Hijira tv Nig.

Hijira tv Nig. Hijira tv Nig. Tasha ce dake kawo maku labaru a cikin harshen Hausa.na gida da na wajen Najeriya tar News/Media House
(2)

Zargin damfara: kotu ta buƙaci a dawo shari'ar AA Zaura Kotun daukaka kara da ke zamanta a Kano tayi fatali da hukuncin ...
13/04/2022

Zargin damfara: kotu ta buƙaci a dawo shari'ar AA Zaura

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Kano tayi fatali da hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta Kano ta yanke tare da wanke guda cikin masu zawarcin kujerar gwamnan Kano a jam'iyyar APC, Abdulsalam Abdulkarim (A.A Zaura), wanda EFCC ke zargi da damfarar wani dan kasar Kuwait kudi dalar Amurka miliyan 1,320,000 (Dala miliyan daya da dari uku da ashirin) bisa zargin cewa yana sana'ar gine-gine a Dubai, Kuwait da sauran kasashen Larabawa.

Ku kasance da Nasara Radio (Amanar Talaka) akan mita 98.5 FM, cikin shirye-shiryenmu na labarai, domin jin cikakken rahoton shari'ar da ma sauran labaran Duniya.

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Dr. Abdul'aziz Yari Abubakar, Ya Ziyarci Tsohon Mataimakinsa Malam Ibrahim Wakkala, Wanda '...
10/04/2022

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Dr. Abdul'aziz Yari Abubakar, Ya Ziyarci Tsohon Mataimakinsa Malam Ibrahim Wakkala, Wanda 'Yan Ta'adda S**a Farmaka Dake Kwance A Asibiti

Daga Al'mansoor Gusau

Mai girma tsohon Gwamnan jihar Zamfara His Excellency, Hon. (Dr.) Abdul’aziz Yari Abubakar (Shattiman Zamfara) ya je har Asibitin 🏥 da aka kwantar da Mai girma tsohon Mataimakin Gwamnan jihar Zamfara, Mataimakinsa Malam Ibrahim Wakkala Muhammad Liman (Sarkin Malaman Gusau) a nan Babban Birnin Tarayya Abuja, ya duba lafiyarsa, ya jajanta masa bisa ga harbin da Yan bindiga s**a yi masa ga kafa a cikin Jirgin Kasa a Kaduna.

Mai girma (Shattiman Zamfara) ya roki Allah (SWT) ya baiwa Mai girma Mataimakin Gwamna cikakkiyar lafiya, Allah (SWT) ya tashi kafadunsa, Allah (SWT) ya tsare gaba alfarmar Annabi Muhammad (SAW).

Al’mansoor Gusau,
Babban daraktan yada labarai na mai girma tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Dr. Abdul'aziz Yari Abubakar.

KAMAR YADDA YA SABA MAI GIRMA DAN MAJALISAR JAHA HON AMINU IBRAHIM SAIDU,7 APRIL 2022  Al'ummar karamar hukumar malumfas...
08/04/2022

KAMAR YADDA YA SABA MAI GIRMA DAN MAJALISAR JAHA HON AMINU IBRAHIM SAIDU,

7 APRIL 2022 Al'ummar karamar hukumar malumfashi na godiya da jinjina ga Hon aminu Ibrahim saidu godiya da fatan alkairi bisa rabon kudin gero da suga Wanda yayi a kalla milyan biyar zuwa shidda domin rage hidimar azumi.

Dan majalisar dokoki ta jihar katsina Hon Ibrahim saidu ya bada wannan tallafin fadin karamar hukumar malumfashi birnin ta da kauyen ta.

Rabon ya kasance daga masallatai kwamitin marayu majalisu kungiyoyi da sauran matasa da dattawa shugabanin jam'iyya ,

AlLah Yasaka masa da mafi alkairi.

Wata Sabuwa: Rashin kunya ne Yahya Bello ya tsaya takarar shugaban ƙasa bayan garinsa ne mafi koma baya wajen lalacewa d...
06/04/2022

Wata Sabuwa: Rashin kunya ne Yahya Bello ya tsaya takarar shugaban ƙasa bayan garinsa ne mafi koma baya wajen lalacewa da rashin biyan albashi, " inji jarumi a kannywood"

Daga Comr Haidar Hasheem Kano

Wani matashi dan shekara 25 mai suna Muyiwa na shirin angwancewa da masoyiyarsa yar shekara 85 Matashin ya ce yadda tsoh...
05/04/2022

Wani matashi dan shekara 25 mai suna Muyiwa na shirin angwancewa da masoyiyarsa yar shekara 85

Matashin ya ce yadda tsohuwar take kula da shi ya sa yace kawai yana sonta kuma yana son aurenta

RA'AYI |• CIRE  MALAM NURA KHALID DAGA LIMANCI| NASAN DAMA ZA'A RINA.Wasu daga cikin ƴan'siyasarnan, tunaninsu yayi Kama...
05/04/2022

RA'AYI |• CIRE MALAM NURA KHALID DAGA LIMANCI| NASAN DAMA ZA'A RINA.

Wasu daga cikin ƴan'siyasarnan, tunaninsu yayi Kamanceceniya dana yara ƙanana! daga lokacin da s**aga wani yayi abu yaci banza, kowa zakaga yana rige_rige shima yayi, domin yana ganin babu abinda zai faru, tunda Honorable wane yayi baayi komai ba.

Idan zamu iya tunawa; lokacin da ake ƙoƙarin tozarta mai martaba Khalifa Muhammad Sunusi11, malamai da sarakuna ƴan'uwansa s**aja baki s**ayi Shiru, domin kowa gani yake bashi bane Abin ya Shafa, don haka ayi masa yadda akaga dama.

Lokacin munyi ta kira, malamai da kuma sarakunan Gargajiya kada su bari a tozarta, malami, kuma sarki Dan'uwansu, amma akayi biriss da maganar! Sannan muun ankarar dasu akan: idan aka samu Nasarar sauke Sarki Sunusi11 abun gaba har malamai yaka iya shafa, gashi har lokacin yazo.

Dolene malamai, sarakuna, su murje idanunsu, su fadawa masu mulki gaskiya, inba hakaba, nan gaba, abun zai Wuce duk inda ake tunanin (Allah ya sawaƙa).

Ku faɗi gaskiya, Allah yana tare daku, talakawa suna tare daku, mutanen kirki daga cikin shuwagabanni suna tare daku! Insha Allah bazaku wulakanta ba duniya da lahira.

Daga Jamilu Sama'ila Dandana
Tue5/April/2022.

Ba Dakatar Dashi Muka Yi Yanzu Ba Korarsa Muka Yi Baki Ɗaya.Shugaban kwamati yayi amfani da 'Executive Order' mai lamba ...
04/04/2022

Ba Dakatar Dashi Muka Yi Yanzu Ba Korarsa Muka Yi Baki Ɗaya.

Shugaban kwamati yayi amfani da 'Executive Order' mai lamba 10 daga dakatarwa ta koma Kora

Shugaban Kwamatinmu na Masallacin Sanata Sheikh Sa'idu Muhammad Dansadau ya bayar da sanarwar korar limamin Apo da aka dakatar gaba daya daga Limanci a Masallacin Apo. A saboda haka, shugaban Kwamati yace Malamin da aka Kora ya zo ya kwashe kayayyakinsa da gaggawa.

A matsayinmu na cikakkun 'yan demokaradiyya ba zamu lamunci yiwa demokaradiyya Karan tsaye ba. Don haka a saurari sako na gaba.

Sanarwa daga
Shugaban Kwamati

Daga Yasir Ramadan Gwale

Shin da gaske Buhari ya bawa yan Najeriya mamaki kamar yadda yace kuwa?Daga Comr Haidar Hasheem Kano
03/04/2022

Shin da gaske Buhari ya bawa yan Najeriya mamaki kamar yadda yace kuwa?

Daga Comr Haidar Hasheem Kano

Gwamnan jihar Kogi ya bayyana ƙudirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2023, gwamnan ya naɗa FFK a matsayin...
02/04/2022

Gwamnan jihar Kogi ya bayyana ƙudirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2023, gwamnan ya naɗa FFK a matsayin wanda zai jagoranci kamfen ɗin takarar ta sa.

Wanne fata kuke masa?

Yanzu-Yanzu: Anga jinjirin watan Ramadan a wurare da dama a ƙasar Saudiyya, inda ake saka ran gobe zai zama ɗaya ga wata...
01/04/2022

Yanzu-Yanzu: Anga jinjirin watan Ramadan a wurare da dama a ƙasar Saudiyya, inda ake saka ran gobe zai zama ɗaya ga wata insha Allah.

Daga Comr Haidar Hasheem Kano

Tsohon hadiman gwamnan Kano Salihu Tanko Yakasai wanda ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar APC kwanakin baya, yau dai ya...
01/04/2022

Tsohon hadiman gwamnan Kano Salihu Tanko Yakasai wanda ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar APC kwanakin baya, yau dai ya sake bayyana aniyarsa ta shiga jam'iyyar PRP mai alamar makulli.

Wanne fata kuke masa a siyasance?

Daga Comr Haidar Hasheem Kano

Namijin Duniya Mai Mata 13 Da Ƙawaye 10Mustafa Magambo ɗan Ƙasar Uganda wanda yake da 'ya'ya 176, jikoki 90, Mata 13 da ...
01/04/2022

Namijin Duniya Mai Mata 13 Da Ƙawaye 10

Mustafa Magambo ɗan Ƙasar Uganda wanda yake da 'ya'ya 176, jikoki 90, Mata 13 da Ƙawaye 10.

Wanne fata kuke masa?

Daga Comr Haidar Hasheem Kano

Jiya Ba Yau Ba!Buharin da ya nemi tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya sauka saboda matsalar tsaro, shine...
31/03/2022

Jiya Ba Yau Ba!

Buharin da ya nemi tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya sauka saboda matsalar tsaro, shine dai a ƙarƙashin mulkinsa ake kashe mutane ba dare ba rana shima ya kasa sauka.

Shin son zuciya ne ko adalci?

Daga Comr Haidar Hasheem Kano

Babu Inda Na Furta Cewa Ina Kaunar Rarara, Cewar Khadijah Muhammad
30/03/2022

Babu Inda Na Furta Cewa Ina Kaunar Rarara, Cewar Khadijah Muhammad

HARIN JIRGIN KASAMaigirma Shugaban Sojojin Nigeria Laftanar Janar Faruk Yahaya ya ziyarci gurin da 'yan ta'adda s**a yiw...
29/03/2022

HARIN JIRGIN KASA

Maigirma Shugaban Sojojin Nigeria Laftanar Janar Faruk Yahaya ya ziyarci gurin da 'yan ta'adda s**a yiwa jirgin kasa wanda ya kwaso fasinja daga Abuja zuwa Kaduna hari

Janar Faruk Yahaya ya umarci sojoji su shiga cikin daji domin su kubutar da fasinjojin da akayi garkuwa da su

Wato labari ya tabbata 'yan ta'adda sunyi garkuwa da mutane da yawa

Muna rokon Allah Ya kubutar da duk wanda ya fada hannun Kidnappers

Mutuwa Rigar KowaAbdurrahman Isa Saeed yana ɗaya daga cikin waɗanda s**a rasa ransu yayin farmakin da aka kai jirgin ƙas...
29/03/2022

Mutuwa Rigar Kowa

Abdurrahman Isa Saeed yana ɗaya daga cikin waɗanda s**a rasa ransu yayin farmakin da aka kai jirgin ƙasa jiya.

Allah ya jiƙan wadanda s**a rasa rayukansu baki daya Ameen Ya Allah.

Daga Comr Haidar Hasheem Kano

Duniya SabuwaAngo Bashir mai shadda ya shilla ƙasar Dubai da amaryarsa Hassana domin yawon shakatawa.
29/03/2022

Duniya Sabuwa

Ango Bashir mai shadda ya shilla ƙasar Dubai da amaryarsa Hassana domin yawon shakatawa.

Gidajen Jaridu Suna Fadan Abunda Ke A Bakunan Mutane Ne Kawai Bawai Albarkacin Bakinsu BaHaka Zalika Sune Tsani Wurin Is...
28/03/2022

Gidajen Jaridu Suna Fadan Abunda Ke A Bakunan Mutane Ne Kawai Bawai Albarkacin Bakinsu Ba

Haka Zalika Sune Tsani Wurin Isar Da Sakonnin Halin Da Talakawa Suke Ciki Zuwa Ga Shugabanni

Alhakin Wayar Da Kan Al-umma Kan Halin Da Ake Ciki, Bashin Baki, Duk Ya Rataya Akan Gidajen Jaridu

~ Shehi Falalu Lawal Katsina, Dan Jarida, Mai Fashin Baki.

RA'AYINA A ZAƁEN 2023•|ATIKU ABUBAKAR NE HASKEN DA ZAI YAYE DUHUN NIJERIYA.Daga ranar da maigirma Alhaji Atiku Abubakar ...
26/03/2022

RA'AYINA A ZAƁEN 2023•|ATIKU ABUBAKAR NE HASKEN DA ZAI YAYE DUHUN NIJERIYA.

Daga ranar da maigirma Alhaji Atiku Abubakar (Wazirin Adamawa) ya ƙaddamar da takarar shi, ya haskawa al'ummar nijeriya irin Kyakkyawan hasken da yake ɗauke dashi ga talakan wannnn ƙasa tamu mai albarka.

Cikin bayanai Irinna ilmi Wanda shi kuma ilmi haskene, ya nunawa jama'a irin hasken da yake tafe dashi izuwa garesu, Idan s**a bashi damar zama shugaban ƙasar nijeriya! Muna fatan Jama'a su amsa kira.

Maigirma waziri, zai cire talaka daga cikin duhun yunwa, ya cire ƴaƴan talaka daga cikin duhun jahilci, ya kuma saka nijeriya cikin hasken wutar lantarki, yadda kowa zai fita daga duhu Wanda jam'iyar share Albarkar ƙasa ta jefamu.

Muna Fatan waziri zai ciremu daga matsalar ruwan sha, Za'a kuma Cire nijeriya daga cikin mugun bashin da aka jibga mata, a kawo dawo mana da hasken da ake ganin kasarmu a ciki kafin zuwan gwamnatin APC.

Jamilu samaila Dandana
26/mar/2022.

Photo Credit: Haske Organization.

Matashi Engr Abubakar Mai Gishiri Ya Tsaya Takarar Northwest Youth Leader Na Jam'iyyar NNPP..... Engr Maigishiri Matashi...
25/03/2022

Matashi Engr Abubakar Mai Gishiri Ya Tsaya Takarar Northwest Youth Leader Na Jam'iyyar NNPP.
.... Engr Maigishiri Matashin Wanda Ke Jagorantar NNPP Youth Agenda Kuma Mai Neman Kujerar Shugaban Matasa Na Jam'iyyar NNPP Shiyyar Arewa Maso Yamma.

Chairman NNPP Youth Agenda ya bayyana aniyarsa ne ta tsayawa takarar musamman duba da yadda matasa suke da gudunmawar da zasu bayar a wannan lokacin.

Matashin ya bayyana cewa tun jamhuriya ta ɗaya zuwa ta biyu kusan kashi 70% cikin 100% na waɗanda s**a taka muhimmiyar rawa matasa ne, don haka ba abun mamaki bane a yanzu don muma mun tsaya tare da tunanin bayar da tamu gudunmawar a wannan lokacin.

Najeriya tayi mana komai domin cikinta muka girma kuma muka yi karatu, tun tasowarmu a wannan ƙasar tamu mukayi komai duk domin cigabanta.

Shigo da matasa cikin abubuwan da s**a shafi siyasa zai taimaka tare da farfaɗo da abubuwa masu matukar yawan gaske akan abinda ya shafi matasan musamman a wannan lokacin da muke tunkarar kakar zaɓen shekarar 2023.

Muna tabbatarwa da uwar jam'iyyar mu ta NNPP mai albarka cewa muddin ta bamu dama a wannan lokacin to za'a samar da kyakkyawan cigaba ga jam'iyyar, bugu da ƙari matasa zasu ƙara tsayawa a lunguna da saƙo domin marawa jam'iyyar NNPP baya.

Gina matasa tare da yanke musu ƙishirwar da ke damunsu a bangaren siyasa da basu dama zai taimaka tare da ƙara Kyautata zaton da matasa suke dashi akan shugabancin jam'iyyar.

Wannan takara da na tsaya ta shugaban matasan jam'iyyar NNPP shiyyar Arewa Maso Yamma ba komai bane face dacewar da matasa s**a gani tawa har s**ayi kira gareni dana tsaya wannan takarar tare da neman kujerar shugaban cin matasan na yankin.

Matasa masu tarin yawa sunyi a'manna cewa akwai rawar da zasu taka domin bayar da tasu gudunmawar a siyasance, wannan dalilin yasa tun kafin tsayawa takarar muke tafi tare da jagorantar matasa a ƙarƙashin Youth Agenda.

Muna fatan uwar jam'iyyar NNPP za ta yi abinda ya dace domin bamu dama tare da nuna basirarmu da fasahar da Allah ya bamu a siyasance.

Ƙuri'ar Jin Ra'ayi!Cikin jerin wadannan gwamnonin wanne gwamna ne yayiwa al'ummar jihar Kano aikin kece raini wanda jama...
24/03/2022

Ƙuri'ar Jin Ra'ayi!

Cikin jerin wadannan gwamnonin wanne gwamna ne yayiwa al'ummar jihar Kano aikin kece raini wanda jama'ar Kano ba zasu manta da shi ba?

Ku rubuta sunan wanda kuke jefawa ƙuri'arku a comment section.

Daga Comr Haidar Hasheem Kano

GIMBIYA TA SIYO FORM DIN TSAYAWA TAKARAR SANATAR KATSINA TA TSAKIYYA!!!DAGA: Cmrd Abubakar Iliya.A yau Laraba, 23/03/202...
23/03/2022

GIMBIYA TA SIYO FORM DIN TSAYAWA TAKARAR SANATAR KATSINA TA TSAKIYYA!!!

DAGA: Cmrd Abubakar Iliya.

A yau Laraba, 23/03/2022. 'Yar takarar sanatar Katsina ta tsakiyya (Katsina Central Senatorial Aspirant), Hajia Aisha Isah Katsina (GIMBIYA). Allah ya bata ikon siyo form din tsayawa takarar da take nema ta Sanata.

Gimbiya ta siyo wannan form ne a babbar hedikwar jam'iyyar PDP da ke Wadata Plaza, Abuja. Domin tabbatar da zaman ta cikin jerin 'yan takarar da ke neman wannan kujera a Katsina ta tsakiyya.

Kuma ta kasance itace 'yar takara ta farko da ta fara siyo wannan form a cikin masu neman wannan kujera a jam'iyyar PDP.

Ta samu rakiyar shugaban matasan jam'iyyar PDP na Arewa maso Yamma (North-West PDP Youth Leader), wato Hon. Hamza Yunusa Jby. Da kuma Chairman din ta na kwamitin yakin neman zabe, Hon. Babangida Mainagari, da kuma shugabar matan jam'iyyar PDP ta shiyyar Katsina Zone (PDP Women Leader Katsina Zone), Hajia Hajara Abubakar.

Daga nan ta samu ziyartar ofishin shugaban matasan jam'iyyar PDP na kasa baki daya (PDP national youth leader), Prince Muhammad Kadade. Domin sada zumunci da gaisuwa a gare shi.

Haka kuma, ta samu damar gaisawa da Hon. Jamilu Lion a lokacin da s**a hadu ofishin Youth Leader. Inda shima ya yi mata fatan alkairi da nuna jin dadin shi

Gimbiya ta hadu da masoya da magoya baya masu fatan alkairi a gare ta daga sassa daban-daban na kasar nan wanda bata ko sansu ba.

Allah ya shige mana gaba, ya tabbatar mana da alkairi a cikin wannan hidima. Allah yasa wannnan form ya zama alkairi ga al'ummar Katsina Zone da jihar mu baki daya.

Allah yasa ya zama silar cin zaben jam'iyyar mu ta PDP. Ameen.

Fata nagari lamiri...

SANATA AHMED BABBA KAITA | KISHIN TALAKA KO NEMAN MAFITAR SIYASA.A karanta, Amma rubutun da yawa.Sanata Ahmed Babba Kait...
23/03/2022

SANATA AHMED BABBA KAITA | KISHIN TALAKA KO NEMAN MAFITAR SIYASA.

A karanta, Amma rubutun da yawa.

Sanata Ahmed Babba Kaita shine; Sanatan dake wakiltar Katsina ta arewa (Daura zonee) a majalisar dattijai ta nijeriya, Inda shugaban ƙasar nijeriya Shugaba Buhari ya fito.

Wanda shine Sanatan da aka zaba bayan rasuwar, Marigayi Madawakin daura! Idan bamu manta ba, zuwansa a majalisar ya nuna cewar: shi yazone domin kare muradun Shugaban ƙasar nijeriya muhamdu Buhari.

Idan muka waiwaya baya, lokacin Sanata Bukola saraki, yana shugaban majalisar, har akwai Lokacin da sanatan ya mike a zauren Majalisar, da nufin kare Gwamnati akan Ƙalubalantar gwamnatin da akeyi akan Matsalar tsaro, Inda shugaban majalisar ya tsawatar masa, da faɗin wasu kalamai dake nuni da sanatan baisan tsarin majalisar ba (Educate yourself).

Duk da Irin ɓarna, da Kuma ta'adi da wannan Gwamnatin takeyi, sanata bai taɓa fitowa a zauren Majalisar ya nunawa gwamnati Cewar; a Gyara ba, domin lokacin yana Neman shiga ne wurin shugaban ƙasa, da kuma Manyan Nijeriya.

Sanatan ya Fara fitowa da nuna shi Masoyin talaka ne bayan da aka fara gabatar da zaben shugabannin Jam'iyar APC daga matakin ƙasa (Ward level) Inda ya tabbatar da yasamu (Political miscalculation) Inda yaga an raba, ya tashi zerro.

Daga lokacin Sai ya fito da Farfaganda, ta gaɓar da takeyiwa talakawan jihar Katsina ƙaiƙayi Wato; zaɓen Ƙananan hukumomi da gwamna Aminu Bello Masari ya gagara yayi! Sai ya fake da wannan ya Fara s**ar Gwamnatin jihar Katsina, da nufin ya samu ya tsarkake kanshi, domin talaka ya Rubuta sunanshi da ruwan zinare.

Ya Fahimci irin magribar jaki da yayi a siyasa, bayan gwamnatin jihar Katsina ta ayyana gabatar da zaɓen na ƙananan Hukumomi! Kenan lokacin Murna ya kamata yayi, Inda zaɓen ne Yakeso ayi. Anayi ya tashi babu komai,ya cigaba da nuna adawar shi a fili da gwamnatin jihar Katsina.

Idan domin kishin talaka yakeyi, daga lokacin daya fahimci, gwamnatin jam'iyar APC Bata Kaunar Talaka sai ya fice daga ita, ya dawo jam'iyar PDP! Amma yanzu an kwashi watanni, sai girgiza Inuwa yakeyi, domin kowa yasan Akwaishi! Idan APC ta razana, ta nemeshi a bashi wani Abu yayi shiru, Idan PDP ta nemeshi tayi masa Alƙawurin Wata kujera, ya koma ciki.

Sanata Ahmed Babba kaita, neman mafita yakeyi, bawai kishin Tallakawan jihar Katsina ba! Idan mutum Zai bishi ya bishi domin siyasa, Shine Magana.

Zan cigaba insha Allah.

Jamilu Sama'ila Dandana
23/3/2022.

Ruwa Ya Ƙarewa Ɗan-kada!Daga Comr Haidar Hasheem KanoA wannan gaɓar zamu iya cewa kallon da mutane suke yiwa rogo a mats...
23/03/2022

Ruwa Ya Ƙarewa Ɗan-kada!

Daga Comr Haidar Hasheem Kano

A wannan gaɓar zamu iya cewa kallon da mutane suke yiwa rogo a matsayin kitse yanzu ya bayyana kowa ya gane rogo ne ba kitse ba tsuransa.

Hujjoji goma da s**a gagara rushewa daga mutanen Osinbajo tun daga masu tallarsa da yan kayi nayi masu neman na tuwo da Osinbajo ɗin, sun matuƙar dulmiyar da lissafinsu tare da mayar da su baya.

A duk lokacin da aka kawo hujjoji to hujja ce take kore hujja ba molanka da surutan banza marasa amfani ba, domin yanzu mutane hujja suke so a bayyane ba roman baka ba kamar yadda aka yi a mulkin Shugaba Buhari.

Babu wani mai tallar Osinbajo da zai iya buɗe baki yace chanchanta ce ta sanya yake tallarsa, domin kuwa baka isa kace kaf Arewacin Najeriya Osinbajo yafi kowa chanchanta ba indai ba miyarka kake gyarawa ba, amma idan ita kake gyarawa to ka iya fadin abinda yafi haka domin neman na ƙashin miya.

Kyautata zato da mutane suke da shi akan Osinbajo ya fara zama tarihi domin illarsa da mutane suke gani kai tsaye tunda aka zayyana hujjojin da aka kasa rushewa, masu bawa Osinbajo kariya domin gyara kuna buƙatar ku ɗauki kowacce gaɓa kuyi sharhi da fashin ɓaki akanta domin mutane su gane hujjarku ta kore wancan hujjar da aka kawo a zayyane.

Ita Najeriya tana buƙatar shugaban ƙasa ne mai jinƙai da tausayi ba wai wanda ke nuna fifiko ga ɓangarensa da kuma take wani ɓangare ba, don Osinbajo yana matsayin Pastor hakan ba shine zai bashi damar nuna fifiko da soyuwar ɓangarensa ba tunda Najeriya yake fatan mulka ba kudancin Najeriya ka ɗai ba.

Najeriya ƙasa ce da ta haɗa yaruka da masu addini kala-kala, don haka nuna fifiko da ɓangaranci zai zama koma baya ga duk ɗan takarar da burinsu aikata haka ga al'ummar Najeriya.

Osinbajo mutum ne da hujjoji s**a bayyana shi a matsayin mutumin da ba ma zai iya yiwa kowa adalci ba, domin duk abinda kaga yayi to akwai manufar yinsa a ƙasa, hatta gidan marayun da ya gina a Borno da wasu abubuwa da yayi dukkansu hujjoji sun bayyana manufar yinsa a zayyane ba molanka irin na masu kare shi ba.

Idan marubuci ya kafa maka hujja, ko ka kira shi da munafuki ko maƙaryaci kai ko me zaka kira shi ba zai yi tasiri ba muddin ba warware hujjojin da ya kafa maka kayi ba, yanzu zamani ne na ilimi da wayewa ba lokutan da wani zaiyi molanka ya rubuta shaci faɗinsa ba.

Hujja ita take kore hujja ba molanka ko yarfe ba.

Ra'ayina Akan Hujjojin Da Aka Zayyona Akan Osinbajo.

Engr Abubakar Maigishiri Ya Taya Hon Umar Haruna Doguwa Murnar Zama Sabon Zaɓaɓɓen Shugaban Jam'iyyar NNPP Na Kano.Yayin...
23/03/2022

Engr Abubakar Maigishiri Ya Taya Hon Umar Haruna Doguwa Murnar Zama Sabon Zaɓaɓɓen Shugaban Jam'iyyar NNPP Na Kano.

Yayin da yake taya Hon. Umar Haruna murna, Engr. Maigishiri ya nuna ƙoƙari da bajintar da jamiyyar tayi na zaƙulo jajirtaccen matashi a matsayin shugaban jam'iyyar.

Maigishiri ya bayyana cewa tabbas wannan shine ajiye ƙwarya a gurbin ta domin hakan da jamiyyar tayi tamkar ta sake busawa jam'iyyar rai ne a fadin jihar Kano tare da sake bawa matasa ƙwarin gwiwa.

A matsayina ɗan takarar dake neman kujerar shugaban matasan jam'iyyar NNPP shiyyar Arewa Maso Yamma, tabbas zaɓen Hon Umar Haruna ya ƙaramin karsashi tare da ƙarfin gwiwa cigaba da fafutukar da muke yi na kawo tabbataccen sauyi a siyasance.

Engr Maigishiri ya ƙara cewa a matsayina na matashi kuma wanda yake jagorantar ƙungiyar "NNPP NATIONAL YOUTH AGENDA" wannan tamkar dama ce da muka samu domin karkato da hankulan dubban matasa dake ƙarƙashin wannan ƙungiya tamu tare da zaburar da su wajen yin abinda ya dace.

Maigishiri ya ƙara nuna goyon bayansa da jindadinsa yayin da yake nuna nasarar da Hon Umar Haruna ya samu a matsayin tamkar kwalliya ce ta fara biyan kudin sabulu.

YANZU-YANZU: Cikin Wannan Daren Abdul'aziz Yari Abubakar, Ya Gana Da 'Yan Majalisun Wakilan Nijeriya Akan Kudurinsa Na Z...
22/03/2022

YANZU-YANZU: Cikin Wannan Daren Abdul'aziz Yari Abubakar, Ya Gana Da 'Yan Majalisun Wakilan Nijeriya Akan Kudurinsa Na Zama Shugaban Jam'iyyar APC Na Kasa

Daga: Al'mansoor Gusau.

Mai girma tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Dan takarar neman Shugabancin Jam'iyyar APC na kasa Hon.Abdul'aziz Yari Abubakar (Shattiman Zamfara) ya gana da 'yan majalisar wakikab Nijeriya domin neman goyon bayan su akan kudurinshi na zama shugaban Jam'iyyar APC na kasa.

Idan baku manta ba, yau sauran kwanaki Hudu a gudanar da gagarumin taron Jam'iyyar APC na kasa wanda zai gudana a ranar Asabar da Lahadi 26, 27 a babban birnin Tarayya Abuja.

Muna yiwa mai girma tsohon Gwamnan Zamfara Abdul'aziz Yari Abubakar, fatan Nasara na zama shugaban Jam'iyyar APC na kasa, a gagarumin taron da za a gudanar.

Matashi Abdullahi Sidi Ali Ya Shiga Cikin Jerin Masu Neman Kujerar Shugaban Matasan Jam'iyyar APC Shiyyar Arewa Maso Yam...
22/03/2022

Matashi Abdullahi Sidi Ali Ya Shiga Cikin Jerin Masu Neman Kujerar Shugaban Matasan Jam'iyyar APC Shiyyar Arewa Maso Yamma.
.. Matashin wanda tun a farko ya bayyana aniyarsa da burinsa na tsayawa takarar shugabancin matasan jam'iyyar APC a zaɓen cikin gida da za'ai.

Abdullahi Sidi yace biyayya da ƙaunar da muke yiwa uwar jam'iyyar mu ta APC shiyasa muka karɓi hukuncin da ta yanke na zoning ɗin da tayi wanda hakan ya sa shugaban matasan jam'iyyar ba zai fito daga yankin Arewa maso yamma ba.

Sidi ya kasance jakadan zaman lafiya ne, kuma ya kasance memba mai biyayya ga jamiyyar APC tun shekarar 2014.

Matashin wanda shine daraktan tsare-tsare na kungiyar "Kano Youth Political Forum", matashin wanda yake da ƙwarewa da gogewa a fannin siyasa tun daga matakin ƙasa zuwa sama.

Sidi shine matashin da matasa masu irin shekarunsa da abokan hamayya daga jam'iyyun adawa s**a ɗauke shi a matsayin "political mentor" kuma ake masa fatan nasara duba da irin iya mu'amalarsa da yadda yake gudanar da harkokinsa a siyasance.

Bisa shawarwari daga manyanmu da abokan gwagwarmayarmu waɗanda suke da fata da burin ganin mun kawo sauyi a siyasance, shiyasa na yanke shawarar tsayawa takarar shugabancin matasan jam'iyyar na shiyyar da na fito wato Arewa maso yammacin ƙasar nan.

Yankunan sun haɗa da jihohi bakwai irinsu Kaduna, Kano, Jigawa, Katsina, Zamfara, Kebbi, Sokoto, wannan sune shiyyar da muka fito kuma muke fatan yin nasara ciki insha Allah.

Na bi jerin masu neman takarar wanda tuni na sayi Form tare da bin jerin waɗanda aka tantance a jam'iyyance domin tsayawa wannan takarar.

Babban burinmu shine tallafawa da inganta duk wani abu daya shafi matasa daga matakin farko zuwa mataki na sama insha Allah.

Babban burinmu shine inganta kowanne harka da ta shafi matasa musamman a siyasance wanda hakan shine ƙashin bayan tsayawa takararmu.

YANZU-YANZU: Abdul'aziz Yari Abubakar, Ya Isa Majalisar Nijeriya domin neman goyon bayan 'Yan Majalisun akan Kudurinsa n...
22/03/2022

YANZU-YANZU: Abdul'aziz Yari Abubakar, Ya Isa Majalisar Nijeriya domin neman goyon bayan 'Yan Majalisun akan Kudurinsa na zama Shugaban Jam'iyyar APC na Kasa

Daga: Al'mansoor Gusau.

Mai girma tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Dan takarar neman Shugabancin Jam'iyyar APC na kasa Hon.Abdul'aziz Yari Abubakar (Shattiman Zamfara) ya isa majalisar dokokin Nijeriya domin neman goyon bayan 'yan majalisun kasar akan kudurinshi na zama shugaban Jam'iyyar APC na kasa.

Idan baku manta ba, yau sauran kwanaki Hudu a gudanar da gagarumin taron Jam'iyyar APC na kasa wanda zai gudana a ranar Asabar da Lahadi 26, 27 a babban birnin Tarayya Abuja.

Muna yiwa mai girma tsohon Gwamnan Zamfara Abdul'aziz Yari Abubakar, fatan Nasara na zama shugaban Jam'iyyar APC na kasa, a gagarumin taron da za a gudanar.

Sadiya Umar Sabuwa Kuma Fitacciyar Jaruma A Masana'antar Kannywood.Wannan Itace Sa'adiyya Umar, Yar Kabilar Nufawa Wacce...
22/03/2022

Sadiya Umar Sabuwa Kuma Fitacciyar Jaruma A Masana'antar Kannywood.

Wannan Itace Sa'adiyya Umar, Yar Kabilar Nufawa Wacce Tafi To Daga Garin Minna Jihar Niger, Sabuwar Jarumar Da Tauraruwarta Ke Haskawa A Farfajiyar Masana'antar Fina-Finai Ta Kannywood.

Ta Taka Rawar Gani A Shirye-Shirye Masu Dogon Zango Kamar (ADUNIYA) Da (SANDA) Da Sauransu, Ta Kware Matuka Wajen Hawa Wakokin Soyayya, Itace Jarumar Da Mawaki Kawu Dan Sarki Yayi Wakar " Sanadinki" Da Wakar "Ingallo" Wadda Take Tashe.

Masu Karatu Wane Fata Zaku Mata?

DR MUSTAPHA MUHAMMAD INUWA YA GANA DA ƘUNGIYOYIN SIYASAR JAHAR KATSINA DANA GIDANSHI AKAN TAKARAR SA TA NEMAN KUJERAR GW...
21/03/2022

DR MUSTAPHA MUHAMMAD INUWA YA GANA DA ƘUNGIYOYIN SIYASAR JAHAR KATSINA DANA GIDANSHI AKAN TAKARAR SA TA NEMAN KUJERAR GWAMNAN JAHAR KATSINA A 2023.
.. Inda yayi jawabi gaban dukkannin ƙungiyoyin Siyasa wanda s**ai gauro s**ai mari kan ya fito takarar Gwamnan Jahar Katsina a 2023.

Yayi ganawar Da Sama da Ƙungiya 1,300 yan Siyasar cikin gidan shi, wanda s**a hada da ƙungiyoyin matasa, Dalibai, Da manyan mutane stakeholders dadai sauransu. Inda ya shaida musu cewa ya masa kiran su, kuma ya amince zaiyi takarar Gwamnan Jahar Katsina.

Taron ya gudana bisa jan ragamar Abdullahi Aliyu Yar'adua Director Press na Ofishin Sakataren Gwamnatin Jahar Katsina

Akwai mutane da dama da s**ayi magana A wannan taro inda s**a hada dashi darakta kamfen na Dr Mustapha Muhd Inuwa Wato Abubakar Tsanni inda yayi bayani cewa to tabbas ya fito takara kuma sunyi alkawari zasuyi aiki kafada-da-kafada da sauran ƙungiyoyin domin cimma wannan aikin alheri.

A wurin taron An zabi Wasu zakwakuran matasa inda s**ayi magana A madadin sauran ƙungiyoyin, cikin wanda s**ayi magana akwai "Hamisu Hara" DG Zawiyya Alheri inda ya bayyana tabbas ƙungiyoyi sunyi ta kiran Dr Mustapha ya fito takara to yau ya amsa kira abinda ya rage mana mu koma mu gayawa jama'a waye Dr Mustapha domin ta hakane zamu Ida aikin da muka dauko na ganin Ya zama Gwamnan Katsina a 2023 insha Allah.

Abdulrahaman Haruna Danja Yayi bayani DG Inuwalikesmind inda ya bayyana cewa aikin dake gaban Waɗannan ƙungiyoyi bayan fadi-tashi na kiran Dr Mustapha Muhd Inuwa ya fito takara to aikin dake gabanmu shine mu fadakarwa cewa Dr mutumin kirki ne, Sannan mu gayamasu Ajendodin shi kamar haka÷

-Gyara fanni Ilimi
-Tabbatar da tsaro
-Samarwa jaha kudin shiga
-Gyara fannin Tattalin arziki da kuma samawa marassa aikiyi wata madogara/Da kuma nemo hanyoyi da zasu bawa matasa aikin yi da walwala da jin dadinsu a cikin al'umma.

A karshe Dr Mustapha Muhd Inuwa yayi bayani inda ya godewa Waɗannan ƙungiyoyi gamida yan Media masu rajin siyasar sa, Inuwa ya kara da cewa bai fito takarar Gwamnan ba domin ya samu wani abu sai domin al'ummar jahar Katsina.


CONTINUITY AGENDA

Tambuwal Ne Zai Iya Gyara Yardar Da Aka Bata Tsakanin Arewa Da Kudu, Tare Da Dinke Duk Wata Barakar Da Ke Tsakani, Inji ...
18/03/2022

Tambuwal Ne Zai Iya Gyara Yardar Da Aka Bata Tsakanin Arewa Da Kudu, Tare Da Dinke Duk Wata Barakar Da Ke Tsakani, Inji Yemi Arokodare

Daga Comr Abba Sani Pantami

Tsohon dan majalisar wakilai, Yemi Arokodare ya roki 'yan Najeriya da su baiwa gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal damar shugabantar kasar da kawo sauye-sauye don inganta kasar.

Arokodare, wanda ya kasance a majalisar wakilai daga 2003 zuwa 2007 kuma shugaban kwamitin majalisar kan labarai, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa a Abuja a ranar Alhamis, 17 ga watan Maris.

Ya ce: “Tambuwal na da jajircewar shugabanci, kankan da kai da kuma juriya don sauya fasalin kasar, gyara ta da kuma ceto ta.”

Ya kuma roki jam’iyyar PDP da ta baiwa gwamnan na jihar Sokoto kuma tsohon kakakin majalisar wakilan damar zama dan takararta.

A cewarsa: “Gwamna Tambuwal ya yiwa majalisar wakilai jagoranci mai kyau, ya nuna adalci da daidaito a shugabancinsa; yakamata mu bashi dama domin ya gyara yardar da aka bata tsakanin Arewa da kudu.

“Idan za mu iya ba Tambuwal gagarumin dama na shugabancin wannan kasa mai albarka wacce aka yiwa riko mara kyau, lallai mu kwana da sanin cewa wannan mutumin zai hada kan Arewa da kudu domin gyara Najeriya.

“Ya taba jagorantar yan majalisa daga yankuna daban-daban na kasar, kuma ya nuna shugabanci nagari da ba a saba gani ba, wanda ya sanya shi a mizanin wanda zai iya jagorantar Najeriya bisa adalci da daidaito.

“Najeriya na bukatar a sauya fasalin ta tare da sabbin shugabannin da aka gwada kuma aka aminta da su wadanda za su iya ciyar da kasar gaba, kuma Tambuwal mutum ne da za mu iya yarda da shi a kan hakan.

“Tambuwal ya jagoranci kungiyar gwamnonin PDP da kyau; ya yi alaka da shugabanni da ‘yan jam’iyyar cikin mutuntawa; shi ne irin shugaban da zai iya hada kan kasar.”

Kungiyoyin Matasa da ke fadin Arewacin Najeriya sun bayyana kwarin gwiwarsu na ganin Sadiq Fakai ya zama memba cikin kwa...
18/03/2022

Kungiyoyin Matasa da ke fadin Arewacin Najeriya sun bayyana kwarin gwiwarsu na ganin Sadiq Fakai ya zama memba cikin kwamitin gudanarwa na jam'iyyar APC na ƙasa.

Kungiyayoyin sun yi kira ga masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC, musamman na shiyyar Arewa-maso-Yamma na kasar nan da su taka muhimmiyar rawa, da kuma bukatar a yi aiki da su wajen bayar da goyon baya da kuma tabbatar da hazikin matashin shugaban a fannin siyasa na dimokuradiyya ta gaskiya, wanda ya nuna matsayin kasa a matsayin Shugaban Matasan APC a shiyyar.

Sadiq Fakai ya jajirce wajen hada kan matasa a fadin shiyyar ta hanyar ayyuka da shirye-shiryen da suke karawa jam’iyyar karfi fiye da da.

Ya kamata a lura cewa, kungiyoyin matasa sun kasance suna jin dadin tsarin jagoranci nasa duba da kishin kasa, sadaukarwa da hadin kai daga matashin Abubakar Sadiq Fakai a matsayin shugaban matasan jam’iyyar na shiyyar. Yana da kyau a san cewa jihar da ya fito (jihar Kebbi) ba ta taba samar da dan kwamitin aiki na kasa ba tun kafuwar jam’iyyar don haka akwai bukatar a ba wa irin wannan matashi damar shiga kwas din da ya riga ya kware akai.

Daga karshe kungiyar ta yi kira ga masu ruwa da tsaki da su duba wannan al’amari tare da yin abin da ya kamata domin daukacin matasan jam’iyyar APC a fadin kasar nan su ji dadin zama duba da yana daya daga cikin manufofin jam’iyyar APC.

18/03/2022

Babu Wanda Ya Chanchanta Da Zama Shugaban Ƙasa 2023 Kamar Gwamnan Jihar Bauchi.

Gwamnan jihar Bauchi Sen. Bala Mohammed Ƙauran Bauchi, shine wanda yafi kowa chanchanta a kakar zaɓen 2023.

Mayar da tsofaffin gine-gine na tarihi zuwa sauyawa su tare da mayar da su ga sabon fasali a faɗin jihar Bauchi.

Samar da hanyoyi masu inganci a lungu da saƙo na jihar Bauchi wanda Sen Bala Muhammad yayi.

Duba da yadda yake shiga cikin talakawa da yin cuɗanya da su a wuraren bukukuwansu ko kai musu ziyara ƙafa da kafa a kowanne lokaci wannan ya ƙara nuna chanchantarsa a fili domin shine ya san damuwar talakawa.

Gaisuwa gare ku,'Yan uwa da abokan arziki.Na aiko da wannan sako ne don in sanar muku da kudirina na fara tattaunawa kan...
16/03/2022

Gaisuwa gare ku,'Yan uwa da abokan arziki.

Na aiko da wannan sako ne don in sanar muku da kudirina na fara tattaunawa kan burina na tsayawa takarar gwamna a wannan jiha tamu ta Kaduna a zabe mai zuwa.

Allah Madaukaki ya ba ni daman yin aiki da baya gaya-goya-marayu, uba kuma jajirtaccen gwamnanmu na wannan jiha, Malam Nasir El-Ruaf'i tsawon shekara bakwai don ganin tabbatuwar kyakkyawan kudirinsa na ciyar da jiharmu gaba. Ina da tabbacin hatta masu hamayya za su ba da shaida kan cewa ba a tab samun irin cigaban da aka samu a Jihar ba kamar Yadda aka samu daga shekara ta 2015 zuwa yau a tarihin kafuwar Jihar Kaduna.

Hakika ina mai cike da alfahari da mika dumbin godiya kan wannan dama da Malam Nasir El-Ruaf'i ya ba ni, ina da kyakkyawan darussa da na koya karkashin jagorancinsa. Na kuma sami daman ba da tawa gudumawa wajen samar da dumbin cigaban da jiharmu ta samu a cikin shekara bakwai kacal.

Da farko na yi kwamishina,daga nan,cikin ikon Mai Duka,na zama shugaban ma'aikatan Jiha, sannan na sake yin kwamishina. Wannan ya ba ni damar yin ruwa da tsaki da saka hannu cikin dukkan wasu tsare-tsare da gwanatin Jam'iyyar A.P.C. ta aiwatar. Domin haka ne nake da gwarin gwiwar cewa ina da gogewar da ta dace don cigaba da gudanar da ayyukan cigaba a jiharmu mai albarka.

Kwadayin tabbatuwar cigaba ta fuskar jagoranci musamman ciyar da Jihar Kaduna gaba shi ne ke kara min shaukin yin takarar kujerar gwamna a zaben 2023. A matsayina na Dan Jihar Kaduna mai rajin samar da cigaban Jihar,zan yi matukar takaicin ganin dukkan cigaban da Jihar ta samu ya ruguje.Don haka ne nake gurin cigaba da ba da gudumawata domin tabbatar da ganin dorewar cigaban da muka shaida a shekara bakwai da ta gabata.

Kudirina na fari shi ne ganin dorewar ayyukan alkhairi da gwamnanmu ya fara.Sannan kuma mu dora kan wannan domin fadada ayyukan cigaba a wannan jiha ta fuskar bunkasa tsaro da habaka tattalin arziki da samar da walwala ta hanyar ingantattun ayyuka da shugabancin da babu kumbiya-kumbiya.

Na dauki watanni ina nazari kan irin kalubalolan da Jiharmu ke fuskanta da ma wadanda ka iya bijirowa nan gaba kuma ina da tsare-tsaren da ,in Allah ya Yarda, da za su shawo Kan su. Zan sanar da alumma nan gaba kadan

Domin haka, a makwanni masu zuwa, ina da niyyar kai ziyara don neman shawarwari gare ku. Ina barar gudumawar shawarwarinku da ra'ayoyinku da tunaninku du addu'o'inku wanda su ne kashin bayan nasararmu da ikon Mai Duka.

Da wannan nake cewa samun kwarin gwiwa daga gare ku da addu'o'inku abubuwa ne masu matukar muhimmnci a wannan tafiya.

Ina mika godiya mara misaltuwa ga dai-daikun mutane da rukunonin al'umma wadanda s**a yi ta ba da irin tasu gudumawar ba dare ba rana wajen ganin cikar wannan buri. Godiya gare ku maras adadi.

Wannan tafiya ce domin al'umma. Don haka muke fatan dukkan jama'a za ta shigo cikinta tun daga matakin farko domin Dora ta kan kyakkyawan turba.


Danna wannan shafi domin yin rijista www.dattijo.ng .Mu fadi tare mu tashi tare domin ciyar da Jihar Kaduna gaba.

Naku,

Muhammad Sani Abdullahi

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hijira tv Nig. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share