shahararren ɗan Daudun nan mai suna Idiris, wanda aka fi sani da Bobrisky ya bayyana cewa zai riƙa ciyar da mutane 500 kullum har tsawon kwana 30 na watan Ramadana.

DA DUMI-DUMI: Sanata Abdul'Aziz Yari, ya kaddamar da fara raba abinci da ya hada Shinkafa, Sugar, Masara da Gero Tirela ...
11/03/2024

DA DUMI-DUMI: Sanata Abdul'Aziz Yari, ya kaddamar da fara raba abinci da ya hada Shinkafa, Sugar, Masara da Gero Tirela 358 a jihar Zamfara, wanda gidajen Talakawa sama da dubu 250,000 ne zasu amfana.

A bisa al’adar karamci da Sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta Yamma yake yi a kowace shekara na rabon abinci, a yauma ya sake rabawa domin ragewa talakawa radadin halin kunci da ake ciki.

Ga yadda rabon ya kasance;

- Kananan hukumomi 13, kowace ta samu buhunnan abinci dubu 17,500.

- Karamar hukumar Gusau, ta samu buhunnan abinci dubu 22,500.

- Marayu, sun samu buhunnan abinci dubu 10,000.

- An baiwa marayu kayan Sallah da kudin dinki kowannen su Naira 2,000.

- An baiwa marayu Mata Atampa da kudin dinki kowannen su Naira 2,000.

Tuni wannan abincin da kayyakin sun isa kowace karamar hukuma, domin isar dasu ga al-umma ba tare da bam-bancin jam'iyya ko wariya ba.

A makon da ya gabata Sanata Yari, ya bawa Tinubu gudunmuwar Tirelolin abinci na kayayyakin masarufi wadanda s**a hada da shinkafa, mai, taliya, suga, makaroni, gishiri, da sauransu domin a rabawa talakawan Najeriya kimamin mutane miliyan biyu.

Al'mansoor Gusau,
Babban daraktan yada labarai na Sanata Dr. Abdul'aziz Yari Abubakar.

YANZU-YANZU : :  Dokta Sanusi Bala Turaki Gusau (Sarkin Dawaki Maituta) Ya ɗauki Nauyin ciyar da Musulmai 2200 kullum  t...
10/03/2024

YANZU-YANZU : : Dokta Sanusi Bala Turaki Gusau (Sarkin Dawaki Maituta) Ya ɗauki Nauyin ciyar da Musulmai 2200 kullum tsawon watan Ramadan a fadin kananan hukumomi 14 na jihar Zamfara.

Shirin ciyar da abinci a cikin wannan wata mai alfarma da Dokta Sanusi Bala Turaki Gusau Ya ɗauki Nauyi Na nufin samar da abincin Buɗa baki ga marasa galihu da kuma sauran al'ummar Domin Faranta Ransu Alfarmar Wannan Wata Mai Daraja da kuma Falala.

Allah Yasaka Masa Da Mafificin Alkhairi. Ameen

Duk Arewa Babu Mawaƙin Irina Kuma Nine Ginshikin Zaman Ali Nuhu Shugaban Hukumar Shirya Fina-finai Ta Najeriya A Karkash...
10/03/2024

Duk Arewa Babu Mawaƙin Irina Kuma Nine Ginshikin Zaman Ali Nuhu Shugaban Hukumar Shirya Fina-finai Ta Najeriya A Karkashin Gwamnatin Tinubu Da Na Kafa, Cewar Dauda Kahutu Rarara

Fitaccen mawakin siyasa Dauda Rarara ya bayyana cewa a sana’ar waƙa a Najeriya ya zarce kowa.

Rarara ya bayyana haka a lokacin da yake hira da jaridar TRT da ta buga a shafinta ranar Lahadi

A hirar Rarara ya yi ikirarin cewa shi ne ya fi kowa rera wakar siyasa a Najeriya kuma dole ake biyo shi har inda ya ke don ya yi waka

Da aka tambayeshi game da mukamin da gwamnatin Tinubu ta yi wa Ali Nuhu, Rarara ya ce shine ginshiƙin zaman Ali Nuhu MD a masana’antar fim n ƙasa.

Ni na kafa gwamnatin Tinubu, kuma na ji daɗin muƙamin da aka naɗa Ali Nuhu akai, saboda haka ina farinciki matuka, amma ba a wai an saka min bane tukunna.

Idan ba a manta ba Rarara ya ce shine ya kafa gwamnatin Tinubu, kuma ya k**ata a bashi akalla kujerun minista biyu ya raba sannan a saka shi cikin ƴan gaban goshin gwqmnatin Tinubu da za su rika gudabar da mulki a yanzu

A baya dai Rarara ya yi fice ne wajen rera wa tsohon shugaban Kasa Buhari waƙa, sai dai kuma tun bayan kammala mulkin Buhari, Rarara ya raba jiha da Buhari, inda ya caccaki mulkin sa ya kuma yi Allah Wadai da salon mulkin sa.

Saudiyya Ta Rage Raka'o'in Sallar Taraweeh Daga 20 Zuwa 10A Yanzu Masallatan Harami Na Makkah Da Madinah Za Su Riƙa Guda...
10/03/2024

Saudiyya Ta Rage Raka'o'in Sallar Taraweeh Daga 20 Zuwa 10

A Yanzu Masallatan Harami Na Makkah Da Madinah Za Su Riƙa Gudanar Da Sallar Taraweeh Raka’a Goma-goma, Sai Kuma A Cika Da Raka’o'i Ukku Na Shafa’i Da Wutiri.

YANZU-YANZU: Wani bawan Allah ya sa kyautar kuɗi har ₦10,000 ga duk wanda ya faɗi sunan “Shayi” mai ɗauke da madara da h...
09/03/2024

YANZU-YANZU: Wani bawan Allah ya sa kyautar kuɗi har ₦10,000 ga duk wanda ya faɗi sunan “Shayi” mai ɗauke da madara da harshen Hausa.

Hotunan yadda Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi, ya kaddamar da raba abinci ga al-ummar jihar Jigawa a jiya Jumma'a...
09/03/2024

Hotunan yadda Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi, ya kaddamar da raba abinci ga al-ummar jihar Jigawa a jiya Jumma'a na tallafin Azumin watan Ramadan, kimamin Shinkafa buhu dubu 150,000 da Masara buhu dubu 150,000 da Taliya kwali dubu 100,000.

DA DUMI-DUMI: Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi ya kaddamar da rabon tallafin kayan abinci na sama da Naira biliyan...
08/03/2024

DA DUMI-DUMI: Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi ya kaddamar da rabon tallafin kayan abinci na sama da Naira biliyan biyu gar mabukata a fadin jihar Jigawa, domin su gudanar da Azumin watan Ramadan cikin wal-wala.

Idan baku manta ba a shekarar da ta gabata, Gwamnan jihar ya raba mak**ancin wannan rabon tallafin bayan janye tallafin man fetir, wanda ya raba kayan abinci da kudade ga rukunin al'umma wadanda su ka hada da masu bukata ta musamman, wadda jimillar kudin yakai Naira biliyan hudu da doriya.

Gwamnan ya raba buhunnan shinkafa dubu 150,000 sai buhunnan masara guda dubu 150,000 da kwalin taliya guda dubu 150,000.

Muhammad Isma'el
SA Publication and Photography.

Mace ta farko da ta fara shan sigari a ƙasar Hausa. Sunanta Ladi bushe-bushe.Ko za ku iya fada mana ƴar wace jiha ce a A...
08/03/2024

Mace ta farko da ta fara shan sigari a ƙasar Hausa. Sunanta Ladi bushe-bushe.

Ko za ku iya fada mana ƴar wace jiha ce a Arewacin Najeriya ??

Hotunan Waliyai Mabiya Addinin Sikh a Kasar IndiyaWanda Mark Hartman Ya Dauka A Lokacin Daya Ziyarci Kasar A Shekarar 20...
08/03/2024

Hotunan Waliyai Mabiya Addinin Sikh a Kasar Indiya
Wanda Mark Hartman Ya Dauka A Lokacin Daya Ziyarci Kasar A Shekarar 2014 📷.

Saliadeen Sicey

DA DUMI-DUMI: A yau Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi zai sake kaddamar da rabon abinci ga talakawan jihar na talla...
08/03/2024

DA DUMI-DUMI: A yau Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi zai sake kaddamar da rabon abinci ga talakawan jihar na tallafin azumin watan Ramadan, kimamin Shinkafa buhu dubu 150 da Masara buhu dubu 150 da Taliya kwali dubu 100.

A wannan shekarar shine Gwamna na farko da zai fara raba irin wannan tallafin a jiharshi, idan baku manta ba kaf Arewa shine Gwamnan farko da ya fara raba tallafin abinci mai yawan gaske har sau biyu tun bai dade da hawa karagar mulkin jihar ba.

Maganar Gaskiya Rigar Lauyoyin Nan Ta Yi Man, Ina Zan Same Ta Jama'a? Tambayar Farida Tofa
08/03/2024

Maganar Gaskiya Rigar Lauyoyin Nan Ta Yi Man, Ina Zan Same Ta Jama'a? Tambayar Farida Tofa

Address

Zoo Road
Maiduguri

Telephone

+2347039629181

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Daily 24 Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Daily 24 Hausa:

Videos

Share


Other Media/News Companies in Maiduguri

Show All