Jaridar Mafita

Jaridar Mafita Shafin jaridar MAFITA domin samun labarai da rahotanni mabambanta kuma masu inganci.

A Zariya kaɗai ana da masallatan Idi 45Ɗariƙa na da Masallatan İdi Ashirin Da huɗu (24), Izala da Salafiyya suna da Goma...
06/04/2024

A Zariya kaɗai ana da masallatan Idi 45

Ɗariƙa na da Masallatan İdi Ashirin Da huɗu (24), Izala da Salafiyya suna da Goma sha takwas (18), Shi’a na da ɗaya (1), Habibiyya da NASFAT na da biyu (2), gaba-ɗaya sun zama Arba’in da biyar (45).

Kuma a hakan ban da ƙaramar hukumar Sabon Garin Zariya.

Don darajar Alƙur’ani mene ne amfanin hakan.?

-Inji Shaikh Muhammad Auwal Sharif.

Daga Mustapha Muhammad.

Yarjejeniyar: Dinke baraka tsakanin mazhabobin Musulunci..Doka ta daya:"Musulmai al'umma ce guda daya, suna bauta wa Uba...
23/03/2024

Yarjejeniyar: Dinke baraka tsakanin mazhabobin Musulunci..

Doka ta daya:

"Musulmai al'umma ce guda daya, suna bauta wa Ubangiji daya, suna kuma karanta littafi daya, suna kuma bin Annabi daya, a kuma duk inda suke alkiblarsu daya ce, lallai Allah ya girmama su da sunan Musulunci, a wani bayani da yake a bayyane tamkar bayyanar rana, bai k**ata a sauya shi da waninsa ba, bayan Allah ya zaba mana shi: (Shi ne ya sanya maku suna Musulmai), saboda haka, babu bukatar kowane irin suna, ko sifa da s**a yi kutse, wadanda suke rarraba kawuna ba sa hadawa, suke kuma nesanta al'umma da juna, ba sa kusanto da su.. Banda wadanda suke karfafa da bayyana manhaji, masu karfafa ayyukan Musulunci, su ma din, da sharadin kada su zama an canja sunan Musulunci da su, ko su zama suna gasa da sunan da Allah ya kira mu da shi, k**an yada su a farfajiyar Musulunci, don su kawar da sunan da ya hade mu gaba daya, musamman abubuwan da batattun jam'iyyun da s**a kaurace wa hadin-kan al'umma, da wasu 'yan tsirarun sunaye da wasu tsirarun batattu suke sifantawa".

Taron Makka 2024, a gefen dakin Allah mai alfarma, karkashin kungiyar رابطة العالم الإسلامي

Daga Saleh Kaura.

Kwanan nan Insha'Allahul Azeem za a ga rugurgujewar Dala.-Inji Shaikh Zakzaky Jagoran mabiya mazhabar Shi'a a Nijeriya.D...
21/02/2024

Kwanan nan Insha'Allahul Azeem za a ga rugurgujewar Dala.-Inji Shaikh Zakzaky Jagoran mabiya mazhabar Shi'a a Nijeriya.

Daga Mustapha Muhammad.

Hisbah ta k**a ƴar Tiktok Murja Kunya.
13/02/2024

Hisbah ta k**a ƴar Tiktok Murja Kunya.

Allah Ya yi wa Matar Abdul Sahir Rasuwa Allah Ya Gafartawa Rahama Ya Baka Hakurin Rashin Ya Albarkaci Yaran Data Bari
13/02/2024

Allah Ya yi wa Matar Abdul Sahir Rasuwa Allah Ya Gafartawa Rahama Ya Baka Hakurin Rashin Ya Albarkaci Yaran Data Bari

BINTUN DAƊINKOWA TA RASU.Jarumar Kannywood da take fitowa a matsayin Bintu ta shirin Daɗinkowa na tashar AREWA24 ta rasu...
11/02/2024

BINTUN DAƊINKOWA TA RASU.

Jarumar Kannywood da take fitowa a matsayin Bintu ta shirin Daɗinkowa na tashar AREWA24 ta rasu yau Lahadi sak**akon rashin lafiya da ta sha fama da shi.

Allah Ya gafarta mata.

Rundunar ´yan sanda a jihar Bauci da ke Najeriya ta ce tana neman Malamin addinin Musulunci Dr. Idris Abdulaziz Dutsen T...
08/02/2024

Rundunar ´yan sanda a jihar Bauci da ke Najeriya ta ce tana neman Malamin addinin Musulunci Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ruwa a jallo.

YANZU-YANZU: Murja Kunya ta bada Sanarwar Cewa; Zata Goge Duk Wani Bidiyoyin Da Ta Yi A Babban Manhajarta Na Tiktok.
25/01/2024

YANZU-YANZU: Murja Kunya ta bada Sanarwar Cewa; Zata Goge Duk Wani Bidiyoyin Da Ta Yi A Babban Manhajarta Na Tiktok.

'Ya'yanmu mata sun cancanci a ba su kayan aikin da s**a dace don fuskantar dukkan ƙalubalen rayuwa. Ina jaddada cewa ya ...
22/01/2024

'Ya'yanmu mata sun cancanci a ba su kayan aikin da s**a dace don fuskantar dukkan ƙalubalen rayuwa. Ina jaddada cewa ya k**ata a ƙarfafa mata saboda duniya na buƙatar ƙarin taimako, mata ma za su iya ba da gudummawa daidai gwargwado.

Iyaye mata ku faɗawa 'ya'yanku mata zama mai ƴanci a duniyar yau yana da matukar muhimmanci.

-Inji Layla Ali Othman.

Inbox ɗina ya cika maƙil da baƙaƙen maganganu.-Inji Barrister Abba Hikima Ina buƙatar ɗauki fa jama’a. Don Allah ku gaya...
22/01/2024

Inbox ɗina ya cika maƙil da baƙaƙen maganganu.-Inji Barrister Abba Hikima

Ina buƙatar ɗauki fa jama’a. Don Allah ku gayawa mata iyayenmu ba fa ni na yi waccan doka ba. Inbox ɗina ya cika maƙil da baƙaƙen maganganu.

Wai kai da kake shirin yin aure ne kake jayayya a kan lefe.? is alright. Za ka ga abin da ya fi lefe bayan an ɗaura aure...
22/01/2024

Wai kai da kake shirin yin aure ne kake jayayya a kan lefe.? is alright. Za ka ga abin da ya fi lefe bayan an ɗaura auren in dai kai 'responsible husband' ne. Ci gaba da jayayya kan lefe.

-Inji Ammar Muhammad Rajab

Idan kana soyayya, za ka rinƙa murmushi babu dalili.-Inji Mama Uwa Aishatu Gidado Idris
22/01/2024

Idan kana soyayya, za ka rinƙa murmushi babu dalili.

-Inji Mama Uwa Aishatu Gidado Idris

13/01/2024

Wane Namiji ne a “Facebook” idan kika samu dama za ki iya auren shi da gaske.?

13/01/2024

Wacce mace ce a ‘Facebook’ idan ka samu dama za ka iya auren ta da gaske.?

Allah a cire maganar wasa, babu hankali kwata-kwata a yin Bilicin ɗin da ƴan matan nan ke yi.Har koraye suke komawa fa. ...
13/01/2024

Allah a cire maganar wasa, babu hankali kwata-kwata a yin Bilicin ɗin da ƴan matan nan ke yi.

Har koraye suke komawa fa. Ni ina kallon wannan Bilicin ɗin da ƴan matan nan ke yi a matsayin Algush.

-Inji Mustapha Muhammad Rajab.

Yanzu haka wannan kuɗin anko zai kai wa Budurwar shi.Shin kun taɓa ganganci irin wannan.?
13/01/2024

Yanzu haka wannan kuɗin anko zai kai wa Budurwar shi.

Shin kun taɓa ganganci irin wannan.?

Ni bani son abin da zai raba ni da alƙur'ani. -Inji matar Shugaban ƴan Shi’a dake Nijeriya Malama Zinatu.
13/01/2024

Ni bani son abin da zai raba ni da alƙur'ani. -Inji matar Shugaban ƴan Shi’a dake Nijeriya Malama Zinatu.

Duk wanda ya taɓa Sahabi kafin a je wani kotu ka yanka shi kawai.Duk wanda ya taɓa Sahabi kafin a je wani kotu ka yanka ...
09/01/2024

Duk wanda ya taɓa Sahabi kafin a je wani kotu ka yanka shi kawai.

Duk wanda ya taɓa Sahabi kafin a je wani kotu ka yanka shi kawai, ana zuwa me ya faru.? Ka ce Sahabi ya zaga, sahabin kuma ya fi ka, ya fi baban ka, ya fi maman ka, ya fi kakan ka, ya fi yafande, ya fi yagwalgwal, ya fi kowa ɗin nan da kake kallo.

A ce za a kai ka wajen ƴan Sanda, ka ce kai ni wajen sanda sai na kashe shi.

-Inji Shaikh Jamil Albany Samaru Zariya.

Daga Mustapha Muhammad Rajab

Da Tunubu ya ƙara kuɗin mai ina murna saboda baƙi za su ragu.-Inji Buhari.
01/01/2024

Da Tunubu ya ƙara kuɗin mai ina murna saboda baƙi za su ragu.

-Inji Buhari.

FASSARAR JAWABIN SHUGABAN KASA BOLA AHMED TINUBU A SABUWAR SHEKARAR 2024Ya ku `yan uwana yan Najeriya,Ina cike da farin ...
01/01/2024

FASSARAR JAWABIN SHUGABAN KASA BOLA AHMED TINUBU A SABUWAR SHEKARAR 2024

Ya ku `yan uwana yan Najeriya,

Ina cike da farin ciki a yayin da nake wa Ilahirinmu, matasa da tsofaffi maraba da shigowa sabuwar shekara ta dubu biyu da ashirin da hudu. Dole ne mu daga Hannuwanmu sama mu gode wa Allah madaukakin Sarki saboda albarkar da Ya yi wa kasar mu da kuma rayukan mu a cikin shekarar da ta gabata wato shekara ta dubu biyu da ashirin da uku.

Ko da yake Shekarar da ta gabata na kunshe da kalubale da dama, amma duk da haka an yi abubuwan alheri masu yawa, Ciki har da mika mulki daga tsohuwa zuwa sabuwar gwamnati cikin lumana, wadda hakan alama ce da ke nuna irin gagarumin cigaban da demokaradiyarmu mai shekaru ashirin da hudu a jere ta samu

Shekara ce wacce ku al’ummar wannan kasa mai Albarka kuka amince min da in jagorance ku, kan bayyanannen kudiri na yin gyara ga kasar nan, da yin garambawul a fannin tattalin arzikinta, da inganta tsaro a iyakokin kasarmu da farfado da masana`antun mu, da inganta noma, da cigaba na bai-daya, sannan in dora kasa a tafarkin cigaba mai dorewa ta yadda mu da `yan baya za mu yi alfahari da ita.

Aikin gina ingantacciyar kasa mai dauke da al’ummar da take kishin kowanne dan kasa, shine makasudin tsayawata takarar shugaban kasa. Kuma shine taken yakin neman zabena wato SABUNTA-FATA-NA-GARI a kansa kuka zabe ni a matsayin shugaban kasar mu don na tabbatar da shi.

Daukacin abubuwan da na gudanar a Ofis, k**a daga matakan da na dauka, da tafiye-tafiye na zuwa kasashen waje tun daga ranar ashirin da tara ga watan Mayu na shekara ta dubu biyu da shirin da uku duk na yi su ne domin amfanin kasar mu da cigabanta.

A cikin watanni bakwai da s**a gabata na gwamnatin mu, na dauki wasu tsauraran matakai da s**a zama tilas domin ceto kasar mu daga mummunan yanayi. Daya daga cikin wadannan matakan shine cire tallafin mai wanda ya zama wani nauyi ko tarnaki ga kasar nan na tsawon shekaru arbain da biyu, da kuma cire damar da wasu `yan tsirarru suke da ita a harkar hada-hadar kudin kasashen waje, wadda wasu shafaffu da mai ne kawai a cikin mu ke cin gajiyarta. Ko shakka babu wadannan matakan sun kawo matsi ga daidai kun mutane da iyalai da kuma kasuwanci.

Ina sane da cewa tattaunawar da ta zama ruwan dare a wannan lokaci ita ce ta tsadar rayuwa da hauhauwar farashin kayan masarufi wadda ya zarce kashi ashirin da takwas cikin dari ga kuma rashin aikin yi ga wasu yan kasa

K**a daga manyan cibiyoyin kasuwanci na Lagos zuwa cikin birnin Kano har zuwa loko-loko na gaɓar teku da ke Bayelsa ina jin koke da ƙorafin `yan Najeriya masu aiki dare da rana domin neman abinda za su ciyar da iyalansu

Ina sane da abubuwan da suke damunku wadanda ku ka bayyana da wadanda ma ba ku bayyana ba. Na san wasu ƴan ƙasa sun fara tambayar shi a haka wannan gwamnatin take son ta sabunta fata na-garin na mu?

Ya ku `yan uwana ƴan Nijeriya, ina kira gare ku ku amince da ni. yarda da ni. Na san wannan lokaci ne da ake cikin wahala, amma kada mu sake mu yi kasa a guiwa saboda babu wata wahala dake dauwama. Mun shirya wa wannan lokacin kada mu tsorata, kada mu raunana. Ya k**ata kalubalen tattalin arzikin da muke fuskanta yau ya kara mana kwarin gwiwa kuma ya sa mu kara so da imani ga kasar mu Najeriya. Ya k**ata matsalolin da muke fuskanta su sanya mu kara jajircewa wajen gina kasa. Halin da muke ciki yanzu yasa mu kara dagewa ta yadda shekara ta dubu biyu da ashirin da hudu za ta amfani duk yan kasa.

Tun lokacin da gwamnatinmu ta karbi ragamar mulki ake samun gagarimin ci gaba ta fuskar tsaron kasa, mun kubutar da da dama cikin wadanda aka yi garkuwa dasu daga hannun masu garkuwa. Duk da cewa ba zamu iya bugun kirjin mu ce mun shawo kan duk matsalolin tsaro ba, amma muna aiki tukuru domin samar da zaman lafiya a gidajen mu da wuraren aiyukanmu da lungu da sakon mu.

Bayan mun samar da hanyoyin farfado da tattalin arzikin kasa cikin watanni bakwai na shekara ta dubu biyu da ashirn da uku, yanzu mun shirya domin samar da haka a duk fannoni.

Ba da dadewa ba a taron sauyin yanayi na COP28 da akayi a watan Disamba a Dubai, ni da Shugaban Gwamnatin Jamus ,Olaf Schlz muka kulla yarjejeniyar yin aiki cikin gaggawa domin kammala aikin da kamfanin Siemens ke gabatarwa wanda zai samar da wutar lantarki zuwa ga Gidaje da wuraren kasuwanci a karkashin shirin Shugaban kasa wadda aka soma a shekara ta dubu biyu da Goma sha takwas.

Baya ga wannan muna shirin kaddamar da wasu ayyukan shimfida layukan samar da wutar lantarki da kuma inganta tashoshin samar da wutar a ko’ina a fadin kasar nan.

Gwamnatin da nake jagoranta ta fahimci cewa babu wani cigaba da za a samu muddin wutar lantarki bata wadata ba. A cikin shekara ta dubu biyu da ashirin da hudu zamu kara hobbasa wajen soma tace danyen mai a matatar mai ta Fatakwal da ta Dangote wadanda zasu soma aiki gadan-gadan.

Domin tabbatar da samar da abinci da tsaro zamu gaggauta noma hekta dubu dari biyar na masara da Shinkafa da alk**a da dawa da sauran hatsi. Mun kuma kaddamar da noman rani a filin da ya kai hekta dubu dari da ashirin a jihar Jigawa a watan Nuwamban da ya gabata a karkashin shirinmu na bunkasa noman alk**a.

A wannan shekarar za mu yi hobbasa wajen ganin cewa duk wasu batutuwa na kudi da haraji da s**a k**ata a Sanya su bisa tsari an yi su yadda ya dace saboda kada a samu koma baya. A duk wata tafiya da nayi zuwa kasashen waje, sakon da nake bayarwa shi ne Najeriya a shirye take domin yin kasuwanci da kowa.

Zan yanke duk wani abu da zai kawo tarnaki ga kasuwanci a kasar nan kuma ba zan yi kasa a gwiwa ba wajen kawar da duk wani abu da zai hana Najeriya zama cibiyar kasuwanci ga masu son zuba jari daga nan cikin gida da kuma kasashen waje.

A cikin kasafin kudi na shekara ta dubu biyu da Ashirin da hudu dana gabatar a gaban majalisar dokokin kasa na bayyana manufofi guda takwas da gwamnatina tasa a gaba wadanda s**a hada da tsaron kasa ciki da waje, da samar da aiyuka da inganta kasuwanci da samar da daidaito a zuba jari, da rage talauci da kuma inganta zamantakewa. Saboda mun dauki tsarin cigaban mu da matukar mahimmanci, kasafin kudin mu na shekara ta dubu biyu da ashirin da hudu ya nuna karara mahimmancin da muka bai wa cimma burin mu a gwamnatance.

Za mu yi aiki tukuru domin tabbatar da ganin cewa duk dan Najeriya ya amfana da wannan gwamnatin. Har marasa karfi duk babu wadda za a bari a baya. A cikin wannan tsarin zamu gabatar da sabon tsarin Albashi mafi karanci ga hazikan ma`aikatan mu a cikin wannan Shekaran. Ba wai kawai abu ne daya k**ata a yi saboda tattalin arziki har ma saboda dacewarsa a babin kyautatawa da kuma a siyasance.

Nayi rantsuwa cewa zanyi iya kokari na wajen bauta wa kasan nan a koda yaushe k**ar yadda na fada a baya, don haka ba zan daga kafa ga duk wani wanda na bai wa mukami ba idan bai yi aiki yadda ya dace ba.

Don haka ne na samar da ofishi na musamman a ofishin shugaban kasa da zai rinka sanya ido kan manufofi da tsaretsaren gwamnati ya kuma tabbatar da ganin cewa anyi aiki yadda ya dace ta yadda gwamnati za ta inganta rayuwar alummar mu.

Tuni muka tsara hanyar bin diddigin ayyukan masu rike da muƙamai wanda zai fara aiki a kashin farko na sabuwar shekara. Ta haka za mu gane masu makoma a gwamnatina a cikin masu rike da madafun iko

Ya ku yan uwana yan Najeriya, bubban buri na a matsayina na Sanata a jamhuriya ta uku da kuma Gwamnan Lagos na tsawon shekaru takwas da kuma yanzu a shugaban wannan kasa mai dumbin albarka shine in gina kasa wacce za’a yi adalci ga kowa sannan a rage rashin daidaito a tsakanin alumma. Na kuma yi na`am da masu arziki suci moriyar arzikinsu da s**a mallaka ta hanyar halal. Mun gamsu da cewa duk wani dan Najeriya da ya yi aiki tukuru yana da damar samun cigaba a rayuwa. Dole ne a nan in kara da cewa Allah ya hallicce mu da baiwa daban daban don haka ba dole ne dukkan ninmu mu samu sak**ako iri daya ba idan muka yi aiki tukuru, amma gwamnatin mu, a cikin shekara ta dubu biyu da ashirin da hudu zuwa gaba za tayi aiki domin bai wa kowanne dan kasa dama domin ya samu cigaba.

Domin sabuwar shekarar ta amfani dukkan mu, a matsayin mu na yan adam dole ne mu shirya mu yi namu kokarin. Aikin gina kasa mai albarka ba aikin shugaban kasa ko gwamnoni da ministoci da yan majalisa ko kuma jami`an gwamnati kawai ba. Makomar mu ta na da alaka da juna a matsayin mu na yan kasa daya wato Najeriya. Ko da Yarukan mu da aladun mu da Addinai ba daya bane bai k**ata mu rinka samun rashin jituwa ba.

Acikin wannan sabuwar shekarar ya k**ata a matsayin mu na yan Najeriya mu yi aiki tare domin samar da zaman lafiya da cigaba da kuma daidaito a kasar mu. Ina kuma kira ga abokan hamayyar siyasa ta a zaben daya gabata, cewa zabe ya wuce, yanzu lokaci ne daya k**ata mu yi aiki tare domin cigaban kasar mu.

Dole ne mu bari fitilar da kowanne acikin mu yaro da babba mace da namiji ke dauke da ita, ta cigaba da haskaka hanyar mu ta zuwa ga nasara.

Ina muku barka da shiga Sabuwar Shekara ta dubu biyu da ashirin da hudu.

Allah ya Albarkaci Najeriya.

Bola Ahmed Tinubu,GCFR

1 JANAIRU 2024.

Jaridar Sabuwar Najeriya ta fassara.

Jaridar Mafita ta karrama.Kabir MukhtarDM Balarabe Jibreel Ibraheem Amb Aliyu Ishaq Mus'abulkairi Ubale Sharifee Jaridar...
22/12/2023

Jaridar Mafita ta karrama.

Kabir Mukhtar
DM Balarabe
Jibreel Ibraheem
Amb Aliyu Ishaq
Mus'abulkairi Ubale Sharifee

Jaridar Mafita na taya ku murna.

YANZU YANZU: Ɓangarorin ƴan’uwa Musulmi dake Unguwar Jaba ƙaramar hukumar Sabon Garin Zariya sun fito kan t**i suna zang...
08/12/2023

YANZU YANZU: Ɓangarorin ƴan’uwa Musulmi dake Unguwar Jaba ƙaramar hukumar Sabon Garin Zariya sun fito kan t**i suna zanga-zangar lumana na kira da a yi adalci kan Musulmin da Sojoji s**a kashe a harin Bom ɗin da s**a kai a ƙauyen Tudun Biri Kaduna.

Limamin Masallacin Juma'a na ƴan ɗariƙa dake Unguwar Jaba ya sauke na shi nauyin. Ya yi kira da a gaggauta ɗaukar mataki a kan waɗanda s**a kashe waɗannan ƴan’uwa musulmi a wajen Mauludi.

Bayan ya kammala Huɗuba ne aka gabatar da Sallahr Juma'a, sai ƴan’uwa musulmi masoya Manzon Allah (SA) s**a hau kan t**i domin Alla-wadai da kisan da Sojoji s**a yi wa masoya Manzon Allah a Tudun Biri dake jihar Kaduna.

Shaikh Abdullahi Usman ne ya rufe wannan zanga-zangar ta lumana da ta gudana yau Juma'a.

Daga Mustapha Muhammad Rajab.

08/12/2023

Ci gaba da karrama masu bibiyar mu.

Mutane (20) ɗin da s**a fara Comments a ƙarƙashin Posting ɗin nan.

Jaridar Mafita ta karrama.Muhammad S Abdullah Ali Dayyab Alhaidary Jaridar Mafita na taya ku murna.
07/12/2023

Jaridar Mafita ta karrama.

Muhammad S Abdullah
Ali Dayyab Alhaidary

Jaridar Mafita na taya ku murna.

Jaridar Mafita ta karrama Alhaji Zafar Ishaq Ansari, ɗaya daga cikin masu jimirin bibiyar shafin Jaridar dake kan Facebo...
07/12/2023

Jaridar Mafita ta karrama Alhaji Zafar Ishaq Ansari, ɗaya daga cikin masu jimirin bibiyar shafin Jaridar dake kan Facebook.

Jaridar Mafita na taya ka murna.

Zafar Ishaq Ansari

Jaridar Mafita ta karrama Hajiya Zahra'u Gambo Lawal ɗaya daga cikin masu jimirin bibiyar shafin Jaridar dake kan Facebo...
07/12/2023

Jaridar Mafita ta karrama Hajiya Zahra'u Gambo Lawal ɗaya daga cikin masu jimirin bibiyar shafin Jaridar dake kan Facebook.

Jaridar Mafita ta karrama.Malumfashi Imran Muhammad Gogeru Kampani Usman Ibraheem Umar MtzMuazzam Khaleefa Muhammad Amin...
07/12/2023

Jaridar Mafita ta karrama.

Malumfashi Imran
Muhammad Gogeru Kampani
Usman Ibraheem Umar Mtz
Muazzam Khaleefa
Muhammad Amin

Jaridar Mafita na taya ku murna.

Jaridar Mafita ta karrama. Ali Abdurra'uf Kabir Bawa Muhammad Ali Hafizy Muhammad Sani UmarAbeedah M Siraj Jaridar Mafit...
07/12/2023

Jaridar Mafita ta karrama.

Ali Abdurra'uf
Kabir Bawa
Muhammad Ali Hafizy
Muhammad Sani Umar
Abeedah M Siraj

Jaridar Mafita na taya ku murna.

Jaridar Mafita ta karrama.Yaseer Alhassan Sirdeq El-Palestiny Abubakar Babangida Mani Sadiq Hussaini Mahmud Shüãêb Süräj...
07/12/2023

Jaridar Mafita ta karrama.

Yaseer Alhassan
Sirdeq El-Palestiny
Abubakar Babangida Mani
Sadiq Hussaini Mahmud
Shüãêb Süräj Bïçhí

Jaridar Mafita na taya ku murna.

Jaridar Mafita ta karrama.Ali Zakariyya Teemah Sabaty Ibraheem Musa Sabaty  Aminu Usman Iro Jaridar Mafita na taya ku mu...
07/12/2023

Jaridar Mafita ta karrama.

Ali Zakariyya
Teemah Sabaty
Ibraheem Musa Sabaty

Aminu Usman Iro

Jaridar Mafita na taya ku murna.

Address

Zaria
Kaduna

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jaridar Mafita posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Jaridar Mafita:

Videos

Share

Category



You may also like