27/02/2024
Zanga-zangar NLC ta mayar da hankali ne kan yunwa, ba karancin albashi ba – Ajaero
Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC ta bayyana cewa zanga-zangar ta kwanaki biyu da mambobinta ke jagoranta ta mayar da hankali ne kan magance yunwa, maimakon neman kawai a sake duba mafi karancin albashi.
Da yake yiwa manema labarai jawabi a ranar Talata, 27 ga watan Fabrairu, shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero ya bayyana cewa sabanin yadda wasu ke ikirari, zanga-zangar kungiyar ba wai kawai neman karin mafi karancin albashin kasar nan na N30,000 ba ne. Ya ce: "Dole ku fahimce ta, wannan zanga-zangar ta shafi yunwa ne, wadanda ba sa aiki fa?, mafi karancin albashi, yaushe za a kammala? Yaushe zai fara aiki? Menene mafi karancin albashin da zai kawar da yunwa?” “Majalisar Dinkin Duniya ta ce mafi talaucin abinda mutum zai ci shine dala 2 a kowace rana. Wannan shi ne mafi talauci, kuma idan kana da iyali mai mutum shida, $2 a kowace rana sau shida dala $12 kenan” in ji shi yayin da yake magana da manema labarai a Abuja. A wata daya kana da dala 360 wanda ke nufin kusan N700,000 shine mafi karancin albashin da kake magana kenan shine zai ciyar da kai shine ciyar da kai kadai banda maganar sufuri da wurin kwana to menene? Me za mu ce, “To, ka sani, ba mu yi ba, ba mu zamu gaya musu abin da za su yi ba, za mu gaya musu yadda muke ji ne kawai, ga yunwa a ƙasar, amma an kasa yin komai akai.
Mun ba da shawarar duk abin da muke bukata, da ace sun magance matsalar sufuri nan da nan, da sun warware kusan kashi 50% na matsalar. "Saboda ko da za ku sarrafa garri. a kauye sai ka kai shi gari, kudin da ka kashe wajen sufuri, kawai shine zai kara wa garri tsada.".
Ajaero ya zargi gwamnatin tarayya da gaza biyan bukatun kungiyar tun bayan cire tallafin man fetur wanda ya janyo tsadar rayuwa, “Don haka da zarar sun taba man Fetur , ba za ka iya cika tankinka da komai ba. N30,000, N40,000. To a lokacin da s**a taba shi, sai muka ce, “Ok, ku kawo motocin masu amfani da Gas, wata 7-8 kenan, babu wata