Jaridar Tauraro Hausa

Jaridar Tauraro Hausa Abude wannan dandaline domin kawo muku labarain duniya.

15/05/2023

រឿង លោកមេទ័ព គួនអុីង កុំកុំ

13/05/2023
10/05/2023
Micheal Taiwo Akinkunmi Shine Wanda Ya Tsara Tutar Najeriya An ƙaddamar da ƙirar Zane kusan 3,000, Amma Wanda A ka zaba ...
01/10/2022

Micheal Taiwo Akinkunmi Shine Wanda Ya Tsara Tutar Najeriya

An ƙaddamar da ƙirar Zane kusan 3,000, Amma Wanda A ka zaba shine Na Michael Taiwo Akinkunmi, dalibi dan Najeriya a Landan. A cikin tutarsa da ya zana kore-fari-kore a tsaye, kore yana nuni da Arzikin noma Da wadata, fari Kuma haɗin kai Da zaman lafiya.

Michael Taiwo Akinkunmi yana da shekaru 23 kacal, lokacin da ya zanawa Najeriya alamar kasa, tuta mai launin kore da fari.

An daga tutar Najeriya a ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 1960 da aka yi bikin ranar samun yancin kai a karon farko.

Michael Taiwo Akinkunmi OFR ma'aikacin Najeriya ne mai ritaya. Ya shahara wajen zana tutar Najeriya, kuma ana kiransa da “Mr. Flag man” An haife shi : 10 Mayu 1936 ( Yanzu Yana da Shekaru 86 A Raye), A Ibadan.

Rubutawa: Saliadeen Sicey

Allah buwayi gagara misali: Likitoci a kasar Brazil sunyi nasarar raba wasu Yara da aka haifa kansu a manne kamar yadda ...
22/09/2022

Allah buwayi gagara misali:

Likitoci a kasar Brazil sunyi nasarar raba wasu Yara da aka haifa kansu a manne kamar yadda ake gani cikin (Hotuna)

Wasu Yan biyu da aka haifa a kasar Brazil da kansu a manne da juna, Likitoci sunyi nasarar raba kawunan nasu bayan anyi musu tiyatar data dauke awanni da dama. Likitocin da s**ayi wannan aiki sun bayyana cewa wannan na daya daga cikin tiyata mafi daukar hankali da aka tabayi a fadin duniya.

Yan biyun masu suna Bernardo da Arthur Lima an dauki tsawon lokaci ana bincike kafi gudanar da tiyatar tasu, Dr Noor ul Owase Jeelani daga kasar England shine ya jagoranci aikin.

Yaran masu shekaru 3, an shafe awanni 33 ana gabatar musu da aikin, Wanda sama da Likitoci kwararru 100 ne s**ayi aikin.

Bernardo da Arthur a yanzu Haka sunaci gaba da samun sauki a asibitin da suke.

CBello

Abin mamaki!!! Bunsuru na shugabantar kauyen Nabankaha a kasar Côte d' Ivoirekabailar Senoufo na matukar daraja wannan b...
16/09/2022

Abin mamaki!!! Bunsuru na shugabantar kauyen Nabankaha a kasar Côte d' Ivoire

kabailar Senoufo na matukar daraja wannan bunsuru a matsayin sarkinsu Kuma jagora a garin Nabankaha dake Cote d ivore. Babu wani dan kauyen da ke iya cutar da shi, maimakon haka ma suna daraja shi. Sunanshi na sarauta Bakoroni na daya.

A wata hira da wani gidan jarida yayi da wani tsoho a kauyen, tsohon ya bayyana cewa Suma haka s**a taso s**a tadda wannan al'ada ta shugabantar da dan Akuya a matsayin sarkin kauyen Kuma jagora. Ya bayyana cewa suna ganin duk randa sabani yasa akaki bawa Dan Akuya damar shugabantar wannan kauye tofa bala'i ne zai sauka a wannan kauye.

Ya Kara da cewa ko wannan dan Akuya rai yayi halinsa, ana daukar wani daga cikin iyalin dan Akuyan domin yaci gaba da zama jagora a kauyan.

Kuma dan akuyar nada damar shiga ko Ina a kauyan nasu batare da wani ya tabashi ko hantararsa ba.

Ainihin kauwo Labarin: Dan malam

Fadada bincike: Jibril Sunusi

Ɗan Takarar Sanatan Shiyyar Katsina A Ƙarƙashin Jam'iyyar PDP, Alhaji Surajo Aminu Makera Ya Ziyarci Mahaifiyar Abokin T...
15/09/2022

Ɗan Takarar Sanatan Shiyyar Katsina A Ƙarƙashin Jam'iyyar PDP, Alhaji Surajo Aminu Makera Ya Ziyarci Mahaifiyar Abokin Takararsa Na Jam'iyyar APC, Kanal Abdu Soja, Hajia Dada Musa Yar'adua A Gidansu Dake Yar'adua Cikin Garin Katsina

Yanzu-yanzu| Gadar Kubarachi A Karamar Hukumar Madobi Ta KaryeWanan Gadar Kubarachi, kenan Wacce ta B***e itace ta Hada ...
11/09/2022

Yanzu-yanzu| Gadar Kubarachi A Karamar Hukumar Madobi Ta Karye

Wanan Gadar Kubarachi, kenan Wacce ta B***e itace ta Hada Karamar Hukumar Kura da Madobi, Dubban Al'umma ne Kullum ke Binta a Dukkan Nau'ikan ababan Hawa Masu tafiya a Kasa.

Tajima tana Barazanar Karyewa Kuma Al'ummar yankunan Kura da Madobi sundade Suna Kiraye kiraye ga Mahunkuntan Wannan Yanki da Sukaimata Agajin Gaggawa Domin ceto ta Daga Nutsewa Cikin Ruwan

Tushe: Vanguard Hausa

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya kaiwa abokinsa ziyara Mallam Audu Sarkiyo Gantsa a gidansa dake Gantsa.Baya...
05/09/2022

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya kaiwa abokinsa ziyara Mallam Audu Sarkiyo Gantsa a gidansa dake Gantsa.

Bayan hadimin Sule Lamido, ya wallafa hotunan ziyarar jama'a da dama nata tofa albarkacin bakinsu, na cewa tsohon Gwamnan bai kyautawa abokin nasa ba, duba da ganin muhalli da kuma yanayin da abokin nasa ke ciki.

Jama'a nata addu'ar, kada Allah ya hadasu da abokin da zai samu dama ya gaza taimakonsu alokacinsa suke bukatar taimako.

Ko meya hana Sule Lamido taimakon abokinsa?

Tushe: RA'AYI RIGA

Tuna baya:A yayin da zankadediyar budurwa Mai Suna Khadija dake zaune a jihar Bauchi ta fada soyayya da samari biyu ta k...
03/09/2022

Tuna baya:

A yayin da zankadediyar budurwa Mai Suna Khadija dake zaune a jihar Bauchi ta fada soyayya da samari biyu ta kuma kasa zabar Wanda tafi kauna a cikin samarin nata.

Hakance tasa mahukunta a garin Giade dake jihar Bauchi s**a shirya zabe Wanda duk wani Dan garin yake da damaryi akan kowa ya zabi zabinsa akan saurayin Daya kamata ya auri Khadija, bayan kammala zaben ne Jami'an zaben s**a bayyana cewa Inusa ne ya zama Wanda yafi samun ruwan kuri'u. Inda Khadija da Inusa s**aje s**aci gaba da soyewa.

Photo Credit: Mubarak Umar

Hotunan Zahra mansur na gaskiya idan ba zaku manta ba a kwanakin baya wani mai suna Musa L Maje yayi amfani da sunan don...
18/07/2022

Hotunan Zahra mansur na gaskiya idan ba zaku manta ba a kwanakin baya wani mai suna Musa L Maje yayi amfani da sunan don damfarar mutane a shafin Facebook

Hon Sageer tarda

Gwamnatin Jihar Kano ta haramta Zirga-Zirgar Babur din Adaidaita Sahu daga karfe 10 na dare zuwa safiya.Cikin wata sanar...
18/07/2022

Gwamnatin Jihar Kano ta haramta Zirga-Zirgar Babur din Adaidaita Sahu daga karfe 10 na dare zuwa safiya.

Cikin wata sanarwa da Kwamishinan yada Labarai Muhammad Garba ya sanyawa hannu, yace an dau matakinne dan inganta harkokin Tsaro a Kano.

Jaridar Daily News 24 ta wallafa Labarin.

Arewa radio

Zuwan Sarauniyar England 🇬🇧 Queen Elizabeth II Kaduna A Lokacin An Tare Ta Da Kyautar Zalbe. A ranar 16 Ga Watan Fabrair...
17/07/2022

Zuwan Sarauniyar England 🇬🇧 Queen Elizabeth II Kaduna A Lokacin An Tare Ta Da Kyautar Zalbe. A ranar 16 Ga Watan Fabrairu 1956.

~ Saliadeen Sicey

Shugaban kasar Guinea Conakry Mamadi Doumabuya kenan yau yayin gyaran tsaftake muhalli na kasa a bakin daga.Babangida Ad...
16/07/2022

Shugaban kasar Guinea Conakry Mamadi Doumabuya kenan yau yayin gyaran tsaftake muhalli na kasa a bakin daga.

Babangida Adam yusuf

KO KUN SAN CEWAR: Alhaji. Ahmad Idris ne tsohon Akanta Janar na Najeriya tareda matasa ƴan jihar Kano da ya samawa aikin...
16/07/2022

KO KUN SAN CEWAR: Alhaji. Ahmad Idris ne tsohon Akanta Janar na Najeriya tareda matasa ƴan jihar Kano da ya samawa aikin ɗamara, Kuma an ce dukkanin su ba dangin iya ba na Baba.

Tabbas ya yi ƙoƙarin sosai domin irin su aka rasa a cikin al'umma, Allah Ta'ala ya saka masa da alkairi ya ƙaro mana irin su.

DAGA Anas Saminu Ja'en

Dokin karfe

Daga jiya zuwa yau jama’a da dama sun ja hankali na akan danyan aikin da wani jami’in KAROTA ya yiwa wannan bawan Allah....
15/07/2022

Daga jiya zuwa yau jama’a da dama sun ja hankali na akan danyan aikin da wani jami’in KAROTA ya yiwa wannan bawan Allah.

Ina sanar da jama’a cewa tun jiya danuwan shi wannan yaro ya same ni kuma inshaAllah zamu yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da cewa ya samu adalchi.

A halin yanzu dai ta lafiyar sa ake yi tukunna. Allah ya taimake mu. Ameen.

Daga Shafin: Lauya mai rajin kare hakkin talakawa, Barista Abba Hikima

Hausawa sunce nakasa ba kasawa ba:Yadda wani Wanda Allah ya jarraba da lalurar kafa yake aikin leburanci domin ciyar da ...
15/07/2022

Hausawa sunce nakasa ba kasawa ba:

Yadda wani Wanda Allah ya jarraba da lalurar kafa yake aikin leburanci domin ciyar da iyalinsa, ya bayyana cewa tunda Allah ya jarrabeshi da Wannan lalura ya fara tunanin wacce sana'a ya kamata yayi a maimakon bara.

Hakance tasa ya fara neman sana'a ka'in da na'in saidai anyi rashin sa'a bashida jali inda hakance tasa yayanke shawarar fara bin abokansa masu aikin gini domin fara sana'ar gini.

Ya bayyana cewa aikinsa kawai shine kwana cement inda ake zuwa ana dauka idan ya Gama kwabawa.

" Idan na kwaba buhu Daya ana bani 200, tun bana fin buhu 4 nakeyin aikin a yanzu Kuma kullum Ina iya kwaba buhu 10. Wato Ina samun sama da dubu 2 kenan a kullum."

Da wakiliiya tabambayesa kowana abune na alfahari Daya Samu a wannan sana'a Wanda bazai taba mantawa ba. Ya bayyana cewa da wanann sana'a yayi Aure Kuma a yanxu haka matarsa ta Haifa Masa Yara 3 Wanda a duk wata yake saya musu madarar salarank irin wacce akeba yayan masu kudi

Yace Babu wani ko a Yan uwansa ko a abokansa Daya taba taimaka Masa da kudin madarar dazai sayawa yaransa 3 dakansa yake diya ta cikin wannan sana'a Mai albarka.

Da aka tambaya sa kome yafi Bata Masa Rai ya bayyana cewa: Akwai wata Rana da s**aje aikin gini shida abokansa suna zuwa sai I jiniyan ya hangosa Yana ganinsa yace wannan fa aka cemasa shima aiki zaiyi, sai inji niyan yace a cire Masa shi daga cikin ma aikata saboda kudi zai biya Kuma wanna gurgun Babu abinda zai iya.

Ya bayyana cewa da aka Masa wannan Kora har kuka yayi. Kuma akoda yaushe ya tuna da wanna lamari sai ransa ya baci.

YANZU-YANZU: Matasan Jihar kano sun farka domin dakile yaduwar masu kwacen waya da kawo karshen harkar  Daba a cikin Ung...
15/07/2022

YANZU-YANZU: Matasan Jihar kano sun farka domin dakile yaduwar masu kwacen waya da kawo karshen harkar Daba a cikin Unguwanninsu, an dauki wannan hoton ne a unguwar kofar agundi ta jihar kano,

Wani kalar fatan Alheri zaku musu?

Mai Gadin Kabarin Manzon Allah SAW, Agha Habeeb Muhammad al-Afari,  Ya Rasu  A Yau Laraba.  Habeeb Muhammad yana daya da...
13/07/2022

Mai Gadin Kabarin Manzon Allah SAW, Agha Habeeb Muhammad al-Afari, Ya Rasu A Yau Laraba.

Habeeb Muhammad yana daya daga cikin manya-manyan tsofaffin masu gadi a Masallacin manzon Allah SAW.

Za'ayi jana'izarsa a yau bayan sallan Magriba.

Allah ya jikan sa da rahma.

~ Tushe: Aminiya

Magana Zarar Bunu.      Prince Ahmad Amoeva Ba zamu baza idanu muna kallon ana son kai kungiyar nan kasa ba daga bangare...
11/07/2022

Magana Zarar Bunu.

Prince Ahmad Amoeva

Ba zamu baza idanu muna kallon ana son kai kungiyar nan kasa ba daga bangaren waddanda aka daura alhakin kula da kungiyar à gwamnatacce da kuma hukamar dake kula da kwallon kafa na ta kasa.

A kan batun wasan mu da Dakada an rainawa mutane hankali da cewa an daki official nasu an kuma fasa wa ma'aikacin su Camera alhalin kowa ya sani anyi wasa ne ba 'yan kallo.
Yah wasan Dakada da kansa s**a fidda official nasu cikin ruwan sanyi kamar yadda wani daga cikin fashin baqin wasanni ya fada wanda Allah cikin ikonsa ya bayyana cewa ya na video clip abun in har PRO na kulub din da waddanda gwamnatin da dora akai zasu karfa ayi amfani dasu wajen appeal.

Banda rainin wayo da son rai da kiyaya à zahiri don me yasa hukumar LMC ba zata bibiyi wasan Katsina ba wanda aka kara lokutan da hankali ba zai dauka ba duba na gaskia.

Dan mai yasa ba za'a dau hukunci akan Dakada ba lokacin da s**a ci zarafin daya daga alkalin wasa.

A makon da ya wuce kowa yaga tsantsar ha'inci inda Dakada taje har gida taci Eyimba à Aba, ko makawo yasan wanann fixing match ne haka zalika Abia .

Banda kisa da kissinar LMC da NPL akan Kano Pillars akwai na jami'an gwabnati daga kan Kwamishina zuwa Kasa.

Muna fada muna kara fada mudin Kano Pillars ta fadi wallahi muma sai mun rama kuma an san kashi 90 na magoya baya matasa ne waddanda s**a haura shekaru 18.

Ya rage ga gwabnati da su shiga su fita su nemo hanyar da zamu tsira suma su tsira.

Prince Ahmad Amoeva
11-07-22

share it pls

UBAN RUBUTU: Wani ma'aikaci kenan ya ke gabatar da Birukkan da ya yi amfani da su da su ka kare a lokacin da yake aiki z...
29/06/2022

UBAN RUBUTU: Wani ma'aikaci kenan ya ke gabatar da Birukkan da ya yi amfani da su da su ka kare a lokacin da yake aiki zuwa lokacin da ya yi ritaya.

Tushe: Dokin karfe TV

DAGAGIRAU: Wasan Saran Kai na unguwar mahaukaci, wanda ya samo asali tun lokacin maguzawa shekarun baya masu yawa. Za Ka...
12/06/2022

DAGAGIRAU: Wasan Saran Kai na unguwar mahaukaci, wanda ya samo asali tun lokacin maguzawa shekarun baya masu yawa. Za Kaga sun sari kansu duk sun ji ciwo kuma babu wani zafi ko damuwa, haka zasu cigaba da mu’amalar su har ciwon ya warke. mai neman Karin bayani sai ya tuntubi sarkin sara kuma sarkin kasuwar Gaya. 08079349853 Kuma a garin na Gaya kadai ake wannan wasan, suma sai dan gado.
Hoto: Sani Maikatanga /

Source: Sani Mai Katanga Photography

TURUWAR MASOYA MANZON ALLAH (SAW) DA S**A FITO DAN NUNA SOYAYYAR SU DA KUMA RASHIN JIN DADIN WASU AZZALUMAN DA S**AI FAT...
11/06/2022

TURUWAR MASOYA MANZON ALLAH (SAW) DA S**A FITO DAN NUNA SOYAYYAR SU DA KUMA RASHIN JIN DADIN WASU AZZALUMAN DA S**AI FATANCI CIKIN JANABI MAFI TSARKI

ALLAH YAKARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH (SAW)

YA ALLAH KADAUKAKI MUSULINCI DA MUSULMAI DA MASU TAIMAKON MUSULINCI

Genetic Engineering: Kimiyyar Juya Kwayoyin HalittaA yau binciken kimiyya ya kai inda za a iya canja jinsin jariri (kafi...
10/06/2022

Genetic Engineering: Kimiyyar Juya Kwayoyin Halitta

A yau binciken kimiyya ya kai inda za a iya canja jinsin jariri (kafin ya samu asalin siffarsa ta cika mutum) daga namiji ya koma mace ko kuma daga mace ya koma namiji.

Wannan kimiyya ta juyin kwayoyin halitta mai suna Genetic Engineering ta na kokari ne wajen juya halittu ko sabunta su daga asalin yadda kwayoyin halittarsu s**a kasance zuwa wasu daban, ko kuma hada su da wasu daban don samar da wata halittar.

A nan halittu masu rai kan iya zama mutane, dabbobi ko tsirrai. Wannan kimiyya kuma tana kokari ne wajen juya asalin kwayoyin halittar wadannan halittu domin samar da wata halitta a cikinsu ko daidaita wata.

Har ila yau da wannan kimiyyar a kan iya hada kwayoyin halittar mutum da na wata dabba tare da rainonsu daga bisani kuma a samu cikakkiyar halittar jinsi biyu, mutum da dabba —kenan mutum-dabba.

Saboda kada a gurbata ilimin, har yanzu gwamnati ba ta rattaba cikakken hannu kan wannan tsarin ba, amma ana ci gaba da gwaji a kan dabbobi.

Muhimman Bayanai
—Za a iya canja jinsin jariri (tun yana ciki) daga namiji zuwa mace, ko kuma daga mace zuwa namiji
—Za a iya hada kwayoyin halittar halittu biyu sai a samu halitta daya; kamar a hada kwayoyin kare (dog) da mage (cat)
—Wannan kimiyyar tana amfani a bangaren magunguna, amfanin gona da makamantansu

—Mohiddeen Ahmad
Scientist, technologist, Founder/CEO of Stackplaza

Zabi gwaninka
10/06/2022

Zabi gwaninka

"Shiru zinari ne lokacin da ba za ku iya,"Tunanin amsa mai kyau ba. "In ji Muhammad Ali.Saliadeen Sicey
10/06/2022

"Shiru zinari ne lokacin da ba za ku iya,
"Tunanin amsa mai kyau ba.
"In ji Muhammad Ali.

Saliadeen Sicey

Sarauniyar Kyau Ta Najeriya Edna Park, A Lokacin Da Ta Yanke Jiki Ta Fadi Saboda Gazawarta A Lashe Gasar Sarauniyar Kyau...
07/06/2022

Sarauniyar Kyau Ta Najeriya Edna Park, A Lokacin Da Ta Yanke Jiki Ta Fadi Saboda Gazawarta A Lashe Gasar Sarauniyar Kyau Ta Duniya. A Birnin Miami Da ke Kasar Amurka 1964.

Lokacin da aka fitar da sunayen wadanda s**a yi takarar karshe, ( Final ) Edna Park ba ta cikin su. Nan take Madam Park ta fadi cikin kuka, Nan Da Nan aka dauke ta daga dandalin. Lokacin da ta kasa daina kukan bayan awa biyu, likita ne ya ba ta maganin kwantar da hankali sannan aka kwantar da ita a asibiti domin duba lafiyarta a daren, kafin daga bisani ta dawo Najeriya. Abin ya ba ta mamaki, ta gano cewa lamarin ya janyo mata ba'a a jaridun Najeriya.

Saliadeen Sicey

Hasashen Kimiyya: Ko Nan Gaba Mutum Zai Iya Bacewa Kamar Aljani?Wani hasashen kimiyya yana kokarin cimma kudirinsa wajen...
06/06/2022

Hasashen Kimiyya: Ko Nan Gaba Mutum Zai Iya Bacewa Kamar Aljani?

Wani hasashen kimiyya yana kokarin cimma kudirinsa wajen kawo wani fasali ta yadda mutum zai iya bacewa daga wani wuri ya isa wani wuri ba tare da amfani da ababen tafiye-tafiye ba, kawai sai dai ya bace daga wani wuri ya isa inda yake so a fadin duniya kamar wani aljani.

Hakika wannan hasashen kimiyya mai suna Teleportation of Matter ya girgiza mutane a inda s**a dauka abun kawai almara ne, wato ba zai taba zama gaskiya ba. Dalilinsu na fadin haka bai wuce ganin cewa mutum zai iya bacewa kamar aljani ba.

Masana s**a ce watakila hasashen zai iya tabbata saboda la'akari da nazariyyar Quantum Entanglement wacce Albert Einstein ya kira da spooky action at a distance; wato duk suna nufin faruwar wani al'amari a fadin kaunu (universe) yana ta'allaka ne da faruwar wani al'amari makamancinsa a wani wuri.

Sannan ana so a yi amfani da kimiyyar Quantum mechanics wajen cimma wannan hasashe ta yadda mutum zai iya bacewa a cikin lokaci kuma ya dawo a cikin lokaci.

Misalin yadda yake a fasahance shi ne kamar yadda ake tura bidiyo daga wani wuri mai nisa zuwa wani wuri kuma ya isa cikin dakiku ta hanyar amfani da yanar gizo, to haka ake so shi ma mutum ya kasance irin bidiyo, ya bace daga nan zuwa can kamar wani aljani.

—Mohiddeen Ahmad
Scientist, technologist, Founder/CEO of Stackplaza

RASUWAR SARKIN KANO ALHAJI ADO BAYERO 2014.A rana irin ta yau a 6 Ga Watan Yuni shekarar 2014, Sarkin Fulanin Kano na 13...
06/06/2022

RASUWAR SARKIN KANO ALHAJI ADO BAYERO 2014.

A rana irin ta yau a 6 Ga Watan Yuni shekarar 2014, Sarkin Fulanin Kano na 13, Alhaji Ado Bayero ya rasu a fadarsa yana da shekaru 84 a duniya, kuma an yi masa jana’iza a makabartar kakanninsa a Gidan Sarki da ke Nassarawa yayin da dubban al’umma s**a fito domin yi masa bankwana na karshe Tare girmamawa.

Ado Bayero da ne ga Abdullahi Bayero, tsohon sarki, wanda ya yi mulki na Tsahon shekaru 27. Ado ya hau karagar mulki ne a ranar 22 ga Oktoba, 1963, inda ya zama sarkin Fulani na Kano na 13 kuma ya zama sarki na 56 a masarautar Kano. Yana daya daga cikin sarakunan da s**a fi dadewa kan karagar mulki a tarihin masarautar. Marigayi Sarkin Kanon Ya Shafe Shekaru 51 A Kan Mulki.

Ya kasance tsohon shugaban jami'ar Najeriya kuma har zuwa rasuwarsa, shugaban jami'ar Ibadan. A ranar 19 ga watan Janairun 2013, wani yunkurin kisan gilla da bai yi nasara ba, ya yi sanadin Rasuwar wasu mutanensa biyu da direbansa da mai tsaron lafiyarsa, da dai sauransu.

Saliadeen Sicey

Garin Dadi na Nesa: Dutsen Asteroid 'Psyche 16' Zai iya Azurta Kowa a Duniyar EarthMasana kimiyyar sararin samaniya s**a...
06/06/2022

Garin Dadi na Nesa: Dutsen Asteroid 'Psyche 16' Zai iya Azurta Kowa a Duniyar Earth

Masana kimiyyar sararin samaniya s**a ce akwai wani Asteroid mai suna Psyche 16 da aka gano da jimawa, sai dai tarin arzikin da ke tattare da shi ne abun burgewa.

Masana s**a ce akwai zallar bakin karfe da gwal da wasu sinadarai masu muhimmancin gaske a jikin wannan Asteroid din. Sannan s**a ce yana tsakanin duniyar Mars da Jupiter.

An yi kiyasin cewa Psyche 16 zai kai Dala tiriliyan dubu sau dubu dari, a kalla kusan $10,000 quardrillion. Masana sun hakaito cewa da za a iya kawo shi duniyar earth, da kowane mutum daya a duniya sai ya zama biloniya.

Masana kimiyyar sararin samaniya da ke hukumar NASA suna shirin aika wa wannan Asteroid din sako a wannan shekarar 2022, sannan akwai yiwuwar ya isa a shekarar 2026. Wannan sako ne irin na masana wanda na'ura ce za ta binciki wannan Asteroid sannan ta rinka aiko da rahotanni.

Abun Lura: Asteroid wani dutse ne da ke shawagi a sararin samaniya, zan kawo rubutu na musamman akan sa.

—Mohiddeen Ahmad
Scientist, technologist, Founder/CEO of Stackplaza

Dan Najeriya da ya taso daga Birtaniya zuwa Najeriya a kan babur ya iso birnin Legas. Idan za ku tuna a ranar 26 ga wata...
29/05/2022

Dan Najeriya da ya taso daga Birtaniya zuwa Najeriya a kan babur ya iso birnin Legas.

Idan za ku tuna a ranar 26 ga watan nan ya sanar da cewa yana sa ran karasowa Legas a ranar 29 ga watan bayan tasowarsa daga kasar Ghana.

Hoto: Adebimpe Olajiga.

Atiku ya lashe zaben dan takaran shugaban kasa na Jam'iyyar PDP.
28/05/2022

Atiku ya lashe zaben dan takaran shugaban kasa na Jam'iyyar PDP.

Sarkin Musulmi Da Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Kasa Sun Jagoranci Tattataunawa Da Malaman Jami'o'in Najeriya ASUU ...
12/05/2022

Sarkin Musulmi Da Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Kasa Sun Jagoranci Tattataunawa Da Malaman Jami'o'in Najeriya ASUU Don Ganin An Kawo Karshen Yajin Aikin Malaman

Sun fara gudanar da tattaunawar tun da misalin karfe 4 na yamma, har zuwa yanzu basu kammala ba.

Akwai alamun za'a iya shawo kan malaman jami'o'in domin dalibai su cigaba da karatu.

Shin wane irin sakamako kuke dakon ji?

Daga Comr Abba Sani Pantami

ASALIN SUNAN KASUWAR SINGER A BIRNIN KANO. Wani Kamfanin Keken Dinkine Na Kasar Indiya Maisuna SINGER Daya Bude Reshe ( ...
23/03/2022

ASALIN SUNAN KASUWAR SINGER A BIRNIN KANO.

Wani Kamfanin Keken Dinkine Na Kasar Indiya Maisuna SINGER Daya Bude Reshe ( Branch) A Kano A Cikin Shekarun 70's/80's A Wajen Da Ake Cewa, Kasuwar SINGER A Yanzu Daga Nan Sunan Wannan Kasuwa Ya Samo Asali ( KASUWAR SINGER) Yanzu Babu Kamfanin Sun Rufe Tuntuni Sunbar Kasuwar Da Sunan.

Tushe: B Salia Sicey

Yaƙin Duniya: Me Ka Sani Game da Ƙasashe?…taƙaitaccen bayani game da Yaƙin Duniya –Rikicin Russia da Ukraine da mu’amala...
25/02/2022

Yaƙin Duniya: Me Ka Sani Game da Ƙasashe?
…taƙaitaccen bayani game da Yaƙin Duniya –Rikicin Russia da Ukraine da mu’amalarsu da sauran ƙasashe

1.0 Gabatarwa
Duk wani dattijon da bai wuce shekaru 70 ba, to haƙiƙa ba shi labarin abun da ya faru a Yaƙin Duniya I da II aka yi, to ballantana kuma matashin da bai wuce 40 ba, ko kuma mu jarirai. Don haka ba mu san yaƙi ba, kuma ba mu san wace illa yake tattare da shi ba. Amma duk wanda ya amsa sunansa “mutum” da ke rayuwa a gabas-maso-arewacin Nigeria, to haƙiƙa ya san “yaƙi” walau kai-tsaye ko ta bayan fage.

An yi Yaƙin Duniya I daga shekarar 1914-1918, an yi na II daga 1939-1945; Ɗan Adam ya kalli tashin hankalin da bai taɓa gani ba, an kashe miliyoyin mutane, an karya tattalin arziƙin duniya, an wahalar da na wahalarwa, an kashe na kashewa, an kuma durƙusar da na durƙusarwa. Haƙiƙa mun ji labari daga iyaye da kakanni abun babu dadi. Ba ma fatan irin hakan ya sake faruwa.

2.0 Me Ke Faruwa a Yanzu?
2.1 Wacce Ƙasa ce Russia?
Russia wata ƙasa ce mai ƙarfin iko a duniya da wani mutum mai suna Vladimir Putin yake mulka a wannan zamanin, karni na 21. Tana da ƙarfin makamai sosai, tattalin arziƙi haɗi da bunƙasa. Wasu abubuwa da za ka iya sani game da ita:
– Ba ta shiri da America da NATO
– Tana ƙawance da China
– Tana da kayan yaƙi ƙwarai da gaske
– Ta ninka Ukraine sau sama da 10 a kayan yaƙi
– Tana da yawan mutanen da s**a kai Miliyan 144

2.2 Ina ne Ukraine?
Ukraine wata ƙasa ce da ke gabashin Turai kuma tana makwabtaka da Russia. Da suna zaune cikin lumana kafin ƙudirin sabon shugaban ƙasarsu ya tayar da hatsaniya. Matashin shugaban mai suna Volodymyr Zelensky ya nuna aniyarshi ta shiga ƙungiyar haɗakayyar ƙasashe mai suna NATO. Maƙwabciyarta Russia ta ce a’a. Ga wasu abubuwa da za ka iya sani game da Ukraine:
– Suna da yawan mutanen da ya kai Miliyan 44
– Ukraine tana maƙwabtaka da Russia
– Tana yunƙurin shiga NATO
– Tana tunanin America da NATO sune ƙawayenta

2.3 Mene ne NATO, G7, UN, EU?
– NATO (North Atlantic Treaty Organization) gamayyar ƙasashe ce da aka samar bayan Yaƙin Duniya II. Akwai ƙasashe 30 a wannan gamayyar, inda suke yunƙurin bayar da kariyar tsaro ga duk wata memba ɗinsu da aka taba. Cikin waɗannan ƙasashe akwai US, UK, Canada, France, Germany, Italy, Portugal, Turkey da sauransu.
– G7 (Group of Seven) wannan ma zauren wasu ƙasashe ne guda 7 da s**a haɗa kai don samun wani tagomashi da tallafin juna a ɓangaren siyasa da tattalin arziƙi. Waɗannan ƙasashen sune: US, UK, Italy, Germany, Japan, Canada da France.
– UN (United Nations) majalisar ɗinkin duniya da aka samar bayan Yaƙin Duniya II, inda ta haɗa ƙasashe 193 a cikin 195 da suke duniya.
– EU (European Union) haɗakayyar ƙasashen Turai da ta ƙunshi ƙasashe 27.
– CSTO (Collective Security Treaty Organization) haɗakayyar wasu ƙasashen Soviet Union da s**a haɗa da Russia, Uzbekistan, Kazakhstan, Tajikistan, Azerbaijan, Armenia da Georgia da sauransu.

2.4 Mece ce Alaƙar America a Cikinsu?
– America ba ta shiri da Russia
– Russia ba ta shiri da NATO da G7
– Russia tana ƙawance da China da CSTO
– China ba ta NATO da G7; a zahiri ba ta ƙawance da US, NATO ko G7

3.0 Mene ne Silar Faɗan Ukraine da Russia?
Ukraine ta nuna ƙudirinta na son shiga NATO amma sai Russia take son katse mata hanzari. Shugaban Russia Putin ya ce ba zai yiwu ba, don ba zai yarda a masa zagon ƙasa ba. Dalilinsa a nan shi ne, idan ya bari Ukraine ta shiga NATO, kenan an kawo masa maƙiyi har gida tunda ba ya shiri da NATO. Zai fi kyau maƙiyinka ya kasance nesa da kai, don suna maƙwabtaka da Ukraine, kenan duk abun da NATO ta ga dama za ta iya yi a Ukraine din don yi wa Russia zagon ƙasa. Putin ya ce ya gano wannan logar, don haka sai ya ƙudiri aniyar shafe Ukraine a doron ƙasa kafin ta yunƙura.

Ukraine ba ta kai Russia ƙarfin soji ba, ko kusa. Ita kawai ta dogara da NATO da kuma America. Amma NATO ta yi shiru, US kuma tana kallon abun da ke faruwa tana alhini.

4.0 Wane Sakamako Duniya Take Jira?
Duniya tana tunanin Yaƙin Duniya III zai iya kaurewa, saboda da zaran NATO da US sun yunƙuro wajen mayar martini ga Russia kan cin zalin da take yi, to haƙiƙa ita ma China da ta kasance ƙawar Russia za ta ƙaddamar da yaƙi a kan NATO da ƙawayenta. Su ma ƙananan ƙwari da ke CSTO za su kai wa Russia agaji a matsayin kara. Wannan kuma shi ake tsoro, domin shi ne zai kasance Yaƙin Duniya III a wannan ƙarnin idan ba a yi sulhu ba.

Ba ma fata ko kaɗan, amma idan hakan ta tabbata, to:
– Nahiyar Europe za ta hargitse
– Nahiyar Asia za ta hargitse
– Tattalin arziƙin duniya zai durkushe
– Africa za ta shiga halin ƙaƙa-ni-ƙaƙa

5.0 Rufewa: Yaƙi Ɗan Zamba Ne!
Yaƙi Ɗan Zamba ne! America ba za ta shiga kowane faɗa ba matuƙar ba ta yi abun da ake ƙira “analysis” ba. Sai ta caje komai ta tabbatar tana da “interest” kafin ta faɗa.

Zan maimaita, babban fatanmu a nan shi ne sulhu.

Allah Ya tsare mu, amin.

–Mohiddeen Ahmad
24th February, 2022

'PATH TO NIGERIAN GREATNESS'By Chief Obafemi Awolowo. A cikin littafin yayi wani Batu Mai daukar hankali a shafi na 8 na...
18/02/2022

'PATH TO NIGERIAN GREATNESS'
By Chief Obafemi Awolowo. A cikin littafin yayi wani Batu Mai daukar hankali a shafi na 8 na littafin.

"Ni, ...., bana cikin kabilar da s**ace ni nasu ne.
Yan NIGERIA da s**a zama na gari kawai ga kabilarsu, ko addininsu ko yan yankinsu.

Wannan sashe na mutane sune munafukai Kuma makaryanta...."

Page 8

02/01/2022

Messi ya kamu da cutar Corona Virus

Yau an fara da Van De Beek, Bruno Fernandes a benci.
23/11/2021

Yau an fara da Van De Beek, Bruno Fernandes a benci.

Marigayi, Kyari Magumeri daga jihar Borno shine soja na farko daga Nigeria daya fara rike mukamin CAPTAIN a sansanin run...
02/11/2021

Marigayi, Kyari Magumeri daga jihar Borno shine soja na farko daga Nigeria daya fara rike mukamin CAPTAIN a sansanin rundunar sojan kasar England a shekarar (1953) Bayan nuna bajinta ta gaske a yakin duniya na 1 dana 2.

An haifesa a shekarar 1897 a jihar Borno, Nigeria, Chari Magumeri ya shiga aikin soja ne a sansanin sojojin rundunar mulkin mallaka mallakin kasar Jamus lokacin Yana da shekaru 16, a yakin duniya na 1 inda ya nuna gagarumar jarumta a wannan yaki, inda aka basa kyautar "Iron Cross 2nd Class" sakamakon jarumtar Daya nuna a yakin da s**ayi a Arewacin Cameroon da kasar England. Hakance tasa rundunar sojan kasar Germany ta daga mukaminsa zuwa mukamin sergeant. A lokacin da sojojin kasa England s**a fara kwace wani fangare na kasar, daga Nan ne aka chanja Masa wajan aiki izuwa sansanin West African Frontier Force a 1917.

Yayi aiki a sansanin sojojin Nigeria ta 5th Bn, Wanda a wannan runduna mahaifinsa shima yayi aiki harna tsawon shekaru 26.

Daga Nan ne aka chanja mishi wajan aiki izuwa India da runduna ta 81st West African Division, inda s**a fafata yaki a Naga Hills da Burma da rundunar soja ta 14th; Magumeri ya samu kyautar MM da BEM a shekarar 1944 sakamakon aiki maikyau da yayi na tsawon lokaci. long and excellent service. Inda ya dawo kasa Nigeria bayan kammala wannan yakuna, RSM Magumeri MM BEM MID ya shiga aikin koyar da sabbin sojoji a Nigeria inda daga karshe yakai mukamin Captain a shekarar 1953 kafin yayi ritaya.

Baza a taba mantawa da magumeri ba a tarihin Nigeria ba. Hakance tasa aka sakawa barikin sojan Lokoja sunan Maigumeri.

Hoton da kuke gani a kasa anyisa ne a shekarar 1953, Royal Sergeant Major Chari Magumeri, a Woolwich Barracks, dake London. A bikin nadin sarauniyar England Queen Elizabeth ta II a kasar England.

jibrilsunusi007

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jaridar Tauraro Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share

Category



You may also like