Kaduna oniine news

Kaduna oniine news Mune a sahun gaba wajen kawo muku labarai da ɗumi ɗuminsu

Ɓarayin Daji A Birnin Gwari Sun Sha Ruwan Wuta Wotowoto.....Boderi da Bodeji Sun Wuce Barzahu Babu Shirin...Rundunar soj...
23/02/2024

Ɓarayin Daji A Birnin Gwari Sun Sha Ruwan Wuta Wotowoto.....

Boderi da Bodeji Sun Wuce Barzahu Babu Shirin...

Rundunar sojin Najeriya ta 1 division Kaduna tayi nasarar ragargazar ƴan ta'addar daji a ƙananan hukumomin Igabi da Giwa a Birnin Gwari na jihar, sun kuma samu mak**ai da Alburusai.

Maharan a yankin Maganda-Dausayi - Mugaba sun kai harin ƙwanton bauna ga Jami'an tsaron yayin da suke aikin sintiri, inda s**a yi musayar wuta, take Jami'an tsaro s**a maida martani.

Faɗan ya ɗauki kimanin awa guda ana fafatawa Inda Jami'an s**a kashe ɓarayin guda biyu tare da samun Bindiga 1 ƙirar AK 47 , tare da 1 AK 47 Magazine, 3 rounds of 7.62mm Special, waya 1 ƙirar Techno, Motoci guda 3 ƙirar Hilux da makullan babura, an samu ɗaurin wasu abubuwan da ake zargin ma*****na ce ko Wiwi, ƙwayoyin tramadol da kuma tsabar kuɗi Naira 13,200.

Cikin rashin Sa'a ɓarayin sunyi amfani da Shanu domin kai harin Sojojin kuma s**a kashe dayawa daga ciki, jamian suna ci gaba da neman ɓarayin da s**a gudu.

A wani yunƙurin na Jami'an tsaro wajen kauda ɓata gari, Jami'an na 1 Division a ranar Larabar 22 February 2024, sunyi nasarar farmakar ɓarayin daji a yankin Bada - Riyawa kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari, a yayin farmakin Jami'an sunyi nasarar aika ɓarayin guda shidda zuwa barzahu tare da samun Bundigogi 2 ƙirar AK 47 , 5 AK 47 rifle magazines, 300 rounds of 7.62mm Special ammunition da Babura 19.

Wasu bayanan sirri sun nuna cewa ƙasurgumin ɗan ta'addar nan mai suna Boderi wanda ya kitsa satar yara ƴan mata daga Makarantar Yauri, da Kuma jami'ar Greenfield Kaduna da harin ta'addanci da aka kai a Nigerian Defence Academy ya ƙwanta dama, tare da wani babban yaron shi mai suna Bodejo Jami'an na ƙoƙarin tabbas da sahihancin waɗannan maharan da aka kashe.

Akwai hotuna marasa daɗin gani waɗanda idan an sanya su Facebook suna Iya kulle shafi saboda su.

- Muhammad Aminu Kabir

Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya karyata ikirarin shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio na cewa jihohi sun samu...
23/02/2024

Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya karyata ikirarin shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio na cewa jihohi sun samu karin Naira biliyan 30 kowacce domin magance matsalar karancin abinci.

Tsohon Sanata daga jihar Kaduna Shehu Sani, ya  zargi gwamnonin kasar nan game da halin matsin rayuwa da talakawa ke cik...
22/02/2024

Tsohon Sanata daga jihar Kaduna Shehu Sani, ya zargi gwamnonin kasar nan game da halin matsin rayuwa da talakawa ke ciki inda ya ce Naira bilyan 30 da gwamnatin tarayya ta ba kowane gwamna ta isa a magance matsalar yunwa a Nijeriya.

Mene ne ra'ayinku game da kalaman na tsohon Sanatan?

Ba A Nijeriya Kadai Ake Fama Da Tsadar Rayuwa Ba, Kasashen Amurka Da Ingila Na Suna Fama, Cewar Sanata Barau Maliya
22/02/2024

Ba A Nijeriya Kadai Ake Fama Da Tsadar Rayuwa Ba, Kasashen Amurka Da Ingila Na Suna Fama, Cewar Sanata Barau Maliya

Wani bawan Allah yayi wannan rubutu ranar 10/02/2015 Fatan Allah yasa yana raye yanzu munason muga mi zai sake rubutawaD...
21/02/2024

Wani bawan Allah yayi wannan rubutu ranar 10/02/2015 Fatan Allah yasa yana raye yanzu munason muga mi zai sake rubutawa

DUNIYA:

In banda Goodluck da rashin iya lissafi, wai ace Azumi na nan tafe nan da 2 Months, amma ji yadda kayan abinci s**a ƙara kuɗi, ko wannan kadai ya isa mu kayar dashi a zaɓen da zamu yi nan da 1 week me zuwa duk da mun ji cewa wai zasu daga sai zuwa watan march

Yanzu fa 50kg foreign rice ya zama ₦11,000 daga ₦8,500 kuma loka ɗaya na foreign rice din ₦350 haba!...

Crate na kwai ya koma ₦750 daga ₦600, yanzu ko wane kwai ₦20 ya koma a madadin ₦15...

Kwandon tumatir ya koma ₦12,000 daga ₦9,500...

Ice fish da ake siyar da ko wanne babba guda daya akan ₦60 - ₦80 yanzu ya koma ₦110 Haba Goodluck...

Goran mangyada me cin 10ltr da ake siyar dashi a ₦2,800 yanzu ya koma ₦3,500...

Buhun jan wake da ake siyar dashi ₦15,000 yanzu ya koma ₦17,200...

Gwagwanin peak milk na gari da ake siyar dashi ₦650 ya koma ₦700...

Buhun gyada 50kg da ake siyar dashi ₦9,500 ya koma ₦11,800...

Taliya ko wacce kwara daya ta koma ₦90 daga ₦70...

Lemu ko wanne kwara daya ya koma ₦15 daga ₦10...

Ayaba kuma duk bunch guda ya koma ₦130 daga ₦80...

Ledan semovita ya koma ₦1,700 daga ₦1,450...

Lokan wake ya koma ₦350 daga ₦250...

Lokan gero ya koma ₦80 daga ₦65...

Masara duk loka daya ₦120 daga ₦100...

Buhun sugar ya koma ₦10,000 daga ₦8,000 kuma lokan sugar ya koma ₦280 daga ₦220

Goodluck must go... Nigeria sai Buhari
Everyone
bawan Allah yayi wannan rubutu ranar 10/02/2015 Fatan Allah yasa yana raye yanzu munason muga mi zai sake rubutawa

Wata Sabuwa: Majalisar dattawan Najeriya ta kafa wani kwamiti da zai binciki tsohon shugaban kasa Buhari kan hanyoyin da...
21/02/2024

Wata Sabuwa: Majalisar dattawan Najeriya ta kafa wani kwamiti da zai binciki tsohon shugaban kasa Buhari kan hanyoyin da ya kashe Naira tiriliyan 30

Za kuma su binciki Naira tiriliyan 10 da aka kashe a shirin Anchor Borrowers Programme.

Inna LillaHi Wa Inna IlaiHi Raji'un !!! An yi zana'idar mutum 6 da yan bindiga s**a kashe a Yan-nasarawar FaskariA daran...
20/02/2024

Inna LillaHi Wa Inna IlaiHi Raji'un !!!

An yi zana'idar mutum 6 da yan bindiga s**a kashe a Yan-nasarawar Faskari

A daran jiya wayewar garin yau Talata ne yan bindiga s**a shiga garin Yan-nasarawa dake gabas da garin Faskari, kusa da Daudawa, nan jihar Katsina inda s**a kashe mutum 6 nan take.

Cikin wadanda s**a kashe har da mai unguwa Malam Haruna Wakili, mahaifi ga mabiyin wannan shafin na Katsina Daily News, wato Lado Haruna da aka fi dani da Lado Horo

Ta'addancin da s**a yi a jiyan sun hada da;

Sun Dauki Mutum 38

Sun kashe Mutum 6

Sun Harbi Mutum 10

Sun Kone mota 8

Sun Kone Shago 10

Sun kone gidaje 6

Sun kore Shanu da har yanzun ba a san Adadin Su ba, k**ar yadda wanda lamarin ya shafi yan uwansa a ciki Auwal Hassan Liman Nasarawa da kuma akai zana'idar a gabansa ya aiko mana..

Kotun shari'ar Musulunci dake zaman ta a unguwar Kwana Hudu karkashin mai Shari'a Mallam Nura Yusuf Ahmad tayi umarni da...
20/02/2024

Kotun shari'ar Musulunci dake zaman ta a unguwar Kwana Hudu karkashin mai Shari'a Mallam Nura Yusuf Ahmad tayi umarni da a kai Murja Ibrahim Kunya wajen likitan kwakwalwa domin duba lafiyar kwakwalwar ta la'akari da yanayin maye da kotun tace ta lura tana ciki.

Ministan Tsaro Bello Matawalle yayi gargadi Ga ‘yan Najeriya cewa A yi taka-tsantsan Wajen s**ar Gwamnatin Shugaba Tinub...
19/02/2024

Ministan Tsaro Bello Matawalle yayi gargadi Ga ‘yan Najeriya cewa A yi taka-tsantsan Wajen s**ar Gwamnatin Shugaba Tinubu.

Matawalle, ta bakin mai magana da yawun ma’aikatarsa, Henshaw Ogubike, Yayi gargadi Game da illolin dake tattare da kalaman batanci. Yayi gargadin cewa kalaman Rashin da'a na iya tayar da husuma, da haifar da sabani, har ma da haddasa tashin hankali a cikin al’ummarmu da muke ƙauna.

Da yake la'akari da kalubalen da kasar nan ke fuskanta, Matawalle ya tsaya tsayin daka kan kokarin da Shugaba Tinubu ke yi na magance matsalolin tattalin arzikin da ke addabar 'yan Najeriya. Ya jaddada jajircewar shugaban da tawagarsa wajen sauke nauyin da ke kan al’umma, inda ya Buƙaci masu zage-zage dasu guji ci gaba da tsokaci.

Yayin da al’ummar kasar ke fama da rashin tabbas da kunci, kalaman Matawalle sun zama abin tunatarwa ne kan daidaiton da ke tsakanin ‘yancin fadin albarkacin baki da alhakin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Ƴan bindiga sun ƙone mutane 12 da ransu a ƙauyen Gindin Dutse Makyali, Doka da ke gundumar Kufana, a Karamar Hukumar Kaj...
19/02/2024

Ƴan bindiga sun ƙone mutane 12 da ransu a ƙauyen Gindin Dutse Makyali, Doka da ke gundumar Kufana, a Karamar Hukumar Kajuru a Jihar Kaduna.

Maharan sun kuma kone gidaje 17 a ƙauyen yayin farmakin da s**a kai da misalin karfe 6:00 na safiyar ranar Lahadi.

Na yi mamaki matuka jin cewa, maigirma shugaban kasa Tinubu ya goyi bayan abinda gwamnatin jihar Kano ta yi na takura ma...
18/02/2024

Na yi mamaki matuka jin cewa, maigirma shugaban kasa Tinubu ya goyi bayan abinda gwamnatin jihar Kano ta yi na takura ma masu taskace kayayyakin da suke sayarwa na masarufin rayuwa har yana kira ga wasu jihohin su yi koyi da ita.

Tambayata a nan:
1. Masu rumbunan abinci su ne s**a haifar da yunwa ko tsadar abinci?
2. Idan ba ayi runbun kayan masarufi ba a ina ne za a ajiye kayan da aka sayo daga wasu kasashen kafin a rarraba su a shaguna?
3. Abinci ne kadai ya yi tsada ko har da sauran ababen k**ar karfe da katako da zinari da fetur da tufafi dss?
4. Farashin kaya ne ya tashi ko darajar Naira ce ta sauka? Idan Naira ce ta lalace wa ya lalatar da ita?
5. Kayan da ke a Store an neme su a kasuwa ne aka rasa bale ace boyewa su aka yi?

Ina gudun a bar dukan "Sa" a dawo bugun taiki. Masu mulki sun san in da matsalar tsadar rayuwa take; su daina yin zaluncin da zai kara shigar da mu wata sabuwar damuwa.

Ya Allah!
Muna tawassuli da addu'oin bayinka duk da suke cikin matsatsi a Najeriya da sauran kasashe ka yaye mana wannan musiba ta hanyar da ka fi amincewa da ita.
Daga : Farfesa Mansur Sokoto

TSADAR RAYUWA: Kamfanin BUA a Nijeriya ya rubanya albashin ma'aikatansa da kaso 50 sak**akon tsadar rayuwa.
18/02/2024

TSADAR RAYUWA: Kamfanin BUA a Nijeriya ya rubanya albashin ma'aikatansa da kaso 50 sak**akon tsadar rayuwa.

Gwamnonin jam'iyyar adawa ta PDP a Nijeriya sun bukaci jam'iyya APC mai mulkin kasar da ta hakura da mulki idan har ba z...
17/02/2024

Gwamnonin jam'iyyar adawa ta PDP a Nijeriya sun bukaci jam'iyya APC mai mulkin kasar da ta hakura da mulki idan har ba za ta iya magance matsalolin Nijeriya ba.

Mun Gaji Da Bawa Talakawa Haƙuri Don Suna Gab Da Yi Wa Gwamnati Tawaye - Sarkin Musulmi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaj...
17/02/2024

Mun Gaji Da Bawa Talakawa Haƙuri Don Suna Gab Da Yi Wa Gwamnati Tawaye - Sarkin Musulmi

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na uku ya Gargaɗi gwamnatin Najeriya ta gaggauta ɗaukar matakin sauƙaƙa wa talakawa rayuwa da fatattakar yunwa, matukar ba haka ba kuma ta kuka da kanta kan matakin da talakawan zasu ɗauka a kanta.

Da ya ke yiwa manema labarai jawabi a Arewa House da ke jihar Kaduna, Sarkin musulmin yace Sarakunan gargajiya dana shugabannin addini sun gaji da tausar talakawa da kuma basu haƙuri, don haka babu makawa illa gwamnati ta ɗauki matakin sauƙaƙa rayuwa.

Ya ce a yanzu talakawa sun kai geji kuma tura ta kai bango kana Sarakunan gargajiya ba zasu iya tare talakawa ba idan s**a fusata da gwamnati.

Ya ce kullum maganar kenan da gwamnati ke yi musu kan suci gaba da tausar talakawa, har zuwa yaushe ne za’a ci gaba da bada hakuri? Har zuwa yaushe ne talakawa zasu ci gaba da mutuwa da yunwa da sunan haƙuri? A yanzu lokaci ne da gwamnati zata yi haƙuri ta ɗauki matakin da ya dace.

“Mun jima muna roƙon talakawa, a yanzu mun gaji, kunyar su muke ji, sun fara daina yarda da maganar mu, don babu wata alamar sauƙi daga gwamnati don haka matuƙar gwamnati bata dawo cikin hayyacin ta ba, to duk matakin da talakawa s**a ɗauka tabbas ta kuka da kanta” inji Sarki Musulmi.

Me zaku ce kan wannan batu?

Gwamna Kaduna ya bada umarnin a fara bincike kan lamarin da yafaru da Hausa GuysIdan baku manta ba a kwanakin baya Wasu ...
15/02/2024

Gwamna Kaduna ya bada umarnin a fara bincike kan lamarin da yafaru da Hausa Guys

Idan baku manta ba a kwanakin baya Wasu jami'an Kasteliya sun karɓi har Naira dubu ashirin a hannun hausa Gaye da sunan ya karya doka.

Alhali babu wata doka da matashin ya taka a kundin tsarin hukumar. Yanzu dai gwamna malam uba sani ya bada umarnin yin binciken kwakwaf kan al amarin

YANZU-YANZU: Jarumin shirin Dadin Kowa na Arewa 24 Mallam Nata’ala na Na Barar Addua’ar Ku ubangiji Allah Ya Bashi Lafiy...
15/02/2024

YANZU-YANZU: Jarumin shirin Dadin Kowa na Arewa 24 Mallam Nata’ala na Na Barar Addua’ar Ku ubangiji Allah Ya Bashi Lafiya.

Matashin ɗan wasan ƙasar Ivory Coast Simon Adingra ya yanke shawarar sadaukar da Naira Miliyan 49 daga cikin Naira Miliy...
14/02/2024

Matashin ɗan wasan ƙasar Ivory Coast Simon Adingra ya yanke shawarar sadaukar da Naira Miliyan 49 daga cikin Naira Miliyan 123 da ya samu a gasar AFCON domin tallafawa yara marayu a ƙauyen su.

Da dumi'dumi Domin kawo karshen ta'addanci Gwamna Uba sani ya sa hannun a Sabuwar Dokar Tsaro a jihar Kaduna.Gwamna Uba ...
13/02/2024

Da dumi'dumi Domin kawo karshen ta'addanci Gwamna Uba sani ya sa hannun a Sabuwar Dokar Tsaro a jihar Kaduna.

Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya rattaba hannu a kan kudirin dokar asusun tsaro na jihar Kaduna na shekarar 2024. Kudirin ya soke dokar asusun ajiyar tsaro ta jiha mai lamba 22, 2018.

Manufofin dokar dai su ne samar da kudi domin saye da tura kayayyakin tsaron mutane, kayan masarufi da na kudi wadanda s**a wajaba don gudanar da ingantaccen aiki na dukkan hukumomin tsaron tarayya, jihohi, kananan hukumomi da sauran hukumomin tsaro da ke aiki a jihar. Za a keɓe wani ɓangare na Asusun don horarwa da sake horar da jami'an tsaro.

Dokar ta kafa Kwamitin Amintattu da ake kira State Security Trust Fund Board of Trustees

A turance dokar ta ha'da da....
(a) be a body corporate with perpetual succession and a common seal;

(b) have power to sue and be sued in its corporate name;

(c) be capable of holding, purchasing, acquiring any property movable and immovable.

Ba k**ar Dokar Asusun Amincewar Tsaro ta Jiha da aka soke na 2018 ba, Dokar Asusun Amincewar Tsaro ta Jihar Kaduna ta 2024 za ta kasance ne da kamfanoni masu zaman kansu. Wakilan kamfanoni masu zaman kansu za su taka rawar gani wajen tafiyar da Asusun. Wakilan kamfanoni masu zaman kansu za su gudanar da Asusun tare da haɗin gwiwar sauran masu ruwa da tsaki a fannin tsaro. An kuma tsara sabuwar Dokar don dacewa da mafi kyawun ayyuka na duniya. Abin koyi ne ga sauran ƴan ƙasa.

Rattaba hannu kan wannan muhimmin kudiri, Gwamna Sani ya bayyana cewa, ya nuna karara na irin yadda gwamnatin jihar ta himmatu wajen cin karfin ‘yan ta’adda, ‘yan fashi, masu garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka da s**a addabi wasu al’umma a jihar Kaduna. Asusun Amincewar Tsaro zai baiwa Gwamnatin Jiha damar tallafawa hukumomin tsaro na kananan hukumomi da na tarayya da kayan aiki.

Bugu da ƙari, za a horar da jami'an tsaro da kuma horar da su don mayar da martani mai kyau ga barazanar tsaro da ke tasowa a halin yanzu.

DA DUMI-DUMI: Bayan nasiha da jan hankali, hukumar Hisbah a jihar Kano, ta k**a fitacciyar jarumar TikTok, Murja Ibrahim...
13/02/2024

DA DUMI-DUMI: Bayan nasiha da jan hankali, hukumar Hisbah a jihar Kano, ta k**a fitacciyar jarumar TikTok, Murja Ibrahim Kunya.

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Ramalan Yaro ya fice daga Jam'iyyar PDP zuwa APC a yau Litinin.
12/02/2024

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Ramalan Yaro ya fice daga Jam'iyyar PDP zuwa APC a yau Litinin.

ABIN KUNYA: An sake gano rumbunan kayan abinci da ƴan kasuwa s**a boye, domin su samu riba mai yawa, a Dawanau da ke jih...
12/02/2024

ABIN KUNYA: An sake gano rumbunan kayan abinci da ƴan kasuwa s**a boye, domin su samu riba mai yawa, a Dawanau da ke jihar Kano.

Allah kasa sauran jihohi suyi koyi da Gwamnatin Jihar Kano akan wannan ƙoƙari na saukakawa mutane rayuwa

Anje hutun rabin lokaci, Nigeria na cin Ivory Coast Nigeria 🇳🇬 1 🆚️ Ivory Coast 🇮🇪 0
11/02/2024

Anje hutun rabin lokaci, Nigeria na cin Ivory Coast

Nigeria 🇳🇬 1 🆚️ Ivory Coast 🇮🇪 0

Inna lillahi wa inna ilaihi raji'unAllah ya yi wa Jarumar Kannywood Fatima Sa'id, "Bintu" a cikin shirin Dadin Kowa rasu...
11/02/2024

Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un

Allah ya yi wa Jarumar Kannywood Fatima Sa'id, "Bintu" a cikin shirin Dadin Kowa rasuwa.

Rahotanni daga masana'antar sun ce jarumar ta rasu ne a yau Lahadi bayan ta sha fama da jinya.

Allah ya gafarta mata.

Taliya Leda ₦150Masara Kwano ₦250Shinkafa Kwano ₦500Fetir litter  200Insha Allah Cikin Kwanakin Nan Zasu Dawo Haka.
10/02/2024

Taliya Leda ₦150
Masara Kwano ₦250
Shinkafa Kwano ₦500
Fetir litter 200

Insha Allah Cikin Kwanakin Nan Zasu Dawo Haka.

DA DUMI-DUMI: Hukumar EFCC Naneman Matar Emefele Ruwa a jallo dawasu mutum uku.Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzik...
10/02/2024

DA DUMI-DUMI: Hukumar EFCC Naneman Matar Emefele Ruwa a jallo dawasu mutum uku.

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa a Nijeriya EFCC ta ce tana neman matar tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya Godwin Emefiele da wasu mutane uku ruwa a jallo.

DA DUMI-DUMINSA: Kotu ta bada umarnin kayaddade farashin  na'uikan wadanan kayayyaki, Madara da Fulawa da Gishiri da Suk...
09/02/2024

DA DUMI-DUMINSA: Kotu ta bada umarnin kayaddade farashin na'uikan wadanan kayayyaki, Madara da Fulawa da Gishiri da Sukari da Keke sai Ashana da Babur da Motoci da farashin Man fetir da Kananzir da sauransu nan da Mako daya.

Ban gudu don tsoron kamu ba - Dr. Idris Abdulaziz ya magantu bayan hukumar yan sanda ta fitar da sanarwar nemansa ruwa a...
09/02/2024

Ban gudu don tsoron kamu ba - Dr. Idris Abdulaziz ya magantu bayan hukumar yan sanda ta fitar da sanarwar nemansa ruwa a Jallo.

Malamin ya bayyana haka ne a cikin wani matsakaicin sauti mai mintuna 18, Sheikh Idris ya ce, ya bar jihar Bauchi ne saboda tsoron kar a zubar da jini a jihar. Domin babu kalar wahala ko cutarwa da bai gani ba a jihar Bauchi.

Tsohon Sarkin Kano Sunusi ll Shine Ya Fara Baiwa Buhari Shawarar A Rufe Boda, Tare Da A Cire Talalfin Mai - Ibrahim M Bu...
09/02/2024

Tsohon Sarkin Kano Sunusi ll Shine Ya Fara Baiwa Buhari Shawarar A Rufe Boda, Tare Da A Cire Talalfin Mai - Ibrahim M Buba

Rundunar ´yan sanda a jihar Bauchi. ta ce tana neman Malamin addinin Musulunci Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ruwa a ...
08/02/2024

Rundunar ´yan sanda a jihar Bauchi. ta ce tana neman Malamin addinin Musulunci Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ruwa a jallo.

Isah Lawal, Dan Shekaru 33, Dan Ta'adda ne dake zaune a kauyen Kaya, Karamar Hukumar Giwa, Jihar Kaduna. An k**ashi da s...
07/02/2024

Isah Lawal, Dan Shekaru 33, Dan Ta'adda ne dake zaune a kauyen Kaya, Karamar Hukumar Giwa, Jihar Kaduna. An k**ashi da shanu 55 da tumaki 6 a Garin Karaye, bayan ya baro Dajin Birnin Gwari da yunkurin kafa sansanin garkuwa da mutane a daji tsakanin Gwarzo da Karaye dake Jihar Kano.

Address

Rigasa
Kaduna

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kaduna oniine news posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share

Category