03/12/2023
JAN HANKALI KAN SHARI'AR GWAMNAN KANO.
Yakamata Al'ummar Jahar Kano Susani Cewa Wannan Shari'a da akeyi Tsakanin Gwamnatin Kano ta NNPP da Kuma Gwamnatin Kasa ta APC Akwai Wasu Abubuwa da Yakamata Al'ummar Jahar Kano Su Fahimci Ina aka Dosa.
Wannan Abu Tsarashi aka Zauna Akai Kuma Aka Samu Wasu Bara Gurbi Marasa Kishin Jahar Kano Aka Labe a Bayansu Dan Cimma Wannan Bukata ta Lallai Sai Jahar Kano tabar Hannun NNPP ta Kowane Hali.
Tun a 2019 da Eng.Abba Kabir Yusif Ya Lashe Zaben Jahar Kano Wanda a Wancan Lokacin Aka Shirya Makarkashiya Aka Mayar da Zaben Inconclusive tun a Lokacin S**a So Mayar da Zaben Kano Yazama Yasha Banban da Sauran Jahohi Domin a Arewa Kaf Ita Kadaice Al'ummar Suke Zabar Ra'ayinsu,Wanda Sukuma a Gurinsu Koma Bayane a Gunsu.
A 2023 Tun Kafin Asanar da Cewa Eng.Abba Kabir Yusif Yaci Zaben Gwamnan Kano ba Irin Abunda Wancan Mutanen basuyiba na Ganin Cewa Bai Zamaba,Amma Allah Ya Nuna Musu Ikonsa.
Bayan Wannan Kuma Sai S**a Kudiri Aniyar Cewa Ko Yazama Sai Sun Karbeta a Kotu Hakan Zai Basu Damar Cimma Bukatarsu na Ganin Cewa Zaben Kano Yazama Iri Daya da na IMO da KOGI Domin Kaje Wannan Jahohi Zakaga Cewa Tamkar Babu Gwamnatin Jaha a Jahohin Domin Babu Wani Cigaban Azo a Gani Kasancewar Gwamnatocin Jahar ba Al'ummar Jahar ke Zaba ba A'a Gwamnatin Taraiyya ce ke Zabar Musu ta Hanyar Taron Dangi Yayin Zaben Jahohin Kasancewar ba Bai Daya Bane da Kowane State.
Bukatar su Anan Itace Jahar Kanon dake Basu Matsala a Zabe to Zasu Maidata Matsayin Kamar Kantoma Za'adinga Yi Mata,Domin Duk Lokacin da Za'ai Zabenta to Taren dangi Za'aiwa Kanawa A Kakabamusu Wanda Gwamnatin Taraiyya keso ,Kunga Kenan Sunyi Maganin Karfin da Al'ummar Kano kedashi Wajen Zaben Ra'ayinsu.
Babbar Matsalar Shine Su Wanda Aka Labe a Bayansu Maitar Mulki ta Hanasu Ganin Illar Hakan Basa Duba Mai Zai je da Dawo, Domin Idan Yau Sune Gobe Basu Bane a gun,Kuma Wannan Abun ba Karamar Illa Zaiwa Kanawaba Anan Gaba,Domin A Kano Kowace Gwamnati tana Tsayawa taiwa Al'umma Aiki ne Sakamakon ta Tabbatar da Cewa Zabarsu Akai,Amma daga Lokacin da Muka Koma Kan Wancan Tsari tofah Sai Abunda Muka Gani,Domin Gwamnatin Taraiyya Itace Zata Dinga Zabar Mana Wazai Mulkemu ko Munaso ko Bamaso,Kuma Shima Bazai Mana Aiki ba Domin Yasan ba Zabarsa Mukaiba Iyayen Gidansa S**a Zabesa Domin Cinmma Bukatarsu.
Dan Haka Wannan Fadan Bana Iya 'Yan Siyasa bane,Fadane Wanda Akeyi da Daukacin Al'ummar KANO Wanda Ake so a Karya Mana Kwarin Gwewar da Muke dashi na Wajen Zabar Ra'ayinsu,Dan Haka Yakamata Mu Aje Babban cin Gidan Siyasa da na Addini Mu dubi Makomar Jahar Kano da Kuma Makomar 'Yayan mu da Jikokinmu.
Dole ne Mutashi Tsaye Muyi Addu'a Domin Allah Ya Karemana Jahar mu daga Mugun Nufin da Ake Shirya Mata,Sannan Dole Mufito Muyaki Wannan Tsari Domin Goben mu tai Kyau.
Muna Addu'a Allah Ya Taimaki Kano da Al'ummar Cikinta da Dukkan Masusan Cigaban Jahar mu Ameen,Allah Yaimana Maganin Makiya Jahar Kano na Ciki da Wajenta Ameen.
Daga
Usman Ibrahim (Kwankwason Rijiyar Lemo)