17/02/2023
ABOKIN FIRA
30. Haɗarin Zina
Wata budurwa ce ta nemi izinin mahaifiyarta, tana neman ta amince mata ta riƙa yin Zina.
Uwar ta nuna mata cewa wannan ba sana’ar arziƙi ba ce, abar ƙyama ce al’adance, kuma haramtacciya ce a addinance.
Amma yarinyar ta kafe kan ita dai tana so lallai uwar ta yarje mata, domin tana ganin akwai tagomashin abin duniya mai yawa a ciki.
Uwar ta ce: “Tun da kin kafe sai kin yi, to zan amince miki amma bisa sharaɗi sai kin ci wata jarabawa da zan sa ki yi”.
Cike da murna yarinyar ta ce ta yarda. “Shin mece ce jarrabawar farko?” Uwar ta ce: “Gobe idan gari ya waye,
ki je ƙofar fada, daidai inda Sarki kan wuce. Idan ya fito sai ki yanke jiki ki faɗi, ki sassandare k**ar mai ciwon fyarfyaɗiya. Ki zo ki faɗa min abin da zai faru”.
Kashegari yarinyar ta je qofar fada, ta yi abin da uwar ta faɗa mata. Nan take Sarki ya tsaya. Ya je wurin da ta faɗi da kansa, ya sa aka tashe ta zaune. Sai da ta buɗe idon ta, ta nuna alamar ta farfaɗo, sannan ya tafi.
Cikin murna yarinyar ta koma gida, ta shaida wa mahaifiyarta abin da ya faru. Sannan ta tambayi mece ce jarabawa ta biyu? Uwar ta ce, “Komawa za ki yi gobe, ki maimaita abin da kika yi yau”. Kashegari ta koma, ta sake maimaitawa, amma Sarki bai ko waiwaye ta ba, sai Waziri ne ya je wurin ta.
Da ta nuna alamar ta farfaɗo ya tafi. Ta koma ta faɗa ma mahaifiyarta, tare da neman sanin jarabawa ta uku. Uwar ta ce, “Wannan ce dai za ki koma ki maimaita.”
Da ta je ta yi a rana ta uku, Sarki da Waziri ba wanda ya kula ta, sai Sarkin Dogarai ne
ya je wurin ta, ya sa aka tashe ta zaune. Da ta nuna alamun ta farfaɗo ya tafi abinsa.
Ta koma ta faɗa ma uwar yadda aka yi, tare da tambayar ko jarabawar ta ƙare? Uwar ta ce: A’a, sai kin sake maimatawa sau uku tukuna”.
Yarinyar ta yi ta zuwa tana maimaita abin da ta yi a ƙofar fada. A rana ta shida sai ta je ma uwar tana kuka. Ta faɗa mata cewa, a rana ta huɗu wasu mutane kaɗan daga masu wucewa ne s**a kula ta. A rana ta biyar kuma babu ma wanda ya kula ta sam. A rana ta shida kuwa mutane s**a yi ta zagin ta, wasu ma har s**a sa ƙafa s**a shure ta, tare da gaya mata baƙaƙen maganganu!..
Uwar ta ce: “Madalla. To k**ar yadda kika ga wannan al’amari, haka halin mazinaciya yakan kasance. Komai kyawonta da darajarta, a farkon lamari, Sarakai da masu hannu da shuni ne za su riƙa tarairayar ta. Daga nan sai su bar wa mabiyansu. A hankali darajarta na faɗuwa, har ta koma sai ya-ku-bayi ne za su yi hulɗa da ita. A ƙarshe ma sai ta rasa mai kula ta, sai ƙasƙanci da wulaƙanci da za ta riƙa fuskanta a kodayaushe. Wannan fa, idan har ta yi sa’ar ƙetare haɗuwa da miyagun cututtuka kenan, waɗan da za su ƙarar da ƙazamin abin duniyar da ta tara.
To yanzu za:i yana hannunki. In har yanzu kina nan bisa ra’ayinki, sai ki je ki yi.”
Yarinyar ta ce: “Allah Ya kiyashe ni. Ai komai matsin rayuwar da zan shiga, ba zan yi Zina ba.” Uwar ta ce: “To Allah Ya yi miki albarka!”
Darasi:
Abin da duk ka ga Allah Mahalicci ya haramta ma bawansa, to akwai babban lahani a cikin sa.
✍️ Prof. Mansur Sokoto