23/10/2021
*ƳAR FILM* (1/10)
-
"Wannan saƙo ne na musamman ga masu harkar film, mazansu da matansu, amma abin yafi karkata ga matan cikin su, kuji tsoron Allah ku canza sana'a, domin lallai wannan ba sana'ar arziƙi bace"
-
"Galibi dai wacce za kaga ta biyewa wannan harkar, ba ilmin addini gareta ba sosai, kuma ba kunya gareta ba, burinta kawai shine ta sayarda mutuncinta domin ta sami kuɗi kuma ta burge jama'a"
-
"Ta manta da cewa wata rana za tayi takaici da nadamar kasancewar ta ƴar film, a lokacin da tsufa yacim-mata, a lokacin da ta tara ƴa'ƴa da jikoki, a lokacin da komai nata ya ƙare, a lokacin da mutane s**a daina yayinta"
-
"Ta manta da cewa waɗannan jama'ar da take burgewa, suke kallonta tana raye-raye, da lanƙwasa murya, ba komai yasa take burgesu ba kuma suke son kallon film ɗinta ba face sai don suna son kallon tsaraicinta da take bayyanarwa"
-
"Ta manta da cewa waɗanda take burgewa ɗin inda ace ke ƴar'su ce k**e yin wannan fitsararriyar harkar da tuni sun hanaki, amma da yake basu damu dake ba, gashi nan kullum sai zuga ki suke yi ke kuma kina tunanin k**ar burgesu k**e yi"
-
"Kina bayyanar musu da wasu sassan jikinki suna jin daɗi, kina bayyanar musu da tsaraicinki kina motsar musu da sha'awarsu, kin manta da cewa hakan kina fusata ubangijinki Allah ne?"
-
"Ko kin san da cewa ubangijinki Allah ya haneki da bayyanar da kwalliyarki ga kowa face sai ga jinsin mutane sha-uku (13)?, to a lokacin da kika tsaya a gaban camera, kin san mutane miliyan nawa ne suke kallonki a wannan yanayin na bayyanar da tsaraici da shigar banzar?" an-noor 31
-
"To kina tunanin milyoyin mutanen da suke kallonki a duniya duk sun cika waɗannan sharuɗan?, ko kuma dai kawai kina zubarwa da kanki mutunci ne domin ki burge jama'a da janyowa kai fushin Allah?"
-
"Na tabbata, shi kansa daraktan da yake zuga ki, yake daɗa dulmiyar dake cikin wannan ƙazamar harkar, bazai taɓa barin ƴar'sa tayi wannan banzar harkar ba ta kasancewa jarumar film, b***e kuma mutanen gari waɗanda s**a san abinda sukeyi