17/08/2023
KWAƊAITARWA GA MATA: Ku Riƙa Bari Mazajen Ku Na Tsotsar Nonón Ku Akai-akai, Cewar Ƙwararriyar Malamar Ungozoma
Wata ƙwararriyar malamar Ungozoma Roseline Oladimeji, ta shawarci mata su riƙa bari mazajen su na tsotsar nonón su musamman a lokacin da suke da ciki.
Malama Oladimeji ta bayyana haka ne a wajen taron makon shayarwa da aka yi a jihar Legas, Nijeriya.
”Baya ga ƙara danƙon soyayya da zai daɗa ƙarfi a tsakanin ma’auratan, idan maigida na tsotár nonón matar sa yakan sa bakin nonón ya fito sannan yayi ƙarfin da idan jariri ya zo duniya zai ji daɗin tsotsa da kyau. Haka kuma ana iya saka man shafawa a bakin nonón da dare idan za a yi barci." Inji ta
A karshe ta yi kira ga mata da su riƙa shirin nónuwansu suna gyara su domin shirin shayar da jariri a lokacin da suke da ciki.
- IDON MIKIYA